Showing 84001 words to 87000 words out of 241367 words

Chapter 29 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1597

matar ta sake dawo mata, gani take tana cin abu zata yi aman da bata yi ba daxu, gyara kujeranta tayi ta kwanta ta lulluba da blanket din da jirgin yayi providing for business class passengers, nan da nan bacci ya dauketa, da za su sauka Turkey wajen karfe hudun asuba sai da wata Flight Attendance daban ta zo ta tasheta ta sanar mata jirgi zai sauka, Khaleesat ta mike zaune da kyar don ciwo kanta ke mata, tayi fastening seat belt dinta, bayan sun sauka Istanbul ta bi AJ da kallo har sai da ta daina hangosa sannan ta mike ta dau handbag dinta da waya ta bi bayansa tana tafiya da kyar leaving her Amenity kit behind, jiran awa biyu za su yi a Business Class waiting lounge na airport din kafin a canza masu jirgin da zai kai su Nigeria, ta riga AJ shigowa lounge din kilan masallaci ya tafi, ita ma tana ganin lokacin sallahn asuba yayi ta tafi tayi sannan ta dawo ta zauna a business lounge din, after like 15 mins sai gashi ya shigo, not far away from her ya zauna da ruwan gora a hannunsa, Ita dai ta jinginar da kanta jikin kujeran da take zaune ta daura handbag dinta a kafarta, she is having a terrible headache a lokacin, after almost 30 mins of sitting wani Wan Nigeria ya dawo kusa da ita ya zauna, wanda shi ma daga nan Turkey zai je Nigeria a Business class, kuma jirginsu daya kamar yanda ta ga ticket irin wanda ta amsa bayan sun sauka Istanbul din a hannunsa shima, yana kallonta yayi mata sallama cikin nutsuwa, ta Wan kallesa sannan ta amsa, yace "Guess you are coming from America right?" Tace "Uhm" Yana kallon Flight ticket dinta yace "Oops you are having the same name as my Mum, can i call you Jiddah instead of the real name?" Khaleesat dake sauraronsa without looking at him tace "Ohk" Yana murmushi yace "Alright, are you traveling alone Jiddah?" Ta girgiza kai tace "No" Ya buda ido yace "Ohk with who?" Ta kalli direction din AJ, shi ma mutumin ya kallesa suka hada ido don kallonsu kawai Ajayn yake yana jin conversation dinsu, mutumin na murmushi ya tashi yaje ya gaisa da AJ sannan ya koma ya zauna, shikenan Khaleesat ta samu lafiya, don bai sake ce mata komai ba kawai danna wayarsa yake tayi tunda shi dai bai san ko waye Ajayn a gunta ba, daga karshe ma ya tashi ya bar wajen, at last aka fara boarding din jirgin da zai kai su Lagos Nigeria daga Istanbul, Usman ya juya ya kalli Khaleesat da ta mike tana rike da handbag dinta, har AJ ya wucesu sai kuma ya tsaya amma bai juyo ba, ita dai tana tafiya a hankali har ta isa inda yake tsaye sannan ya ci gaba da tafiya tana biye da shi, har jirgi ya tashi Usman dake zaune not far from Khaleesat but close to AJ bai ce mata komai ba, this time around ma dai bacci kawai tayi har zuwa Nigeria. Karfe hudu saura suka sauka Nigeria washegari Friday, ita dai Khaleesat tun da ta ganta Lagos bayan ta gama da Custom da Immigration ta fara tunanin kuma yanda zata yi, to ko dai kawai ta tafi gidan Aunty Farida tunda a nan Lagos take, to ko tace zata je bata da sim din da zata kirata don ba gane anguwan zata yi ba kuma bata da lambarta a kai balle ko waya ne ta ara ta kirata a airport din, sai kuma tayi tunanin kiran Ummanta tunda tana da numberta a kai sai tace ta turo mata number Aunty Farida, gun wata mata warce taga kamar Bahaushiya ce ta nufa, ta gaisheta sannan tace "Don Allah Aunty wayarki zaki ara min in Wan yi kira nawa ba caji" Matar ta fara kallonta daga sama har kasa, sai kuma ta bude handbag dinta ta ciro wayarta ta mika mata, Khaleesat ta amsa tace "Nagode" Dialing number Umma tayi ta kira taji a kashe, sosai jikinta yayi sanyi, ta kira har sau uku duk ana ce mata a kashe, a hankali ta zame wayar a kunnenta ta mika ma matar tace "Nagode, wayar ma a kashe yake" sai da matar tayi dialing wayar ta tabbatar eh a kashe din yake, kana ganin matar kasan she is not comfortable giving off her phone, Khaleesat na jan trolley dinta a hankali ta fito daga cikin airport din tana tunanin yanda zata yi, ko dai kawai ta tafi tashan da zata samu mota zuwa kano, since she have some money in her bank account, wani mutumi ne taga ya nufota, ya gaisheta da ladabi yana mata barka da zuwa, sannan ya nuna mata mota yace "Ke mu ke jira ki fito dama" She was looking at him with confusion, can ta kalli motar, shi ko har ya amshi Akwatunanta yayi booth din mota da su, sannan ya dawo ya bude mata back seat, zata yi magana sai ta hango AJ zaune front seat din motar, ta Wan yi jim, sai kuma ta fasa cewa komai, ta tafi ta shiga motar, hotel drivern ya kai su kasancewar next available flight to lagos na karfe bakwai na magrib ne, dakin da aka biya mata na downstairs, shi kuma AJ sama taga ya tafi, All this while kuma bai ce mata komai ba, ita dai tana son ce masa ta gode amma bai bar space din hakan ba, ko tsayawa bai yi ba balle tayi godiyan, sai da driver din ya amshi passport din ta da zai mata booking din jirgi tare da AJ zuwa kano sannan ya bar hotel din, bayan Khaleesat ta shiga dakin babu dadewa aka kawo mata lafiyayyen lunch, duk da tana jin yunwa bata iya ta ci da yawa ba she is just restless, taje bandaki ta wanke baki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, bayan ta saka wasu kayan tayi sallah sannan ta dau handbag ta bude zata ciro lip gloss dinta, a nan taga kudin da Jay ya saka mata, ta dinga kallon kudin ko kiftawa bata yi a sanyaye. Karfe shidda da yan mintuna drivern ya sake zuwa ya daukesu ya maida su airport, daga nan kuma suka hau jirgi zuwa garin kano, inda suka sauka airport din Aminu kano karfe tara saura na dare, this time around ma sai da drivern da ya zo daukan AJ ya sauka yayi mata magana tare da kai akwatunanta booth, ita dai tana ta tsaye don taxi kawai ta so dauka da zai kai ta gida, ganin drivern ya bude mata back seat ta karasa jiki a sanyaye ta shiga motar, sai da suka fita daga Airport din drivern ya kalleta ta madubi yace "Ranki shi dade wani anguwan za a ajiye ki?" Khaleesat ta Wan kalli AJ dake zaune gaban motar yana danna wayarsa, sai kuma ta kalli drivern tace "Inda zan je da nisa, kar in bata maku lokaci gashi dare yayi, duk inda ka samu kawai ka ajiye ni zan samu abun hawa" Sai a sannan AJ yace "Ce maki yayi sauri yake?" Khaleesat tayi shiru, sai kuma tace "Ni Mariri zan je" Driver yace "Toh Allah ya kai mu lafiya Hajiya" Bayan tafiyar kusan minti arba'in suka iso Maririn, A hankali Khaleesat dake kallon drivern tace "Zan iya sauka a nan sai in karasa cikin layin saboda kar ku shiga baku samu wajen juyawa ba...." Drivern yace "Layin baya bulla ne? In dai yana bulla babu damuwa za mu samu hanya in sha Allah" Tace "Toh shikenan, nagode" Nan ta nuna masa inda zai bi ya shiga unguwan, shi dai AJ kallon ikon Allah kawai yake without uttering a word, haka jama'an anguwan suka dinga bin motar da ya dalle ko ina da haske da kallo, ba ko wani mai mota bane zai yarda ya shiga hanyar nan da motarsa cause driving is uncomfortable there in baka yi hankali ba sai ka goge motarka, gashi gidan nasu can ciki ciki ne, at last dai tace "Kawai in ka samu waje a nan zan sauka, ga gidan can" Drivern yace "Toh shikenan Hajiya" Haka ya samu yayi parking motar, sannan ya sauka zai dauko mata akwatunanta a bayan booth, ta bude motar ta sauka tana kallon kofar gidansu hankalinta ya Wan kwanta ganin bata ga Babanta a kofar gidan ba, kan kace me yara yaran anguwan da suka ga ita ce a motar suka taho da gudu ana mata oyoyo, haka dai ta samu ta hadasu da akwatunanta sannan ta zaga zuwa side din da Ajay yake, tana wasa da gefen gyalenta ta kasa kallonsa tace "Thank you so much Allah ya saka da alkhairi" yace "Wanda ya hada ki jirgi daya da ni zaki ma godiya, Jay kenan" Sai a sannan ta Wan kallesa, bata dai ce komai ba ta juya tana tafiya a hankali ta bar wajen, godiya tayi ma drivern ta masa kwatancen unguwan da zai shiga wanda a nan zai samu hanyar billa zuwa titi, yayi mata godiya shima ya shiga mota sannan ta nufi cikin gidansu gabanta na faduwa, a hankali tayi raising sack din cement that was use as barrier between the door and inside of the house zata shiga cikin gidan ta ci karo da kanninta da suka fito yi mata oyoyo da gudu bayan yara sun shiga da akwatunan ta, a haka suka shiga cikin gidan tare tana Rungume da su, zazzaune taga kishiyoyin ummanta biyu da 'ya yansu rakacaa a tsakar gidan har a lkcn ba a sauke tuwon dare ba gashi ana neman karfe goma, kananun yaransu ne kawai suka taso yi mata oyoyo da gudu, muryar wata makociyarsu dake zaune cikin gidan taji tana cewa "Ikon Allah sannu da zuwa Amarya ashe dai kina hanya dama" Khaleesat dai kallonta kawai take jin abinda tace, taji kishiyoyin ummanta na cewa "Ai ko dai, kinga mu da muke gidan ma ko gaya mana ba ayi ba balle mu shiga mu fita tahowar nata ya fasu, kinsan haka aka maida mu a gidan, to ga dai ta mun ganta kamar an jefota, mun kuma yi murna" Khaleesat ta gaishesu without waiting for response ta shige dakin Ummanta, zaune ta ganta a bakin kofa Umma dake kallonta cike da damuwa tace "Khaleesat me ya samu wayarki kusan wata daya? Dama kina hanya shine Abdul din bai gaya mana ba?" Khaleesat ta rungumeta a hankali tace "Umma lalacewa wayar yayi" Umma ta dago kanta tana kallonta tace "To shi ya dauko ki a tashar jirgin?" Khaleesat ta sauke idonta tace "A'a" Muryar kawar Ummanta da taji a dakin yasa ta daga kai don bata ma san tana ciki ba, Khaleesat ta gaisheta da murmushi, Mama Salame ta amsa da fara'a tace "Ashe dai kina hanya amarya" Khaleesat tace "Amarya kuma Mama?" Mama Salame tace "Au shi Awdul din bai gaya maki ba dama, ai yau ana saukowa sallan juma'a aka daura auran ku"




*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 =?H? [5/26, 9:48 AM] khaleesat Haiydar =???
'?: Khaleesat ta kwala wani karan da ya gigita Ummanta da Mama Salame, Umma ta mike da sauri tana kallonta a kidime, haka ma Mama Salame da tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, menene haka Khaleesah?" kishiyoyin Umma duk suka yo dakin a guje su ma don Khaleesat bata fasa ihun da take kwalawa ba cikin tashin hankali take cewa "Wallahi bana son shi bazan iya zaman aure da shi ba, na shiga uku na lalace, don Allah Umma ku min rai ku rufa min asiri, wallahi bana son sa" Umma dai sake baki tayi tana kallon Khaleesat tashin hankali karara a fuskarta gashi ta kasa cewa komai, daya daga kishiyoyin Umma da ake kira Mama Shatu tana gyara zaninta da ya kusa kwancewa saboda gudun da suka yi tace "Ji wani gulma da kinibibi? Shi Abdul din ne da ya daukeki ya kai ki kasan turai karatu yayi ta kashe kudadensa ne baki so yau? A ajiye batun ubanki a gefe, ke abinda ya kashe maki yau ko kaf kasar da uwarki ta baro za a siyar za a iya biyansa aka ce maki?" Ita ma daya Co-wive din da suke kira Mama Zubaida tace "A'a rainin wayo mana Shatu, gwara ai a rena mana hankali, don uwarta kasuwa ne nan da zata cika mana gida da ?uwa, wannan ai iskanci ne da walakanci" Khaleesat bata fasa kuka da ihun da take a dakin Ummanta ba tana surutai ita kanta bata san takamaiman abinda take cewa ba tsabar tashin hankali, Kanninta Noor da Islam kuwa har sun fara kuka su ma a dakin, kan kace me har makota sun fara tururuwan shigowa gidan, aka tsaya cirko cirko bakin kofar dakin Ummanta ana salallami, Mahaifinta ne Malam Ali ya shigo gidan yana zazzare ido, shi ma ya karaso da sauri yana tambayar abinda ke faruwa a gidan, Mama Shatu ta tabe baki tace "Wai er da ta fi kowa ce ta sauka yau daga Amurka shine uwar ke sanar mata ai an daura aurensu da shi wanda ya kai ta waje karatu har ta dena ganin kowa da gashi, shine fa ta cika anguwa da ihu da koke koke wai ita bata son auren bazata zauna da shi ba, ga jama'a na ta shigowa an zata gobara muke, wannan ai tsabar sangarci da iya shege ne" Juyawa Malam Ali yayi ya nufi gun da ake ajiye itacen girki da sauri ya suri daya ya dawo ya nufo dakin Umma yana cewa "Ina take..." Matan makota dake tsakar gidan suka hau basa hakuri suna don Allah ya kyaleta, yaki sauraron kowa yana zazzare ido, Khaleesat na hangosa ta tafi bayan Ummanta da gudu tana kuka ta rungumeta, kanninta ma suka yi bayan Umma gaba daya suna kuka, Mama Salame ta tsaya tayi bake bake gabansa tace "Haba haba, haba Malam Ali, meye haka kake kokarin yi?" Yace "Salame ki bar ni dai inci malfar ubanta a wajen, mu zata tona ma asiri? Ni zata ja ma sabon bala'i da fitinan da ya girmeni?" Mama Salame tace "A'a wallahi baza ka doketa da wannan rafkeken icen ba ita ba jaka ba, mu je waje Malam Ali" Ita dai Umma kanta na kasa bata ce komai ba, haka Mama Salame ta samu ta tasa keyarsa ya fita daga dakin tana biye da shi, Mama Zubaida ta rike haSa tace "Ikon Allah, mu muke ganin kinibibi iri iri a gidan nan, to in aka bibiya wani ta kyallara ido ta gani a Amurkan shine zata tona ma uban asirinsa da ke rufe, da can menene yasa ta hakura zata aurensa? Sai ranan da aka daura aure ta nemi tara mana mutan anguwa tace bata san zance ba? Yau ni nake ganin iskanci, to ta tsotsi nonon buzuwa ba dole ta iya makirci da kissa ba" Ita dai Khaleesat kuka kawai take a jikin Ummanta siblings dinta na kusa da ita suna taya ta, Mama Salame ta sake labulen dakin Umma duk don matan dake tsaye bakin kofar su kama gabansu, Umma ta juya tana kallon Khaleesat gaba daya ta kasa cewa komai, zamewa kasa Khaleesat tayi ta hade kanta da gwiwa tana kuka kamar ranta zai fita tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace" a sanyaye Umma ta tafi gefen katifar dakin ta zauna ta kasa cewa komai. Karfe biyun dare Umma na zaune kan darduma da carbi a hannunta, Khaleesat ta tsallake kanninta ta fito daga cikin net din da take kwance bayan ta tuna ko isha'i bata yi ba, tunda Mama Salame ta daura mata net tace ta shiga ta kwanta wajen karfe sha daya take kwance duk da ba bacci take ba, don ko bacci barawo bata gani ba, amma tayi shiru cikin net din tunani iri iri na yawo a kanta, gaba daya ta ji kamar hawayenta ma ya kafe, har a lkcn babu maganar da ya hadata da Ummanta, tana jin jiri da zazzabi ta nufi kofa zata fita ta dauro alwala, Umma dai ta bi ta da kallo, bayan ta dauro alwalan ta dawo ta saka hijab dinta ta tada sallah, bayan ta idar tayi nafila raka'a biyu, tana zaune kan darduman ta jingina da bango tayi nisa tunanin da take, gani take kamar a mafarki ake sanar mata an daura mata aure da Abdul amma ta ki farkawa daga mummunan baccin nan har yanzu, muryar Ummanta yaji ta kirata a hankali, Khaleesat ta juya ta kalleta amma ta kasa amsawa, Umma ta mike ta koma kusa da ita ta zauna tana kallonta, cikin sanyin murya tace "Me ya faru kuma tsakaninki da Abdul din Khaleesat? Wani abun ya kara maki? Me yasa kika ce baki son auren?" Khaleesat ta fashe da kuka a hankali tace "Umma wallahi bana son sa, bazan iya zama da shi ba, in aka ce za a kai ni gidansa zan iya mutuwa wallahi, don Allah Umma ku taimakeni ku yi min rai" Umma ta kasa ce mata komai hawaye ya cika idonta ta fara gogewa da hijab dinta, Khaleesat ta daura kanta kan kafadar Ummanta tana kuka me tsuma zuciya tace "Don Allah ku taimakeni Umma, bazan iya ba wallahi" Umma ta rungumeta tana patting bayanta ita ma hawayen na sauka idonta amma bata iya ta ce mata komai ba, they sat there for almost 40 mins, jin tana sauke numfashi a hankali Umma ta gane bacci tayi, a haka Umma ta zauna wajen Khaleesat na jikinta don bata son tashinta har kusan lokacin sallahn asuba. Da safe wajen karfe tara Umma ta shigo dakinta rike da cup din kunu da kosai a roba, ta karasa kusa da Khaleesat dake kwance gefen katifarta ta ajiye mata sannan ta zauna cikin kwantar da murya tace "Ta so ki ci ko kadan ne Khaleesat" Khaleesat

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login