Showing 90001 words to 93000 words out of 241367 words

Chapter 31 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1551

suka hau yi sojan na kokarin calming dinsu, Sai kuma ya sake kallon Khaleesat yace "Baki san shi ba? To garin yaya kika shiga motarsa?" Tana shessheka tace "Kawai dauko ni yayi a unguwanmu wallahi, ni ban san shi ba" Tuni matasa yan zaman kashe wandon dake wajen suka fusata suka zagaye Abdul suna dure duren ashar suna kokarin fara mazgarsa, gaban Eatry din ya cika da jama'a an zo kallo wasu har sun fara video, with the intervention of the soldier and the security men da wasu responsible mutanen dake wajen aka saka Abdul cikin motar Sojan don tsaf sun kula matasan za su yi aika aika ne a wajen, wannan opportunity din Khaleesat tayi using cikin dubara ta sulale cikin jama'ar wajen without letting anyone to notice her don gaba daya hankalin mutane ya koma kan Abdul a wajen, a haka ta samu ta tsallaka titi ko waigawa bata yi ta afka wani layi, nan ma tayi ta tafiya da sauri da sauri gabanta na faduwa, duk inda taga alamar hanya ce haka ta dinga bi ba tare da tasan inda zata ba, tafiyar kusan minti arba'in tayi a kafa hawaye na zuba idonta, ko sanin unguwan da take bata yi ba, daga karshe tsabar yanda ciwon kai ya matsa mata ga jiri dake ta kwasarta ya sa ta samu gaban wani gida ta zauna ta hade kanta da gwiwa tana shesshekan kuka, tana ta zaune for almost 10 mins wani mutumi dake Wan nesa da ita yana zaune kofar gidansu ya mike ya nufota, don tun da ta shigo layin ta zauna ya ganta, sallama yayi mata ta dago kanta a tsorace, yace "Baiwar Allah lafiya dai ko?" Ta girgiza masa kai da kyar tana goge idonta tace "Bana jin dadi ne, kuma gida zan je" Yace "Ikon Allah, to ina ne gidan naku?" Without second thought tace "Hotoro" Yace "Hotoro? To bari in samo maki adaidaita sahu sai ya kai ki" Ta gyada masa kai cikin rawan murya tace "Nagode" Ya juya ya bar wajen, bayan wani minti goman sai gashi ya dawo cikin adaidaita sahu bayan yaje har bakin titi ya samo mata adaidaita sahun, ya sauko daga ciki yana kallonta yace "Toh ga adaidaita sahun na samo maki Hajiya" Tace "Nagode" Ta mike da kyar ta dafa adaidata sahun sannan ta shiga ciki, mutumin ya ciro wayarsa ya mika mata yana kallonta yace "Ki saka min lambarki sai inji ko kin isa gida lafiya" Ta girgiza masa kai a hankali tace "Matar aure ce" Mutumin yace "Ohh, na gane to, Allah ya tsare Hajiya, Allah ya baki lafiya, na biya sa kudinsa ba sai kin basa ba" Ta gyada masa kai tace "Nagode, Allah ya saka da alkhairi" yace "Ameen ya Allah" a haka mai adaidaita sahun ya bar layin. Har suka isa hotoro Khaleesat bata san sun iso ba, sai da me adaidaita sahu ya ankarar da ita, dai dai kofar gidan Gaje ta sa ya tsaya, ta sauka tayi masa godiya ta shige cikin gidan, nan gaban Gaje dake zaune tsakar gida ta zuba tana kuka kamar zata shide, Gaje tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Khaleesah? Me ya faru? daga ina kike haka?" Da kyar Gaje ta lallashi Khaleesat tayi shiru bayan lokaci me tsayi, sannan ta fara gaya mata abinda ya faru, Gaje ta saki salati a rikice tace "Mun shiga uku mun lalace, yanzu gidan yan sanda suka tafi da Awdul din kenan?" Cikin kuka Khaleesat tace "Ban sani ba nima" Gaje tace "To kuwa zaman gidan nan bai kama ki ba Khaleesah, yasan bayan gidanku baki da inda zaki taho a kano da ya wuce gidana ko gidan Nenne, wannan fa ba karamin kess bane, Awdul na zuwa nan ya ganki sai ya zata da hadin bakina kika yi abinda kika yi, ya sa yan sanda su kulleni in shiga uku" Cikin kuka Khaleesat tace "Toh ya zanyi yanzu Baaba Gaje?" Gaje ta mike ta figi gyalenta a igiya tace "Ta shi mu je" Jikin Khaleesat na rawa ta mike ta bi Gaje suka fita daga gidan, da kafa suka tafi gidan kawar Aunty Farida da ake ce ma Maman Fu'ad, bayan sun shiga gidan Gaje tayi mata bayanin duk abinda ke faruwa, Maman Fu'ad tunda ta rike haSa har gaje ta gama bada labari bata iya tace komai ba, Gaje tace "Don haka ki rufa mana asiri Sadiyah ta kwana gidanki zuwa gobe a ga abinda hali zai yi" Maman Fu'ad ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Khaleesat, gwalo ido tayi ganin jinin da ya kwanta idonta tace "Me ya samu idonki?" A hankali Khaleesat tace "Marina yayi" Maman Fu'ad ta saki salati tace "Mari?? Har sai da jini ya kwanta maki a ido? ga lebenki ma a fashe? A'a gaskiya tsinanne ne wannan mutumi" Gaje ta rike haSa tana kallon idon Khaleesat sai kuma ta fashe da kuka tace "Yanzu wannan har mijin aure ne in ba don Ali ya cuceki ba, dubi fa tafin hannunsa a fuskarta?" Maman Fu'ad tace "Da kyar ma in baya shaye shaye wannan, gaskiya duk yanda za ayi a raba auren nan domin ceto yarinyar nan daga halaka, yanxun nan zan kira farida kuwa" Gaje ta rufe bakinta da sauri tace "Ki kirata kice mata me? Rufa mana asiri ba wanda yasan tana nan, ina me tabbatar maki kilan yanzu an tafi da Awdul din police station, kinga ai dole ya kai yan sandan gidansu Khaleesat don wanke kansa su tabbatar matarsa ce, in kuma yayi haka ai za a bazama nemanta ne a gari" Maman Fu'ad tace "Ba komai Gaje, ki tafi kawai ki kyaleta a nan kar su je can gidan naki baki nan" Gaje ta mike da sauri tace "Don Allah ki bata ruwan zafi in kina da shi tayi wanka" Maman Fu'ad tace "Kar ki ji komai Gaje" A haka Gaje ta bar gidan, yanda Khaleesat taga daren jiya wannan daren ma haka ta gansa, ga ciwon kai, ga ciwon ido, ga zazzabi duk ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, she don't even know who to speak to at this point. Washegari karfe tara Gaje ta shigo gidan, tun daga bakin kofa ta fara ba Maman Fu'ad labarin abinda ke faruwa tace "Sadiyah wajen karfe goma suka zo nemanta a gidana wallahi jiya har da shi Awdul din, ni dai jikina sai rawa yake don tare yake da yan sanda, yanxu haka daga can Mariri nake, uwarta na can hankalinta a tashe ko bacci bata yi ba sai koke koke, uban kuma yace da hadin bakin uwar Khaleesat ta gudu, babu kalan tijaran da Awdul bai yi ba jiya, keee abun dai babu kyau, ni dai hankalina ya tashi sosai, ina tsoron kar a gano ni na ajiyeta Awdul ya hadani da hukuma, shine na zo kawai ta shirya tayi hakuri ta koma gida duk abinda Allah yayi dai dai ne" Khaleesat dake jin duk abinda Gaje ke cewa ta fashe da matsanancin kuka tace "Don girman Allah kar ki ce masu ina nan Baaba Gaje, wallahi har duka zai iya min" Maman Fu'ad dai na tsaye da atamfar mutane da zata yanka ta hau kan keke ta kasa cewa komai sai zazzare ido take, ita ma tsoro take kar daga karshe ace ai a gidanta aka boye Khaleesat, ta ina zata fara ma Baban Fu'ad bayani in aka zo tafiya da ita gashi bai gari, Gaje tace "Toh ya kike so inyi Khaleesah, Awdul fa ya maida maganar nan babban magana wallahi, wai kin tozartasa a cikin mutane jiya kin sa an tafi caji opis da shi, ba ki da kowa da zai tsaya maki a lamarin nan sai Allah, Malam Ali na can kamar zai haukace shi ma ya saka uwarki a gaba sai ta fito dake" Khaleesat ta hade kanta da gwiwa tana shesshekan kukan, Gaje ta make hannun Fu'ad dake ta jan yakunannen gyalenta sannan ta ja kujeran tsugunno ta zauna ta rafka uban tagumi tace "Ni dai ban san kuma yanda zan maki ba Khaleesah, ina talaka da ni Awdul yasa a daureni wa zai cece ni, sai ma Kinga kallon da yake min jiya kamar bai yarda da ni ba" Khaleesat ta dago da kyar tana kallon Baaba Gaje hawaye na sauka idonta, Baaba Gaje dai zai zazzare ido take tace "Ni ban ma yarda bai sa CID unguwar nan su kula da shige da fice na ba, yanxu hka sai da na zaga kamar zan je Yan kaba sannan na taho gidan nan" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "Don Allah Baaba Gaje ki min alfarman dauko min jakana a can gidanmu" Baaba Gaje ta gwalo ido tace "Wani jakar?" Khaleesat tace "Karamin jakata, akwai wayata a ciki zanyi amfani da shi" Baaba Gaje tace "Um um Khaleesat, ta yaya zan dauko jaka ana gani na da rana tsaka?" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "Karamin jaka ne bai da girma, ko a gyalenki zaki iya boyewa don girman Allah ki rufa min asiri ki taimakeni Baba Gaje ki dauko min, har da kudi cikin jakan, zaki ga jakar kusa da akwatina a gefen katifar Umman mu" Maman Fu'ad dai sai baza ido take taji Khaleesat zata bar gidanta amma shiru bata ji ba, can dai tace "To ke ina kika nufa daga gidan nan yanzu?" Khaleesat na share hawayenta a hankali tace "Idan ta dauko min jakar zan san inda zan je in sha Allah" Maman Fu'ad ta sauke boyayyen ajiyar zuciya, faridan ma bazata kira ba kar daga karshe a gane ita ta ajiye Khaleesat a gidanta ta shiga uku, Da kyar Baba Gaje ta yarda zuwa Mariri dauko jakan don duk a tsorace take, shi ma sai da Maman Fu'ad ta saka baki tunda taji ance in dai aka dauko jaka to za a bar gidanta, shi sa tayi ta lallaba Gaje taje Mariri dauko jakar, bayan kusan awa daya sai ga Gaje da jakar ta kudundunosa a gyalenta, Khaleesat ta amsa jakar ta bude ta ciro wayar Jay dake ciki, ta ga dollars din da ya bata suna ciki har sannan, Call log ta shiga sai kuma ta kalli Maman Fu'ad tace "Don Allah ki ara min wayarki bani da Sim card a nawa" Maman Fu'ad tace "Ai ko babu kati, tunda ga wayar Gaje bari in bada dari biyu a siyo sai ki saka a nata wayar ki kira" Nan duk dubara Maman Fu'ad tayi kar a ga Khaleesat tayi kira da wayarta idan bincike yayi bincike, Gaje ta mika ma Khaleesat wayarta ta fita ta amso mata katin dari biyun da Maman Fu'ad ta dauko ta bada, Khaleesat na saka katin ta fara dialing number Jay, ta kira yafi sau biyar sai dai kiran ya dawo mata alamar bai je ba, bata hakura ba still tayi ta kira baya shiga bata san ko katin ne yayi kadan ba kuma Number sa na Nigeria yake using a can din ma, wasu sabbin hawayen suka fara sauka idonta ta sake shiga call log din wayar tana scrolling slowly, number AJ ta gani shi ma Nigeria Line dinsa, ta Wan yi jim tana kallon number, sai kuma tayi dialing tana share hawayen dake zuba idonta, ringing ya fara yi har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa, sai da ya kusa katsewa sannan yayi picking, muryarta na rawa tace "Good Afternoon" Shiru yayi, kafin yace "Wacece?" Ta sauke idonta tace "Ni ce" Yace "Ke wa?" Da kyar tace "Plss i want to speak to you" Kawai ta fashe da kuka uncontrollably, shiru yayi for almost 15 seconds, can yace "What happened?" Tana kuka tace "I need to speak to you pls" Ya kara yin wani shirun, can yace "Where are you?" Tace "Hotoro" He still kept quiet for some seconds kafin yace "Address" Katse wayar Khaleesat tayi ta tambayi Maman Fu'ad address din unguwan, Maman Fu'ad ta gaya mata sannan ta tura masa ta message, Gaje dake zaune kan kujera tace "Wanene wannan din da kika kira?" Ita dai Khaleesat tayi shiru wasu hawayen na taruwa idonta, Baba Gaje tace "Gashi idon naki sai kara ja yake yi, wallahi makantar da ke kawai yayi niyyar yi matsiyacin nan" Bayan kusan 35 mins wayar Gaje ya fara ring, Gaje ta mika ma Khaleesat da sauri tace "Ko wanda kika kira ne?" Khaleesat ta amsa tana kallon wayar taga AJ ne ke kira, dagawa tayi yace "I am outside" Khaleesat ta ajiye wayar sannan ta kalli Maman Fu'ad tace "Aunty don Allah kina da Nikab?" Maman Fu'ad tace "Yaushe rabona da Nikab, bani da shi yanzu kam" Khaleesat ta mike tana rike da handbag dinta da wayar Jay ta fita daga gidan, not far away from the house yayi parking, yana jingine jikin motar ya rungume hannunsa looking at a different direction, tana tafiya a hankali ta nufesa tana kallonsa, tana isowa kusa da shi ya juya jin Footstep, ya gyara tsayuwarsa ya dinga kallon idonta babu ko kiftawa, she tried her best na ganin bata fashe da kukan da ya taho mata ba amma ta kasa daurewa ta hade kanta da jikin motar ta fara kuka har da shessheka.
[5/26, 9:21 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Ajay bai ce mata komai ba sai da tayi kukan me isarta don kanta tayi shiru, tana share idonta ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake har sannan, Calmly yace "He did all this to you?" Kai ta gyada masa wasu hawayen na taruwa idonta, yayi shiru for a while kamar me nazari, sai kuma yace "?an kano ne?" Nan ma ta gyada masa kai, yace "A ina yake a kano?" Muryarta na rawa tace "I don't really know" Zai yi magana Baba Gaje ta leko kofar gidan kamar munafuka tana zazzare ido, Ajay ya Wan sauke kansa ya gaisheta bayan sun hada ido da ita, fitowa tayi da sauri tana kalle kallen Unguwan tace "Lafiya lau Wan nan, wallahi yarinyar nan tana cikin mummunan masifa, bata da kowa sai Allah, ta dawo daga turai ta tarar an daura mata aure da lafcecen yaron nan Wan iska, dama kuma duk mun san Wan iska ne muke kauda kai tunda bamu da yanda za mu yi, ashe bai ma yi shawara da ita ba kansa tsaye ya taho ya samu iyayen da ya raina suka daura aure shekaranjiya, to tunda tace bata son auren in dai ba tsinannen mutumi ba ai sai ya kyaleta ga mata kaca kaca a duniya, wani mugun kuduri ne a ransa haka da yasa aka daura auren a gaggauce ko shiri babu? dubi fa abinda ya mata a fuska daga ya dannata a mota taki bin sa, yanxu haka duk ya baza CID a unguwan nan ana nemanta, sai kaga tijaran da yaje ya ma iyayen nata jiya da daddare, shi sa ka gan mu duk a tsorace" Tun da ta fara magana Ajay ke kallonta ko kiftawa baya yi, mamaki ne sosai kwance a fuskarsa, can ya kalli Khaleesat dake kuka kamar Baaba Gaje na dada tunzurata, ya sake kallon Gaje yace "Aure kuma Mama?" Gaje tace "Wallahi da gantalallun igiyoyinsa har uku a kanta yanxu haka, tun jiya ta gudo nan bayan ta samu ta tsere da kyar daga hannunsa" Gaje ta fashe da kuka tana matsar kwalla da gyalenta tace "Wallahi bata da kowa sai Allah, iyayen basu da bakin magana, basu da ta cewa, ni kuma ba kowa bace makociyarsu ce mun yi zaman Mariri tare kuma ni talaka ce, ni ko taimaka mata ne kayi ka kai ta wajen masu kare hakkin Wan Adam ta kai masu kukanta su kwato mata hakkinta da ake neman tauyewa" Har sannan Ajay ya kasa cewa komai, can ya bude gaban motarsa yana kallon Khaleesat, Baaba Gaje ta fara tura ta ciki tace "Maza shiga ku je ya kai ki ofishinsu, in ma rike ki za su yi su rikeki ki zauna har sai sun bi maki hakkin ki, amma kar ki ce nasan komai, kar ma ki saka ni a maganar" Khaleesat dai kuka kawai take ta shiga motar, Baba Gaje ta amshi wayarta dake hannunta ta kulle motar gbamm tace "Maza ku je" Ajay dai ya zaga ya bude driver seat ya shiga, Da sauri Baaba Gaje ta koma gate din Maman Fu'ad kamar ba daga kusa da motar ta taho ba, ta makale tana kallonsu har suka fita daga layin, driving kawai AJ yake idonsa a kan titi, gaba daya he look speechlesss, tunda ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba, ita dai Khaleesat ta rufe fuskarta da Hijab dinta saboda hasken rana dake damun idonta kuma tana tsoron kar ace su hadu da Abdul dan motar babu Tint, har sannan bata daina kukan tashin hankalin da take ba, after driving for 20 mins AJ ya kalli wayarsa dake vibrate, Number Jay ne ke kiransa, hakan ya sa ya rage tafiyar da yake ya gangara gefen titi yayi parking sannan ya dau wayar yayi picking ya kai kunne a hankali yace "Jay" Khaleesat ta zame hijab dinta daga fuska jin sunan da ya kira ta juya ta kallesa, Calmly taji yace "I am cool" tambayarsa Jay yayi ko ya bar Kano, AJ yace "Am still around, when are you leaving Maryland?" After few seconds AJ yace "Alright, we will talk later" Daga haka ya katse wayar ya ajiye ya jinginar da kansa jikin kujerar motar ya kafe titi da ido for almost 2 mins, can ya sake daukar wayarsa don duba available flight to Abuja ranan, yaga jirgin karfe uku kuma saura just few seats, National ID card dinta da passport dake motarsa tun ranan da suka dawo US da drivern su na Lagos ya amsa a wajenta don mata booking ticket to kano, ticket ya siya mata immediately na zuwa Abuja sannan ya ajiye wayar, Aunty na nan gidansu na kano sun zo biki shi sa ma bazai fara kai ta can gidan ba, juyawa Khaleesat tayi da kyar ta kallesa tana dafe kanta pleadingly tace "Kanwar Ummata tana Lagos, don girman Allah ka taimakeni i want to go to

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login