Showing 201001 words to 204000 words out of 241367 words

Chapter 68 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1553

tausayin kofar, Ajay da har ya kashe wutan dakinsa ya kalli kofar babu ko kiftawa, sai kuma ya gyara kwanciyarsa bai motsa daga inda yake kwance ba, Khaleesat ta fi minti biyar bakin kofar bata kuma fasa knocking din da take ba, cire Duvet din jikinsa yayi ya jefar gefe sannan ya sauka daga kan gadon fuska daure ya nufi kofar ya bude yana kallonta at the same time cutting her a serious warning yace "Ki ka sake knocking din min kofa zan maki walakanci wallahi, why are you such a nuisance? Pls get out before i loose my temper" Khaleesat dake kallonsa ta wani hade rai tace "To ta window kake son in fita daga gidan bayan kofar parlon a kulle yake??" Yace "Ki bi ta roof ma ba window ba" Yana fadin haka zai kulle kofarsa tayi saurin shiga cikin dakin kamar zata fashe da kuka ta nufi tsakar dakin ta tsaya tace "Kasan dalilina na cewa zan tafi gida ne? Kawai kayi ta ma mutum masifa baza ka tsaya kayi considering dinsa ba ka basa listening ears, kawai haka nan zan taso cikin daren nan in ce zan tafi gida? Ni ban ce sai kai ka kaini ba ka zo kawai ka bude min kofa inyi tafiyata...." Magana take amma gaba daya hankalin Ajay na kan dakinsa da ta shiga kai tsaye, he look shock irin he didn't see that coming, he ignored her ailment that he understood immediately, ya Wan yi calming din kansa yana kallonta yace "Saboda kin ga ranan ya shigo dake nayi persuading kaina ban yi reacting ba sai kika yi zaton public room ne wannan? An gaya maki ko shi Jay din yana shigar min daki anyhow? Baki da hankali ne or are you out of ur mind? Come and get out before u push me to the wall, kuma kar ki kuskura ki taka min carpet dina da wannan kafafuwan naki, wannan filthy dakin da kika shiga kika kwanta duk ?ura da datti common sense dinki bai gaya maki ki share dakin ki goge ba sannan kiyi changing bedsheet, sannan zaki shigo min da?i ki kakkabe min du? kuran da kika kwasa a jikinki ki cuceni, plss come and get out before i loose my temper...." A fusace ya kare maganar yana kara bude mata kofa da kyau ta yanda zata zo ta fita, Khaleesat ta wani taSe baki tace "To ai sai kaje ka bude min kofar parlor" Tsawa yayi mata yace "Baza ki fice min daga daki ba?" Ta fashe da kuka ta nufi kofar tace "To kasan me yasa zan je gida ne, ko ba saboda urgent issue bane" Yace "Ke kika san urgent issue din, get out of my room" Ganin he is damn serious don gaba daya mood dinsa ya canza tun da ta shiga dakin yasa ta fita daga dakin tana kallonsa tace "Don Allah ka bude min kofar parlon before it's too late" Banging kofar dakinsa yayi ya kulle, Khaleesat ta dinga kallon kofar, after a minute sai gashi ya fito, ya saka takalmin da yake yawo da shi a gidan, ta bi sa da kallo sai kuma ta bi bayansa tana hararansa, downstairs ya sauka ya tafi ya bude mata kofar parlon, tana tafiya a hankali ta karasa bakin kofar sannan ta fita tana kallonsa, kulle kofar parlon yayi, Khaleesat taji wani sanyi don iya Hijab ne jikinta babu rigar sanyi, walking slowly ta fita daga compound din gidan gaba daya wani mugun sanyi ke shigarta, sai yanxu ta kara tabbatar da Ajay mugu ne kuma ba shi da conscience, ta ciro wayarta taga ko zata iya order din ride, tana ta tsaye a Neighborhood din bayan ta duba ride din, after almost 5 minutes taga hasken fitilar mota daga compound din gidan, dauke kai tayi har ya fito da motar, taga yayi parking inda take tsaye, ta wani kallesa, fuska daure yace "Do not waste my time Malama" Ta wani tura baki ta bude front seat, sai dai kuma tsoro take kar ta zauna ta Sata masa motar ta shiga uku, haka dai ta shiga sai bata sake jikinta gaba daya a zaune ba, tana shiga ya ja motarsa, har suka isa apartment dinta bai ce mata komai ba, bayan yayi parking murya can ciki tace "Nagode" Daga haka ta sauka daga motar ba tare da ta kallesa ba ta nufi kofar apartment dinta ta bude da makulli ta shiga ciki, bata kulle kofar ba ta tsaya jikin window ta Wan bude labule kadan tana lekawa taga ko ya tafi, haska inda ta zauna taga yana yi da wayarsa, ta zaro ido ta juyo hijab dinta da sauri sai taga bata yi stain ba, ta sake kallonsa taga ya gama haske haskensa ya kashe fitilar wayan, ta ma san kilan ya gane me yasa tace zata dawo gida, turo baki tayi saboda kunyan da taji, tana ta tsaye jikin window har bayan minti biyar bata ga yayi Reverse ba, ita kuma so take taga tafiyarsa sannan ta kulle kofarta da makulli don saboda zuwan da yayi daxu ya bar mata kofa a bude Aymaan ya fado mata gida kamar barawo, bude motar taga yayi after almost 10 mins ya fito, sai da taga ya nufo kofar apartment din sannan ta ruga sama da sauri ta shige dakinta... Ko da Khaleesat ta shiga bandaki taga hatta kayan jikinta ma bai yi stain ba, pad din da ta siyo tun daga Nigeria ta dauka a cikin akwatinta, bayan ta gama gyara jikinta ta fito ta canza kaya sannan ta saka rigar sanyinta ta kwanta, wajen karfe dayan dare Khaleesat ta farka daga baccin da ya dauketa a firgice duk da bata dade tana baccin ba ta mike zaune zuciyarta na bugawa, mafarki tayi wai Aymaan ya zo yana ta bubbuga mata kofa, dama kuma har tayi bacci hankalinta na kan kofar parlor ko ya tafi ya kulle mata kofar ko a bude ya bar mata oho, a hankali ta sauka daga kan gadon ta bude dakinta ta fita corridor tana leka downstairs, kwance ta gansa kan kujera idonsa a lumshe ya maida wutan parlon zuwa dim light, a hankali ta sauka downstairs din yanda bazata yi making sound ba, after some seconds ta koma sama ta dauko masa duvet, tana dawowa parlon ya bude ido, ta koma baya tana kame kame tace "Duvet ne, naga akwai sanyi sosai yau...." Ya nuna kansa yace "I should use ur duvet? Me? Ke da kika iya shiga daki duk ?ura da datti comfortably ki kwanta shi ne zaki kawo min duvet din ki i should use saboda nayi hauka, ai duk macen da zata iya zama comfortably cikin daki me datti da ?ura without cleaning it, kuma ta dinga yawo a gida babu takalmi a kafarta to babu kalan kazantar da bazata aikata ba, shi yasa taku ta zo daya da Jay, bird of the same feathers, ba gwara in kwanta sanyi ya kasheni ba da inyi amfani da abinda ya fito daga dakin ki, kujeran nan ma don sabbin furnitures ne yasa na kwanta" Khaleesat ta wani kallesa, sai kuma ta juya ta koma sama da duvet din, kuma sabo ne ko amfani da shi bata taSa ba a ledansa ma ta ciro yanxu, can kasan ranta ta dinga ce ma kanta Allah ya kara mata, tsaki ta ja bayan ta shiga daki ta kulle kofarta da makulli tayi kwanciyarta. Washegari wajen karfe bakwai Khaleesat ta fito daga dakinta, bata gansa a parlon ba, hakan yasa ta sauka downstairs ta tafi kofar ta murda taji a kulle, ta leka garage taga babu motarsa, tabe baki tayi ta wuce kitchen don dama da yunwa ta kwana, sai wajen karfe goma ta gama duk abinda take ta bar gidan zuwa school, har suka gama lectures bata sake fuska ba ranan, tun Safiyyah na jan ta da magana har ta gaji ta kyaleta, bayan sun fito department Safiyyah na kallonta tace "Is there any problem Khaleesat? Naga gaba daya yau mood dinki babu kyau" A takaice Khaleesat tace "Nothing" Safiyyah tace "Ke dai ki gaya min gaskiya, kila ma haushina kike ji ban sani ba ma" Sai a sannan Khaleesat ta kalleta tace "Saboda me bazan ji haushin ki ba Sophie? Kawai kin ja Wan iska mara kamun kai ya shigo rayuwata ina zaman zamana, you caused me all this wallahi" Safiyyah tayi shiru, sai kuma a hankali tace "Wai Aymaan? Wallahi ban san Wan iska bane Khaleesat, kin ji na rantse, na zata yana da kamun kai ne yanda nake ganinsa sumi sumi a department" Khaleesat tace "To jiya wajen karfe shidda na yamma sai gashi a apartment dina unfortunately na bar kofa a bude kawai ya fado min cikin parlor kansa tsaye" Bude baki Safiyyah tayi tana kallon Khaleesat ko kiftawa babu with shock, a hankali tace "Apartment din ki kuma Khaleesat? Na shiga uku, sai aka yi yaya?" Khaleesat taki bata amsa don takaici, Safiyyah ta hade rai tace "To kuwa sai nayi masa hauka, uwarsa yaje nema maki a gida ko an gaya masa kowa shege ne kamar sa?" Kallonsa kawai Khaleesat take daga nesa har ya nufo inda suke zaune, Safiyyah kuwa ko lura da shi bata yi ba rai bace take cewa "To ke baki kira masa Cops ba? don Allah ki gaya min sai aka yi yaya da yaje apartment din naki? Yau ga mahaukaci kai" Juyawa Safiyyah tayi ganin shadow din mutum a gabansu, yana kallon Khaleesat da kyau yace "Kara ta kika kai gun wancen garan don ya min me? Me kike tunanin zai iya min? Muscles dinsa na banza har ni zai nemi ya daka? Who did he think he is? Me yake takama da shi? Sarautar tasu da bata taka kara ta karya ba ko me? Sannan naga kamar yana mance a America mu ke not Nigeria, ni zai nuna ma dabanci bai san course dinsa nayi a Nigeria ba?" Safiyyah ta mike tace "Look Aymaan, ita fa Khaleesat ba irin wa ennan shegun matan da kake tunani bane gaskiya, ka bar ganinta sakaka a Amurka, yarinya ce ita me mutunci da ta san ciwon kanta, kuma harkar duniya bata gabanta wallahi, wannan get together din ma ni na ja ta don dole taje ba wai ra'ayinta bane shi yasa throughout ta kebe gefe daya a wurin u saw that too, shi kuma wanda kake kira da gara fiance dinta ne, ba wai shisshigi yake yi ba, sannan sarautarsu kuwa ta taka kara ta karya don gidansu a nan Amurka ma ba ko wani shege bane a Nigeria ke iya mallakan irin wannan babban gidan a wata kasar, kai kuma naga hayan apartment kake a Amurkan, Sannan iyayen Khaleesat basu fara turata wata kasa karatu ba sai da suka tabbatar da mijinta a hannu, kuma shi ma a kasar yake, ka ga ai baza kace masa gara ba" Aymaan na mata wani kallo yace "Ke ki iya bakin ki kar ki ja ma kanki matsala a rayuwarki, Fiance din banza, a ina Fiance ya zama miji? ranan daurin aure ma an fasa balle common Engagement, shi da Engagement din yake takama dama?" Safiyyah tayi wani shewa tana rike kugu tace "Na ga kamar ba zaman lafiya kake so ba Malam, to wallahi idan baka fita harkar kawata ba a kasar nan a gaban idon ka zan kira maka 911 in lafta maka sharrin da babu me fitar da kai sai Allah, kamar yanda ka fada nan ba Nigeria bane tuni za ayi mana maganinka wallahi, kuma Unguwan da take tsaf za a bincika surveillance camera a ga sanda ka shiga apartment dinta ta yanda za a tabbatar ba sharri aka maka ba..." Aymaan ya gyara tsayuwa yana kallonta da kyau yace "Really?? dama ke mahaukaciya ce ban sani ba?" Safiyyah tace "Dawanau ce ni karewa, wallahi idan baka yi hankali da mu ba a kasar nan zaka ga jahilci tsantsa, ai ni da nake ganin ka sumi sumi a makaranta ban san gogaggen dan iska bane kai sae yanxu, to banda Wan iska waye zai fada apartment din mutum kamar gidan ubansa? Ashe dama ciwon ?wa?walwa gare ka ake yada jita jitar ciwon zuciya gare ka?" Har ya daga hannu zai wanka mata mari sai kuma ya rike fist dinsa ya cije hakora yana kallonta yana huci, Safiyyah tayi wani dariya tace "No slap me, try it plss, mare ni mana.... wallahi rabon ayi deporting dinka back to Nigeria a cikin jirgin ruwa ne ke tunzura ka, try slapping me ka ga ikon Allah" Yace "Daga ke har kawar taki zan yi maganin ku wallahi...." Daga haka ya juya kamar zai tashi sama ya bar wajen, Safiyyah tace "Ni wallahi da aka ce min babanka Deputy ne sai da kunya ya kamani ranan na rufe fuska, na zata Wan vice president ne kai irin wannan jijji da kan da kake ashe common Deputy ne ma da ba a san da ku ba a Nigeria, kuma in ka fasa maganinmu baka cika namiji ba wallahi, dama ana ganinka an ga kwararren Wan shaye shaye Wan codeine, ban san wani tsautsayin yasa har mu ke gaisawa da kai ba banda nima dai gantalalliya ce bani da kamun kai"
[7/13, 1:42 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Khaleesat tsabar yanda ta zama shock kasa cewa komai tayi a inda take zaune kamar ruwa ya cinye ta, ta shiga uku ita kam ga kuma wani da yafi Abdul tashanci, Safiyyah na huci tace "Ta shi mu je, don dai ban san yanda ake yi bane a kasar nan, da Nigeria ne ai daga nan police station na nufa in je in kai report, to su nan ban san ko ana haka ba" Ita dai Khaleesat ta kasa tashi don duk jikinta yayi sanyi kamar an watsa mata kankara, Ganin Khaleesat taki tashi Safiyyah tace "Ki tashi mu tafi don Allah kar ya sake dawowa" Khaleesat ta kalleta tace "In tafi ina? Am not going anywhere Safiyyah, haka kawai in koma apartment dina ya bi ni can?" Safiyyah na huci tace "Kuma fa haka ne" Khaleesat ta dafe kanta da yayi mata nauyi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Safiyyah tace "Wannan fa kamar ya fi Abdul zama Wan daba, ni wallahi ban san haka yake ba da ko hanyar da ya bi a makarantar nan ma bazan dinga bi ba, in ba dai in danna 911 yanxu su taho ba gaskiya" Khaleesat ta wani kalleta tace "Su taho su yi maki me? Kar kiyi dialing ki bari sai na bar nan tukunna" Safiyyah ta koma ta zauna tayi tagumi, Khaleesat ta bude handbag dinta duk jiki a sanyaye ta ciro wayarta, ta fi second talatin ta kasa dialing number Ajay don ta tsani masifarsa ita kam, but did she have a choice? Haka kawai ta koma Apartment dinta Aymaan ya bi ta ko kofar a kulle yake ya balle ya shigo mata ta shiga uku, ita sai yau ma ta kare masa kallo kana ganinsa kaga someone on drug shi yasa idonsa suka zama kamar me sexy eyes ashe tsabar shan kwaya ne, Safiyyah ta kalleta tace "Dole dai wancan mara mutuncin za ki kira, don ni wallahi bana son Ajayn nan gwara Housemate sau miliyan, ki ji fa ranan har da korata saboda kawai zai maki magana sai kace bai san yanda muke da ke ba, ya maida ni kamar wata bare ranan, abinda Housemate dinki bazai taSa yi ba kenan yace in tashi wai zai maki magana, tun daga ranan na kullacesa a raina wallahi, ashe haka yake da ba?in hali ban sani ba, nace masa good afternoon wai ya amsa da evening tsabar rainin hankali, pls i don't like him" Khaleesat tace "To ina da wanda zan kira bayan shi ne?" Safiyyah tace "Yaushe Housemate din naki zai dawo ne? Gaskiya we are missing him yayi maza ya dawo" Khaleesat tace "Oho" Daga haka tayi dialing number Ajay, sai da ya katse ta sake kira sannan ya daga, taji yace "What again Madam?" Hurriedly yayi tambayar as if in a haste to cut the call, ta sauke idonta a hankali tace "Zuwa yayi ya same mu a department ni da Safiyyah" Ajay yayi shiru, sai kuma yace "Sai aka yi yaya?" A sanyaye Khaleesat ta gaya masa abubuwan da ya zo ya fada da kuma yanda suka yi da Safiyyah daga karshe, Ajay dake ta sauraronta yace "Kin ga wannan kawar taki me shegen rawan kai sai ta ja maki bala'in da baki yi tunani ba a rayuwarki, who sent her to exchange words with him? Duk ba ita ta kai ki inda kika hadu da gayen ba? And meye kike son in maki da kika kirani yanxu?" Khaleesat ta katse wayarta ta ajiye, Safiyyah dake ta kallonta tace "What is he saying?" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, sai ga wayarta ya fara ring ta duba taga shi ke kiranta, Safiyyah ta taSe baki tace "Allah sarki Housemate gaskiya yana kokari da wannan Ajay din ashe haka yake? Wallahi yanda kika san Malamin islamiyya haka nake ganinsa ni dai yanxu, kullum a fusace yake, ki daga kar ya katse, ni yanxu na gaya ma Mustapha wannan magana ai zai gano na tafi Party bayan ce masa nayi baki da lafiya zan je apartment din ki daga schl ranan" Khaleesat tayi picking call din ta kai kunne taki cewa komai, yace "Kashe min waya kika yi?" Tace "To me zan yi idan ban kashe ba, kawai kayi ta ma mutum masifa kullum" Yace "Sai ki je kiyi sorting self din ki out" Daga haka ya katse wayarsa, Safiyyah tace "Tirrr, anya wannan zai iya zama da mace kuwa? Ina ga a world din da ya tashi iya maza ne kawai suka yi surrounding dinsa, amma sam bashi da sympathy wa mace, kawai tashi zaki yi mu tafi gidan Yaya Mustapha don nima ban baki goyon bayan zuwa apartment din ki ba, Aymaan drugs din da yake sha basa gaya masa gaskiya" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, gaba daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login