Showing 6001 words to 9000 words out of 241367 words

Chapter 3 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1591

wanda iyakarsa lips after paying attention to their conversation, mikewa Khaleesat tayi tana share hawayen dake sauka idonta, sai a sannan ta lura da shi a parlon, dauke kai tayi da sauri bayan sun hada ido, gaba daya ta ma mance yana parlon, taji yace "Is that ur Father?" Wani kallo ta jefa masa tayi wucewarta dakinta wasu sabbin hawayen na zuba idonta, ruf da ciki tayi kan gadonta tana kuka har da shessheka, ta kusa minti arba'in kwance a yanda take, zuwa sannan ta dena kukan da take kawai ta lumshe ido, knocking din kofar dakinta da taji anyi at the same time aka bude ne yasa ta mike zaune da sauri don bata san bata kulle kofar ba, hada ido suka yi da new Housemate dinta, yayi dropping ledan hannunsa ya jingina jikin kofar dakin ya rungume hannu yana kallonta da kyau, calmly yace "Like seriously, Namiji kika kwanta kike yi ma kuka?" Ta wani hade rai ta kauda kanta zuwa wani direction din daban, how did he even know she understands Hausa?? yana juya counter din hannunsa as if counting his words yace "It's... funny" Ta juya ta kallesa har sannan fuskarta a daure tace "Excuse you, why will u barge into someone else's bedroom just like that?" Ya daga kafadarsa yace "Zan yi shisshigi in baki shawara ni dai, run for ur dear life cause u are dating a monster as a boyfriend" Yana kai wa nan ya juya ya fita daga dakin closing the door behind him, Khaleesat ta dafe kanta da yayi mata nauyi, daga karshe ta mike ta kulle dakinta da makulli sannan ta shiga bandaki, karfe sha biyu da yan mintuna ta gama shiryawa don wanka tayi, kallon ledan da ya ajiye mata tayi ta dauke kai sannan ta nufi kofa ta bude ta fita, satan kallon kofar bedroom dinsa tayi ta karasa living room, tana tafiya a hankali ta tafi kofar parlon ta murda taji a kulle an sa makulli, leka windon parlorn tayi taga babu motarsa a garage alamar ya fita, tana tafiya a hankali ta shiga kitchen, ta jingina da kofa tana kallon Cereal da bowl din da ta dauko daxu an ajiyesu kan cabinet din kitchen din, juyawa tayi ta fita daga kitchen din ta koma dakinta, ledan da ya ajiye mata ta dauka ta zauna kan kujeran dake dakin tana duba abinda ke cikin ledan, Breakfast Sandwiches ne sai fresh fruit smoothie a ledan.....


07087865788
' [4/30, 5:36 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: https://chat.whatsapp.com/KBwGIidDZY683SzzudJ0zc



('(' HALYSAAH('('




By _Khaleesat Haiydar_
'


3.....


Bayan magrib Khaleesat ta fito living room saboda yunwan da take ji, har sannan bata ji alamar House mate din nata ya dawo gidan ba, gaba daya haka ta wuni ranan babu walwala, all of a sudden yau ta ji a zuciyarta ta fara gajiya da attitude din Abdul da abubuwan da yake mata, da ta tuna Housemate dinta overheard all her conversation with Abdul da kuma maganar da ya gaya mata sai taji wani bakin ciki da takaici ya tokareta at the same time tana wishing that never happened, zaunawa tayi kan kujera ta jinginar da kanta jikin kujeran ta afka duniyar tunanin rayuwarta, after a while ta sauke ajiyar zuciya ta mike tana tafiya a hankali ta shiga kitchen tana tunanin abinda zata dafa ta ci, absently ta fara wanke few utensils din da yayi amfani da shi ya bari a sink sannan ta kunna gas, stir fry pasta ta girka, bayan ta gama ta debi kadan da zata ci ta fita daga kitchen din, dai dai corridor din dakunan ta kusa cin karo da House mate din nata, a firgice tace "Innalillahi...." Sai kuma tayi shiru ta hade rai, ya koma gefe yana kallonta, har ranta taji tsoro don bata san yana gidan ba amma tayi pretending ta hanyar daure fuska, ya daga kafada ya bar wajen ta bi sa da kallon gefen ido.... reading nook dake cikin living room din ta ga ya nufa yana kwashe takardunsa dake kan table, ta dauke kanta ta shiga cikin dakinta ta kulle da makulli, karfe takwas da few minutes ta gama duk abinda zata yi ta dauro alwala sannan kwanta don gobe Monday tana da aji da safe, tana lumshe ido bacci ya dauketa. Cikin bacci Khaleesat taji ana knocking kofar dakinta, ta mike zaune da kyar tana murza ido ta jawo wayarta tana kallon agogo taga karfe goma saura minti biyar, kallon kofar tayi da mamakin dalilin da yasa yake mata knocking by this time, can dai ta daure fuska tace "Waye wannan?" Taji yace "I could use ur help if u don't mind" Bluntly tace "I beg ur Pardon?" A takaice yace "Nayi misplacing makullina again" Da farko rasa ma me zata ce masa tayi don mamaki, she was mute for almost a minutes, taji yace "Hello" Sosai ta hade rai tace "I don't understand kayi misplacing makullin ka?" Yace "Look, ni fita zan yi yanzu idan na fita sai ki kulle gidan" Bata san sanda tace "Idan fita zaka yi ka fita mana, me yasa zaka tambayeni makulli? ko makullinmu a hade yake?" Shiru yayi at first, sai kuma yace "Ta yaya zan fita nace maki ban ga makullin kofa ba" Tace "But our keys are separate isn't it?" Yace "Sai yanzu da kika fada na sani ai, fito ki bude min kofa zan fita" Wani bakin ciki taji ya tokareta, yace "I am waiting at the parlor" Bata tanka sa ba, can tayi tsaki ta sauka daga kan gadonta ta dau hijab ta sa, ta bude handbag dinta ta dau makullinta ta nufi kofar dakin, fuskarta a daure ta bude ta fito ta karasa living room ta gansa tsaye bakin kofar parlon yana jiranta, ko kallonsa bata yi ba kamar yanda shi ma din wayarsa yake dannawa bai kalli inda take ba, ta karasa ta bude kofar parlon da makullin hannunta tace "You weren't given a needle as key da zai dinga Sata kullum, and i shouldn't be responsible always for someone else carelessness" Shi dai bai ce mata komai ba ya fita without looking at her yace "Na zata ai needle aka bani Housemate" Da ido ta bi sa har ya isa inda motarsa take, wato godiyar da zai mata kenan? Ta gyada kai ta kulle kofar parlon a ranta kuma tayi vow bazata sake masa amfani da makullinta ba sai dai kar ya fita, banda ma rainin hankali me yasa baya misplacing makullin motarsa sai na gida, next time sai dai ya fasa zuwa inda za shi don bazata sake sharing key dinta da shi ba, fuska daure ta koma cikin parlor, sai kuma ta tsaya tana kallon plate din da ya ci abinci ya bari a parlon da container din soft drink ga goran ruwa, tsabar mamaki bata san sanda ta nemi waje ta zauna ba, is this guy okay? After fetching her food without asking for permission he still have the mind to leave the plate for her at the parlor, anyway... she believe he didn't leave it for her, he left it for himself instead, don ko sati daya zai yi bai dawo gidan ba zai dawo ya tarar da plate din at that same spot don bazata daukesa ba, tashi tayi ta tafi daki fuskarta a daure. Da safe Khaleesat ta gama shirin fita makaranta, har a lkcn bata dauke plate din da ya bari a parlon ba, amma fa zuciyarta kawai ta kai nesa don ta tsani ganin abu ba inda ya kamata ba, zata kai cup din da ta sha shayi kitchen taji ta taka makulli a kan ash carpet din parlon, dukawa tayi ta dau makullin tana kallo taga nasa ne, he is just careless, tabe baki tayi ta mike ta ajiye makullin nan kan kujera, ta kalli plate din jiya da ya bari, tsaki tayi ta dauke tare da gwangwanin soft drink din da na ruwa, ta hada da cup din hannunta ta tafi kitchen, bayan Wan lokaci ta dawo parlor ta dauki handbag dinta tana duba wayarta, ganin Lyft din da tayi order ya kusa isowa ta nufi kofa ta fita. Wajen karfe sha biyu Khaleesat na zaune tare da Safiyyah warce shigowarta makarantar kenan, Khaleesat na kallonta tace "Kun sha birthday" Safiyyah tace "Oho dai tunda ke baki je ba, yau me ku ka yi a aji?" Khaleesat tace "Nothing much" Safiyyah ta bude handbag dinta ta ciro cake tana mika ma Khaleesat tace "Gashi ba don halin ki ba" Khaleesat tayi murmushi ta amsa tace "Nagode" Safiyyah tace "Kun yi waya da Abdallan ne?" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "Sophie me kika ce masa ta chat?" Safiyyah ta dau wayarta tayi unlocking cikin few seconds ta shiga DM din Abdul sannan ta mika ma Khaleesat wayar, Khaleesat ta amsa tana duba chat din, it was nothing worth taking personal Safiyyah ta gaya masa a chat din, Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba tana kallon wayar hannunta, Safiyyah tace "Me yace maki halan?" Khaleesat ta mika mata wayarta tace "Nothing, kawai yace min kin masa magana" Safiyyah ta tabe baki tace "Kin dai ga yanda yake amsa min chat din ma kamar wani Wan sarki, wallahi Abdallah bai yi deserving dinki ba, u are too good to be Abdul's or to end up with him, Allah ya maki sauyi cikin ruwan sanyi ya kawo maki mafita" a hankali Khaleesat tace "Ki tashi mu je aji" Safiyyah tace "Oh baza ki ce Ameen ba??" Murmushi Khaleesat tayi tace "Wani mafita kenan Safiyyah? Cewa zaki yi Allah ya canza min halayyarsa kawai...." Safiyyah ta tabe baki ta mike tace "Mu je" Khaleesat ta mike suka bar wajen a tare... Khaleesat na sauka Uber din da ya dawo da ita gida ta nufi apartment dinta, dai dai sanda Co-tenant dinta ya fito daga cikin motarsa dake inda aka tanadar domin parking, sau daya ta kallesa ta dauke kai tana ci gaba da tafiyarta toward their apartment, ya bi bayanta yace "I've waited all day long, i forgot some paperwork a cikin gidan gashi zanyi Submitting tun daxu" Ba tare da ta juyo ba tana ci gaba da tafiya tace "Serves you right" Kallonta yake yana biye da ita, ta ciro makulli a jakarta ta bude kofar ta zare makullinta sannan tayi shigewarta ciki ta nufi dakinta da makullin... Bayan Khaleesat ta idar da sallah ta sauya kaya ta fito parlor don daura girki, bata gansa a parlon ba, kuma bata ji alamar ya shiga dakinsa ba, ta nufi tagar living room din tana leka parking space, ganin babu motarsa ta karasa gun kofa ta murda taji a kulle, kallon inda ta ajiye makullinsa daxu da safe tayi taga ya gani har ya dauke, wucewarta tayi zuwa kitchen. Wajen karfe tara na dare Khaleesat ta gama karatun da take ta jawo wayarta ta bude WhatsApp dinta don ganin ko Neighbor dinsu Aunty Sha'awa tayi replying sakon da ta tura mata amma sai taga bata yi reply ba har sannan kuma ta bude message din, ajiye wayar tayi ta mike ta dauke darduman da take zaune kai, ta dau hijab ta saka sannan ta fito parlor zata debi abinci, Zaune taga House mate dinta a parlon yana operating laptop dinsa, without looking at him ta tafi kitchen, after some minutes ta fito, ya daga kai yana dubanta yace "Can i have some of ur food if you don't mind?" Mamaki ma ya bata, har da baza ta tanka sa ba sai kuma ta tsaya tace "Duk na baya da kake diba gaya min kake halan?" Ya Wan buda ido yana gyada kai yace "Haka ne kuma fa, i just decided to ask politely today" Bata sake bi ta kansa ba tayi tafiyar ta daki, in har sai tace ya diba to ashe bazai ci ba. Washegari da safe Khaleesat na kitchen tana ma kanta snacks da zata kai school don har yamma suke da Lecture gashi suna da er jarabawan da za su yi ranan da safen, Housemate dinta ne ya shigo parlon, tun jiya da daddare da ya fita sai a sannan ya dawo gidan, har zai tafi dakinsa sai kuma ya tsaya yana kallon Handbag dinta da makulli dake ajiye gefen jakar, karasawa yayi ya dau makullin sannan ya juya ya fice daga parlon gaba daya closing the door gently ya kulle da key, Khaleesat tafi minti sha biyar tana duba makullinta bayan ta fito daga kitchen, tun daga dakinta har parlor zuwa kitchen babu inda bata duba ba amma bata ga alamar makullin ba, she can't even tell ko ta fito da shi parlor, she was so confuse gashi tayi latti, daki ta koma sai da ta birkice ko ina amma babu alamar makullin, how comes will her keys disappear just like that, tunda ta fara karatu a kasar bata taSa misplacing makulli ba banda wani lkci da Safiyyah ta yar mata guda daya, ko gyara dakin da ta birkita bata yi ba ta dawo parlor looking so frustrated, tsaye tayi trying to calm her brain ko Allah zai sa ta tuna inda ta ajiye keys din, ta Waga kai da sauri tana kallon kofar parlon jin ana budewa, House mate dinta ne ya shigo living room din da wasu takardu a hannunsa, sai da ya kulle kofar ya zare makullinsa sannan ya karasa cikin living room din ya ajiye takardunsa kan kujera without looking at her yace "Good morning Housemate...." Bai tsaya yaji amsarta ba yayi wucewarsa daki yana cire jacket din jikinsa, Khaleesat ta bi sa da kallo har ya shige daki ya kulle, zaunawa tayi gefen kujera ta dafe kanta da taji har ya fara ciwo, yanzu ina ta jefar da mukullin nan for God sake gashi lokaci na ta wucewa, after few minutes sai gashi ya sake dawowa parlon, har sannan bai yarda ya kalli direction dinta ba, taga yayi wucewarsa kitchen ya fito rike da ruwan gora ya sake komawa dakinsa ya kulle, wayarta dake jaka ne ya fara ring ta bude jakar ta ciro wayar taga Safiyyah ce, dagawa tayi ta kai kunne Safiyyah tace "Ya baki shigo schl ba har yanzu, duk latti na yau na riga ki shigowa makaranta, ko kin manta muna da test ne" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "Ina sane Safiyyah" Safiyyah tace "Na fa ce akwai tutorial da zaki min kafin mu shiga test din" a hankali Khaleesat tace "Zan taho yanzu" Safiyyah tace "Don Allah ki taho, wallahi ba abinda na sani a course din kema kin sani" Khaleesat ta ajiye wayar bayan Safiyyah ta katse, agogon wayarta ta kafa ma ido, bayan wasu yan mintuna ta mike after gathering courage to do what her mind is telling her, walking slowly ta nufi dakinsa, tsaye tayi tana facing kofar, a hankali ta kai hannu kofar tayi knocking tana turo baki, Yana jin knocking din ya kalli kofarsa, gyada kai yayi letting out a grin, sai da ta sake knocking din sannan yace "Waye wannan?" Exactly yanda take yawan fada, Shiru tayi bata ce komai ba ta kara turo baki, ya mike ya tafi gun kofar ya bude yana kallonta daga sama har kasa da alamar mamaki, tuni ta kauda kai, still keeping a surprise face yace "Madam hope nothing??" Trying to sound a little polite tace "I need you to open the door for me" ya gyara tsayuwa yace "I don't understand, dama a hade makullinmu suke? Where is ur key?" A takaice tace "It's fine, no long talk" Juyawa tayi zata bar wajen, yace "Ko baki ga naki bane?" Ta wani kallesa tace "Banda haka ai da ban zo nan nace ka bude min kofa ba" Yace "Ohh i see, does this mean u are careless too?" Barin wajen tayi ta koma parlor ta zauna, ya gyada kai with smile of satisfaction sannan ya koma daki ya dauko makullinsa ya fito, sai da ya shigo parlon yace "Ta yaya ma zaki yi misplacing a whole bunch of key sai kace allura, this is kind of weird" Daukar handbag dinta tayi ta nufi kofar yana budewa ta fice daga parlon tayi wucewarta without turning her back, ya gyada kai yace "Zaki dawo ai, zan ga ta inda zaki shigo gidan" Kulle kofar parlon yayi still smiling, ko ba komai ya rama abinda ta masa jiya. Safiyyah na kallon Khaleesat tace "To ko ya shige cikin Couch ne makullin?" Khaleesat tace "Ta yaya zai shiga kujera?" Safiyyah tace "Kuma har kitchen din kin duba?" Khaleesat tace "Babu inda ban duba ba fa" Safiyyah tace "Toh kawai kiyi ma agent din gidan magana su baki wani makullin mana" Khaleesat tace "Gani nake kamar dogon process ne hakan, kuma ai biyu ne makullin kika yar min da daya shine na dauko spare key din nake using, to shima gashi ban gansa ba yanzu" Safiyyah tace "Kar ki wani damu kanki, makullin na nan zaki gansa, kawai kin mance inda kika jefar ne, amma definitely it's either in ur room ko kuma parlor, yanzu jira zaki yi sai sanda housemate dinki ya dawo ki koma gidan kenan?" Khaleesat tace "Wani housemate? Shi da ba kwana ma yake a gidan ba, kuma ba shi da exact time da yake zuwa" Safiyyah tace "Kai haba, to a ina yake kwana?" Khaleesat ta zaro ido tace "Kin ji ki da wani tambaya, ta yaya ni kuma zan sani? what is my business with him da zan san inda yake kwana" Safiyyah tace "To kawai mu je gidanmu ki kwana" Khaleesat tace "Kina ganin babu matsala hakan?" Safiyyah tace "Wani irin matsala? To gidanta ne ko na ubanta da za a samu matsala? ta shi mu tafi jare" Safiyyah na gaba Khaleesat na biye da ita a baya suka shigo parlor da sallama, Surayya matar cousin brother din Safiyyah dake zaune parlorn ta daga kai tana kallonsu, Safiyyah tace "Sannu da gida Mom Aslam" Surayya ta ci gaba da danna wayar hannunta tace "Yauwa" Khaleesat ta zauna kan kujera ta gaisheta, Surayya ta amsa without looking at her tana danna wayarta, Safiyyah tace "Ai kin ganeta Mom Aslam, kawata ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login