Showing 66001 words to 69000 words out of 241367 words

Chapter 23 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1566

Jay yace "Da gaske fa you are Heartless Junaid, ince maka yarinya ko tashi bata iya yi? Why are you like this pls?" AJ yace "But like seriously kai uban me hannunka yake da bazaka mata allura ba sai ni? Baka fi ni zama likita ba? Wato ni ne Wan iska ko?" Juyawa Jay yayi ya bar wajen ya koma sama, yana bude kofar dakin ya ganta duke kusa da kofar bandaki, ya karasa kusa da ita da sauri ganin yanda ta galabaita yace "Did you throw up?" Kai kawai ta gyada masa tana maida numfashi, gun da ya ajiye hot chocolate din ya tafi ya dauko mata yace "Pls ki sha ko kadan ne sai in baki magani" Ta girgiza masa kai, yace "C'mon Halysaah, kadan fa za ki sha" Yana rike da cup din don kar ya sakar mata ta zubar, a haka ta kurbi shayin kadan, sai da yasa ta kara sha sannan ya ajiye shayin ya dauko magani, tana ganin maganin ta fara girgiza masa kai da sauri don har taji wani aman zai taho mata, bude kofar dakin aka yi Jay ya juya, AJ ya gani tsaye bakin kofar yana kallonsu, Jay bai sake kallon inda yake ba ya maida dubansa kan Khaleesat yace "Pls ki daure ki sha Halysaah, ko baki son ki samu relieve?" Kara girgiza masa kai tayi hawaye ya fara sauka idonta, lallabata Jay ya fara yi akan ta sha maganin, AJ ya wani hade rai yace "Kee baza ki amshi maganin da ake baki ba? Wa zaki ba wahala?" Jay yace "Ba ruwanka pls AJ, get out" Ita dai Khaleesat ko kallonsa bata yi ba tana fama da kanta, Jay bai sake takurata kan ta sha maganin ba ya mike yace "Toh ki daure ki hau kan gado ki kwanta, i am coming now" Ta gyada masa kai, ya juya ya nufi kofa, ko kallon Ajay bai yi ba ya fita daga dakin, AJ ya tabe baki ya juya ya koma downstairs. Haka nan Jay ya hado alluran da za mata don saukar mata da zazzabin, sai da ta ga ya dawo dakin sannan ta daure ta koma saman gadon tana ganin jiri ta kwanta, ya tsaya gefen gadon yana rike da alluran yana kallonta, ta marairaice ta girgiza masa kai kawai alamar bata so, ya kwantar da murya yace "To ya kike son in maki Halysaah? Kin ki shan magani" wayarsa dake aljihunsa ya ciro jin yana ringing ganin Salem ke kiransa ya ajiye alluran hannunsa yace "I am coming Halysaah" Fita yayi daga dakin, ya sauka downstairs ya tarar da Salem zaune parlor, bayan sun gaisa Salem yace "Slide dina nake son zaka duba min Jay" Shi dai AJ na zaune yana kallon kwallo ga Legend a gefensa, Jay yace "Ohk, but tunda ka zo pls zaka yi injecting Housemate dita she is sick" Salem yace "Ayya, shi sa ta kira jiya, Allah ya bata lafiya, tana can gidan nata ne?" Jay yace "No, she is upstairs, mu je in nuna maka dakin da take" A tare suka wuce sama, AJ dai kallonsa kawai yake a TV kamar bai san suna parlon ba, Jay bai shiga dakin ba bayan ya nuna ma Salem ya dawo downstairs ya zauna, Khaleesat bata yi ma Salem wani musu ba don ba ma ta da wannan strength din duk da yanda bata son allura haka nan ta bari ya mata, tsabar zazzabin dake jikinta ko zafin shigar alluran bata wani ji ba, Salem yayi mata Allah ya sauwake sannan ya fita daga dakin ya koma downstairs, Jay yace "Thank you, bari in duba maka" Sai bayan kusan minti talatin Jay ya tafi dakin Khaleesat ya sameta tayi bacci, ya sauke ajiyar zuciya ya karasa kusa da gadon ya kai hannu kusa da goshinta sai dai bai taSa ta ba, nan yaji temperature dinta ya fara sauka, juyawa yayi ya dau sauran shayin da ta bari ya fita daga dakin..... Wajen karfe sha daya da rabi Khaleesat na kwance hannunta rike da wayar Housemate dinta, tun 20 min ago ta tashi daga baccin da ya dauketa daxu, she felt a bit relieved now da alluran da Salem yayi mata, sai dai har sannan kanta bai daina mata ciwo ba kamar ta cire ta huta, tayi kokarin ta tashi ma ta tafi bandaki amma ta kasa, she is so weak kamar warce ta dade tana ciwo, hakan yasa kawai ta jawo wayar Jay, da har zata shiga gallery dinsa to while away time amma sai taga it's not proper ta shiga hotunansa, hakan yasa ta shiga wani game da ta gani kawai tana yi daga kwancen da take, bude kofar dakin aka yi ta daga idonta, Jay ne ya shigo dakin AJ dake bayansa yaki karasowa ciki ya tsaya daga bakin kofar, Jay ya nufota yace "Ashe kin tashi, how are you feeling now Halysaah?" Ta gyada masa kai a hankali tace "Good morning" Yace "Morning Housemate, are you feeling much better now?" Kai kawai ta gyada masa, yace "Ohk bari a kawo maki breakfast, idan kinyi sai ki daure ki sha magani kin ji" Ita dai bata ce masa komai ba ya juya ya nufi kofa ya fita ya mika ma AJ wayarsa sannan ya sauka downstairs zai kawo mata breakfast, shi dai AJ daga sama har kasa yake kallonta, ta Wan saci kallonsa to see if he is still standing by the door ko ya tafi, hada ido suka yi ta dauke idonta tana ci gaba da game dinta da take, after a while ta kara satan kallon bakin kofar taga ya bar wajen, sai ga Jay ya shigo ya ajiye mata tray din breakfast ta dinga kallon plate din baked beans irin na turawa a gefe da soyayyen kwai a gefe, with veggies, sai sausages, ga cup din hot chocolate with few slices of bread a gefe su ma, ita dai tasan ba iya cin wannan abincin zata yi ba, yana kallonta yace "Can you give me ur frnd Safiyyah's Home address?" Ta sauke idonta ta gaya masa address din, yace "Ohk, na ma san area din, i have a frnd there" Ita dai tayi shiru, ya dauko mata maganin da taki sha daxu ya ajiye kusa da ita yace "Pls ki daure kiyi breakfast din, sai ki sha drug din kafin in dawo" A hankali tace "Toh nagode" ya mata murmushi ya juya ya fita daga dakin ta bi sa da kallo. Jay ya tarar da AJ zaune a waje gurin shan iska dake compound din yanna danna wayarsa, hakan yasa ya nufesa ya zauna kujeran dake facing dinsa yace "AJ, i think i am confuse at this point, what do u suggest about this young girl's issue?" AJ ya daga ido ya kalli Jay yace "My suggestion is that... ka barta ta tafi duk inda ma zata ka cire hannunka da bakinka cikin wannan case din babu abinda ya shafe ka, a cikin kunnenka kaji tace shi gayen ne ke sponsoring dinta, babu kuma ta yanda zai yi sponsoring dinta without the consent of her parent, kaga they are comfortable with that, so who are you to intrude Jawwad? Baka san komai akan ta ko kan saurayin ba don me zaka zakalkale haka? Tare fa ka gansu, da can baya zuwa America din ya sameta ne a gidan? sai yanzu tasan yana molesting dinta? Girl's can be very cunning fiye da tunaninka, don't start what u can't finish Jawwad" Jay dake ta kallonsa yace "So now what are you insinuating?" AJ yace "Since you are daft kar Allah ya sa ka gane abinda nake insinuating" Jay dai kallonsa kawai yake, after a while a hankali yace "But duba da abinda ya faru tsakaninka da guy din kasan zai iya hurting dinta idan nace ta koma gidan nan AJ, she is no longer safe in that apartment, ka dai ga ba ma cikakken hankali ke gare gayen ba, ka duba fa wuka yaje ya dauko a kitchen" AJ ya gyara zama yace "Sai kayi mata hanyar komawa gun iyayenta as the good Samaritan that you are from Samaria, kaga in ta koma sai ta gaya ma iyayen nata abinda ke faruwa da abinda selfishness dinsu ya ja mata a kasar mutane, sai su yi sorting kansu a can kawai" Jay yace "Kar kace haka, we know nothing about why they allowed him to sponsor their daughter, we shouldn't judge them har sai mun san dalilinsu AJ" AJ yace "Dalilin banza, babu responsible parent din da za su damka ma kato irin wannan mutumin er su ya kai ta wata kasa da sunan karatu, it doesn't even make sense, sai kace ba musulmai ba, ko da cousin brother dinta ne ma abun bai yi tsari ba balle babu ko wani relationship na jini tsakaninsu, who does that" Jay ya sauke ajiyar zuciya yace "Duk da haka dai ni bazan yi judging dinsu ba tare da nasan komai ba, let give them benefit of doubt" AJ yace "Sai kayi ta basu ai, ni kam bazan bayar ba" Jay yace "But komawarta Nigeria yanzu bazai yiwu ba AJ, ba shine solution ba, Monday za su fara exams, John Hopkins university take ita ma fa" AJ yayi dariya har da kyakyatawa yace "Tabb, lallai gayen ya kashe kudi ba na wasa ba" Jay dai kallonsa kawai yake, AJ yace "Toh za a fara exams me kake nufi kenan? Naji ka ce apartment din nata is not safe for her anymore..." Jay yace "She will remain here har su gama exam kafin ta koma Nigeria wajen iyayenta" AJ ya wani kallesa da sauri yace "What do you mean? Kana nufin mu zauna gida daya da balagaggiyar yarinya da ba muharramar mu ba kamar wasu jahilai marasu tsoron Allah? Kai da wa za ku yi wannan nonsense din??" Jay yace "Duk yan iskan turawan da kake kawowa gidan nan ka basu daki su zauna dama muharramanka ne ban sani ba?" AJ yace "Turawa kace ai, kuma babu komai tsakanina da su kai ma ka sani, i am only helping most of them tunda ba a garin nan suke ba" Jay ya mike yace "Ita ma haka za mu yi helping dinta tunda ba a garin take ba, take it or leave it" yana kai wa nan yayi wucewarsa inda yayi parking motarsa, Ajay ya bi sa da wani kallo, can yace "Sai dai ku je can ku biya wani apartment din ku zauna tare, babu wanda zai takurani a gidan nan wallahi, dama ai kun saba zama gida daya tare, it's not a new thing, dole ne sae ta zauna gidan nan cikinmu mu ba maguzawa ba" Shi dai Jay ya shiga motarsa ya fita daga compound din ya kama hanyar gidansu Safiyyah....


*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 =?H? [5/20, 5:24 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Jay na isa unguwan da gidansu Safiyyah yake sai ya mance apartment din da Khaleesat ta gaya masa, hakan yasa ya kira wayarsa dake wajenta, Khaleesat na zaune saman gado har sannan tana playing game da wayar, sosai gabanta ya fadi ta dinga kallon screen din wayar ganin image din hotonsa da number da yayi appearing, sai taga kamar shi din ne a gabanta take gani, sai da kiran ya katse ta zaro ido bayan tayi realizing bata yi picking ba har ya katse, bayan few seconds ya sake kira, dagawa tayi ta sa handsfree tayi shiru, yace "Halysaah" Tace "Na'am" Yace "I think i forgot the apartment u told me" Gaya masa ta sake yi yace "Thank you" Daga haka ya katse wayar ya ci gaba da driving dinsa, dai dai gaban apartment din yayi parking don motar Mustapha baya nan, yana tsaye bakin kofa yayi knocking gently, after a minute aka bude kofar parlon, komawa baya Safiyyah tayi tana kallonsa da mamaki daga sama har kasa, ya Wan mata murmushi yace "Hi Safiyyah" Ta bude ido sosai tana leka motarsa da taga yayi parking thinking may be he is together with Khaleesat, ganin motar ba kowa ciki tace "Hi, good afternoon" Yace "How are you doing Safiyyah?" ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????Lokaci daya tace "Ko dai Khaleesat bata da lafiya ne?" Da damuwa sosai tayi tambayar, Yace "Yeah bata da lafiya" Tace "Wallahi yanzu na gama shiryawa nake son in ci abinci inje gidan naga miss call dinta jiya ina ta kira har yau wayar baya shiga, and i am disturb" Yace "Shi yasa na zo in dauke ki idan ba damuwa so you can be together with her she is sick, probably idan kin mata magana zata ci abinci ta sha magani" Da sauri Safiyyah tace "Sure, bari in dauko gyalena" Juyawa tayi da sauri ta koma cikin gidan, shi kuma ya koma parking space, Surayya dake zaune a parlon ta kasa kunne duk tana jin conversation dinsu kafin Safiyyah ta shigo, Safiyyah ko kallon direction dinta bata yi ba ta tafi dakinta da sauri ta dauko jakarta da gyale sai wayarta sannan ta fice daga gidan, ganin Jay cikin motarsa yana jiranta ta bude gaban motar ta shiga tana cewa "Tun jiya ne bata da lafiyan? Kuma me yasa ta kashe wayarta?" Jay yace "Tace wayar ya fada ruwa ne" Safiyyah tace "Ohk" Sai da suka dau hanya sannan Jay yace "Amma tana can gidanmu fa, can za mu je yanzu" Safiyyah ta juya da sauri tana kallonsa da mamaki tace "Gidanku? Why? What happened?" Calmly yace "Before then za mu fara zuwa apartment dinmu sai ki dau mata kayanta da zata yi amfani da shi, we left yesterday with nothing" Safiyyah bata sake cewa komai ba tunani iri iri na yawo a ranta, to me ya faru? ta yaya Khaleesat da ta sani me shegen taurin kai ta yarda har ta bi sa can gidan nasu? Ko dai rashin lafiyar nata is critical ne haka? Da tunane tunanen nan suka isa apartment din, suka shiga ciki tare da Jay ta nufi dakin Khaleesat shi kuma ya zauna a parlor, bayan few minutes ta fito tace "Kala daya zan dau mata kayan ai ko?" Jay ya mike yace "No, 3 to 4 will be okay" Duk da confusion din da Safiyyah ta shiga bata dai ce masa komai ba ta juya ta koma cikin dakin, ta dau akwati ta saka ma Khaleesat kayanta da duk abinda zata bukata a ciki, tana fitowa daga dakin Jay ya mike yace "Kin dau mata duk abinda zata bukata?" Safiyyah ta gyada masa kai, suka fita daga parlon, duk ta kagu taje wajen Khaleesat ita dae, silently suka yi tafiyar har suka iso gidan, bayan Jay yayi parking ya sauka Safiyyah ma ta sauka, ya fiddo akwatin sannan suka nufi entrance din apartment din Safiyyah na biye da shi, bai ga motar AJ a gidan ba alamar ya fita, suna haurawa sama Jay ya tafi dakin da Khaleesat take yayi knocking, ya mika ma Safiyyah akwatin yace "Zaki iya shiga, zan je inyi sallah" Safiyyah ta amshi box din tace "Ohk" Bude kofar dakin tayi Khaleesat ta dinga kallonta har ta shigo, Safiyyah ta ajiye box din hannunta ta nufeta da sauri tace "Me ya sameki Khaleesat?" A hankali Khaleesat ta sauke idonta ta kasa cewa komai don bata ma san ta inda zata fara ba, sai ga hawaye. Safiyyah na tsaye dakin kusa da window bayan Khaleesat ta bata labarin duk abinda ya faru, tsabar yanda labarin ya kidima Safiyyah kasa ci gaba da zama tayi gefen gadon, Safiyyah tayi shiru for almost 2 minute tana tsaye jikin window tana girgiza kafa, ita dai Khaleesat goge hawayen dake sauka idonta kawai take, can Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya me cike da takaici tace "A baya da nake gaya maki Abdul Wan daba ne ba kin maida maganata abun wasa ba? Tunda uwata ta haifeni ban taSa ganin Wan iska kamar Abdul ba, yanzu da baki samu lambar kowa ba haka zai lalata maki rayuwa babu digon tsoron Allah a ransa? Ya kashe uban kudin zuwa USA kawai don ya zo yayi lalata? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, amma naji haushi da Wan uwan Housemate dinki bai sumar da shi ba an maida sa Airport a haka, tirr da Abdul, tirr da halinsa, i am so happy that things turn out this way, in sha Allahu karshensa ne ya zo a rayuwarki" Khaleesat ta fashe da kuka tace "Sophie ban san next action dinsa ba idan ya koma Nigeria, i am so restless" Safiyyah tace "Next action dinsa? Sai ya koma ya gaya masu uban da ya kawosa USA da Intention dinsa, ke in zaki dena wannan crocodile tears din naki ki dena don ba tausayinki zan ji ba, tunda dai bai samu nasaran lalata maki rayuwa ba ni duk abinda zai faru ma ya dade bai faru ba, kukan uban me kuma kike ma mutane? Ko nasaran da bai samu a kanki bane ya dame ki? Kuma wallahi ya ci sa'ar baki sameni a waya ba don kafin in karaso gidan sai 911 sun riga ni, tuni zan kirasu ince gashi can za ayi fyade, banda iskanci duk karuwansa basu ishesa ba sai ya zo ya kara dake? Gaskiya ki rike Housemate dinki da Wan uwan nan nasa da kyau don mutane ne su wallahi, da ba don su ba da yanzu wani zancen ake ba wannan ba, don da na kai maki ruwan zafi yafi a kirga zuwa bandaki yanzu" Khaleesat dai bata sake ce mata komai ba tana share hawayen da yaki tsaya mata, Safiyyah ta rike haSa har sannan tana mamakin Abdul, can tace "Kamar irin ya zo wajen matar nan tasa, ni wallahi da yaji suka barbada masa mu ga ta iskanci, shege kawai prostitute" Duk tashin hankalin da Khaleesat ke ciki sai da tayi dariya don ita bata taSa jin inda aka ce ma namiji prostitute ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login