Showing 63001 words to 66000 words out of 241367 words

Chapter 22 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1565

ma ya sauka ya bude back seat ya dauko laptop dinta da takardu ya kulle motar yace "Mu je" Sauke idonta tayi ta fara bin sa a baya walking slowly har suka shiga parlon gidan, ya nuna mata kujera yana kallonta, ta sunkuyar da kai sannan ta zauna, ya ajiye laptop da takardunta dake hannunsa sannan ya wuce sama, ta bi sa da kallo hawaye na taruwa idonta, sai kuma ta fara kuka a hankali tana jin kanta na sara mata, Jay ya tafi dakin AJ yana bude kofar dakin yaji yana wanka a bandaki, hakan yasa ya tsaya bakin kofar dakin don baya son issue, yana ta tsaye da tunani iri iri a ransa har AJ ya fito bandakin, AJ na ganinsa ya dakata da goge gashin kansa da karamin towel yace "Me kake nema a nan kuma?" Jay yace "Ban sani ba" Sai kuma ya karasa cikin dakin that was extra clean, kan kujera ya zauna without looking at AJ yace "We need to talk AJ" Ajay yace "Shi ne sai ka shigo min daki?" Jay yace "Zauna mu yi magana" ?an tsaki AJ ya ja yana ci gaba da goge gashinsa yace "Ina jin ka ba sai na zauna ba" Jay yace "I think my Housemate will stay here for a day or 2, before she sort her self out" AJ yace "As per you are her family member or who? Bata da iyaye ne? Ko nan din hotel ne?" Jay yace "Ban sani ba" AJ yace "No i am just asking a harmless question, like naga dai ba daga sama ta fado ba, kuma ba kai ka kawota America ba balle kace zaka samar mata solution, who are you to her? Yayanta ko Ubanta? Wanda muka mata ma Allah ya bamu lada, come off it Jawwad" Jay yace "Ai ba permission din ka na shigo nema ba Junaid, kawai sanar maka nake yarinyar nan zata yi kwana daya zuwa biyu a gidan nan kafin komai yayi settle" AJ yace "Toh ni na haifeka da zaka shigo ka gaya min zaka kawo yarinya tayi kwana biyu gidan nan? Ai sai dai ka kira su Abba ka gaya masu, beside the house is very big with multiple rooms to accommodate her, so ni ina ruwana, i just pray u don't have to explain ur self one day" Jay ya mike ya fice daga dakin banging the door behind him, AJ ya tabe baki yana feshe jikinsa da turaren jiki. Bangaren masu aikin gidan Jay ya nufa bayan ya sauko downstairs, ya basu umarnin da zai basu sannan ya dawo babban parlon gidan, Khaleesat dai na zaune ta jinginar da kanta jikin kujera tayi nisa tunanin da ta fada, ganin komai take kamar a mafarki, sai in taji tana da ta sanin abinda ya faru amma da ta tuna raping dinta Abdul yayi niyyar yi da Ajay bai zo ba sai taji ta nemi da ta sanin ta rasa, amma fa bata da nutsuwa bata da kwanciyar hankali, she was just restless and sick, bata san kuma me zai faru next ba a rayuwarta, muryar Jay ne ya dawo da ita daga tunanin da take ta gyara zama tana kallonsa a sanyaye, ya zauna kujeran dake kallon wanda take zaune yace "Bana son ki sa ma kanki damuwa Halysaah, ki kwantar da hankalinki pls kin ga kina da jarabawa a gabanki" Khaleesat ta sunkuyar da kanta hawaye ya fara sauka idonta, Yace "Kin yi sallah?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk za a kawo maki abinci sai ki ci kafin mu yi magana" Ta girgiza masa kai tace "Bana jin yunwa" Yace "No, sai kin ci abinci ko ba yawa" Dai dai nan kukun gidan wanda bature ne ya taho da abinci zai kai dinning Area, Jay ya masa umarnin ya kawo parlon sanin abincin AJ na kan dinning din, dawowa kukun yayi Jay ya nuna masa inda zai ajiye abincin, nan ya jerasu a kasan lallausan Centre carpet, ya koma ya dauko sauran, bayan ya ajiye komai ya tafi Jay ya mike yana kallonta yace "Ki sauko ki ci abinci, let me pray" Ta gyada masa kai kawai, ya wuce sama sannan ta sauko kasa a hankali tana duba abincin da aka kawo mata taga duk abincin jajaye ne gashi abincinsu da yawa ita ba iya ci tayi ba duk shekarun da tayi a kasar su. Almost 30 mins after Khaleesat dake ta zaune tana tunane tunane ko abincin ta kasa ci ta daga kai taga Ajay ne ya shigo parlon, sunkuyar da kanta tayi, bai kalli inda take ba yayi wucewarsa dinning Area ya fara cin abincinsa, after a while Khaleesat ta daga kai a hankali jin footstep, taga Housemate dinta ne ke saukowa downstairs, ya karaso har inda take ya zauna kan kujera yace "Kin ci abincin?" Ta gyada masa kai, cook din gidan ya kira ya dauke sauran abincin ya tafi da su, Jay yace "To ki koma kan kujera" Ita dai Khaleesat kanta na kasa bata ce komai ba, har sai da Jay ya sake mata magana sannan ta mike ta koma kan kujeran ta zauna, AJ ya dawo cikin parlon ya tafi reading nook dake parlon, Jay ya bi sa da wani kallo har ya gama kakkabe kakkabensa ya zauna, ko uban me zai yi a can don yasan dai baya ma zuwa nan balle yayi karatun a nan, muryar Jay ya dawo da hankalin Khaleesat jikinta, taji yace "So Halysaah i want to even know what happen first of all at ur apartment today, don ni ban san me ya faru ba, Salem called me yace kin kirani ban daga ba and you sound disturb, and he gave you AJ's number, i rang you back quickly sai kiran bai shiga ba, shine nayi deciding in je can gidan kawai, menene ya faru?" Khaleesat ta sunkuyar da kai don bata ma san me zata ce masa ba, ta yaya ma zata fara cewa raping dinta Abdul ya so yi, muryar AJ suka ji a parlon yace "Allah ma yasa ba rashin kunyan da ta saba yi ma mutane taje tayi masa ba, kawai ta sa na doki bawan Allah a banza" Khaleesat dai bata dago kanta ba, shi dai Jay yayi murmushin da bai yi niyya ba yana kallon direction din da AJ yake, A hankali Jay yace "You are not saying anything Khaleesat" Hawaye ne ya cika idonta, ganin haka Jay yace "Or you don't want to talk about it?" Ta girgiza masa kai hawaye na sauka idonta da kyar tace "Ba haka bane, he tried molesting me" AJ that heard what she said duk da ba kallon direction dinta yake ba yace "He tried molesting you, amma da hannunki ai kika bude masa kofar ba ta window ya shigo ba" Jay ya wani kallesa yace "Stop this please AJ, why are you so wicked and heartless" AJ yayi wata dariyar bosawa, Jay ya dinga hararansa, ita dai Khaleesat hawaye ne kawai ke zuba idonta, tsabar ciwon da kanta ke mata har wani dishi dishi take gani, Cikin kwantar da murya Jay dake kallonta yace "Tell me who he is, and where did you know him from" Ta gyada masa kai tana share hawayen da yaki tsaya mata a hankali tace "Shekara hudu kenan na san shi....."




*Don't even know where to start from, the patronage was massive>?z?, thank you soo much for encouraging me fans, Allah ya biya maku bukatunku na alkhairi, Allah ya raya zuri'a, i soo much appreciate ur patronage, marasu auren cikin ku Allah ya baku mazaje na gari, masu aure kuma Allah ya ci gaba da baku zaman lafiya a gidajenku, Allah ya karo maku budi ninkin ba ninki, ya raba ku da iyayenku lafiya* >?z?


_Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta i owe you 500_

[5/19, 5:53 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Khaleesat ta sunkuyar da kanta har sannan bata daina goge hawayen da ya ki tsaya mata ba, she look pained and traumatized, Shi dai Jay kallonta kawai yake waiting for her to continue with what she is saying, jin tayi shiru yace "Halysaah" Ta daga idanuwanta ta kallesa, Calmly yace "I am listening" muryarta na rawa tace "Kawai dai shi ne ke sponsoring dina" Ba Jay da ya kafeta da ido ba yana mata kallon mamaki, har AJ sai da ya juya ya kalleta daga inda yake zaune jin abinda tace, Jay was just speechlessly staring at her, can dai ya gyara zama yace "You mean shi yake sponsoring dinki a kasar nan? Are you related in anyway with him?" Ta girgiza masa kai kawai, da mamaki kawai yake kallonta, after few seconds yace "And ur parent allowed him to sponsor you har zuwa nan America?" Ta gyada masa kai without looking at him, mikewa AJ yayi, yayi wucewarsa sama, Jay ya bi sa da kallo don shi ma ya rasa abun cewa don mamaki, Jay ya maida dubansa kan Khaleesat a hankali yace "Ya kai kudin aurenki ne an sa maku rana?" Ta daga idanuwanta ta kallesa cikin sanyin murya tace "Nima ban sani ba, amma kamar ya kai" Jay yayi shiru for almost 3 minutes with different thoughts running his mind, everything just took him unaware, bai taSa tunanin saurayin nata ne sponsor dinta all this while ba, can ya daga kai ya kalleta yaga ta jinginar da kanta jikin kujera looking so tired and pale, yana son sanin me ya hadata da Abdul, meye ma dalilin haduwarsu, sannan a ina ma suka hadu da shi din, what is this great thing that motivated her parent har suka amince ma stranger da basu hada komai da shi ba ya turo er su har wata kasa karatu, he just don't want to believe it's because of money they did this.... amma ganin yanayinta yasa yayi keeping all the questions to himself for now don baya son ya kara stressing dinta, she is already stressed, mikewa yayi calmly yace "I will be back now" Ita dai ta bi sa da kallo har ya haura sama, wasu hawaye taji na taruwa idonta, kawai so take tayi kuka me sauti ko zata ji saukin abinda take ji a ranta, ta hade kanta da kujera tana shessheka a hankali, Jay na haurawa sama ya tafi dakin da ya sa daya daga worker din gidan ya kara gyarawa, the room was big sai dai bai kai nasa da na AJ ba, kuma babu abinda babu a dakin sai Duvet na saman bed spread, ya bude press din dakin yaga babu a nan ma, juyawa yayi ya fita ya dau hanyar dakin AJ, yana isa ya danna code din bude kofar dakin ya murda yaga bai buduwa, yasan canzawa yayi kenan saboda ya shigo masa dakin daxu, knocking din kofar yayi, after a while AJ ya bude kofar yana kallonsa alamar what happen, Jay ya turasa gefe ya shiga cikin dakin, AJ ya bi sa da kallo yace "Ka dai san bana son haka Jawwad, what are you looking for?" Jay ya kunna wutan dakin that is more brighter yace "Duvet zaka bani, i don't understand dalilin da yasa zaka kwashe kaf duvet din sauran rooms din all to ur self, this is greed" AJ dai kallonsa kawai yake cause he is already angry shigo masa da Jay yayi daki, ganin Jay ya nufi inda duvet dinsa suke yace "Jay me zaka yi da duvet bayan kana da naka a daki?" A takaice Jay yace "I am giving my visitor" AJ ya bude baki yana kallonsa yace "What??? I don't understand, Duvet dina zaka dauka ka kai ma visitor dinka? are you even okay? Can you hear ur self pls?" Jay bai tanka sa ba ya dau na saman gadonsa kawai ya nufi kofa, AJ ya tare kofar on a serious note yace "In ka fita da duvet din nan ka canza min suna yau" Jay ya wani turasa daga bakin kofar har sai da ya kusa faduwa sannan ya fice daga dakin, sai bayan da ya fita ya juya ya kalli AJ da ya bude baki yana kallonsa with shock, Jay yace "Emmanuel" daga haka yayi wucewarsa ya bar AJ da bin sa da kallo, Jay na komawa ya ajiye duvet din kan gadon dakin da aka gyara ma Khaleesat sannan ya sauka downstairs, tana nan zaune yanda ya bar ta idonta a lumshe amma ba bacci take ba, yace "Halysaah" Bude ido tayi da sauri bayan ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, yace "Tashi mu je sama, u need rest" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, ya dau laptop dinta da takardunta yace "Mu je" Sai bayan da ya fara tafiya sannan ta mike a hankali ta bi bayansa, har wani jiri take ji amma a haka ta daure ta bi sa har zuwa sama, ya bude kofar dakin ya shiga tana biye da shi, bayan ya ajiye laptop din hannunsa ya kunna mata na'uran da zai dumama dakin, ya nuna mata hanyar bandaki ita dai kai kawai ta gyada masa, ya ciro wayarsa a aljihu yayi dialing number sannan ya mika mata yace "In case u need anything sai ki kira number da nayi dialing it's my other line" Nan ma dai kai kawai ta iya gyada masa, yace "Good night Halysaah, pls kiyi bacci sosai, do not bother ur self kin ji?" a hankali tace "Toh" kofa ya nufa ta bi sa da kallo sai da ya bude kofar a hankali tace "Nagode" Ya juya ya sakar mata murmushi yace "I gat ur back" Daga haka ya fita ya kullo mata kofar dakin, Khaleesat ta ajiye wayar tasa da ya bata sannan ta zauna gefen gadon dakin a hankali staring at the window absently. Har karfe dayan dare Khaleesat bata ji ko digon bacci ya zo mata ba, tana dai kwance tayi lamo cikin duvet, her heart is soo heavy, har wani zafi take jin yake mata, ga wani zazzabin da taji ya lullubeta, tun da Jay ya bar ta take kuka, gani take kamar duniyar ya tsaya mata ne cak, ta ma rasa wani kalan tunani zata yi, abubuwan da suka faru daxu suka dinga dawo mata abun sai yake mata kamar mafarki, she wish mafarkin ne ma kawai, yanzu babban tashin hankalinta bata san me zai faru a Nigeria ba, bata san next step din Abdul ba, bata san me zai ma iyayenta ba, duk wannan tunanin ya hadu yayi distabilizing dinta, zazzabin da take ji ya karu sosai, tana son tashi taje tayi alwala tayi sallah ko zata samu sukuni amma ta kasa, duk jikinta ciwo yake mata ga ciwon kai kamar kanta zai fashe, da taji azaban yayi mata yawa kamar zata kira Housemate dinta ta tambayesa maganin ciwon kai amma ta fasa don bata san ko bacci yake ba, haka tayi ta juye juye jikinta yayi zafi sosai, yanda taga rana haka taga daren nan that was soo long to her, bacci ko na barawo bai dauketa ba, jin vibration din da wayarsa yayi yasa tayi karfin halin jawowa tana kallon screen taga alarm ne na karfe biyar, ta kashe alarm din tana son tashi don tayi sallah amma ta kasa, daga karshe dai haka tayi karfin hali ta daure ta tafi bandaki ta dauro alwalan, tana idar da sallan taji zazzabin da yafi na baya ya lullubeta gaba daya, kwanciya tayi saman gado ta rufe har kanta da duvet din. Wajen karfe takwas na safe Jay yayi knocking kofar dakinta, tana ji amma ta kasa amsawa, sau uku yana knocking jin bata amsa ba sai ya kira wayarsa dake wajenta nan ma tana kallon kiran amma ta kasa daga hannu ma ta dau wayar, sai da ya katse sannan ya bude kofar dakin da sallama ya shiga, yana kallonta da mamaki ya nufeta yace "Are you Okay Halysaah?" Kai kawai ta girgiza masa, ya duka kusa da ita yace "Baki da lafiya ne? Why didn't you call my line?" Hawaye ya gani idonta, yace "Haba Halysaah, ba nace kar ki sa ma kanki damuwa ba? Did you want to hurt ur self?" Ita dai bata ce komai ba, ya juya ya fita daga dakin, after some minutes ya dawo da Hot chocolate ya ajiye mata yace "Ki daure ki sha pls, let me get you medicine" Yana fadin haka ya juya ya fita daga dakin, ko da ya dawo ya ga bata tashi ba still, duk yanda yayi da ita ta tashi ta sha shayin ya bata magani taki tashi, gaba daya ya ma rasa yanda zai yi da ita, can ya kara dukawa kusa da ita yace "Did you have ur frnd safiyyah's number offhand?" Da kyar ta girgiza masa kai, yace "U have her IG handle? Is she active on IG?" Bata ce masa komai ba don ta ma kasa maganan, he look confuse at this point, can dai yace "To zaki iya daurewa ki tashi mu tafi asibiti?" Ta girgiza masa kai, mikewa yayi kawai ya fita daga dakin, downstairs ya sauka don AJ na dinning yana breakfast ga Legend dinsa zaune Wan nesa da shi a dinning area din, Jay ya nufesa looking confuse yace "AJ, the girl is seriously sick fa" AJ dake sipping tea dinsa yace "Which girl?" Jay ya masa wani kallo yace "Please be serious AJ, wallahi bata da lafiya sosai" AJ yace "To yanzu daukar ta zaka yi ka kai ta Hospital kenan..." Jay yace "How?? ko tashi fa bata iya yi, plss ko zaka mata allura ta Wan samu relieve tukun?" A hankali AJ ya ajiye Mug din hannunsa yana kallon Jay baya ko kiftawa, can ya matsar da shayin gabansa yace "Amma dai don Allah me yasa ka raina ni haka ne Jay? Me nayi maka? Kai me hannunka yake da bazaka mata allura ba sai ni?" On a serious note Ajay ke masa tambayoyin nan looking at him and waiting for his answer,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login