Showing 18001 words to 21000 words out of 241367 words

Chapter 7 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1589

ki dauraye masu Uniform dinsu, dakin ma na nan sunyi kaca kaca da shi babu kyan gani" Daga haka ta fice daga cikin gidan bayan ta saka slippers dinta, Khaleesat ta cire mayafin abayan jikinta ta dora kan akwatinta sannan ta ci gaba da tankaden da Baaba Gaje ta bar mata, Baaba Gaje makociyarsu ce a can unguwansu Mariri kafin 'ya yanta su siya mata wani Wan kararramin gida a nan Hotoro Tsamiyar boka ta dawo tana zaune da jikokinta biyar tana dubasu, zaman mutunci da amana Baaba Gaje suka yi da Mahaifiyar Khaleesat da ta dauki Gajen tamkar uwa. Wajen karfe shidda saura Khaleesat ta gama duk aikin da Gaje ta loda mata sannan ta dora ruwan da zata yi wanka a sauran rushi, zaunawa tayi kan tabarma ta jingina da bango don ta gaji likis, Housemate dinta ne ya fado mata, ta dai yi shiru staring into space, after a while ta sauke idonta a hankali ta mike ta shiga da kwanukan da ta wanke cikin dakin Gaje, dai dai nan Gaje ta shigo cikin gidan da Aunty Farida, Khaleesat ta tafi da gudu ta rungume Aunty Farida cike da murnan ganinta, Aunty Farida na kallonta tace "Ke kuma da wa kika yi shawara kika biyo hanya Khaleesah? Abdul din ne yace ki taho?" Gaje ta daga hannu sama da sauri tace "Aaaa tace bai ma sani ba" Aunty Farida na kallon Khaleesat da mamaki tace "Ban gane bai sani ba??" Khaleesat ta marairaice ta k??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????auda zancen ta hanyar cewa "Aunty ya jikin Ummanmu?" Aunty Farida ta kamo hannunta suka zauna saman tabarma tace "Ai jikin Umma da sauki sosai Khaleesat, gashi har an sallamemu a asibiti, wa yace maki bata da lafiya ne ma tukun?" Khaleesat da har hawaye ya ciko idonta tace "Aunty Sha'awa" Gaje tace "Lahh ha ila, wato Sha'awa bazata dena munafurci ba ko? Wato bazata canxa hali ba ko? Da kaina fa sai da na jaddada mata kar ta gaya maki ko kin mata sako ta wassol don kar hankalinki ya tashi, ashe sai da munafukar ta zaga ta fada maki" Aunty Farida tace "Toh Allah ya kyauta, kwata kwata Sha'awa bazata canza ba" Khaleesat da hawaye ke cika idonta tace "To Aunty ta yaya zan ga Ummanmu yanzu?" Aunty Farida tace "Kar ki damu kiyi zaman ki nan wajen Baaba Gaje, gobe da safe in za mu tafi asibiti sai mu fara biyowa ta nan da Umman tunda asibitin Malam Aminu kano ne" A hankali Khaleesat tace "Toh Allah ya kai mu Aunty" Sai bayan Magrib Aunty Farida ta bar gidan bayan ta ci tuwon da Khaleesat tayi ma Gaje, sosai Khaleesat taji ta samu rest of mind bayan taji jikin Ummanta da sauki, bayan Isha Gaje ta gyara mata Wan lungun da zata kwanta a dakin ta daura mata net din sauro tace "Allah dai ya rabaki da cinnaku" ita dai Khaleesat tayi murmushi kawai bata ce komai ba, ita matsalarta ma zafi, ko ya zata yi da zafi yau gashi karamin dakin wani Wan mitsitsin window ne kawai ke garesa, su bakwai kuma zasu kwana a ciki, Khaleesat ta gama shirin kwanciya don tayi wanka sannan ta shiga net din ta kwanta, ta amshi maficin da gaje ke mika mata ta cikin net din, tun dawowarta sai a sannan tayi subscription ta shiga WhatsApp dinta, Message din Safiyyah dake tambayarta ko ta isa lafiya kadai tayi ma reply, bata yi mamakin rashin ganin message din Abdul ba don she isn't even expecting his message, ajiye wayar tayi ta gyara kwanciyarta ta lumshe ido, Housemate dinta ne ya fado mata, she have no access to him balle ko godiya ma tayi masa, bata yi tunanin da ta fito zata tafi airport bazai tambayeta phone number dinta ba, ko Airport din ma bata yi tunanin bazai yi offering yace zai kai ta ba, juye juye kawai take yi a net din idonta a rufe, after a while of thinking bacci ya dauketa. Washegari Khaleesat ta gama yi ma Baaba Gaje duk aikace aikacen gidan, ta hura gawayi ta daura ruwa tayi ma kananun jikokinta wanka sannan ta dama kunu, Baaba Gaje ta fita siyo masu kosai a titi, har karfe goma Khaleesat bata ga Aunty Farida sun zo gidan da Ummanta ba, gaba daya ta damu taga Ummanta, Baaba Gaje tace "To ke sai ruwan ya salance zaki je kiyi wankan? Ba fa wani gawayin" Khaleesat tace "Zan yi" Daga haka ta mike ta tafi yin wankan, tana fitowa daga wanka taga takalmin da Aunty Farida ta zo da shi jiya a bakin kofa da wani takalmin daban wanda ko ba a fada ba tasan na Ummanta ne, da sauri ta shiga dakin Baaba Gaje taga Ummanta da Aunty Farida a zaune, tsallake Aunty Farida tayi ta tafi gun Ummanta da gudu cike da farin cikin ganinta ta durkusa gabanta ta rungumeta, Aunty Farida tace "Ko dai baki da hankali ne?" Baaba Gaje tace "Toh da sauki dai kam" Ita dai Umman sai kallon Khaleesat take, gaba daya Khaleesat ta ma mance wai Umma bata da lafiya tsabar farin cikin ganinta, a hankali Umma tace "Meyasa zaki biyo hanya Khaleesah? Abdul din ne yace ki dawo?" Khaleesat ta kamo hannunta cike da damuwa tace "Umma ya jikin?" Umma tace "Naji sauki Alhamdulillah" Khaleesat tace "Aunty Sha'awa tace min ko magana fa baki yi" Baaba Gaje ta rike haSa tace "Oh ni 'ya su, kun ji er iska ko? Wallahi Sha'awa da kyar taga annabi, babu yanda bamu yi da ita ko da wasa kar ta gaya maki ba ashe sai da ta zaga ta fada, har ce mata nayi tace maki tayi tafiya ko da zaki buga nata wassol" Khaleesat ta daga kai ta kalli Baaba Gaje tace "Ni ce na kirata don ina ta magana bata min reply ba" Aunty Farida tace "Ai tsabar munafurci yasa ta gaya maki ba wani abu ba" Khaleesat ta Wan yi murmushi ta gaida Aunty Farida, Aunty Farida ta amsa tace "Amma shi Abdul yasan Umma bata da lafiya shine ko kira ya dubata bai yi ba?" Khaleesat ta sauke idonta kasa tace "Ni fa bai san na dawo ba Aunty" Aunty Farida tace "Wai ban gane bai san kin dawo ba, wa ya biya maki kudin jirgin?" Khaleesat ta daga manyan idanuwanta tana kallonsu, Sai kuma a hankali tace "Wani ne ya biya min ba Abdul ba" Umma ta kalleta da sauri tace "Wani?" Da mamaki Aunty Farida tace "Wani a ina?" Khaleesat na kokarin mikewa tace "Neighbor dina ne" Umma ta bude baki tana kallonta, sai kuma tace "Ko baki da hankali ne, waye ya biya maki kudin jirgi Khaleesah?" Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Gaje tace "Bude baki zaki yi ki mana bayani dalla dalla, waye shi zai biya maki zunzurutun kudi na jirgin da naji ance ya fi miliyan daya? A ina kika san sa?" Still dai Khaleesat taki cewa komai, Aunty Farida tace "Ke bana son rainin wayo uban wa zaki ma shiru ana maki magana? Ko baki ji tambayar da ake maki bane?" Umma dai kallon Khaleesat kawai take da mamaki, Khaleesat ta koma baya ta Wan sunkuyar da kanta a hankali tace "Ni fa nace makocina ne ya biya min, kuma ai gani yayi ina ta kuka Ummana bata da lafiya shine ya biya min jirgi in dawo in dubota" Cikin sanyin murya ta kare maganar, Baaba Gaje tace "Atoh dama ai ko ina ana samun na Allah, Allah ya masa albarka, Bature ne ko?" A takaice Khaleesat tace "Um" don bata son ma a ci gaba da zancen, Baaba Gaje tace "Ko da naji, ai sai baturen dama, wani ba?in fata ne zai biya maki jirgi don yana makocinki, ai ko mutuwa uwar taki tayi iyaka ya maki gaisuwa ya kama gabansa, to Allah ya saka masa da alkhairi, abinda ma baturen kudin jirgin ba wani kudi bane a wajensa, ji zai yi kamar naira dubu goma ya kashe fa" Khaleesat na kallon Aunty Farida tace "Aunty yanzu za aje asibitin ne?" Aunty Farida tace "Aa mu har mun dawo daga asibiti sai kuma na gobe in Allah ya kai mu" a hankali Umma tace "Toh da ya biya maki kudin jirgin zuwa wa zai maki na komawa yanzu? Kinsan dai ko hauka kike baza ki bari Abdul yaji wannan batun ba ki ja mana masifa ko?" Sai da gaban Khaleesat ya fadi, a hankali ta sunkuyar da kanta, ita gaba daya ta ma mance ashe biyan jirgi za ayi a koma, nan da nan jikinta yayi mugun sanyi, yanzu ina zata samu kudin ticket din komawa, she became so weak at once, Aunty Farida tace "Toh shi Abdul din baki ce masa Umma bata da lafiya bane?" Khaleesat da har sannan jikinta yake a sanyaye ta girgiza kai tace "Baya nan ne" Daga haka ta mike ta tafi zata shirya don zanin da tayi wanka ne daure jikinta har a lkcn, Khaleesat na cikin saka kayanta da ta fiddo a akwati 1000 dollar din da Housemate dinta ya bata suka fado mata a rai, ta zaro ido lkci daya taji hankalinta ya kwanta har sai da ta sauke ajiyar zuciya, tasan probably in ta canza har da 100 dollar din da Safiyyah ta bata kudaden za su iya maidata Amurka, she felt so relieved, nan da nan walwalarta ya dawo, tana jin Baaba Gaje na tambayar Aunty Farida ko kishiyoyin Ummanta sun shiga dubata yau, Aunty Farida tace "Jiya ma basu shigo dubata ba sai yau Baaba Gaje" Baaba Gaje tace "Shegu matsiyata, so fa suka yi ace ta mutu, to shi Malam Alin ya ku ka ?arke da shi? Ya bada kudin?" Aunty Farida tace "Aa ni fa ban bi ta kansa ba Baaba Gaje, dama me ya tsinana kafin in zo kanon? daxu ma aka turo min sauran kudin adashina da nake jira, duk na siya sauran magungunan" Baaba Gaje tace "Atoh dai bai taSuka komai ba a takaice, shi ma da zaki basa yanxu tsaf zai amshe" Har aka yi azahar su Umma da Aunty Farida na gidan, Umma har tayi bacci ta tashi saboda maganin da take sha, har a sannan da kyar take taka kafarta daya, hannunta dai ya sake ya dawo normal tun a jiya, Khaleesat ta shigo dakin da shinkafa da waken da ta dafa, Baaba Gaje kuma ta shiga makota dubiya, Aunty Farida dai sai bin Khaleesat take da kallo, sosai taga ta kara kyau tayi fresh, duk da dai tana nan a yanda take babu kiba, komawa tsakar gida Khaleesat tayi ta dauko man gyadan da ta soya ta dawo dakin, ta fara zuba ma Umma da Aunty Farida abincin, Umma dake zaune kan darduma tana kallonta tace "Kun fara jarabawan ne?" Aunty Farida tace "Haba dai sun fara jarabawa zata taho? Ai bazai yiwu ba, ko ana haka ne?" Khaleesat dake sauraronsu ta girgiza kai tana Wan murmushi tace "Da sauran lokaci bamu fara ba tukun" Aunty Farida tace "To yanzu dai tun kan wani munafukin yasan kina garin nan mu shiga uku yaushe za ki koma Khaleesah?" Khaleesat ta daga kai a hankali tace "Cikin satin nan in sha Allah" Aunty Farida tace "Toh inji dai Abdul din ya rage abubuwan nan nasa da yake maki?" Khaleesat ta ajiye masu abincin a gabansu kamar bazata ce komai ba sai kuma tace "Babu abinda ya fasa, ni na gaji da halinsa ma yanzu" Umma ta daga kai tana kallonta, Aunty Farida ma kallonta take don bata taSa cewa ta gaji da halin Abdul ba, Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya ta fara cin abincin gabanta tace "Na dai gaya maki babu me canza maki shi sai ke da kanki, ke macece ya kamata ace zuwa yanzu kinsan wanene Abdul kinsan kuma yanda zaki zauna da shi" Mikewa Khaleesat tayi without saying anything don ita yanzu taji ko zancen nasa ma bata so har cikin ranta, tun shekaranjiya da yayi fushi har yau bai kirata ba ita kuma as far as tayi masa miss calls har biyu to bata ji zata iya sake kiransa ba unlike before da ta dinga kiransa kenan ko da bazai daga ba, ko kuma tayi ta masa magana ta WhatsApp, to yanzu kam bata ji zata iya ba.....


07087865788
'
*Still on free pages*
[5/4, 8:14 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: ('('HALYSAAH('('





By _Khaleesat Haiydar_
'




7.....

Kwanan Khaleesat hudu yau a garin kano, kuma har a sannan babu wanda yasan da zuwanta a cikin yan gidansu, ko nan da can bata fita a gidan Baaba Gaje don ma kar tsautsayi ya sa ta hadu da daya daga cikin yan gidan nasu, a kwanaki hudun nan sau biyu Ummanta da Aunty Farida suka zo gidan Baaba Gaje dominta, zuwa sannan Umma ta warware gaba daya tafiyarta ya dawo normal, tun kwanaki biyu da suka wuce ta gama amsan treatment dinta a hospital sai magunguna da take sha kawai, har zuwa ranan kuma Abdul bai kira Khaleesat ba, ita kuwa kawai taji ko a jikinta da ya kira da kar ya kira, there wasn't an atom of disturbance a tattare da ita, ko ta WhatsApp bata yi gigin yi masa magana ba Unlike before da bazata iya hakuri ba sai ta masa, tana bakin murhu tana dafa shinkafa da wake ga turmi gabanta tana Waka yajin da za ayi amfani da shi wajen cin shinkafa da waken, Su Ummanta da Baaba Gaje kuma na can uwar Waka, tunanin yanda zata fara shirye shiryen komawa USA take don suna da wani presentation nan da kwana uku, daxu da safe ta duba available flight da farashinsu online and she is hoping in ta canza dollars din da Housemate dinta ya bata zai isheta ta koma, Khaleesat ta bar da?an yajin da take yi bayan taji Aunty Farida na kwalo mata kira, mikewa tayi ta wuce dakin tana amsawa, tun da ta zo gidan Baaba Gaje ta sakar mata aikin komai, hatta jikokinta ita ke masu wanka kan su tafi makaranta, ita taga kamar har ta Wan yi duhu tsabar girki cikin rana da take yi tun zuwanta, Aunty Farida tace "Ana kiran wayarki" nan da nan mood din Khaleesat ya canza ta karasa gun wayar without much interest, duk tunaninta Abdul ne cause she isn't expecting any call from anybody, Number mutumin da ya tarbeta a Airport din Lagos ta gani a gaban Screen din wayarta, ta dinga kallon number bata ko kiftawa, duk da bata yi saving ba amma ta gane nasa ne, daukar wayar tayi ta fita daga dakin ta koma bakin murhun sannan tayi picking ta kai kunne, sallama yayi ya gaisheta da ladabi, tace "Ina yini?" Yace "Alhamdulillahi Hajiya, ya jama'ar gidan?" Tace "Alhamdulillah" Yace "To maa sha Allah, dama na bugo ne inji ko zaki kara kwanaki nawa nan gaba kan ki koma America?" Khaleesat tayi shiru trying to understand why he is asking her that, yace "Hello?" Tace "Ina jin ka, ban gane tambayar bane" Calmly yace "Aa so nake in san ranan da zaki koma ne Hajiya, in ya kama ayi rescheduling din ticket dinki sai ayi hakan in sha Allah" Khaleesat was speechless, a ranta tace Ticket kuma? Kasa cewa komai tayi with surprise, taji ta ma kasa ci gaba da tsayuwa, jin ya sake cewa "Hello" ta kifta ido da kyar ta duka kusa da turmin da take daka yaji tace "Ina ji" Yace "Ina ga a bari duk sanda kika shirya zaki nemeni ta waya ko Hajiya?" Sauke idonta tayi kasa, lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, cikin sanyayyen murya tace "Ranan Lahadi nake son zan koma idan Allah ya yarda" Yace "To Maa sha Allah, dama booking din ranan aka maki da zaki taho, flight din karfe daya ne, za ku tashi ta Airport din Abuja in sha Allah" Ita dai Khaleesat ta kasa cewa komai, yace "Sai kin ji ni in sha Allah Hajiya" A hankali Khaleesat tace "Nagode" Khaleesat na zaune dakin Baaba Gaje tana jujjuya shinkafa da waken dake gabanta da cokali, gaba daya ta kasa cin abincin, ita kanta ta rasa dalili, ko tsabar yanda jikinta yayi sanyi ne tun bayan da suka yi waya da mutumin daxu da ya sanar mata da ticket dinta na komawa America sannan tana gama aikin da take ta bude WhatsApp taga ya aiko mata da Flight Ticket dinta which was also business Class kamar dai yanda ta zo, this made her so weak, gaba daya ta ma rasa gane feeling din dake ranta a lokacin, bata taba tunanin Housemate din nata zai mata ticket din komawa ba, Duk Ummanta na lura da sauyawanta lkci guda, Aunty Farida ta gama shafa powder din da take zata leka gidan wata kawarta Maman Fu'ad a nan hotoron, ta dau jakarta da mayafi tana kallon yayarta tace "To sai na dawo Umma" Umma tace "Amma kar ki dade don Allah Farida" Aunty Farida tace "Haba ai yamma tayi bazan zauna ba Umma" Daga haka ta fita daga dakin tayi ma Baaba Gaje dake waje tare da bakuwarta sallama sannan ta fita daga gidan, Umma ta daga kai tana kallon Khaleesat tace "Menene kika saka abinci a gaba kika kasa ci Khaleesat?" Khaleesat ta daga kai da sauri tana kallon kyakkyawan fuskar Ummanta, babu wanda zai ce Umma ce ta haifeta sai dai ma yayi tunanin yayarta ce don kama suke ba na wasa ba kamar an tsaga ?ara, Khaleesat tayi murmushin yake ta kai shinkafa da waken baki tace "Babu komai fa Umma" Umma tace "Yaushe za ki koma? Kuma yaya za ayi da batun kudin jirgi? Har yanzu Abdul din bai san kina nan ba?" Khaleesat ta girgiza kai tace "Umma ai nace baya nan kuma ba a samunsa ta waya, ranan lahadi zan koma in sha Allah" Umma tace "Ranan Lahadi? To ina za ki samu kudin komawa?" Khaleesat ta gyara zamanta tace "Makocin nawa ai tare ya biya min na zuwa da dawowa" Kallonta Umma ta dinga yi da alamar tuhuma ga mamaki kwance fuskarta, Khaleesat taki yarda ta bari su hada ido sai tura abincin gabanta take, Umma tace "Khaleesah"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login