Showing 222001 words to 225000 words out of 241367 words

Chapter 75 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1574

samu ta ja Safiyyah suka bar wajen gaba daya, banda rawa babu abinda jikinta yake yi don tsoro, Safiyyah ta warce hannunta tana kallonta a fusace tace "Kin dai ga Wan iskan da kike tausayi ko? ashe da sabon salo kawai ya dawo don ya samu attention din ki, ke kuma ga sarkin masu tausayi, to kuwa rabon a karyasa yasa ya dawo Amurka don wallahi Ajay karyasa kawai zai yi" Khaleesat ta zauna ta rufe fuskarta da hannunta tana kuka a hankali, gaba daya ta gama tsorata, ta ma rasa wani irin tunani zata yi, zaman apartment din nata ita kadai ya fara bata tsoro kuma, can ta kalli Safiyyah dake ta bambami cikin rawan murya tace "Sophie ko dai in ma Ya Musty magana da kaina ki dawo apartment dina da zama tunda exams za mu fara? Wallahi bazan iya zama ni kadai ba kuma a gidan nan Sophie, i am afraid..." A fusace Safiyya tace "Ai baki zama afraid ba tunda har kika iya boye kasungumin Wan daba a gidanki ya kwana, Abdul har abun yarda ne bayan duk mun san Wan iska ne shi? Wani dadin baki zai maki har ki yarda da shi? Kin dai ga abinda yayi min ai yanxu, dama kuma me hali baya taSa fasa halinsa" A hankali Khaleesat tace "To ko dai in yi ma Ajay bayanin abinda ya faru jiya kar ya zo ya gano yaji haushina? Wallahi i am so confuse Sophie" Safiyyah tace "To nima naji haushin ki balle Ajay da yayi gadin ke da Abdul ku ka sharbi baccin ku? ai wallahi kin cuce Ajay kuma sai Allah yayi masa sakayya" Khaleesat ta goge hawayen gefen idonta tace "To amma sai dai inje can gidan nasu in masa magana ko? Don kar yaje yayi misinterpreting dina ta waya idan na kirasa, i want to explain to him ta yanda zai gane" Safiyyah tace "Dama ai gwara ki samesa face to face kiyi masa bayani, sannan kar ki kuskura ki ce masa a gidan Abdul ya kwana don daga nan zai fatattake ki ya kora ki, ko ya hadaki da karensa ya kora ki, inda Ajay ke burgeni kenan wallahi, no nonsense Man kike ji, sam baya daukan wargi, tsayayyen namiji kenan, kawai ce masa zaki yi kin shiga kitchen zaki zuba abinci sai kika ga kamar Abdul a jikin window din kitchen dinki yana kallonki, shi ne duk kika rude kika kirasa jiya da daddare, daga baya kuma kika ga wajen wayam ba kowa, amma da ya zo sai baki gaya masa hakan ba tunda baki tabbatar ba kin zata hallucination kawai ki ke yi don dama kanki na ciwo jiyan, sai ki ce masa yau kina department muna zaune ni da ke kawai sai ga katon a gabanmu, ashe jiya shi din dai kika gani a jikin window, kinga ai maganata tayi making sense akan ki ce masa ai boyesa kika yi a daki jiya...." A hankali Khaleesat tace "To bari inyi order din Uber zuwa gidan" Safiyyah tace "Sannan idan kin je gidan ki fara masa godiyan gadin ki da yayi jiya ya hana kansa bacci, don nasan ba hankali gare ki ba kina iya zuwa ki fara maganar da ya kai ki kanki tsaye...." Khaleesat ta ciro wayarta za tayi order din Uber da zai kai ta gidansu Ajay, kafin tayi order din ta kalli Safiyyah tace "Ko zaki rakani mu je mu biyu?" Safiyyah ta rike haSa tace "Wa?? Ni? Salon inje ya koro ni mutumin da ba kirki ne da shi ba, a'a wallahi bazan je ba, ko kadan bai taSa burgeni ba dama ni, tun farko tamu bai zo daya da shi ba don na tsani mutum fitinanne, da dai Housemate ne sai in bi ki mu je, kuma banda ma yafi Housemate zafi me zai sa ma a sako sa cikin wannan case din, to tsorona muna iya sako Housemate yaje ya fara ba Abdul din hakuri kinga ai lamari ya lalace kenan, babu dai yanda muka iya Ajayn zaki je ki sama duk da mugun halinsa, ayi mutum ace bai son mutane kullum yayi ta daure fuska yana fushi shi kadai" Khaleesat na kallon Safiyyah cikin sanyin murya tace "Ko dai kawai in gaya ma Housemate in kyale Ya Junaid din?" Safiyyah ta wani hade rai tace "Wani Housemate, hakuri kike son ya tafi ya ba Abdul din kenan yanda zai ji dadin ci gaba da iskancinsa, ai karki kuskura ki gaya ma Housemate he won't help matters at all, gwara Ajay no nonsense, tsaf zai mana maganin Abdul, amma Housemate ai har durkusawa sai ya iya yi ya ba Abdul din hakuri yanda suka yi ma Aymaan shi da Ya Musty, Ajay ai shi ne namiji" Khaleesat dai bata ce mata komai ba tayi order din ride din, Safiyyah ta zaro ido tana kallon hannun Khaleesat tace "Ina zoben naki? Mun shiga uku ko dai Abdul din ya kwace?" Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tace "Ga fa shi nan a jaka" Safiyya tace "Atoh, don ni yanda na gansa wujiga wujiga anya karayar arziki bai fada masu ba kuwa, kamar wanda yake yunwa duk ya rame sai idanuwa da hanci, da kyar idan ba talauci a tattare da shi" Khaleesat dai bata tanka Safiyyah ba, Safiyyah tace "To ki saka zoben mana, ko jere zaki yi da shi a gaban madubi?" Khaleesat ta bude ido sosai tace "Ina zan je da zan saka zobe Sophie?" Safiyyah tace "Ke dai kin ki wayewa a rayuwarki Khaleesat, ba don gayu ya siya maki ba dama?" Warce jakar tayi ta ciro box din zoben tace "Dalla ki saka" Khaleesat tayi murmushi ta amshi zoben ta saka tana kallonsa admiringly, cif ya zauna mata ta kalli Safiyyah dake ta murmushi ita ma kamar bakinta zai yage tace "It's sooo cute, gaskiya Housemate is so romantic, har na hango kun yi aure, wallahi kashe ki zai yi kawai da soyayya, in soyayya ne a bar ma Housemate kawai, in kuma kwato hakki ne a bar ma Ajay" Dariya sosai ta ba Khaleesat, kawai ta mike bayan ta maida wayarta da empty box din zoben cikin jaka, Safiyyah ta rakata har zuwa inda Lyft dinta ke jira, ta bude motar ta shiga, hannu ta daga ma Safiyyah dake ta murmushi tana kallon zoben yatsanta dake ta kyalli, a haka Lyft din ya bar wajen, tun da suka kama hanya Khaleesat ke ta waige waige to be sure babu motar dake bin su a baya, don ita kam yanxu duk a tsorace take, tunda har Abdul ya iya gano apartment dinta to babu kuma abinda bazai iya yi ba, har dai suka isa bata ga alamar ko wani mota dake biye da su a baya ba, ta sauka daga lyft din tana tafiya a hankali ta shiga compound din, it's almost 4pm na yamma, motar Ajay ta fara gani a parking space din gidan, sannan ta ga motar Jay ma alamar duk suna gidan, walking slowly ta karasa har entrance din parlon dai dai sanda aka bude kofar parlon, ta Wan koma baya tana kallon Housemate dinta dake kallonta da mamaki, cikin dubara ta boye zoben finger dinta da veil dinta kar ya gani, tana kirkiran murmushi a hankali tace "Good evening" Yace "Evening Housemate, come in" Ta sauke kanta kasa ta bi bayansa har zuwa cikin parlon, ta zauna kan kujera shi ma ya zauna yana kallonta hoping all is well don sai yaji gaba daya hankalinsa ya tashi ganinta a gidansu, jin tayi shiru yana kallonta yace "Hope all is well Housemate?" Tana murmushi tace "Alhamdulillah, babu komai, Ya Junaid yana nan? I came to greet him" Jay yayi shiru yana kallonta, after some seconds yace "Yeah, he is upstairs" Ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Ohk, i want to meet him" Jay ya gyada mata kai yace "He is at the parlor upstairs, ki samesa a can" A hankali tace "Sai na je sama?" Jay ya mike yace "He is there, ni zan fita yanxu...." Khaleesat tayi shiru tana kallonsa, ya Wan yi murmushi ya nufi kofar fita parlon ta bi sa da kallo har ya fita, bayan fitarsa da kusan minti goma Khaleesat ta mike, walking slowly ta tafi sama, tsaye tayi Wan nesa da parlon dake sama tana kallon Ajay dake kallon kwallo a Tv, ga grapes a gefensa yana sha, ko lura da ita bai yi ba, he was so engrossed in the football match he was watching.....


*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 =?H?


https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegM


Khaleesat ta sauke idonta daga kallonsa ganin for almost 2 minute bai lura da ita ba kallon ball kawai yake da duk attention dinsa, ta Wan yi kasa da murya tayi masa sallama, juyawa yayi da sauri suna hada ido ya gyara zamansa don kishingide yake saman kujeran, nan da nan yayi keeping straight face ya ci gaba da shan grape dinsa idonsa a kan TV, tana tafiya a hankali ta karaso cikin parlon ta tsaya jikin kujera trying to gather up courage tace "Good evening..." Ya Wan kalleta, sai kuma yace "Yes?" Ta Wan langwabar da kai tana kara rungume handbag dinta tace "Ina son zan maka magana ne pls" a takaice yace "I am busy as you can see...." Ta kalli football din da yake kallo, a hankali tace "To shikenan, sai anjima" Tana fadin haka ta juya zata bar parlon yace "Ke.... awa daya zaki yi using kiyi min maganar ne, say what u want to say in few seconds i am listening" Tayi shiru tana kallonsa, after few seconds ta zagayo ta zauna kan 1 sitter tana kallonsa, har a sannan kusan duk hankalinsa na kan TV din kamar baya son missing kwallon da yake kallo, bayan kusan minti biyar ya juya ya kalleta, shi har ya mance tana wajen, yace "Kee fadi abinda ya kawo ki and stop staring at me that way" Tace "To ai naga kallo kake" Yace "Ido ke ji ko kunne? Ina ruwanki da kallon da nake yi?" ?an taSe baki tayi, ita shi yasa bata ma son abu yana hadata da shi, komai sai yayi masifa, ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "Dama Abdul ne ya biyoni school yau..." Lokaci daya ya juya ya kalleta, ta sunkuyar da kai, can yace "Waye Abdul?" Ta Wan kallesa taga kallonta yake, tayi karfin halin cewa "My ex" Shiru ya sake yi, after some seconds yace "In zaki min bayani in details ki bude baki kiyi min and stop wasting my time" Ta Wan saita kanta ta yanda zata fara koro masa duk abinda Safiyyah tace ta gaya masa, tayi inhaling numfashi sannan ta fara masa bayanin exactly yanda Safiyyah tace tayi, ya rage volume din TV, yana sauraronta attentively amma ba kallonta yake ba, har ta kai aya tana kallonsa, bai ce komai ba for almost a minute as if yana processing duk bayanin nata a kansa, still not looking at her yace "So now what did you want me to do?" Shiru Khaleesat tayi don bata san me zata ce ba, can taji yace "Saki nawa yayi maki?" Ta sauke idonta a hankali tace "Kawai ce min yayi ya sakeni, bayan da na dawo gida kuma aka aiko takarda daga gidansu da saki uku a jiki, amma ba rubutunsa bane" Ajay ya wani kalleta yace "Rubutun ki ne kenan?" Sunkuyar da kanta tayi, ya sauke idonsa kan zoben hannunta dake kyalli, ta Wan saci kallonsa taga he is still looking at her, dauke kansa yayi bai sake cewa komai ba na Wan lokaci, sai kuma taji yace "So what did you want me to do now da kika zo kika gaya min?" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kallesa, lkci daya jikinta yayi sanyi, yace "Ko nan gidan kike son ince ki dawo?" Ta girgiza masa kai tace "A'a, i will cope in sha Allah, kawai na gaya maka ne" Sai kuma ta mike a hankali tace "Nagode, i am going back home" Ya watsa mata wani kallo yace "Are you okay? Ina maki magana zaki mike tsaye? Ni nace ki tashi?" Ta sunkuyar da kanta sai kuma ta koma ta zauna, nan da nan taji hawaye ya cika idonta, da ta sani kawai da Housemate dinta ta gaya ma duk da Safiyyah tace kar ta gaya masa, Ajay ya dau grape dinsa yana ci yace "Shi Guardian din naki me ya hanaki gaya masa sai ni? Baki fi kusa da shi ba a kaina zaki tsallakesa ki zo ki sameni? Am i ur Bodyguard?" Jin tayi shiru ya juya ya kalleta, hawaye ya gani a idonta, ta kai hannunta tana goge hawayen, bai sake cewa komai ba idonsa a kan grape din gabansa, after almost 30 seconds ya kalleta yace "Ya ma kike da suna, Yaushe zaku fara exams?" Bata dago kanta ba cikin sanyin murya tace "In less than a month time" Yace "Amma kinga silly frnd din nan taki wataran sai ta jefa kanta masifar da bazata iya fita ba, har ke sai ta jefa cikin matsala, shi tout din ta tsaya take exchanging words da saboda rashin kamun kai...." Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Ajay bai sake cewa komai ba a parlon yana nazarin how to tackle the issue, shi ya dade bai ga Wan iska kamar Abdul ba, amma zai yi maganinsa, shafa kansa yayi still thinking of where to start from, a yanxu dai baza su fara cewa ta zauna a gidan nasu ba don Mai martaba went on a trip to Toronto, kwanansa hudu kenan a can kuma basu san ko zai biyo ta Amurka ba, infact zai ma biyo don in dai ya taho overseas komin nisan inda yaje da Amurka dole sai ya zo Maryland in har suna kasar to check on them, so they won't take the risk of accommodating her in the house, assuming the semester isn't late da kawai sun mata applying for On-campus residence halls a cikin makarantar ta zauna, Ajay ya daga kai yana kallon Cousin brother dinsa Mukhtar that was coming towards the parlor, Mukhtar yayi kasa da murya yace "Tare mu ke da Mai martaba...." Ajay bai san sanda ya mike tsaye ba dai dai sanda yayi ido hudu da Abbansa dake biye da Mukhtar a baya, ?amewa yayi a inda yake tsaye with surprise, what a bad coincidences this is, Mai martaba ya shigo parlon with a broad smile on his face yayi kamar ma bai ga Khaleesat ba, Ajay ya sauke kansa kamar wanda ruwa ya cinye a wajen, at first ya ma rasa abun cewa, can kuma yayi karfin halin cewa "Barka da zuwa ranka shi dade....." Khaleesat ta daga kai tana kallon Mai martaba sai kuma ta sunkuyar da kanta ta zamo kasan carpet ta gaishesa cikin sanyin murya, sai a sannan mai martaba ya kalleta still smiling ya amsa gaisuwarta, Mukhtar yayi offering masa kujera ganin bai zauna ba, Mai martaba yace "I am fine Mukhtar..." Sai kuma ya kalli Ajay da ya kasa kallonsa har sannan yace "Ina Jawwad?" A hankali Ajay yace "I think he went out just now..." Mai martaba yace "Ohk" Mikewa Khaleesat tayi da niyyar barin parlon, Mai martaba ya kalleta yace "No yi zamanki yarinya, ya sunanki?" Ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta koma ta zauna a hankali tace "Sunana Jiddah" Yayi nodding kai yace "Maa sha Allah, ke er Nijar ce?" Khaleesat ta Wan yi murmushi tana wasa da gyalenta tace "A'a, er Nigeria ce" Mai martaba yace "That's good, Nigeria wani state?" Tace "Kano" Ajay dai yaki daga kansa yana jin zufa na karyo masa a forehead, can kawai ya juya ya bar parlon yana tafiya a hankali, Mai martaba ya zauna saman kujera still looking at Khaleesat yace "Karatu kike a kasar nan Jiddah?" Khaleesat tace "Eh karatu nake" Yace "That's good, wace makarantar?" A hankali Khaleesat tace "John Hopkins university..." Mai martaba na jinjina kai yace "Maa sha Allah, kano a wani unguwa iyayenki suke?" Khaleesat tace "Muna mariri ne" Shi dai Mukhtar na ta tsaye a parlon yana mamakin yanda Mai martaba ya tsaya ya bada lokaci yana conversing da Khaleesat bringing her down to his level, Ita kanta Khaleesat bata yi tunanin sarki bane shi duk zaton ta ko dai brother din babansu ne shi din, Mai martaba yace "Maa sha Allah Jiddah, Allah ya bada sa'an karatu" Tace "Ameen Abba Nagode" Mikewa tayi zata bar parlon ya kalli Mukhtar yace "A bata dala dubu biyar Mukhtar" Mukhtar ya Wan risina kai da ladabi yace "To ranka shi dade" Khaleesat na kallon Mai martaba a hankali tace "Abba Nagode, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara girma" Daga mata hannu kawai yayi with smile, sannan ta mike ta bi bayan Mukhtar, tun basu fita parlon ba sai ga Jay ya shigo, kasa karasowa yayi bayan yayi ido hudu da Khaleesat ga Mai martaba zaune a parlon, can ya kalli Mukhtar da ya daga masa hannu alamar gaisuwa, ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, shi kam ya sunkuyar da kai walking slowly, a hankali tace "Sai anjima" Murmushin karfin hali kawai yayi mata without saying anything, ta bi bayan Mukhtar suka bar parlon, Jay ya karasa har cikin parlon ya zauna kasan carpet yana gaida Mai martaba da ladabi, Mai martaba ya amsa yace "Ina Ahmad din?" Jay ya mike ya bar parlon zai kira Ajay, ba a dau lokaci ba suka dawo tare, shi dai Ajay ya kasa hada ido da mahaifin nasa, ya zauna kan carpet gefen Jay, sae kuma yayi karfin halin cewa "Ya hanya ranka shi dade?" Cikin nutsuwa Mai martaba yace "Alhamdulillah...." Daga haka mai martaba bai sake cewa komai ba, Jay da Ajay ma duk suka yi shiru kamar masu jiran hukunci a gabansa, after a while Mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login