Showing 225001 words to 228000 words out of 241367 words

Chapter 76 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1568

martaba ya kalli Ajay yace "Ita ce yarinyar da za aje gidansu kenan..." Ajay ya Waga kai yana kallon Abban nasa, can ya Wan sosa kai yana murmushin karfin hali yace "Abba ai budurwar Jawwad ce, wajensa ta zo ba wajena ba" Mai martaba ya kalli Jay da bai dago kai ba, Can Abba yace "Budurwar Jawwad kuma na gan ku zaune tare a parlor" Ajay ya gyara zama yace "Ranka shi dade abinda na fada gaskiya ne, ba wajena ta zo ba wajensa ta zo" Mai martaba ya kalli Jay, cikin nutsuwa yace "Jawwad" Jay ya dago kai amma ya kasa hada ido da mai martaba, jin mai martaba yayi shiru yasan bayani yake jiran ji daga garesa, hakan yasa ya fara magana with calm yace "Gaskiya ya fada Abba, haka ne..." Mai martaba yayi shiru na kusan minti daya kafin yace "Ita Hadiyar fa?" Jay ya kasa cewa komai, Mai martaba sam bai yarda da abinda suka ce masa ba don gani yake kamar Jay is covering for Ajay, after some minutes cikin hikima Mai martaba yace "Ko hakan yasa kake ta jan maganar Hadiyah?" Jay ya gyada masa kai still not looking at him, Mai martaba ya numfasa speaking with calmness yace "So ta yaya zan yarda da ku yanxu? Don na fara kokonton ka yanxu Jawwad, a da dai baka min karya amma yanxu ka fara" Jay yayi karfin halin cewa "Allah ya taimake ka, believe me ba karya nayi maka ba" Mai martaba yace "Ai shi ne nake tambayarka ta yaya zan yarda da hakan? Yanxu nema maka auren yarinyar zan sa ayi idan na koma Nigeria so i can clear away my doubt?" Jay ya daga idanuwansa ya kallesa, a hankali yace "Da zan yi farin ciki da hakan ranka shi dade" Mai martaba yace "To batun Hadiyah fa?" Jay ya rasa abinda zai ce, after few seconds yace "I will be glad idan aka amince min na janye daga batun auren Hadiyah" Mai martaba ya Wan yi murmushi yace "Ai bazan maka dole ba Jawwad, ya rage naka kayi ma iyayenka mata bayani su bar maganar Hadiyah tunda kana da yarinyar da kake so da aure, don wa?a a bakin me ita tafi dadi, in kuma kaga zaka hadasu su biyun it's fine, as far as zaka yi adalci... By so doing iyayenka mata baza su dau lamarin da zafi ba tunda duk sun saka ran auren ka da Hadiyah" A hankali Jay yace "But i am afraid za su yi shunning batun idan na kai masu ranka shi dade" Mai martaba yace "Not when i am alive Jawwad, duk abinda kake so shi zan maka in sha Allah" A hankali Jay yace "Allah ya kara girma ranka shi dade...." Mai martaba ya kalli Ajay yace "Kai kuma ina sauraron ka har yanzu" Mikewa Mai martaba yayi ya bar parlon, bayan tafiyarsa suna ta zaune kamar wa enda aka yi planting a wajen sai dai ko wannensu akwai abinda yake tunani a ransa, Ajay ya Wan kalli Jay sai kuma yayi breaking silence din yace "Allah ya sanya alkhairi me mata biyu" Jay ya wani kallesa, Mikewa Ajay yayi zai bar wajen Jay ya sa masa kafa sai gashi timmm ya fada kan kujera, juyowa yayi ya hade rai yana kallon Jay da ya fara dariya, yaushe rabon su zauna waje daya a gidan, har magana ma sama s???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ama suke yi... Jay ya dakata da dariyan da yake, sai kuma yayi kasa da murya yace "So what did you think about all this?" Ajay yace "About what?" Jay ya juya ya kallesa bai ce komai ba, Ajay yace "Getting married to ur Ward?" Jay dai kallonsa kawai yake, Ajay ya Wan yi murmushi yace "All this while ka zata wataran zan so ta ne da kake creating attitude a gidan nan? Saboda me ma zan so ta? Dama shi son haka yake very cheap? Ai ba class dita bace yarinyar nan, i like nothing about her most especially her silly cry, duk abinda nake mata saboda kai nake mata, if not because you bazan taSa saninta from anywhere ba, ba ma abinda zai sa nayi crossing path da ita, so chill bruh.... Just that har na fara hango maka challenges din da zaka yi facing a wannan familyn naka, considering the fact that ta taSa aure, sannan she is a nobody, familynka kuwa basa son someone that is a nobody not to talk of bazawara, kaga you have to tighten up ur belt kayi facing all the up and downs that will approach you.... Wishing you the very best of luck" Yana kai wa nan ya mike ya nufi dakinsa, Jay dai ya bi sa da kallo, sai kuma Ajay ya tsaya sannan ya juya yace "In addition, tsohon mijinta na bibiyanta yanxu haka, that was why she was here earlier on" Daga haka Ajay yayi tafiyarsa Bedroom dinsa ya bar Jay da ya mike tsaye jin abinda Ajay yace. Ajay na shiga dakinsa ya tafi jikin window ya tsaya yana kallon Neighborhood dinsu, everywhere was so silent and calm as usual, sai kuma ya sauke idonsa ya juya ya tafi ya dau wayarsa ya koma jikin windon ya tsaya, number Khaleesat yayi dialing, yana fara ringing tayi picking, yace "Where are you?" Khaleesat dake cikin Lyft tace "Ina cikin mota" Yace "Za ki ina?" Kallon wayarta tayi jin shigowar kira taga Jay ne ke kiranta, ta maida wayar kunne a hankali tace "Gidansu Safiyyah zan je" Yace "Ohk, remain there idan kin je, do not go back to ur apartment...." Yana kai wa nan ya katse wayarsa, Khaleesat tayi picking call din Jay don bai katse ba har sannan yace "Kina ina Halysaah?" Tace "Ina hanya" Yace "Kar ki koma apartment din ki, wait for me somewhere, i will be on my way now" A hankali tace "Dama gidansu Safiyyah zan je" Yace "Ohk to ki je, zan same ki a can" Tace "To Nagode" Katse wayar tayi ta mayar cikin jakanta, wai yau ita ce zata kai kanta gidansu Safiyyah yau saboda rashin choice, to ya zata yi, ko zaginta Surayyah tayi ai sai dai kawai ta bata hakuri in dai zata barta ta zauna a gidan, a haka ta isa gidan, bayan ta sauka Lyft ta nufi kofar apartment din ta danna bell......


*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*

07087865788



=???? HADJIBS DATA SERVICES

Barkan ku da zuwa HADJIBS DATA SERVICES
Wannan wuri ne da muke:

=??? Siyar da data (MTN, Airtel, Glo, 9mobile)
=??? Siyar da airtime cikin sauki (VTU)
=??? Biya kudin DSTV, GoTV, Startimes
=??? Biya wutar lantarki (NEPA/PHCN)
=??? Siyar da WAEC Scratch Cards
=??? Reseller Wallet System  zaka iya siyarwa da riba
=??? Dama ga masu so su fara sana'a a wayarsu

Kawai zaku bude account dinku ku fara sana'ar ku cikin sauki.

=ر?? Shiga: https://hadjibsdata.com.ng

=??? App Win mu yana nan a Play Store da App Store.

Idan kana da tambaya ko bukatar taimako, tuntubi admin kai tsaye, 07017133099.


Safiyyah na bude kofa ta washe baki tana kallon Khaleesat tace "Wallahi na zata wasa kike da kika ce kina hanya, shigo ciki mana" Khaleesat ta Wan yi murmushi ta shiga parlon, Safiyyah ta ja ta zuwa Bedroom dinta tace "Ni kadai ce a gidan, ko ina suka tafi oho, ni sai nake ga kamar fa ciki Surayyah tayi, in ko haka ne zan kama kaina in dena biyeta a gidan nan kar taje ta haifi kyakkyawa kamar ni..." Khaleesat ta cire veil din jikinta tace "Sallah zan yi" Safiyyah tace "Kin ci abinci a can kuwa?" Khaleesat tace "Abinci kuma?" Safiyyah tace "Ko da yake waye zai baki gida duk maza, bari inje in dafa maki noodles kafin ki idar da sallahn" Mikewa Khaleesat tayi ta shiga bandaki, Safiyyah kuma ta fita zuwa kitchen, bayan Khaleesat ta idar da sallah Safiyyah ta shigo dakin da indomie da kwai da ta dafa mata ta ajiye, Khaleesat ta kalleta tace "Thank you" Safiyyah tace "Naga duk kinyi wani sanyi, ko dai koran ki Ajayn yayi?" Khaleesat tayi er dariya tace "Saura kadan dai ya kore ni" Safiyyah ta kankance ido tace "Fitinanne, to sai aka yi yaya? Did u meet Housemate in the House?" Khaleesat tace "Eh na gansa" Sai kuma ta jawo handbag dinta ta bude ta ciro kudin da Mai martaba ya bata, Safiyya tace "Wa ya baki wannan kuma?" Khaleesat tace "I think their uncle, ya zo ya same mu a gidan ne, shi ne ya bani da zan tafi" Safiyyah ta Wan bude ido tace "Ko dai babansu?" Khaleesat tace "Babansu kuma? babansu fa Sarki ne, a'a ba babansu bane" Safiyyah ta amshi kudin tana kirgawa tace "Atoh, dama sai dai ko uncle din nasu, amma ina sarki yaga lokacin tsayawa dake har ya baki kudi, da sarki ne ai kya gansa da guards dinsa kuma yaushe ma zai tsaya maki magana, dogarawansa ma baza su bari ba, amma fa ke Hajiya ce kinsan nawa kudin nan in an canza a Naira?" Khaleesat tayi murmushi ta fara cin indomie din gabanta, Safiyyah tace "Wallahi kudade ne masu yawa, har karamin gida sai ya iya siya maki a maririn ku, yanxu ya ku ka yi da Ajay din bayan kin gaya masa abinda ya faru?" Khaleesat tace "Ai bamu gama magana ba Uncle din nasu ya zo, but after i left the house ya kirani yace kar in koma apartment dina, Housemate dina ma ya kirani...." Safiyyah ta hade rai tace "Ba nace kar ki sako Housemate a ciki ba? Shi fa Abdul namiji fitananne ne kawai zai iya dealing da shi, shi kuma Housemate dinki ba mutum bane me son hayaniya" Khaleesat tace "Kilan Ajay din ne ya gaya masa...." Safiyyah ta mike jin ana danna bell tace "Kilan sun dawo daga gantalin da suka je" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba Safiyyah ta mike ta fita daga dakin, ba a dau lokaci ba ta dawo tace "Ban ga kowa a bakin kofar ba kuma, ko dai kunne na ne yaji kamar an danna bell?" Khaleesat ta ajiye fork din hannunta tace "Kuma kin bude kofar?" Safiyyah tace "Haba dai sai kace ni ce ke, ta peephole na duba mana" A hankali Khaleesat tace "Ban san me yasa gabana ke ta faduwa ba Sophie, Abdul can be cunning kar ace ya fa biyo ki yaga gidan nan baki sani ba" Safiyyah tayi wani dariya tace "Saboda yana shan codeine sai ya biyo ni gidanmu, ai yasan ni ba ke bace hauka tuburan zan masa wallahi, to ya biyo ni akan me?" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, taji abincin ma ya fita ranta, Safiyyah tace "In zaki ci abincinki ki ci, idan su Ya Musty sun dawo zan sa ya duba surveillance camera din bakin kofar mu ga wani shege ne ya danna bell" After a while Khaleesat ta tura abincin gabanta don ya isheta ga baccin da take ji, Safiyyah dai chatting kawai take da wayarta, Khaleesat ta dau kudin da Safiyyah ta ajiye mata ta cire dala dubu biyu a ciki ta ajiye mata kusa da ita, Safiyyah ta hade rai tace "Meye wannan?" Khaleesat bata kalleta ba tace "Na baki" Safiyyah tace "Inyi me da shi? A'a bana so wallahi, ki ajiye kudin ki kawai zai maki wani amfanin" Khaleesat bata tanka ta ba ta mike tayi kwanciyarta gefen gado ta lumshe ido, cikin dubara Safiyyah ta jawo handbag dinta ta mayar mata da kudin ciki sannan ta ajiye. Wajen karfe shidda da rabi Safiyyah ta tashi Khaleesat dake bacci ta dalilin wayarta dake vibrate, Safiyyah tace "Ana kiran ki a waya" Khaleesat ta mike zaune ta jawo wayar ta duba taga Housemate ne ke kiranta, daga kiran tayi ta kai kunne, daga daya bangaren yace "I am outside Halysaah" A hankali Khaleesat tace "To" Veil dinta ta dauka Safiyyah ta rakata zata bude mata kofa, Khaleesat ta riko hannunta da sauri tace "Ki fara duba waje kafin ki bude mana" Safiyyah tace "Ke dai matsoraciya ce wallahi, shi Abdul din ai ba Wan iska bane da zai zo ido na ganin ido, baki ga kamar barawo ya shige maki gida ba ranan da daddare" Bude kofar tayi Khaleesat ta makale a bayanta gabanta na faduwa, bayan ta hango motar Jay ta Wan sauke ajiyar zuciya, Safiyyah na washe hakora tace "Yau dai Allah yayi za mu gaisa da shi" Khaleesat ma murmushin tayi suka fita zuwa gun motarsa a tare, yana ganin Safiyyah ya sauko daga motar, ya rungume hannu yana kallonta yace "Good evening kawar Housemate" Safiyyah ta tuntsire da dariya tace "Welcome Yaya Housemate, sai yau Allah yayi za mu hadu tunda ka dawo" Yace "Amma ai ina ce ma kawarki ta gaisheki" Safiyyah tace "Wallahi bata taSa gaya min ba" Jay ya Wan kalli Khaleesat dake kallonsa, ta sauke idonta da sauri bayan sun hada ido, murmushi yayi yace "Gaskiya ban taSa cewa ta gaishe ki ba, it's not her fault..." Safiyyah tayi dariya tace "Wai don ka kareta ko, ai nafi ka sanin wacece Housemate dinka" Jay na murmushi yace "Ya mutan gidan?" Safiyyah tace "Duk lafiya lau suke, yanxu take gaya min uncle dinku gave her much money a taya mu yi masa godiya plss, ranan kuma ta nuna min diamond ring da ka siya mata, Allah ya saka da alkhairi Yaya Housemate, Allah ya bar ku tare" Khaleesat ta bude baki tana kallon Safiyyah with shock, Jay dai yayi murmushi yace "Our father... not uncle Safiyyah" Daga Safiyyah har Khaleesat kallon Jay suka yi, Safiyyah ta bude ido sosai tace "Kana nufin Mai martaba da kansa? That's surprising, Allah ya kara masa girma....." Jay na murmushi yace "Ameen" Ita dai Khaleesat tayi shiru tana tunanin yanda yayi ta hira da ita a parlon kamar random person babu wanda zai yi tunanin sarki ne, Safiyyah tace "To ni zan koma ciki Housemate" Jay yace "Alright Safiyyah, thank you so much" Tana murmushi ta juya ta koma cikin gida, shi dai Jay kallon Khaleesat yake, sai kuma ya bude mata front seat, ba musu ta shiga motar ba tare da ta kallesa ba, ya zaga ya shiga driver seat yana kallonta yace "Kin ci abinci ne?" Kai ta gyada masa, jin bai sake cewa komai ba ta daga idanuwanta ta kallesa, zoben hannunta taga yana kallo baya ko kiftawa, tayi saurin boye hannun a bayanta kamar ta nutse don kunya, yayi murmushi yana kallonta a hankali yace "Wai yaushe kika fara jin kunyata Housemate? I am only admiring the ring, it look soo cute in your finger" Taki daga kai ta kallesa, ita kanta ta rasa gane wannan sabon kunyan nasa da take yi, ya jinginar da kansa da kujeran motar yana kallonta babu ko kiftawa, tunda taji yayi shiru tasan kallonta yake hakan yasa ko da wasa bata yarda ta dago kanta ba balle su hada ido, murya can kasa taji yace "Me yasa ni baki gaya min Ex dinki yaje wajenki a schl ba sai Ajay?" Shiru tayi jin tambayar da yayi mata, can ta dan kallesa, still speaking slowly yace "Why?" Tace "Ae ko an kira ka baka picking call dinka..." Yayi shiru yana kallonta kafin yace "Yaushe kika kira ban yi picking ba?" Ta langwabar da kai tace "Anytime i call, you don't pick" Jay ya sauke idonsa kasa, after some seconds yayi kasa da murya yace "I promise i won't do that again, i will prioritize ur call from henceforth yanda nake prioritizing na Mami da me martaba" Khaleesat ta daga kai suka hada ido, tayi saurin dauke idonta daga nasa, yace "Me yace maki da ya sameki a school din?" Khaleesat tace "Safiyyah ce ta kulasa suka yi exchanging words" calmly Jay yace "Do not worry Halysaah, i will bring an end to ur fright about ur Ex Husband very soon in sha Allah, i promise you this, zaki samu kwanciyar hankali fiye da yanda kike tsammani" Khaleesat ta kallesa, cikin sanyin murya tace "But i don't want you to confront him pls, he can be cunning" Jay ya Wan yi murmushi yace "I am not confronting him Halysaah, kawai dai zan yi abinda zai yi cutting duk wani Intention din da yasa ya dawo yake bibiyan ki, i will put a total stop to that, kuma babu yanda ya iya haka nan zai hakura ko ba don Allah ba...." Khaleesat tayi shiru tana kallonsa, After some seconds tace "Amma yanxu i will prefer inyi ma brother din Safiyyah magana to let me stay in their home har sanda zan gama exams, don bazan iya zama a apartment dina ni kadai ba kuma, i am very afraid" Jay yace "Kar kiyi inconveniencing dinsu Housemate, and I don't want you to be a burden to them considering the high cost of livelihood in this state.... ki zauna a apartment dinki kawai, i will be there also, i will be there to protect you...." Khaleesat tace "Zaka dinga zuwa kamar sanda muke former apartment dina?" Yayi murmushi yana kallon kwayar idanuwanta yace "Sure, anything for you Halysaah" Sosai taji hankalinta ya kwanta, cikin sanyin murya tace "To Nagode" Yace "Lokacin sallah ya kusa, can we go home now" Tace "Let me get my handbag" Gyada mata kai yayi, ta bude motar ta sauka, ya bi ta da kallo har ta shiga apartment din, after some minutes sai ga ta ta fito daga gidan da handbag dinta da waya, ta shiga motar ta rufe tana kallonsa taga kallonta yake.... Khaleesat na zaune dakinta wajen karfe takwas da rabi na dare suna WhatsApp call da Aunty Farida, gaba daya jikinta a sanyaye yake ga faduwar da gabanta yake ta yi jin abinda Aunty Farida ke gaya mata, labarin biyota da Abdul yayi har sabon Apartment dinta da kuma cikin makaranta take ba Aunty Farida, a nan ne Aunty Farida ke sanar mata ai yaje Mariri ma yafi a kirga few weeks ago kawai gaya mata ne bata yi ba don bata son daga mata hankali, Cikin sanyin murya Khaleesat tace "To Aunty ya aka yi yasan ina America

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login