Showing 168001 words to 171000 words out of 241367 words

Chapter 57 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1607

take sosai ta kasa ce ma Safiyyah komai, tasan duk bayanin da zata mata bazata taSa fahimtar ta ba, Safiyyah ta ciro wayarta ta fara dannawa bata sake ce ma Khaleesat komai ba don da gaske ta Sata mata rai, after a while Khaleesat ta mike zata je ta wanke wake ta zuba a ruwan da to dora kan wuta, bayan ta gama wanke waken ta zuba ta rufe tukunyar tayi tagumi tana zaune gaban Coal pot din, a haka Umma ta shigo gidan ta sameta, Khaleesat ta sauke hannunta daga tagumin da tayi tana kallon Umma da ta nufota, tace "Umma kin dawo" Umma tace "Na dawo, ina Safiyyar?" Khaleesat tace "Tana ciki" Umma tace "Shi ne kika bar ta ita kadai" Khaleesat tace "Yanxu na fito in zuba wake ne" Aunty Farida ce ta shigo gidan da abubuwan da ta siyo a kasuwa, Umma tayi welcoming dinta sannan ta karasa dakinta ta shiga ciki da sallama, Safiyyah ta amsa tana mata sannu da zuwa, Umma ta cire Nikab da hijab dinta ta linke tace "Bata baki ko ruwa ba?" Safiyyah tayi murmushi tace "Umma ni ke nake jira ma tafiya zan yi" Umma ta zauna tana kallonta tace "To gani Safiyyah, lafiya dai ko?" Safiyyah tace "Lafiya lau Umma" Kafin Safiyyah ta ce komai Aunty Farida ta shigo dakin, Safiyyah ta gaisheta tana murmushi, Aunty Farida ta ajiye kayan hannunta tana amsa gaisuwan Safiyyah da fara'a, Umma dai kallon Safiyyah take tana jiran jin abinda zata ce, Babu bata lokaci Safiyyah ta fara yi ma Umma bayanin duk yanda suka yi da Housemate din Khaleesat, ita dai Aunty Farida na tsaye ita ma tana sauraron bayanin Safiyyah, Umma ta Wan yi murmushi bayan Safiyyah tayi shiru tace "Allah sarki, mun gode sosai da kulawan sa, amma dai ki maida masa kudinsa Safiyyah, don ko babanta ma bana jin zai yarda, Abdul ma da ya kai ta karatun ba mu da yanda muka iya ne Safiyyah, Allah ya amfana abinda ta samu" Safiyyah was speechless, Aunty Farida ta dinga kallon Umma jin abinda tace, can tace "Allah ya amfana abinda aka samu kuma Umma? Shikenan fa tayi asaran karatun gaba daya idan bata karasa ba, kamar ka fara gini ne fa ya ruguje har kasa ya rage Foundation, ai kin ga kuwa baza kace Allah amfana abinda aka samu ba" Umma ta kalli Aunty Farida tace "Farida kin fi kowa sanin ban taSa goyon bayan fitar Khaleesat karatu waje ba tun asali, daga ni har mahaifinta babu yanda muka iya ne, don haka Khaleesat bazata koma Amurka da sunan karasa karatu ba, ashe ma bamu dau darasin abinda ya faru a baya ba kenan" Aunty Farida bata sake ce ma Umma komai ba ta hau fiddo abubuwan da ta siyo a kasuwa, Ita ma Safiyyah tayi shiru don bata ma san me zata ce ba, Umma na kallon Safiyyah tace "Ki masa godiya kawai ki mayar masa da kudinsa Safiyyah, Allah ya dubi niyyarsa na alkhairi ya saka masa, ba wai ni kadai ba, hatta Mahaifinta ma ba yarda zai yi ba Safiyyah, cutar da ita da muka yi da farko ma da muna da wani dubaran da baza ayi haka ba, kin ga in mu iyayen arziki ne ai baza mu yarda ayi na biyu ba" Aunty Farida ta mike tace "To shi Umma ce maki yayi da wata manufa zai biya mata kudin karatun har kike tunanin za ayi na biyu? Shi fa Abdul duk abinda yayi yana da manufar yin hakan duk mun sani, ba haka kawai ya dauketa ya kai ta karatu ba...." Umma ta dakatar da ita tace "Ban ce shi wannan bawan Allahn yana da wata manufa ba amma dai kam Khaleesat bazata koma Amurka ba Farida" Aunty Farida bata sake tanka Umma ba ta fitar da albasan da ta siyo zata je ta shanya a bakin kofa, Safiyyah ta sauke boyayyen ajiyar zuciya a hankali tace "Toh shikenan Umma, ni zan koma gida, dama abinda ya kawo ni kenan" Umma tace "To ki gaida mutanen gidan Safiyyah mun gode kwarai, shi ma ki yi masa godiya don Allah" Safiyyah tace "To Umma" Jiki a sanyaye ta mike ta fita daga dakin, Aunty Farida ta dau hijab dinta da ta rataye a igiya tayi ma Safiyyah alamar su je waje, ita dai Khaleesat na zaune inda take bata tashi ba don duk taji conversation din Safiyyah da Ummanta, Aunty Farida na fita kofar gida da Safiyyah tace "Safiyyah kar ki yarda ki gaya masa abinda Umma ta ce, ki bari Babanta in ya dawo anjima zan samesa in yi masa magana" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya tace "To Aunty, don Allah ki yi convincing dinsa shi ma, It will be very sad idan aka ce bata karasa karatun nan ba, shekara daya fa kawai ya rage mana" Aunty Farida tace "In sha Allah zan yi bakin kokarina, kuma Khaleesat zata ci gaba da karatun ta" Safiyyah tace "To Aunty, gobe da safe zan kira ki sai inji yanda ku ka yi da Baba" Aunty Farida tace "To babu damuwa, ki gaida gida" a haka suka rabu Aunty Farida ta juya ta koma cikin gida... Khaleesat ta gama girkin da take bayan ta kashe gawayin tayi alwala ta shiga dakin Ummanta, tana idar da sallah ta kwanta, gaba daya taji damuwarta ya dawo sabo fil maganar Housemate dinta da Safiyyah ta kawo mata, Umma na kallonta tace "Baza ki ci abincin bane yanxu?" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "Sai anjima" Ita dai Aunty Farida linke kayan su Islam take don tun bayan tafiyar Safiyyah bata ce ma Umma komai kan maganar da Safiyyah ta kawo ba sanin Umma bazata taSa fahimta ba. Bayan Magrib Aunty Farida ta samu Malam Ali yana zaune kofar dakinsa, bayan sun gaisa yace "Amma ba Lagos kika zo gaya min zaki koma ba Farida?" Murmushi kawai Aunty Farida tayi don in akwai abinda ya tsana zamanta Lagos yayi fadan har ya gaji, ta kauda tambayar da yake mata tace "Magana na zo mu yi kan Khaleesat" Yayi shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace "To ina sauraron ki" Cikin nutsuwa Aunty Farida ta sanar masa batun da Safiyyah ta zo da shi daxu da rana, Malam Ali ya girgiza kai yace "Ashe ban daddara ba kenan Farida, na yi tunanin duk mun dau darasi kan abinda ya faru wanda duk nafi kowa laifi a ciki...." Aunty Farida ta kwantar da murya tace "Ae wancan issue din da wannan ba daya bane Malam, shi fa Abdul da isa da gadara ya turata karatu Amurka kuma babu yanda muka iya haka duk muka sallama masa domin zaman lafiyanmu da nak?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
a, Abdul da manufarsa na tura ta karatu, shi ko wannan bawan Allahn babu wata manufa a ransa, saboda Allah zai biya mata ta karasa karatun kar tayi asaran shekarun da tayi, iya shekara daya fa ya rage mata Malam, ka san muhimmancin karatun nan balle ka kushe komawarta America ta karasa, in kowa zai kalubalanci haka ai banda kai Malam, don Allah ka duba wannan lamari, kuma shi wannan bawan Allahn da ya ce zai dau nauyin shekara dayan da ya rage mata su ne fa suka dau maka lauya har aka wanke ka a kotu aka kashe maganar bashin ka da Baban Abdul...." Malam Ali yayi murmushi yace "Ai nayi appreciating hakan da suka min kuma kullum ina saka su a addu'ata, amma babu zancen komawar Jiddah America karatu Farida, kiyi hakuri a bar batun nan gaba dayanta, we shouldn't be a bad parent for the second time saboda son abun duniya, tayi hakuri in Allah ya hore min sai in biya mata tayi Jamb ta nemi ko BUK ko Northwest, duka duka shekarunta nawa suke? Ai lokaci bai kure mata na karatu ba Farida, kuma ko aro ne zan nema in biya mata in sha Allah, don haka bana son a sake tada zancen ci gaba da karatun ta a America" Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba, after a while tace "To shikenan, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi" Yace "Ameen" Mikewa tayi ta bar wajen rai babu dadi. Washegari wajen karfe tara Aunty Farida ta gama shirin da take, Umma dake kallonta tace "Ina za ki ne?" Aunty Farida na dora Nikab dinta kan Hijabin jikinta tace "Ba nace maki zan je gidan Abida ba shekaranjiya" Umma tace "Shi ne zaki mata sammako?" Aunty Farida tace "Jiya tace min bata da lafiya ne, kuma ina son in dawo da wuri in wanke kai na" Umma ta tabe baki tace "To sai kin dawo" Ita dai Khaleesat juya kokon gabanta take a hankali tana sha ga dumamen tuwo shi ma a gabanta, da kyar take shan kokon, dumamen kuwa ta kasa ci, dama jiya da daddare ma bata wani ci tuwon ba, Aunty Farida tayi ma Umma sallama ta fita daga dakin. Nenne na gyara daurin dankwalinta tayi kasa da murya tace "To ke banda abun ki ai Zahra'u Jahila ce Parida, matar da har yau bata da wayewa kanta a murfi yake kamar matar kauye, ita ta wani san maki muhimmancin karatu kina ganin mata haka kara zube, gashi sai yanda kazaman kishiyoyi suka yi da ita sun mayar da ita Bora? Ai bari ki ji Parida, Zahra'u a yanxu dai ita daga tuwo sai bautan Allah kawai ta saka a gaba, babu ruwanta da wani ci gaba na duniya ko kyale kyalin duniya, ta riga ta amince ta kare rayuwar ta a haka in dai zata ci tuwo tayi bautar Allah, shi yasa kullum zaki ganta rike da carbi a kuturin dakinta da ko Ceiling din arziki babu, ni bana ma jin Zahra'u na yi ma Ali addu'an Allah ya dawo masa da arzikinsa don in tayi hakan gani zata yi kamar ta butulce ma Allah, duk tunaninta fa haka Allah ya so ganinsu cikin ba?in talauci, gani zata yi in tayi ta ma Allah magiyan ya yaye masu talauci kamar butulci tayi bata gode da ni'imarsa ba tunda tana samun tuwo ta ci, to irin tunanin yayarki kenan Parida, in ba haka ba ta yaya zaki dinga yi ma er cikinki bakin cikin karasa karatu ta taimake ku a rayuwa ta cire ku daga kangin talauci? shikenan kuma don kai jahili ne sai ka rasa sanin abinda ya kamata? Har wani kwambo fa take da jahilcin ta da rashin wayewa, ki bar ni da su kawai zan yi maganinsu daga Alin har Zahra'un, da can uban me yasa suka bari aka kai ta Amurkan in har da tsoron Allah a lamarinsu daga ita har Alin? Wato sai yanxu suka zama iyayen kirki masu tsoron Allah ko? To zan yi maganinsu gaba daya, in dai karatu ne kamar Khaleesah taje Amurka ta karasa in har ina numfashi, Allah ya kai mu anjima da yamma, Alin ai zai dawo daga zaman kashe wandon da yake yi a kasuwa, zan je har gidan in samesa inji ko na tauye masa karatunsa duk da talauci na, in de ni na amince taje to ko wani Wan iska ma kar ya amince" Nenne na kai wa nan ta mike ta jawo kofar dakinta ta kulle da kwado, sannan ta dau mayafinta sabo dake rataye saman igiya ta yafa, ta dau handbag dinta ta saka makullin kofar a ciki, ta zura takalmanta ta nufi kofar fita daga gidan tana taku dai dai don sabuwar atamfa ce a jikinta, Aunty Farida ta bi ta da kallon mamaki tace "Wai fita zaki yi ne Nenne?" Ba tare da Nenne ta juyo ba tace "To me zan maki, anguwa har uku zan je yau da kika gan ni, bazan zauna a banza ki bata min lokaci ba, in ba gulma ba ganinki nake yi a gidana, ni dai in kin gama zaman kin fito ki ja min kyauren gidana kar almajirai su shiga su min sata" Daga haka Nenne ta fice daga gidan, murmushi Aunty Farida tayi ta mike ta nannade mata tabarmanta ta ajiye sannan ta daura nikab dinta, bin bayanta tayi da sauri don jadadda mata kar tace ita ta zo ta gaya mata maganar don tasan tsaf sai yayarta ta kullace ta.
[6/30, 6:59 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Wajen karfe shidda na yamma Khaleesat na zaune bakin kofar dakin Ummanta tana yanka mata alaiyahu a cikin roba, stepsisters dinta Labeebah da Lamisah na can zaune su ma daga bakin kofar dakin Mama Shatu da kawayensu sai hira suke suna shewa duk sun cika tsakar gidan kai kace gidan biki ne, Mama Shatu da Mama Zubaida su ma suna tsakar gidan don da su ake hiran da kawayen 'ya yan nasu, magana daya biyu sai su kwashe da dariya, yawanci kuma duk habaici suke jefa ma Umma da Khaleesat, ita dai Umma tana zaune gaban Coal pot tana kwashe tuwon masara da ta gama tukawa, Aunty Farida kuma ta tafi Hotoro tun bayan la'asar da su Noor, Nenne ce ta shigo gidan rataye da jakarta a kafada, lkci daya gidan yayi tsit, a takaice Nenne ta amsa gaisuwan da su Mama Zubaida da Lamisah da kawayensu ke yi mata ta nufi gun Umma tace "Zahra'u Alin ya dawo ko be dawo ba?" Umma ta gaida Nenne sannan tace "A'a bai dawo ba tukun Nenne, sannu da zuwa" Nenne tace "Kin gan ni nan daga Sheka nake daga can na tafi ?an Agundi, ni ce har Na'ibawa yau, tun safe na bar gida sai yanxu nake dawowa 'yan adaidaita sahun kano dai sauransu yawo da bindiga kawai...." Murmushi kawai Umma tayi tana ci gaba da kwashe tuwon da take yi, Nenne ta jawo kujera ta zauna tace "Gidan Katime me Aya na tafi a Sheka, in gaya maki me Aya dai kafafuwanta sun mutu murus Zahra'u, ko tashi bata iya yi, babu yanda ban yi da matar nan ta rage cin nama ba amma taga kamar bakin ciki nake mata don mijina baya kawo min, to yau ni da ban ci nama ba gani da kafafuwana biyu rass, ita kuwa duk sun mutu, wai tana ganina ina taku dai dai na shigo gidan sai ta fashe da kuka, ni dai bata ban tausayi ba wallahi, sai kinga yanda take mana fafa da nama lokacin, kullum kya ji kamshin tafashen nama a gidanta, mu sai dai mu watsa er daddawa a miya" Umma na girgiza kai tace "To Allah Ubangiji ya bata lafiya" Nenne tace "Ba batun Allah ya bata lafiya ba, ai duk kafafuwan sun rube, da kyar in baza ace za a yanke mata su ba tunda ko motsa su bata iya yi " Su Mama Zubaida gaba daya kunnuwansa na kan labarin da Nenne ke ba Umma, Malam Ali ne ya shigo gidan da sallama, Nenne ta juya tana kallonsa, can ta mike ta nufesa tace "Yanxu Ali baza ka hakura da fita kasuwar nan ba tun da ba wani abu kake yi a can ba sai zama cikin rana da iska? Ka dubi yanda duk kayi bakikirin kamar baka taSa haske ba a rayuwarka Ali, tunda ba aikin fari gareka ba balle ba?i a kasuwar ka hakura da zuwa mana" Gaisheta kawai yayi ya dau buta zai debi ruwa ya fita waje ya zauna ya jira Magariba, Nenne ta tabe baki tace "To wajen kai da matar ka Zahra'u na xo" Umma ta juya tana kallon Nenne jin abinda tace, Shi ma ya tsaya yace "To lafiya dai ko?" Nenne tace "A ina lafiyar take, ba sai kun nemi zaman lafiyar za a zauna lafiya ba, labari na samu wai masu kare hakkin 'yan Adam sun zo gidan nan sun ce za su ci gaba da daukar nauyin karatun Khaleesat a Amurka saboda tausayin abinda tsinannen mutumin nan Awdul yayi mata, to amma wai saboda kai da Zahra'u yan bakin ciki ne sai ku ka gwalesu ku ka koresu, da wanne ku ke son yarinyar ta ji fisabilillahi? Da mayar da ita bazawara da aka yi tana da karancin shekaru ko kuma da asaran karatun ta da kuke kokarin yi mata? In ita Zahra'u jahila ce bata yi karatun boko ba kai ma Jahili ne Ali? Ina ne ban shiga nayi aikatau ba don kayi karatu? To wallahi ko karshen bangon duniya ne sai Khaleesat ta koma ta karasa karatun ta tunda har aka ce za a dau nauyinta babu ko sisin ku, to ina ma ku ka ga ko sisin" Malam Ali dake ta kallon uwar tasa yace "A ina kika ji wannan zancen Nenne?" Nenne tace "Labarin duniya na buya ne dama? Ina zaune yan Mariri suka zo suka tsegunta min har unguwan da naje yau...." Mama Shatu ta kalli Mama Zubaida da ta saki baki tana sauraron Nenne, Mama Zubaida ta kasa daurewa ta gyara zama cikin kwantar da murya tace "Amma Nenne na farkon ma ba a wanye lafiya ba shi ne za a sake na biyu? Dama gashi duk garin nan kallon makwaita masu son abun duniya kawai ake mana, ko ina sai zaginmu ake tun da aka samu labarin sakin walakancin da aka yi ma Khaleesat, ana ta cewa ubanta ne ya ja mata, A rayuwar nan yanxu fa in ba iyayenka ne za su yi maka dawainiya ba duk wanda yace zai dau dawainiyar ka sama ta ka to da wani abu da yake hangen zai samu a gare ka ne, Khaleesat fa 'ya mace take ba namiji ba Nenne, kuma ba komai ke rudar maza akanta ba sai kyanta da kalan fatar ta sun ga buzuwa, shi kenan saboda son abun duniya sai a zuba ido har sai yarinyar nan ta lalace tukunna, Abdul ya gama nasa ya samu abinda yake so ya sako mana ita sai kuma yanxu ace ga wani ma ya zo wai zai ci gaba da daukar nauyinta? Haba sam batun nan babu tsari a cikinta, shikenan ita kuma haka ta zama kamar Tasi...." Nenne ta kundumo wani zagi tace "Toh duk wanda ya fasa fadin abinda ke ransa akan Khaleesah Allah ya tsine masa albarka, kuma in de

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login