Showing 207001 words to 210000 words out of 241367 words

Chapter 70 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1619

Farida now" Safiyyah ta zaro ido tace "Me ya faru?" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "Kawai ce min tayi Housemate dina yaje can gidanmu jiya" Safiyyah ta wani kalleta, can tace "Don Allah ji yanda kika sa gabana ya fadi na zata mutuwa aka yi a gidan naku, to don ya je gidanku sai ki fara kuka? Ko dai dama akwai abinda ke damunki kike son kiyi kukan amma sai yanxu kika samu sarari?" Khaleesat ta girgiza mata kai, wasu hawayen na taruwa idonta tace "Gida wai ya siya ma Abbana" Safiyyah ta bude baki da mamaki tana kallon Khaleesat, can ta dafe kirji tace "Gida fa Khaleesat?" Khaleesat ta kasa cewa komai wasu hawayen na sauka idonta, ta bude wayarta ta shiga chat dinsu da Aunty Farida ta tsaya dai dai wajen videos din ta mika ma Safiyyah wayar, Safiyyah was speechless for almost 2 minutes bayan ta gama kallon videos din gidan, wato gida ne har gida irin na zamani that is well furnished, a hankali Safiyyah tace "I am short of words too Khaleesat, wallahi ban san me zan ce ba, but just know that ur Housemate is one in a million Khaleesat...." Khaleesat ta fashe da kuka, Safiyyah ta rungumeta soothingly tace "It's something to be happy about ba kuka za ki yi ba, yanda ya saka iyayenki farin ciki Allah Ubangiji ya dawwamar da shi cikin farin ciki na har abada, Allah ya saka masa da mafificin alkhairi, ya biya masa duk bukatansa na alkhairi, yanxu kina komawa gida sai ki nutsu ki kirasa" Cikin kuka Khaleesat tace "Ko na kirasa baya picking" Safiyyah tayi shiru, can tace "May be he have his reasons Khaleesat, just compose a text for him sai ki tura masa ta WhatsApp, and i will also thank him via WhatsApp on ur behalf, duk wani abun farin cikin ki nawa ne nima...." Ita dai Khaleesat ta kasa cewa komai but she is soo emotional, ta kasa daina kukan da take, a haka driver ya zo daukanta, Safiyyah ta rakata har inda yake parking ta bude mata back seat tace "Don Allah kar ki je gida kina wannan kukan, wannan ai abun farin ciki ne ba na bakin ciki ba da zaki yi ta kuka har haka" Khaleesat ta gyada mata kai kawai tana share hawayenta, Safiyyah ta daga mata hannu tace "Anjima zan kira ki in sha Allah" Nan ma dai kawai kai Khaleesat ta gyada mata a haka drivern ya ja motar suka bar wajen. Bayan sun isa gida Khaleesat ta bude kofar parlor ta shiga da sallama can kasa, kanta a kasa ta gaida Ajay da ta gani zaune parlor da Salem, sannan ta wuce sama, sau daya Ajay ya bi ta da kallo sai kuma ya dauke kansa, after some minutes yana kallon Salem yace "I am going up to get some rest, will you still be around?" Salem yace "Ohk i will wait har ka sakko" Mikewa Ajay yayi ya dau wayarsa sannan ya saka House Slippers dinsa ya wuce sama, kofar dakin da take ciki ya tsaya yayi knocking, Khaleesat da ta kwanta gefen gado ta dora kanta saman pillow feeling so emotional ta mike zaune tana kallon kofar, yana bude kofar ta fara goge sauran hawayen idonta, ya shigo closing the door behind him yana kallonta yace "What happened?" Sauke idonta tayi bata ce komai ba, yace "Ba kya ji na ne?" Girgiza masa kai tayi a hankali tace "Ba komai" Yace "Bakomai zaki shigo ma mutane gida kina kuka?" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, yace "Sake kula ki yayi a school din ne?" Ta daga kai ta kallesa ta girgiza masa kai cikin sanyin murya tace "A'a, kawai kaina ne ke min ciwo" Daga sama har kasa ya kalleta sannan yace "Kukan ya baki magani" Daga haka ya juya ya fita daga dakin.... Wajen karfe biyar Khaleesat ta farka daga baccin da ya dauketa tun bayan da Ajay ya bar dakin, da yake ba sallah take ba, mikewa zaune tayi ta jawo handbag dinta a hankali ta bude ta ciro wayarta, number Housemate dinta da bata kara saving ba har sannan tayi dialing hoping he will pick her call today, amma har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma bai daga ba, to yanxu me ma zata ce masa ta WhatsApp, words failing dinta kawai za su yi in ma tace tayi masa magana ta can, bata ma san ta yaya zata fara ba, Waga kai tayi ta kalli kofar dakin jin ana knocking, sai da aka sake knocking din sannan ta sauka daga kan gadon tana tafiya a hankali ta tafi ta bude kofar, daya daga workers din gidan ne rike da tray din abinci, mamaki tayi don tun zuwanta gidan babu worker din da ya kawo mata abinci har daki, infact ita ce ma ke girka abinda take ci a gidan, ta dai amshi tray din cikin sanyin murya tace "Thank you" Sannan ta juya ta koma daki, bayan ta ajiye tray din ta bude plate din dake rufe a kai taga Jollof rice ne yana tiriri alamar yanxu aka gama girkin, ga wani aroma me dadi na tashi, ta bude wani plate din taga full chicken laps biyu anyi grilling dinsu, sai kuma bowl din veggies da dressing dinsu a gefe, with 2 bottles of water and a glass cup da can drink, still a kan tray din taga maganin ciwon kai, a hankali ta dau spoon ta goge sa da tissue din da aka yi wrapping dinsa sannan ta fara cin abincin, kuma sosai abincin yayi dadi, ya kuma yi yaji kamar a Nigeria aka yi, ta dai ci abinda zata ci ta ajiye sauran for dinner. Washegari still haka aka kawo mata breakfast har daki, bacci ma take tunda ba school zata je ba ta sauka kan gadon ta saka hijab sannan ta bude kofar, bayan ta amshi tray din ta kulle kofar dakin ta tafi ta ajiye breakfast din don sai ta fara wanka.... Wajen karfe biyar din yammacin ranan Ajay na parlor tare da Salem aka bude kofar parlon, tun da ta shigo Ajay ke kallonta da wa enda ke biye da ita a baya, wato jakadiyarta da aminiyarta Hajiya Usaina, sai er aminiyarta da bazata wuce 25 years ba, Salem ya mike tsaye yana welcoming dinta da ladabi, ta amsa masa sama sama without looking at him, sai da ta zauna parlon bayan jakadiyarta tayi saurin gyara mata throw pillow sannan Ajay ya gaisheta, ta amsa cike da isa tace "Daga Massachusetts Boston mu ke, mun je convocation din Afrah a Havard University, we will be passing the night here before leaving for Nigeria tomorrow" Ajay dai bai tanka ta ba, ya gaida aminiyarta warce convocation din er ta suka je a Havard din, Afrah dake ta kallonsa ta gaishesa, ya amsa without looking at her sannan ya mike ya nufi sama, shi dai Salem ya juya ya fita daga parlon, Ajay na haurawa sama direct dakin da Khaleesat take yayi knocking sannan ya bude kofar.
[7/15, 9:49 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Khaleesat dake karatu da Laptop dinta ta juya tana kallonsa, a takaice yace "Don't look at me that way, ki dau duk wani abinda zaki bukata yanxu zaki koma dakin Jay don muna da baki a gidan...." Ko rufe baki bai yi ba aka bude kofar dakin, ta madubin dakin yake kallonta don tsayuwa tayi bakin kofa tana kallon Khaleesat with mouth agape, Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "Ina yini...." Aunty ta karaso cikin dakin da mamaki tana kallon Ajay tace "Junaid? Wacece wannan kuma?" Ba tare da Ajay ya juya ya kalli inda take ba a takaice yace "Kanwar Salem" da wani expression Aunty tace "Kanwar Salem? Me take yi a gidan nan? Kuma a cikin daki zaune a saman gado?" Sai a sannan Ajay ya juya, looking at her in the eyes yace "The apartment she was staying was sold out yesterday, and she is homeless, so she is here for today before moving to her new apartment tomorrow...." Aunty tace "Da iznin wa kayi hakan? Dama gidan ka ne nan din da zaka yanke hukunci kanka tsaye kamar me gidan? I can't remember his Highness saying this house is urs in anyway Junaid, baka da right, sannan iyayenta da suka turota karatu basu nema mata wani alternative ba sai kai sarkin Hausawan Nigeria dake Baltimore? Beside ban ga ta inda take kama da Salem ba, Salem da yake baki me ya hadasa da wannan farar yarinyar? karya kake yi daya daga matan banzan da kake iskancin ka da su ne a kasar nan, ka zata duk bamu san abinda kake yi ba ne?" Calmly Ajay yace "You can say whatever, kawai dai ni dai i also can't remember Abba saying we are to share this house with you and ur visitors, saboda ni da Jawwad Abba ya siya gida a garin nan ba don kowa ba, don haka ban ga dalilin da za ki dinga zuwa da wasu mutane can babu notice ba ki maida mana gida gidan saukan baki, kaf Massachusetts babu hotels da dole sai kin taho Maryland za ki samu masauki? Beside all this... u are not even in the rightful place to tell me what to do and what not don da sunana da na Jawwad Abba ya siya gidan nan, don haka babu ruwanki da duk wanda zan kawo gidan, since you can't do without intruding, ki zo kiyi intrusion dinki in peace kiyi tafiyarki without questioning me...." Aunty da ta bude baki tana kallonsa tace "Zagin nawa da ka saba zaka yi Junaid? Ni kake gaya ma bakaken magana? Rashin kunyan da ka saba yi min zaka yi a nan ma?" Ajay yace "Whatever, all i know is that u can't just be appearing in here without notice tare da wasu mutane can kina inconveniencing din mu kina sa mana ido" Wani murmushi kawai tayi ta kalli Khaleesat sannan ta juya ta fita daga dakin, gaba daya jikin Khaleesat yayi sanyi ta kasa motsi a inda take, after few seconds ta sauka daga kan gadon tana kallon Ajay da ya kafe ma dressing mirror ido yasan fitar da tayi Abba zata je ta kira, cikin sanyin murya Khaleesat tace "Why will u speak to her that way Ya Junaid?" Ya dakatar da ita fuska daure yace "Ba ruwanki Malama, kin san ta ne?" Khaleesat ta sauke idonta bata sake cewa komai ba, ya juya ya fice daga dakin yana birkita gashin kansa, ga wani zafi da yake ji, where is he even going to start explaining this to his dad for the second time, gashi Jay baya gidan just him and the lady in the house, wani bayani zai yi ma Abba da zai yarda da shi? Sangarensa ya nufa ya zauna gefen gado ya dafe kansa da yaji yayi masa nauyi, in mahaifiyarsa ce ai sai dai su kashe su rufe tare da ita without her involving his dad in this issue, infact baza ma ta so wani yaji ba, he felt soo emotional, Aunty na komawa downstairs ta zauna kan kujera ta jawo jakarta ta ciro wayarta, Hajiya Usaina dake kallonta tace "Ya naga ranki a bace Fulani?" Aunty tayi wani murmushin takaici tace "Bari dai inyi waya da mai martaba tukunna Usaina" Tana fadin haka ta tafi dakin da take sauka ta tarar da jakadiyarta a ciki tana ta faman goge goge duk da dakin fess yake, zata fita Aunty ta mata alamar ta ci gaba da abinda take, sannan ta zauna kan kujera tayi dialing number mai martaba tana girgiza kafa at the same time tana fatan Allah ya sa ya samu damar daga kiran don zuwa yanxu dai tasan yana Sangarensa shi kadai, ai ko babu jimawa ya daga kiran, bayan sun gaisa cikin ladabi da kwantar da murya tace "Allah ya taimake ka ya ja zamaninka, mun iso Maryland babu dadewa yanxu" Daga daya bangaren yace "To maa sha Allah fulani..." Ta kara yin kasa da murya tace "Amma Allah ya ja zamaninka ban ji dadin abinda na zo na tarar a gidan nan ba" Shiru Mai martaba yayi bayan yaji me tace, don tana fadin haka babu abinda ya fado masa sai abinda ya gani dakin Ajay kwanaki da ya sauka Baltimore, Jin Mai martaba yayi shiru Aunty tace "Ko kana tare da baki ne ranka shi dade babu sararin mu yi magana?" Calmly Abba yace "Ina sauraron ki" Aunty ta gyara zama tace "Mace na zo na tarar a dakin Yarima cikin wani yanayi mara dadin fade, hankalina yayi matukar tashi ranka shi dade, na dimauce ba kadan ba da abinda idona ya gane min, ban ji dadin hakan ba ko kadan wallahi, kuma da alama ba wannan bane karo na farko, ya saba yin hakan, Allah Ubangiji ya shirya mana su kawai" Mai martaba yayi shiru don sosai yaji abinda ta fada ya dake sa don har sai da ya jingina kansa da kujeran da yake zaune, tayi kasa da murya tace "Amma ba komai ranka shi dade kar hakan ya sa kaji babu dadi a ranka ko kuma ka damu, in sha Allahu idan na dawo sai mu san abun yi, mu san inda za mu billo ma lamarin don baza mu zuba ido a ci gaba a haka ba, kaga wannan big slap to our faces ne idan aka samu labarin abinda yake yi a kasar nan, hakan zai zubar mana da reputation din masarautarmu ne kawai, shi yasa kwanaki nace maka a samu yarinya me hankali da nutsuwa er manya a aura masa ko da kuwa ba er gidan sarauta bace, sai naga kamar hakan bai gamshe ka ba tunda baka ba maganar tawa muhimmanci ba na lura baka son yi masa dole ne, ni kuma abinda yasa na kawo wannan shawaran shi ne saboda shi Yarima ba kula yan matan yake ba a gida Nigeria" Cikin nutsuwa mai martaba yace "Bangaren nasa kika je?" Aunty ta Wan fara kame kame tace "Ehh can na je ranka shi dade, gani nayi tunda muka shigo gidan ga dai motarsa amma shiru bamu gan sa ba, da yake kwanaki ai ya Wan yi zazzabi saboda weather sai nayi tunanin to ko baya jin dadi ne, sai na karasa bangaren nasa, shi ne fa idona yayi mummunan gamon nan" Mai martaba yace "If possible try conversing with the lady u saw ki ji er wace jaha ce a Nigeria, ina son sanin background dinta, just Converse with her Fulani...." Aunty tayi shiru bayan taji me Mai martaba yace, can tace "Ranka shi dade ai ba er Nigeria bace matar, baturiya ce fa, kuma irin tsofaffin turawan nan, da kyar ma in bata haifesa ba" Mai martaba ya sauke ajiyar zuciya yace "Na fahimta" Aunty tace "Yanxu dai idan na dawo za mu tsara komai ur Highness, ka kwantar da hankalinka, in sha Allahu anyi na karshe, we will put a stop to this soon, kuma ko makusantan ka na fada don Allah kar ka gaya ma wannan magana, don ba magana bace da ya kamata ace ya fita" Mai martaba was quite, don tunanin da yake yi ma shi daban, daga karshe Aunty tayi masa sallama ya katse wayar, tana kallon jakadiyarta dake zaune kasa tayi murmushi tace "Mace na samu a dakin ba?i, amma ban san tun yaushe take zaune gidan ba ya dai ce min jiya ta zo gidan, sannan babu cin mutuncin da ya mance bai min ba" Jakadiya ta kara bajewa a kasa tace "Ja'iri, gaskiya ya kamata wannan karan ki dau mummunan mataki akan sa ranki shi dade kar ki dau lamarin da wasa, abubuwan da yake maki sun isa haka, duk baya ganin mutuncin ki kuma wannan abu na saka ni damuwa uwar gijiyata, yanxu dai kamata yayi ki kira daya daga ma'aikatan gidan ku kebe ki tambayesa ki ji tun yaushe ya ajiye yarinyar a gidan nan..." Aunty tayi wani murmushi tace "Kin kawo shawara kuwa...." Mikewa tayi ta fita daga dakin Jakadiya na jero mata kirari.... Bayan wani lokaci Ajay ya fito dakinsa ya tafi dakin da Khaleesat take, without looking at her yace "Ina jiran ki downstairs" Daga haka ya fita daga dakin, har zai sauka kasa ganin su Aunty a parlon ga uban kayan ciye ciyen da aka baje masu a tsakar parlon, sai kawai ya tsaya a corridor, a hankali Khaleesat ta mike tsaye ta dau Hijab dinta ta saka ta bude kofar dakin ta fito, yana jin alamar ta fito ba tare da ya juya ba yace "Mu je, kuma ban ce ki ce zaki gaida kowa Downstairs ba" Daga haka ya fara sauka kasa tana biye da shi a baya jiki a sanyaya, tun da suka sauko Aunty da kawarta da Afrah ke kallon Khaleesat, Ajay dai ko kallonsu bai yi ba ya nufi kofa Khaleesat na biye da shi ita ma bata yarda ta kalli direction din su ba, gun motarsa taga ya nufa ya bude ya shiga, ta karaso gun motar ganin bata shigo ba ya daure fuska yace "Baza ki shigo ba?" A hankali ta bude seat din ta shiga, yana kallonta yace "Haka kika fito baki dauko komai ba?" Tayi shiru, sai kuma tace "Ai baka ce min in dau komai ba" Tsaki ya ja ya bude motar ya fita ya koma cikin gidan, ita dai ta bi sa da kallo, dakin da take ya koma ya dau laptop dinta da charger sai wayarta shima da Chargern sa sannan ya fita daga dakin yayi locking kofar yanda ba wanda zai bude ya sauka downstairs, nan ma su Aunty suka bi sa da kallo, Afrah kamar idanuwanta za su bi sa har compound din.... Har Ajay ya isa apartment din Khaleesat bai ce mata komai ba, ita ma dai tayi shiru da tunani iri iri a ranta, kana ganinta kasan duk a sanyaye take, bayan sun sauka motar ya nufi entrance din shiga apartment din ya ciro makullin a aljihunsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login