Showing 165001 words to 168000 words out of 241367 words

Chapter 56 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1610

koma ko Rijiyar Lemo ne" Dukawa tayi ta kwance ledan da ta ajiye tace "Gashi nan, kasuwa na aiki almajirina ya siyo min kayan ciki me kyau nayi mata farfesu ta sha ta mance abinda ya dameta, saki ai ba kanta farau ba, mu ma duk ai an taSa sakin mu, uban Ali saki nawa ne bai min ba, sai da igiya daya ya rage mana sannan muka nutsu muka zauna har mutuwa ta raba" Wata mata ce tayi sallama bakin kofar dakin Umma, Umma ta amsa mata, matar ta shigo tana gyara yakunannen gyalenta, ganin Nenne ta duka har kasa ta gaisheta, Nenne ta amsa tana rufe farfesun da ta kawo ma Khaleesat kar matar ta barbade farfesun da gyalenta, Bayan matar sun gaisa da Umma tace "Ashe abinda ya faru kenan Ummansu Khaleesah?" Nenne ta juya ta kalleta tace "Me ya faru?" Matar ta langwabar da kai cikin rashin jin dadi tace "Mutuwan auren Khaleesah Nenne" Nenne ta mike tsaye tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, mutuwar auren wace Khaleesar? A ina kika ji auren Khaleesah ya mutu? Na shiga uku na lalace, wato matan Mariri baza ku canza halin ku na tsugudidi ba ko? To daga ke har wanda ya gaya maki kun ci kaza kazan ku yan iska kawai shegu, tashi ki fita ki ba mu waje, sai dai ki ga mutuwar aure a dakin ki ko na uwar ki, kaji min mata dai munafuka, uban mutuwan auren Khaleesah, fita ki bamu waje" Da sauri matar ta fita daga dakin ta saka takalmi wari da wari ta bar bakin kofar, Nenne na huci ta kalli Umma tace "Ke kuma Las spika ki ka dauka kike shelan an saki Khaleesah?" Aunty Farida ta tabe baki tace "Ina fa Nenne, mu ma kawai gani muka yi ana ta shigo mana tun da gari ya waye, wai an zo Jaje, wa enda suka fitar da labarin ai su ne babban munafukai" Nenne na share zufan goshinta tace "Shatu da Zubaida kenan, babu me fitar da zancen nan sai su" Tana kai wa nan ta fice daga dakin, kafin ta fito dama su Mama Shatu duk sun shige dakunan su da sauri bayan sun ji abinda Nenne tayi ma matar da ta fita daga gidan, nan tsakar gida Nenne ta tsaya babu abinda ta manta bata gaya masu ba, zagi kam sun sha har sun gode Allah, Allah ya isa shima tayi masu kwando kwando, daga karshe tace "Kuma in har Ali ya dawo gidan nan anjima bai dau matakin fitar masa da sirrin gida da ku ka yi ba wallahi sai dai ya zaba ko ni ko ku, da dai in zauna da surkai magulmata munafukai gwara in sallame ma duniya Ali in shi bazai sallama maku ba, to ai ita Khaleesar ta samu mashinshini har tayi auren ta fito, ku kuma da naku 'ya yan ke zube kaman gwanjo babu mataya fa? Dama nace ma Ali in har bazai bada su sadaka ba to ni a dena nuna su ace jikokina don kunya nake ji, ko kuma in tattara in bar masa Maririn in har bazai samar ma narka narkan 'ya yanku mafita ba, yanxu in na Jera da Labeebah ba sai ace ita ta haifeni ba, sannan kwata kwata basa wuni a gidan nan ban san inda suke zuwa ba, sai mutum ya shigo sau dari bai gan su sau biyu ba" Khaleesat ta fito daga bandaki tana rike da Shower gel dinta ta nufi dakin Umma, Nenne ta bi ta a baya tana cewa "Kin fito Khaleesah, mu je ga farfesu can na maki" Sai da suka shiga dakin sannan Khaleesat ta gaida Nenne, Nenne ta amsa tace "Kar fa ki ce zaki sa damuwar shegen a ranki kin ji? Allah ne ya dubemu ya rabu dake cikin aminci bai maki wata illa ba, dama kuma ance min uwarsa har tsafi take yi, kinga hada zuri'a da irin wannan mutane ai abun tsoro ne, kar ki saka komai a ranki, rabuwan shi ne mafi alkhairi a gare ki dama an gaya min" Khaleesat dai ta zauna gefen gadon Umma tana shafa cream dinta, Nenne na kallon Umma tace "Ke kuma duk wanda ya shigo maki jaje baki koresa ba Allah ya isa kema, ai mutum daya na shigowa kika rufe ido kika koresa komawa zai yi ya sanar ma sauran, shikenan babu wanda zai sake shigo maki, ni kin ga tafiyata inje in nemi abinda zan ci da rana" Daga haka ta fice daga dakin. Bayan Azahar Khaleesat na zaune kan darduma da qur'ani a gabanta tana karantawa a zuci, sai ga Safiyyah ta shigo dakin Umma da sallama, Khaleesat ta rufe Al-qur'anin ta daga kai tana kallonta tana murmushi, ji tayi kamar all her worries are gone ganin Safiyyah, Safiyyah ta ajiye handbag dinta ta zauna edge din katifar dakin tana kallon Khaleesat a sanyaye, gaba daya ta kasa ce mata komai, Khaleesat ta mayar da Al-qur'anin Aunty Farida gefe sannan ta mike ta koma kusa da Safiyyah ta zauna tana kallonta har sannan murmushin fuskarta bai Sace ba tace "I miss you so much" Hawaye ne ya zubo ma Safiyyah a ido don kawai ta kasa daure hakan, Khaleesat ta sauke idonta kasa, sai ga hawayen ita ma a idonta, rabonta da zubda hawaye tun jiya a gaban Abbanta, bayan kuma ta shigo ta kwanta bata sake yarda tayi kuka ba duk da kusan yanda taga rana haka taga daren ga zafin da zuciyarta ya dinga mata, Safiyyah ta rungumeta tace "It's fine Khaleesat, Allah ya saka maki abinda yayi maki" Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Safiyyah ta goge idonta don taga alamar kukan da take ne yasa Khaleesat kuka, Safiyyah ta dago kanta tana kallonta tace "Su Umma fa?" Khaleesat tace "Sun je gaisuwa ne anyi rasuwa dazu a unguwan" Safiyyah tace "Allah sarki, Allah ya ji ?an musulmi" Khaleesat tace "Ameen, ya su Mama fa?" Safiyyah tace "Duk suna lafiya lau, tace in gaisheki, bayan mun gama waya daxu tace in kira mata ke, na sake kiran wayar Aunty Farida naji a kashe" Khaleesat tace "Ehh babu caji ne, ta bada a kai mata wajen caji" Safiyyah tayi shiru, bata son yi ma Khaleesat maganar da zai kara sa taji ciwo a ranta, amma duk da haka calmly tace "Saki nawa yayi maki?" Khaleesat ta buda manyan idanuwanta tace "Kawai ce min yayi ya sakeni" Safiyyah taji bakin cikin ba saki uku yayi mata ba, don ita ba kukan bakin cikin sakin da yayi take ba, a'a bakin cikin mayar mata kawa bazawara da yayi ne babban bakin ciki da takaicinta shi ne yasa har ta zubda hawaye, a gida ma kukan da tayi kenan don taji ciwon abun sosai, Khaleesat ta kalli inda Aunty Farida ta ajiye Envelope din da Drivern gidan su Abdul ya kawo tace "Ga ma can takardan ya aiko" Safiyyah ta juya ta kalli Envelope din, mikewa tayi ta dauko ta dawo ta zauna ta ciro takardan ciki, ita dai Khaleesat kallonta kawai take don har sannan bata duba abinda ke jikin takardan ba, daga Aunty Farida har Umma babu wanda yace mata saki uku ne, jiya kuma da Nenne ke ta hayaniya a tsakar gida bayan an kawo takardan Khaleesat na kwance duk bata san abinda ake ba don abubuwan da suka dameta daban, Safiyyah ta kalli Khaleesat da sauri tace "Saki uku ne ai a takardan" Khaleesat ta amshi takardan a hankali tana dubawa, after some seconds ta kalli Safiyyah tace "Wannan ai ba rubutun sa bane" Safiyyah ta hade rai tace "Do we care?? Ba dai shi aka kawo mana ba, kinga ai da shi za mu yi aiki, don da kika ce saki daya ne sai da gabana yayi mummunan faduwa don matsiyacin zai iya dawowa yace ya maida ke mu shiga uku, amma tunda ga takarda an rubuta saki uku a jiki shikenan an wuce wajen, Alhamdulillah" Khaleesat dai kallon Safiyyah kawai take, Safiyyah ta ajiye takardan ita ma tana kallonta, can a hankali Safiyyah tace "I don't understand you Khaleesat, ko dai bakin ciki da sakin da Abdul yayi maki ki ke? Kin yi give up kan cewa zaki zauna zaman har abada da shi ne? Pls let me know first so that i will watch my words" Khaleesat tayi murmushin takaici tace "Dukan yau daban, na gobe daban, zagi, hantara cin mutunci, living with hunger...." Kasa ci gaba Khaleesat tayi ta fashe da matsanancin kuka tana girgiza kai, Safiyyah ta rungumeta tace "Allah ya saka maki, Allah ya saka maki cikin gaggawa, in sha Allahu sai yaga karshensa tun ba aje da nisa ba, in sha Allah sai hakkin ki yayi tormenting dinsa har karshen rayuwarsa, komin lalacewan gidanku baza a doke ki ba balle a zage ki ko a hantare ki, uwa uba a bar ki da yunwa, In anyi duniya don manzon Allah sai Allah ya nuna ma Abdul iyakansa, wato punching bag ya mayar dake a gidan, kalli yanda kika rame kalanki ya disashe kamar ba ke ba, dubi yanda duk kika fita hayyacin ki, wallahi hakkin ki bazai taSa barin Abdul ba, ki kwantar da hankalinki ki cire ko wani damuwa a ranki ki dau hakan a kaddarar rayuwarki" Kai kawai Khaleesat ke gyada mata hawaye masu zafi na zuba idonta, Sosai Safiyyah ta dinga bata words of encouragement tana kwantar mata da hankali, har Khaleesat taji sanyi sosai a ranta, taji ta samu relieve din abubuwan da suka tunkushe mata a rai tun jiya, a haka Umma da Aunty Farida suka dawo suka samesu, Umma ta ajiye masu Wanwaken da ta siyo a makota sanin Khaleesat na son Wanwake, ba laifi Khaleesat ta ci Wanwaken me yawa tare da Safiyyah, dama duk yau ta kasa cin komai, ko farfesun da Nenne ta kawo mata kaWan ta iya ci, amma sai ga shi ta ci Wanwaken sosai, sai kusan karfe shidda na yamma Safiyyah ta bar gidan, with the relieve that tayi consoling kawarta tunda gashi har tana dariya ta baro ta, sallan magrib kawai Safiyyah tayi ta jawo wayarta tayi dialing number Housemate, wanda rabon su yi magana tun sanda ya gaya mata abinda Khaleesat tayi masu shi da Ajay.
[6/30, 11:27 AM] khaleesat Haiydar =???
'?: Jay na zaune dakinsa wajen karfe tara na dare yana rike da mug din coffee da yake ta stirring for almost 5 minutes now ya kasa sha, ya daga kai jin an bude kofar dakin, Ajay ne ya shigo ya nufi inda Laptop dinsa yake, shi dai Jay kawai bin sa yayi da ido har ya kunna laptop din ya duka yana dube dube a cikinsa, after almost 2 minute ba tare da Ajay ya kallesa ba yace "Resend me those files u sent yesterday via Email" Jay bai ce masa komai ba, hakan yasa Ajay ya juya yana kallonsa, mikewa yayi ya nufesa, ya cire masa head warmer din kansa ya saka a nasa kan yace "Hey is everything Okay? Me yasa baka fito ka ci abinci ba?" Jay ya mike ya fixge Head warmer dinsa sannan ya koma ya zauna yace "Kai dai ba ka ci ba, cire min Jacket dina Ajay, I can't remember dashing you the Jacket...." Ajay na gyara Jacket din jikinsa ya koma ya ci gaba da abinda yake yi a laptop din Jay, after a while Jay ya ajiye Mug din hannunsa, speaking slowly yace "I spoke to Safiyyah not long ago" Ajay ya kallesa yace "Wacece haka?" Jay yace "My Housemate's friend" Banza Ajay yayi masa ya ci gaba da duba abinda yake yi a laptop, calmly Jay yace "And she...." Ajay ya dakatar da shi sounding pissed off yace "Plss Jay, i am not interested, do not provoke me this night, banda file da nake nema a laptop dinka baza ma ka gan ni a dakin ka da daddaren nan ba" Jay ya mike yace "Whether you are interested or not, Safiyyah ta gaya min gayen ya saki Halysaah" Ajay ya juya ya kalli Jay babu ko kiftawa, after some seconds ya maida idonsa kan laptop din gabansa sai dai bai ci gaba da operating laptop din ba, Jay ya karasa kusa da window din dakinsa ya bude drape din ya rungume hannunsa yana kallon tiny snow din dake zuba kasa, Ajay yace "What did you expect? Were you expecting less? He's satiated his craving, and that is all that he is after, yayi satisfying Lust dinsa" Yana kai wa nan ya rufe Laptop din kawai ya nufi kofa ya fice daga dakin, shi dai Jay da ido ya bi sa kawai, can ya sauke wani ajiyar zuciya ya karasa ya rufe kofarsa da Ajay ya bari a bude. Khaleesat na zaune gaban Coal pot wajen karfe sha biyun rana tana ta fifita gawayin da ta hura zata dora girkin rana at the same time tana gyara waken farantin dake cinyanta, Ummanta ce zata dora girkin don Aunty Farida ta fita kasuwa shi ne ta amshi girkin tace zata yi, shinkafa da wake da mai da yaji ne za su yi da rana, babu kowa a gidan sai ita da Umma don su Mama Zubaida da Mama Shatu sun tafi gidan biki ko girkin siyarwa basu yi ba ranan, Umma ma gidan Nenne take shirin zata je ta kai mata kubewan da ta tambayeta ranan friday, Waga kai Khaleesat tayi jin sallaman Safiyyah a compound din su, ta dinga kallonta bata ko kiftawa don bata ce mata zata dawo yau ba, Safiyyah tayi murmushi ta karasa har inda take sannan ta dau kujeran tsugunno da ta gani a tsakar gidan ta zauna tana kallon Khaleesat tace "Sannu da aiki" Khaleesat ta Wan bude ido tana murmushi tace "You didn't tell me you were coming today Safiyyah" Safiyyah tace "Eh nima ban zata zan zo yau ba, dama ranan Monday ko Tuesday nace maki zan dawo ai" Umma ce ta fito daga dakinta, Safiyyah ta gaisheta da ladabi, Umma ta amsa da fara'a tace "Ya su maman ku?" Safiyyah tace "Sun ce in gaishe ku Umma" Umma tace "Allah sarki, to ina amsawa, bari in je gidan Nenne in dawo yanxu" Safiyyah tace "To sai kin dawo Umma" A haka Umma ta fita daga gidan, Khaleesat ta dora ruwan girkin ta ajiye waken da ta gyara sannan suka shiga dakin Umma da Safiyyah, Safiyyah na kallonta tace "Don Allah ki daure ki dinga cin abinci Khaleesat, kin ga yanda kika rame kamar ba ke ba kuwa" Murmushi kawai Khaleesat tayi tace "To ni dama kiba gareni Sophie?" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Even though, yanxu raman tayi yawa wallahi, ji fa sai idanuwa da dogon hanci kawai" Dariya kawai Khaleesat tayi bata ce mata komai ba, Safiyyah na kallonta tace "Ba dadewa zan yi yau ba Khaleesat, aikoni aka yi wajen ki" Da mamaki Khaleesat ta dinga kallonta, sai kuma tace "Wajena kuma? Wa ya aiko ki" a hankali Safiyyah tace "Ur Housemate" Sosai gaban Khaleesat ya fadi ta dinga kallon Safiyyah babu ko kiftawa zuciyarta na bugawa, Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya ta kamo hannunta tace "Sai dai kiyi hakuri, ni dai na gaya masa abinda ya faru, And...." Sai kuma Safiyyah tayi shiru, Ita dai Khaleesat kallonta kawai take don ta kasa cewa komai tana jin hawaye na taruwa gradually a idonta, a hankali Safiyyah tace "He sent me money for ur flight ticket back to America, and you tuition fee for this semester, ya ce zai samar maki wani apartment din for the one year that is remaining for us...." Hawayen dake makale idon Khaleesat ya zubo, ta kasa ce ma Safiyyah komai, bata san sanda ta fashe da kuka ba sosai, ita dai Safiyyah tayi shiru tana kallonta cause she wasn't expecting less, sai da Khaleesat tayi kukanta me isarta sannan tana girgiza kai muryarta na rawa tace "I don't think za a bari in koma in ci gaba da karatu Sophie" Safiyyah tace "Ban gane ba? Saboda me baza a bar ki ba?" Khaleesat na goge idonta da kyar tace "Saboda Abdul ma da aka bari ya kai ni karatu babu yanda za mu yi ne hakan ta faru, we had no choice then, dalilin haka har sai da Ummata ta samu hawan jini, kin ga yanxu kuwa ai babu wani hujjan da zai sa a sake barin wani ya ci gaba da sponsoring dina a wata kasar" Safiyyah tace "I don't understand Khaleesat, yanxu me kike nufi? So kike kiyi asaran shekarun da kika yi a makarantar kenan?" Hawaye na zuba idon Khaleesat ta girgiza mata kai tace "A'a Sophie, but iyayena za su ji tsoron sake yarda wani ya dau dawainiyata try to understand me" Safiyyah tace "Zan jira har Umma ta dawo daga gidan Nenne in mata magana, ke kam bani da sauran magana dake, cause haushi zaki ci gaba da bani idan na biyeki, banda haka ta yaya ga dama ta samu amma kina neman misusing opportunity din, did you even know what you are saying?shekara daya kacal fa ya rage maki Khaleesat? Dropout kike son ki zama ko me? Ai wani abun mutum ba shi yake bargaining ma kansa hakan ba, you never bargained for all this Khaleesat, situation ne kawai, kina tunanin har a tashi duniya akwai ranan da Yaya Jawwad zai bude baki yace ai ya dau nauyinki a makaranta? Kina ganin Jawwad yayi kama da mutumin da zai maki gori wataran? Ai wallahi daga shi har Cousin dinsa sun girmi hakan, they are too classy for that, Kin zata kowa mahaukaci ne mara aikin yi kamar Abdul? Haba wallahi har kin bata min rai, ban taSa tunanin zaki nemi kiyi turning down din offer dinsa ba, shi fa taimako kawai yayi saboda yana da halin yin hakan, duba da kin kusa gamawa kuma yasan duk abinda ya sameki, amma sbda rashin tunani irin naki kina neman gwalesa, i was thinking zaman da kika yi da Abdul zai sa ki Wan canza wasu tunaninki marasu ma'ana, ko kuma in ce Childish tunani" Ita dai Khaleesat hawaye kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login