Showing 15001 words to 18000 words out of 241367 words

Chapter 6 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1585

dakinta, tana dai zaune har sai da ya kwankwasa kofar sau uku sannan ta sauka daga saman gado, walking slowly ta tafi ta bude kofar, Yace "Good morning Halysaah, how was ur night?" Without looking at him tace "Fine" Yace "Ya jikin Mama? Kun yi communicating da su?" Kai kawai ta gyada masa bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, Paper da pen din hannunsa ya mika mata yace "Can i get ur Email Address?" Ta daga kai ta kallesa da mamaki tace "I don't understand" Yace "I mean ur Email Address" wayarsa ne ya fara ring ya mika mata takardan da pen ya daga kiran sannan ya juya ya bar wajen, ita dai ta bi sa da kallon mamaki, can ta juya ta koma daki ta ajiye takardan da pen da ya bata, after some minutes sai gashi ya dawo yayi knocking yace "Can i get the paper" Tasowa tayi ta bude kofar bayan ta dau pen da takardan tace "Why are you asking for my Email Address?" Yace "Ki dae rubuta ki bani" Shiru tayi, sai kuma ta jinginar da paper din jikin kofa ta rubuta sannan ta mika masa ya amsa ya juya ya bar wajen, yana fita da few minutes taji message ya shigo wayarta, ta dau wayar ganin E-mail ne ya shigo ta bude, kallon Image din da ta gani as Email din ta dinga yi babu ko kiftawa, she look shocked and confused at the same time, ta daga kai tana kallon kofar dakinta babu ko kiftawa, dai dai sanda taji sallamarsa, kasa tashi tayi daga inda take zaune, har sai da yayi knocking sau biyu tayi karfin halin mikewa ta isa kofar ta bude tana kallonsa, Yace "I don't know if you find this okay and a good idea" Ita dai bata fasa kallonsa ba looking speechless, Yace "Hope they won't be Mad at this back home Halysaah?" Jin bata basa amsa ba ya gyada kai yace "I guess it's a bad idea, I should have ask for ur opinion first before doing this" Nan da nan hawaye ya cika idonta ta sunkuyar da kanta, yace "Ok it's fine, i will get the ticket cancelled" Daga kai tayi da kyar tana kallonsa hawaye na zuba idonta tace "Thank you so much, i appreciate" Yace "Sure??" Ta gyada masa kai, yace "Ohk, u can order a Lyft that will be taking u to the airport later, ur flight is at 3pm today" Sauke idonta tayi cause she is totally speechless, ya mika mata travelling documents dinta, amsa tayi cike da mamakin how he got them, ya juya ya bar wajen, komawa cikin daki tayi ta kulle kofar tana kallon inda take ajiye travelling doc din nata a dakin, did he come to her room to check ne, to ai throughout babu inda taje, ta karasa gefen gado har sannan jikinta a mugun sanyaye ta zauna, kallon screen din wayarta ta sake yi tana kallon ticket din don ganin abun take kamar a mafarki, tana kara duba taga tun daren jiya ya siya ticket din and kamar yanda yace the flight is by 3pm today, ta ma rasa ko farin ciki zata yi ko kuma wani reaction zata yi, amma da ta tuna she is going back home to see her Mom which was her wish since yesterday sai taji wani farin cikin da tunda take bata taSa jin irinsa ba a rayuwarta, 80% a cikin dari na damuwarta ya ragu cikin lokaci kankani, kallon agogo tayi taga sha daya ya wuce sosai, the weakness she is been feeling since this morning immediately vanished, mikewa tayi tana share hawayenta ta dau medium box din kayanta.... Karfe biyu Khaleesat ta gama duk abinda take, har sallan zuhur tayi, Lyft din da tayi ordering kawai take jira, tana zaune gefen gado xuciyarta fal da tunani kala kala, babban burinta a yanzu bai wuce ta ganta kusa da mahaifiyarta ba, in yaso koma me zai faru daga baya sai ya faru, kallon wayarta tayi taga Safiyyah ce ke kiranta, tun daxu da safe ta kirata amma sbda damuwar da take ciki ko picking bata iya tayi ba, Khaleesat ta daga kiran ta kai kunne, Safiyyah tace "Khalee me yasa baki shigo schl ba yau? Are you okay?" Khaleesat ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Ummanmu ce bata da lafiya Sophie" Safiyyah tace "Subhanallah, amma ya jikin yanzu?" Khaleesat tace "Da sauki" Safiyyah tace "To Allah ya bata lafiya, plss nasan ki kar ki sa ma kanki damuwa kawata addu'a kawai zaki dinga mata, nasan kilan kina nan kina ta kuka ko?" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah tace "In sha Allah in mun gama lectures zan taho" Khaleesat tace "I am sorry ban kira ki na gaya maki ba i will be leaving for Nigeria by 3pm" Da mamaki Safiyyah tace "Zaki tafi Nigeria? Abdul ne ya siya maki flight ticket?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Uhm" Safiyyah tace "Is it that critical Khaleesat?" Khaleesat tace "To da sauki dai, amma kinsan bazan samu rest of mind ba in ban je ba" Safiyyah tace "To kina airport yanzu ne?" Khaleesat tace "Aa ina jiran Lyft ne yanzu zan tafi" Safiyyah tace "Toh shikenan mu hadu a can kawai sai mu yi sallama, bari in nemi Uber nima" Khaleesat tace "To nagode Sophie" Da haka suka gama wayar, Khaleesat ta mike bayan Lyft dinta ya iso, tana rike da trolley dinta da handbag ta fito daga dakin ta kulle kofa, sanye take da Maroon Abaya sai veil dinta, tana tafiya a hankali ta karaso cikin parlorn, ya ajiye wayar da yake yace "Kin shirya?" Without looking at him tace "Eh" yace "Kin yi ordering ride ai?" Tace "Eh" yace "Ohk" Mikewa yayi ya ciro 1000 Dollars ya mika mata yace "Sort ur self out with this" Girgiza masa kai tayi tace "Aa Nagode" Yace "C'mon, u didn't beg me Halysaah" ?in kallonsa tayi kuma taki amsan kudin, ya dau handbag dinta da ta ajiye saman trolley din gabanta ya bude zip din jakar ya sa mata kudin tare da wani farin takarda, ta Waga kai tana kallonsa, ya koma ya zauna yace "Allah ya tsare, my regards to ur Mom and everyone back home, Allah ya bata lafiya" Da kyar tace "Ameen nagode" Yace "Zaki ga digit na rubuta maki a takarda, idan kun sauka Airport sai ki kira number kice masa kun sauka" Ta kasa cewa komai, after few seconds ta dau handbag dinta cikin sanyin murya tace "Nagode " Yace "U are welcome, wishing u a Safe trip" Tana jan trolley dinta a hankali ta nufi kofa, tana bude kofar ta fita ta daga kai tana kallonsa taga Idonsa na kan wayarsa da yake dannawa, kulle kofar parlon tayi, taga Lyft din dake jiranta ta nufi wajensa. A Airport Khaleesat suka hadu da Safiyyah, Safiyyah na rike da hannunta tace "Tun yaushe ne Umman bata da lafiya?" Khaleesat tace "Jiya Aunty sha'awa ke gaya min" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "To Allah Ubangiji ya bata lafiya" Khaleesat tace "Ameen" Safiyyah tace "Lallai Abdul ya fara hankali da yayi tunanin biya maki jirgi kije ki duba Umma, nayi mamaki sosai wallahi" Khaleesat ta Wan yi murmushi da iyakarsa lips, Safiyyah tace "Yanzu kwana nawa za ki yi?" Khaleesat tayi shiru at first, sai kuma tace "Sai dai naje tukunna in sha Allah" Safiyyah tace "Toh Allah ya kai ku lafiya, don Allah ki gaida min Umma da jiki" Safiyyah na fadin haka ta jawo handbag din Khaleesat ta saka mata dala dari tace "Plss manage this kawata" Khaleesat ta Wan bude baki tace "Haba meye haka Sophie" Sophie bata tsaya ta saurareta ba ta daga mata hannu tana murmushi ta bar ta tsaye wajen, Khaleesat dai ta bi ta da kallo. Khaleesat was more than shock bayan ta amshi boarding pass dinta ganin ticket din Business Class ya siya mata, Business class fa? Kikkifta ido tayi ta sake kallon ticket din sosai to confirm, taga Business class din dai ne still, sosai jikinta yayi sanyi, tana jan kafa da kyar ta shiga jirgin, this is the first time she will be traveling Business class, wata Flight Attendant that gave her all the maximum attention ta yi leading dinta har zuwa Seat dinta a cikin jirgin da fara'a tana welcoming dinta, bayan wani Wan lokaci jirgin ya tashi, Khaleesat ta ajiye Amenity kit da aka bata ko duba abinda ke ciki bata yi ba tana bin ko ina na Business class din da ido, the Flight from Baltimore Washington International to Amsterdam Schiphol Airport in North Holland for Layover was smooth and comfortable, duk zuwanta Amurka bata taSa tafiya feeling so comfortable like this ba, bayan few hours aka sauya masu jirgi zuwa Nigeria a nan North Holland, Khaleesat tayi shiru da mamaki jin announcement na cewar Lagos Nigeria jirgin ya nufa, ticket dinta ta sake dubawa taga ashe haka ne a jiki, bayan tafiyar kusan awa bakwai jirgin nasu ya sauka a MMI Airport Lagos.
[5/3, 6:15 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: ('('HALYSAAH('('





By _Khaleesat Haiydar_
'




6.....


Bayan Khaleesat ta dau trolley dinta a cikin airport after going through custom ta tsaya cikin airport din tana tunanin yanda zata yi cause karfe shidda saura ne na asuba, should she check for available flight to Kano? To nawa ne ma a account dinta before she think of doing so, ko dai kawai ta tafi Motor park ta hau mota zuwa kano, dollars din da Housemate dinta ya bata ne ya fado mata a rai don gaba daya ta ma mance, ta bude handbag dinta ta ciro kudin tana kallo, takardan da ya saka mata hade da kudin a jaka ya fadi kasa, ta duka ta dau takardan tana kallon numbers din jiki sai kuma ta mayar cikin jaka tare da Dollars din, masallacin dake cikin Murtala Muhammad International airport ta tafi don yin sallan asuba, tana ta zaune cikin masallacin bayan ta idar da sallah tana azkar dinta, can ta ciro wayarta a handbag ta duba agogo taga karfe bakwai da minti goma, dollars din jakar ta sake cirowa ta kirga taga dala dubu ce, kallon kudin ta dinga yi jiki a sanyaye don bata yi tunanin har haka ya bata ba, ta dau white paper din dake dauke da digit tana tunanin to ko digit dinsa ne wannan din, kati ta siya ta Ussd sannan tayi dialing number a wayarta, sai da ya kusa katsewa aka daga, daga daya side din aka yi sallama ta amsa, amma sai taji kamar ba muryarsa bane, ta dai ce "Ina kwana?" Yace "Hajiya ko kece kika taho daga America?" Tace "Eh" Yace "To barka da isowa Hajiya, ina ta sauraren kiran naki dama tun daxu, kina cikin airport din ne yanzu?" Tace "Eh" Yace "Ohk to gani nan tahowa ba da dadewa ba in sha Allah" Bayan ya katse wayar ta kalli screen dinta, to waye kuma wannan, maida kudin tayi jaka ta ciro nose mask dinta ta saka sannan ta mike ta fito daga Masallacin da trolley dinta with handbag, bayan wasu mintoci sai gashi ya sake kiranta, ta fito outside of the airport, yana hangota ya nufota ya gaisheta da ladabi har da bowing kansa yace "Ya hanya Hajiya?" Ta sauke idonta tace "Lafiya Alhamdulillah" With respect yace "Ga mota can Hajiya, zaki je hotel ki huta zuwa karfe daya na rana don Flight dinki zuwa kano na karfe Biyu ne in sha Allah..." Khaleesat was speechless ta dinga kallonsa babu ko kiftawa cike da mamaki, can kuma ta kalli lafiyayyen motar da ya nuna nata, tuni ya karasa ya amshi trolley dinta ya tafi ya bude booth ya saka, sannan ya bude mata bayan mota yace "Bismillah Hajiya" Sauke idonta tayi kasa taji kafafuwanta sun mata nauyi amma a haka tana tafiya a hankali ta tafi ta shiga back seat sannan ya kulle motar, ya zaga ya shiga driver seat, Hotel me tsada sosai that isn't far away from the airport ya kai ta, sai da ya tabbatar tayi check in har zuwa dakinta sannan ya bar hotel din, tana shiga babu jimawa wata ma'aikaciyar hotel din ta kawo mata lafiyayyen Breakfast, ita dai Khaleesat ba um bare um um, gaba daya kanta ya gama kullewa, tashi tayi ta bude trolley dinta ta dau Shower gel zata yi wanka. Khaleesat na bacci wajen karfe daya da minti ashirin vibration din wayarta ya tasheta, ta jawo wayar a hankali tana duba me kiranta taga mutumin da ya kawota Hotel ne, ta mike zaune sannan tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren yayi mata sallama sannan yace "Hajiya fatan kin shirya in taho in dauke ki, flight din naki nan da minti talatin ne in sha Allah" a hankali Khaleesat tace "Toh" Yace "Gani nan tahowa yanzu da izinin Allah" Yana katse wayar Khaleesat ta sauka daga saman gado taje tayi alwala a bandaki, tana idar da sallan Azahar sai ga kiransa, ta dau trolley dinta da handbag ta bar dakin hotel din ta sauko downstairs, yana hangota a Reception din hotel din ya tafi da sauri ya amshi trolley din hannunta, ya karbi makullin dakin ya kai ma Receptionist, sannan suka fita haraban hotel din ya bude mata back seat bayan ya saka trolley dinta a booth, cikin mintuna kadan suka isa MMI Airport, sai da ya tabbatar ta amshi boarding pass dinta sannan yayi mata sallama da murmushi fuskarsa yace "Toh Allah Ubangiji ya tsare Hajiya, idan kun sauka kanon za a karasa dake gida in sha Allah... We will keep in touch" a hankali Khaleesat tace "Toh Nagode, Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen Hajjaju, nagode kwarai, Allah Ubangiji ya kai ku lafiya" A haka suka rabu ta nufi Departure lounge walking slowly, bayan kusan minti ashirin jirginsu ya tashi zuwa garin kano. Suna sauka kano Khaleesat ta fito daga cikin airport gabanta na faduwa, sai gyara nose mask din fuskarta take tana waige waige, yanzu ina ma ta nufa tukun, tasan ko da wasa bazata nufi gida ba dai, wayarta ya fara ring ta duba da sauri gabanta na ci gaba da faduwa, wata lamba ce ke kiranta tayi picking tayi shiru, taji an mata sallama ta amsa, mutumin ya gaisheta yace "Hajiya Hamisu ne ya aiko min lambarki, naga jirgin ku ya sauka yanzu, yace za a karasa dake gida, kina ta ina yanzu?" Tace "Na fito outside of the airport" Tahowa taga mutumin yayi zuwa inda take tsaye bayan ya hangota, nan ya kai ta har motar dake jiranta, motar shigen wanda ta shiga a Abuja ne, mutumin ya bude mata back seat ta shiga tace "Nagode" Yayi bowing kansa yayi mata sallama yace "Allah ya kai ku lafiya" Tace "Ameen Nagode" Drivern dake mazaunin driver ya gaisheta yana tambayarta ya hanya sannan ya tada motar suka fita daga airport din yace "Ina muka nufa Hajjaju?" Khaleesat ta Wan yi shiru kamar me nazari, sai kuma tace "Hotoro zaka kai ni" Yace "To Allah ya kai mu lafiya" Suna isa dai dai kofar gidan da ta nuna masa ya tsaya, ya bude motar ya sauka don fiddo mata Trolley dinta a booth, bude motar tayi ita ma ta sauka tana gyara facemask dinta, ta amshi akwatinta a hannunsa sannan tayi masa godiya ta shiga cikin gidan da sauri, Baaba Gaje dake zaune tana tankade garin tuwo ta daga kai tana kallonta, Khaleesat ta Wan sauke Facemask dinta tana murmushi tace "Baaba sannu da aiki" Baaba Gaje ta ajiye rariyar hannunta tace "Khaleesatu? Daga ina kuma haka?" Khaleesat ta duka nan gabanta har sannan tana Wan murmushi tace "Makaranta" Baaba Gaje tace "Ikon Allah, to ai ko minti ashirin banyi da dawowa daga gidanku ba kuma ba ace min kina hanya ba" A hankali Khaleesat tace "Baaba ya jikin Ummanmu fa?" Baaba Gaje tace "Kaddai ba a san kin biyo hanya ba kika taho Khaleesatu?" Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Baaba Gaje tace "Ikon Allah, to ai jikin nata da sauki er nan, shi Awdul din ne ya biya maki kudin jirgi kika dawo?" Khaleesat ta girgiza kai gabanta na faduwa tace "Bai san na dawo ba Baaba" Baaba Gaje tace "Ikon Allah, to bari in kira Parida, ko kuma ke ki kirata da kanki, Gwara da kika yi dubaran zuwa nan kada Salubabben uban nan naki ya sa ki a bakin duniya mu shiga uku, Ga tabarma taho ki zauna ki huta, irin wannan tafiya me nisa haka, naji ance Amurkan har yapi legas nisa ko? Kira Paridan mu ji yanda za ayi" Khaleesat ta zauna gefenta ta bude handbag ta ciro wayarta, duk da yanda gabanta ke faduwa haka tayi dialing din lambar kanwar Ummanta Aunty Farida, Baaba Gaje tace "Auu to ai Parida ba waya a hannunta wai an sace a mota" Khaleesat ta daga kai tana kallonta, Baaba Gaje tace "Abinda zai faru kawai ga garin tuwon nan ki karasa tankade min ga can murhu na dora ruwan tuwo in yayi ki min talgi ki tuka tuwon in ya silala ki kwashe, ga kuma kayan miya can bai dai da yawa ki jajjaga ki kada min miyar kuka, ni kuma sai in koma can Mariri yanzu in sanar ma Ummanku kin zo" Khaleesat tace "Toh Baaba" Mikewa Baaba Gaje tayi ta figi yakunennen gyalenta a igiyar shanyan dake Wan karamin tsakar gidan ta yafa tace "Bara inje, dama ina da canjina dari da hansin sai in roke masu Wan sahu su kai ni ko Farawa ne sai in karasa Maririn da kafa ta" Khaleesat ta bude handbag dinta amma sai taga Dollars kawai, ta daga kai ta kalli Baaba Gaje tace "Wallahi bani da kudin Nigeria a nan Baaba, amma bari in ciro a POS yanzu sai in baki kudin adaidaita sahun" Baaba Gaje tace "Aa yi zamanki kiyi aikin da na sa ki, minti nawa ne nan da Mariri, kawai dai ga wanke wanke can bakin kwararo ki wanke min har su, ki share tsakar gidan nan, in yaran nan suka dawo islamiyya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login