Showing 126001 words to 129000 words out of 241367 words

Chapter 43 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1573

ta tashi ta shiga dakin dake parlon. Da asuba ko sallah ba ayi Malam Ali ya fito da er jakar da yake tafiya da shi bayan ya mulke jikinsa da basilin saboda sanyin da ake, bin dakunan matan nasa yayi duk ya kwankwasa masu kofa, Mama Zubaida da Mama Shatu suka fito suna kallonsa da mamaki suka ce "Lafiya Malam?" Mama Zubaida tace "Ko tafiya kauyen ne ya taso?" Shi dai bai tanka su ba ya dinga goge takalminsa da yayi ?ura, Umma ce karshen fitowa ita ma ta tsaya tana kallonsa ta kasa cewa komai don tasan manufarsa, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya tsabar yanda hankalinta ya tashi, Nenne ce ta shigo gidan yafe da zaninta tana ganin Malam Ali tace "Yauwa ko sallah kar ka jira kayi idan kaje tashar kayi a can Ali, ga er soyayyiyar nama da gurasa na kullo maka ka ci a hanya" Mama Shatu tace "Tafiya zai yi ne Nenne?" Nenne tace "Babu ruwan ku, ku dai ku yi masa fatan Allah ya kiyaye hanya" Malam Ali ya amshi kullin nama da gurasan da Nenne ke mika masa, yana kallon matan nasa yace "Toh sai Allah yayi min dawowa" Mama Shatu tace "To ai shikenan, Allah Ubangiji ya tsare Malam" Mama Zubaida ma tace "Allah ya tsare duk da muna da hakkin ka sanar mana inda zaka je da asuban fari Malam" Nenne tace "Bazai sanar ba Zubaida, uban me sanin inda za shi zai kara maki?" Mama Zubaida ta juya ta koma daki, Mama Shatu ma ta tabe baki ta koma dakinta, Nenne ta kalli Umma tace "Wato ke ce isasshiyar da bazata yi masa Allah ya kiyaye ba ko Zahra'u" Shi dai Malam Ali tuni har ya fice daga gidan, Nenne na nuna Umma tace "Mugun abun ku zai kare maku da ke da er ki wallahi, babu wanda ya isa ya salwantar min da Wa na lokacinsa bai yi ba" Daga haka ta bi bayan Malam Ali da sauri zata rakasa bakin titi ya samu adaidaita sahun da zai kai sa tasha. That same day bayan an idar da sallahn asuba Jay ya shigo parlorn Mai martaba da sleepy face ta dalilin kiran da yayi masa, ganin irin zaman da Abba yayi kamar yana fadarsa ya gane serious issue Abban zai yi discussing da su kenan, ya kalli Ajay dake parlon zaune shi ma alamar kiran sa Abban yayi, Aunty ma na zaune parlon, Jay ya sauke kansa ya karasa kusa da Ajay ya zauna kasan lallausan carpet din parlon, dabi'ar Abba ne sai ya iya minti biyar zuwa goma kamar me nazari kafin ya fara magana in ya tara ku, Jay ya sunkuyar da kansa ya lumshe ido, Ajay ya Wan kallesa sanin sai ya iya bacci a haka, ai ko yaga baccin yake, Ajay ya Wan tunkudesa da elbow dinsa, Jay ya bude ido da sauri yana gyara zama, shi dai Abba kallonsu kawai yake, At last Abba yayi gyaran murya cikin nutsuwa yace "First of.... Ina son sanin zaman me ku ke har yanxu a garin nan baku karasa gida ba?" Duk suka yi shiru babu wanda yace komai kansu a kasa, Calmy Abba yace "Ohk take ur time, amma kuyi kokari ku je gida kafin hutun ku ya kare, Secondly.... maganar da nayi da ku a Maryland naji babu wanda yace min komai a kai har yanxu, ga lokacin da na baku ya cika, nayi maku uxurin mantuwa shi yasa nake tunatar da ku yanxu..." Nan ma duk suka yi shiru babu wanda yace komai, shi ma Abban yayi shiru yana kallonsu yana jiran amsa a duk sanda suka shirya, sun san shirun da Mai martaba yayi amsarsu yake kira ko da zai dau 10min ko fin haka ma kafin su basa amsan he won't mind zai jira su patiently, sanin halin Abban nasa yasa Ajay ya daga kai, Softly yace "Ayi hakuri ranka shi dade ba mantawa muka yi ba, in sha Allah we are working on that very soon" Mai martaba yace "Is that so?" Ajay ya sauke kansa don kalman Abba na nufin bai gamsu da abinda yace ba kenan, Shi dai Jay yaki dago kai, a hankali Ajay yace "A gafarce mu a Wan kara mana lokaci Abba..." Aunty da har ta fahimci maganar da ake ta Wan yi gyaran murya ta nemi permission din magana gun Mai martaba, ya gyada mata kai alamar ta fadi abinda zata fada, cikin nutsuwa tace "In na fahimci maganar da ake ranka shi dade, magana ce akan su fito da matan aure duba da yanda shekarunsu ke gaba ba baya ba, wannan magana kuma ba sabuwar magana bace don an fi shekara 3 ana yin ta amma babu wani progress, a takaice basa daukar maganar da muhimmanci, to amma dai ina ga ka Wan sha'afa ne ur Highness, don shi Jawwad ai akwai maganar sa da Hadeeyah a kasa duk da ba wai maganar tayi karfi bane kuma wannan hadi, hadi ne me kyau da zai kara karfafa zumunci don mahaifiyar Hadeeyah jininka ce kuma ita ta kawo wannan shawara duk da Fulani wato mahaifiyar Jawwad uwar dakinta ce tun asali, shi kuma Junaid a yanda na lura da shi zai fi maraba da zabin ka garesa duba da nature dinsa da rashin choice dinsa, don haka shi Jawwad a tsaida maganar sa da Hadeeyah kawai ina ga hakan zai fi, shi kuma Yarima i think we should get him a princess from neighbouring states, ko ni zan iya jagorantar hakan don arranged marriage zai fi suiting dinsa duba da nature dinsa, kuma ina son a bar komai a hannuna ranka shi dade..." Ajay ya daga kai ya kalleta zai yi magana mai martaba ya dakatar da shi, Ajay ya sauke kansa, Speaking Calmly Mai martaba dake kallon Ajay da Jay yace "Za ku iya tafiya, Allah yayi maku albarka" Sai a sannan Jawwad ya dago kai ya kalli Aunty dake Wan murmushi ganin Mai martaba yayi na'am da shawaranta, tuni Ajay har yayi disappearing daga parlorn fuska a murtuke, Jay ya mike shi ma ya bi bayan Ajay yana tafiya a hankali, bai taSa sanin baya son Hadeeyah da aure ba sai yau da Aunty ke bada shawaran a tsaida ranan aurensu da ita, yasan kuma duk abinda Aunty tace kamar Abba ya aikata hakan ya gama ne, kawai yaji hankalinsa yayi mugun tashi yaji wani zufa na keto masa, dakinsa ya shige ya kulle da makulli ya jingina da kofar ya lumshe ido zuciyarsa na bugawa, Ajay na shiga dakinsa shi ma ya kulle da makulli ya zauna gefen gado ya dafe kansa da hannu biyu, this is not the first time da Aunty ke kasalanda akan duk abinda ya shafesa gashi Abbansa baya basa listening ears ko me Aunty tace masa kawai haka za ayi abun nan komin munin abun, at this point he felt he is of no importance to his father, he felt dejected, and it's been like this for so many years, he have no one to stand for him, a hankali ya juya yana kallon wayarsa dake vibrate, Number Aunty Farida ya gani a gaban screen din wayar, ya kalli agogo yaga karfe shidda da minti biyar na safe, request din Khaleesat na jiya da ta kirasa ya tuna, hakan yasa har kiran ya katse bai daga ba knowing she might be the one calling, kiran ya sake shigowa ya kalli screen din nan ma bai daga ba har ya katse, sau hudu kiran na shigowa continuously, hakan yasa ya maida attention dinsa kan wayar ya Wan yi jim with different thought running his mind, ganin kiran ya katse an sake kira making it the 5th time of calling yasa ya dau wayar ya daga ya kai kunne yayi shiru waiting to hear who is on the line, a hankali ya mike jin abinda Aunty Farida ke ce masa ta wayar, bai san sanda ya zame wayar daga kunnensa ba rate din heartbeat dinsa na karuwa, da sauri ya nufi kofarsa ya bude ya fice daga dakin ya murda kofar dakin Jay yaji a kulle, knocking ya dinga yi non stop kafin Jay ya bude kofar da mamaki yana kallonsa yace "What is it?" Ajay ya shiga dakin yana shafa gashin kansa da wani expression yace "He tracked her to Lagos" Still Jay yayi a inda yake tsaye ko kwakkwaran motsi baya yi yana kallon Ajay, Ajay ya ja numfashi sannan ya zauna kan kujeran dakin ya lumshe idanuwansa ya jinginar da kansa jikin kujeran trying to calm himself, Jay was speechless and shock at the same time, da kyar ya ja kafa ya zauna gefen gadonsa ya dafe kansa da yaji yayi masa nauyi, kamar an tsikare Ajay ya mike yace "Book us ticket to Lagos" Daga haka ya fice daga dakin.
[6/12, 8:02 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Aunty Farida ta share hawayen da yaki tsaya mata tana kallonsu Ajay da kyar tace "Wallahi ban san ko har su nawa bane a motar, ban ma san ya motar take ba tunda ina cikin gida sanda abun ya faru, yaran makota dake diban ruwa a bakin rijiyar tare da ita ne suke cewa kawai suna diban ruwa sai ga motar ta shigo street din, wasu mutane suka sauka a motar suka ja ta zuwa cikin motar suka tafi da ita, a sannan an idar da sallahn subahi kenan kun ga gari bai waye ba ai" Ajay was speechless, bai taSa zama confuse haka a rayuwar sa ba don ya ma rasa abun cewa, likewise Jay dake jingine jikin mota tun da suka iso unguwan dama shi bai ce komai ba, Ajay ya daga kai after some seconds ya kalli Aunty Farida a hankali yace "Amma yana da number ki ne Aunty?" Aunty Farida tace "Ba shi da wannan number tawa gaskiya sai tsohon layi na, kwanaki Maman Khaleesat tayi rashin lafiya sai na tafi kano dubata to a hanya na yar da wayata, da na zo kano sai na siya sabon layi kafin inyi welcome back din tsohon layin, to har yanxu ban yi welcome back din ba" Ajay yayi shiru yana nazari, Aunty Farida na hawaye tace "Tsautsayi yasa ta fita deban ruwan yau, amma tunda ta xo wallahi ni ke diban ruwana bana barin ta dibar min tunda har yanxu gata nan ne dai bata dawo dai dai ba, wani lkcn ma da daddare idan na dawo kasuwa nake yi tunda ana wahalar ruwa a season din nan don yawanci rijiyoyi kafewa suke yi sai ana bari ruwan na taruwa sannan a diba, gashi ba a samun wuta balle a samu ruwan pampo, a jiyan nayi girki me yawa ne na wani biki duk sai na gaji ban deba ruwan da daddare ba, da na tashi kuma sai nake jin zazzabi, kun ji dalilin fitarta ta debo mana ruwa kenan" Ajay ya jingina da motarsa ya lumshe ido ya bude, gaba daya ?ansa ya gama kullewa, bai yi zaton Abdul ya wuce yanda yayi zatonsa ba, the guy is really something else ko wani salon tactics na mugunta ya san sa gashi har yau yaki kunna wayarsa balle a san inda yake, ko by mistake baya kunna layin, shi dai Jay dama bai taSa underrating Abdul ba dai dai da rana daya duba da irin actions din da ya dinga portraying, kawai dai tracing din Halysaah har zuwa Lagos is the least thing da yayi zaton Abdul zai yi, tunda bashi da access da Aunt dinta, but like seriously how did he even find his way, bayan bashi da active line din Aunty Farida sannan bai san unguwan da take ba, ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya yana tunanin ta inda za su fara billo ma wannan lamari, tunda dai babu ta yanda za su ce yayi kidnapping Halysaah da ke a matsayin matarsa ta sunna. Khaleesat na zaune at the far end of the large room ta hade kanta da gwiwa, zuwa sannan ta hakura da kukan da take don ba ma ta da strength din kukan amma tana jin zuciyarta na mata zafi ga wani azababben ciwon kan da take ji da kishin ruwa da ya dameta, tafi awa sha biyu zaune a dakin ba ci ba sha, don tunda aka shigo da ita har zuwa sannan babu wanda ya sake zuwa dakin, infact bata ji motsin kowa a gidan ba alamar ita kadai ce a ciki, bandakin dake cikin dakin take shiga tayi alwala ta fito tayi sallah duk da ba sanin lokaci tayi ba kawai tana amfani da instinct dinta ne, at this point in time tasan bata da wani sauran gata sai wajen Allah, domin kuwa tasan Abdallah ne kawai zai sa a zo ayi mata irin wannan daukan, wasu hawaye masu zafi suka zubo idonta tana tausayin rayuwarta, all she could remember vividly was that tana bakin rijiyan dake kusa da gidansu Aunty Farida tana diban ruwa wasu mutane biyu suka zo a mota, lokaci daya kuma suka yi leading dinta zuwa motar tasu, at first turje masu tayi ta fara kokarin raising alarm tana ihu, yaran dake bakin rijiyan duk suka gudu suka shige gidajensu, tana kururuwa daya mutumin ya rufe fuskarta da wani Handkerchief da sauri, taji ta sha?i wani abu kamar dust, lkci daya kuma ya cire handkerchief din a fuskarta, daga nan kuma ko kokarin ihun bata sake yi ba cause she became weak, ita dai tasan all through the ride she was conscious but not fully, gashi ta kasa tabuka komai don duk jikinta ya mutu, kanta yayi mata nauyi idonta suka dinga juya mata.... Da sauri Khaleesat ta dago kanta ta mike tsaye jin ana ?o?arin bude kofar dakin ta waje da makulli, gabanta ya dinga bugawa da karfi idonta na kan kofar har ya bude ya shigo, she wasn't expecting anyone but him dama, ta sauke kanta bayan sun hada ido, wasu sabbin hawayen suka fara zuba idonta, muryarsa taji ya daki kunnenta cike da isa da gadara yace "Har yanxu Body guards din naki basu biyo bayanki bane? Ai yaci ace sun iso zuwa yanxu don naga It's almost 12 hours now, how comes basu zo cecen ki ba duk capacity din su" Sai a sannan Khaleesat ta daga kai ta kallesa cikin rawar murya tace "Ka ji tsoron Allah...." Kasa ci gaba tayi ta fashe da matsanancin kukan takaici, shi dai yana tsaye yana kallonta da wani murmushin mugunta kwance fuskarsa, ta dago kai da sauri jin yana takowa har zuwa inda take tsaye, mannewa tayi da bango tana jin kamar bangon ya tsage kawai ta shige gabanta na bugawa da karfi, sai da ya zo dab da ita cikin kwantar da murya yace "Me kika ce?" Ta girgiza masa kai da kyar gabanta na ci gaba da faduwa muryarta na rawa tace "Kaji tsoron Allah Ya Abdul, kaji tsoron...." Bata rufe baki ba taji saukan lafiyayyen mari a fuskarta wanda sai da taga taurari, ta dafe kuncinta tana kallonsa babu ko kiftawa, cikin husky voice dinsa yace "You still have the guts to repeat what u just said saboda baki da kunya ko? Ni zaki gaya ma in ji tsoron Allah? To tsoronki zan ji ko tsoron uban ki dake Mariri idan ban ji tsoron Allah ba?" Da kyar Khaleesat ta dake tace "Ka zageni amma kar ka sake zagar min uba" Still bata rufe baki ba ya sake sauke mata wani wawan marin a other side of her face, this time around sai da dakin ya juya mata don ba marin wasa yayi mata ba, ya fixgota yana mata wani irin kallon da ya gigitata don tuni idonsa yayi jajur yana huci yace "Ina magana kina mayar min how dare you poor wretched girl?" Ta fashe da matsanancin kuka tana jin dama Allah ya dau ranta kawai ta huta a wannan lokacin, zata durkusa kasa ya hadeta da bango yace "Yau ina body Guards din naki dake goya maki baya kina min iskanci? Tell me where they are today? Da aurena a kanki kike hulda da wasu banzayen gardawa saboda ke jahila ce warce bata san me take ba" Tana kuka sosai bata san sanda tace "To wai ana aure dole ne dama Abdul? Nace bana son auren, bana son ka, gwara kawai ka kasheni duk mu huta" Da karfi ya bugata da bango har sai da taji numfashinta ya dauke na few seconds, yana mata wani mugun kallo yana huci yace "Dama ke baki san aurena wajibi ne a gare ki ba ko kina so ko ba kya so? Dama shi ubanki bai gaya maki hakan ba ko mantawa kika yi saboda kin fara bin maza? Wallahil Azeem kin ji rantsuwar musulmi ko? Duk ranan da kika sake yunkurin guduwa ko kuma yin wani silly act to rayukan twin siblings din ki za su zama fansar aurena idan kika kuskura kika min jakanci, ko kina so ko baki so lallai dole ki zauna da ni ko kuma in salwantar da ran kanninki i am promising you this Billahil Azeem, kuma babu abinda zai faru don tamkar na kashe banza ne daga ke har iyayenki babu abinda za ku yi, su kansu Body guards din naki ba kyalesu nayi ba don sai na dau revenge din intruding da suka yi a sabgata, i will teach them a lesson kina ji kuma kina gani" Khaleesat ta kasa cewa komai don sama sama kawai take jin numfashinta kalmansa na cewa zai salwantar mata da siblings dinta ya sa jikinta ya fara rawa, ya juya cike da isa ya tafi ya bude closet din dakin wanda duk kananun shegun kaya ne yace "All this are your wears, in kin yi sallah kin shirya ki zo ki sameni a dakina which is 3 rooms away from this, ina jiranki at exactly 7pm and this is just 6:30pm" Yana kai wa nan ya fice daga dakin yana rike da key din dakin, a hankali Khaleesat ta sulale kasa tana sauke numfashi tana jin wani abu ya tsaya mata cak a zuciya, gashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login