Showing 180001 words to 183000 words out of 241367 words

Chapter 61 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1580

yanda Safiyyah bata yi da ita ta kwanta saman gado ba amma Khaleesat taki tace kasan carpet din ya isheta, wayar Safiyyah ya fara ring, ta mike ta dauko handbag dinta ta ciro wayar, kallon Khaleesat tayi tace "Housemate dinki ne ke kira" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah ta zauna gefen gado sannan tayi picking call din tayi masa sallama tare da gaishesa, daga daya bangaren yace "How are you, naga baki yi replying message da na maki ba tun jiya" Safiyyah tace "Kawai bana son inyi stressing dinka ne probably kace zaka zo picking din mu a airport" Yace "Kuna ina yanxu?" Safiyyah tace "Muna gidan yayana, ga Housemate din ka nan, let me give her the phone...." Calmly yace "Ohk..." Safiyyah ta mike ta tafi inda Khaleesat ke kwance ta durkusa tana mika mata wayar, Khaleesat ta kasa amsan wayar, har sai da Safiyyah ta kai mata wayar kunne, daga daya bangaren Khaleesat taji yace "Halysaah...." Kasa ce masa komai tayi, lokaci daya taji hawaye masu zafi sun fara sauka idonta, a hankali yace "Can you hear me?" Muryarta na rawa da kyar tace "Uhm" Shiru yayi, after some seconds yace "I will come over later in sha Allah" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, kashe wayarsa yayi, ta ajiye wayar wasu hawayen na sauko mata, ita dai Safiyyah bata ce mata komai ba. Karfe takwas na safe Safiyyah ta fito daga dakin Yaya Mustapha zata je kitchen ta duba menene available da zata girka masu ita da Khaleesat, ga mamakinta sai taga an ajiye makullin dakinta kan Centre table din parlon, dariya ma abun ya bata, ta karasa ta dauki makullin sannan ta koma dakin ya Mustapha da sauri ta kulle kofar, dariya ta dinga babbakawa Khaleesat na kallonta, tana nuna ma Khaleesat makullin hannunta tace "Kin ga er iskar ta ajiye min makullin kan Centre table saboda taga na tare dakin mijinta, ashe karamar er iska ce ita ban sani ba? ai wallahi boyewa zan yi inyi kamar ban gani ba don ni kam naga dakin zama..." Safiyyah na fadin haka ta bude zip din akwatin ta ta cusa makullin ciki, Khaleesat dake ta kallonta ta girgiza kai tace "Don Allah tunda har ta ajiye maki makullin kiyi hakuri mu koma dakin ki Sophie" Safiyyah tace "Wallahi bazan koma ba for now, next time in ance ta boye min makulli bazata boye ba, ba tace ita er iska bace ni kuma zan nuna mata er daba ce ni, ina nan dakin sai naga abinda ya ture ma buzu nadi" Murmushi kawai Khaleesat tayi bata ce komai ba, Safiyyah ta kyalkyale da dariya tace "To ni ba na manta ke buzuwa bace" Khaleesat tace "A'a ni bafillatana ce, babana bafillatani ne" Safiyyah tace "To Umma fa?" Murmushi kawai Khaleesat tayi bata ce mata komai ba, Safiyyah ta nemi waje ta zauna tace "Ke kiji rashin kunya kiri kiri ta ajiye min makulli kan Centre table da taga ba sarki sai Allah, to da menene nufinta da ta boye makullin in koma garage da zama ko me?" Knocking kofar dakin aka yi Safiyyah ta mike ta bude taga Mustapha tsaye ya shirya alamar zai fita aiki yace "Zaki fito ki yi maku breakfast ne?" Safiyyah tace "Har yanxu duk jikina ciwo yake min wallahi Yaya" Yace "Toh bari ayi maku order" Ta gefen ido Safiyyah ke kallon Surayya da ta fito parlon daga dakinta idonta akan Centre table wato tana duba makullin da ta ajiye, Surayyah ta kalli Mustapha tayi mitsi mitsi da ido tace "Mustapha bayan Aslam ya tashi bacci na tambayesa makullin shi ne ya dauko min wani toy dinsa ashe ciki ya zura, na samu da kyar na ciro makullin sannan na fito na ajiye mata kan Centre table 30 minutes ago, to kaga dai yanxu babu makullin kan Centre table din sannan bata fito daga dakin ka ba, me hakan ke nufi??" Mustapha ya kalli kan Centre table din, can ya kalli Safiyyah da ta hade rai tana rike da waist dinta yace "Safiyyah kin dau makullin ne?" Safiyyah ta wani kallesa tace "Ban gane na dau makullin ba Yaya" Cikin daga murya Surayyah tace "Wallahi in baki fito min daga dakin miji ke da shegiyar kawarki ba duk abinda na maku ku kuka ja ma kan ku a gidan nan" Safiyyah tayi wani dariya tana tafe hannu tace "Toh ni kuma dakin yayana ne, ita kuma Khaleesat dakin yayan kawarta ne, kin ga kuwa baki isa ki ce mu fito ba bayan bamu da wani dakin da za mu zauna in mun fito" Rungume hannu Mustapha yayi yana kallonsu ya kasa cewa komai, Surayya ta yo kan Safiyyah a fusace Mustapha ya tareta yace "Kee baki da hankali ne??" Safiyyah tayi wani shewa tace "Ka kyaleta dai ta zo ta taSa ni zan nuna mata da sabon dabanci na dawo daga Nigeria, wallahi sai na tuge mata gashin kanta gaba dayansa, ta zo ta taSa ni ta ga ikon Allah" Khaleesat dai tayi tagumi duk jikinta a sanyaye tana jin su, Surayyah ta fashe da kuka tace "Wallahi Mustapha zan bar maka gidan nan kai da Safiyyah ku zauna don bazan ci gaba da zama da matsiyaciyar ba a gida daya, sai dai ka zaba ko ni ko ita a gidan nan" Safiyyah tace "Ke din banza, minti nawa ne ya canza ki amma ni bazai taSa canza ni ba tunda jininsa ce ni, ke kuwa tsaf zai iya sakin ki ya auro wata" Surayya tayi wani kukan kura zata cafko Safiyyah, Mustapha yayi saurin riketa ya ja ta zuwa dakinta yana masifa kamar zai ari baki, Safiyyah ta koma daki ta dinga babbaka dariya har da rike ciki, Khaleesat dai sai kallonta take ta kasa cewa komai, after a while Mustapha ya sake knocking dakin, Safiyyah ta fito ta wani kauda fuska tana jiran jin abinda zai ce, nan ya fara lallabata yana cewa "Pls Safiyyah in dai kin san kin dau makullin kiyi hakuri ki kyaleta ki koma dakin ki, don ni zaki yi ai ba don ita ba, kin ga i am almost late for work, don Allah in kin dau makullin kiyi hakuri ko koma dakin ki" Safiyyah taki cewa komai tana girgiza kafa daya, haka ya dinga lallabata daga karshe ta kallesa tace "Na ji, amma wallahi ka ja mata kunne da kyau ta fita sabgata a gidan nan idan ba haka ba za mu yi batattciya da ita, don jahilci zan dinga nuna mata iri iri wallahi" Mustapha yace "Na ji, i will talk to her" Juyawa Safiyya tayi ta koma dakin, shi dai ya koma parlor ya tsaya yana jiran yaga fitowar Safiyyah. Khaleesat felt relieve bayan sun koma dakin Safiyyah, sai sannan ne ma ta samu bacci ya dauketa don kasa bacci tayi a dakin Mustapha. Wajen karfe uku da rabi na yammacin ranan Safiyya ta dau wayarta dake ringing sai kuma ta kalli Khaleesat tace "Housemate din ki ne, kilan ya zo ne, tun daxu yace in tura masa location ta WhatsApp" Tana fadin haka tayi picking call din ta kai kunne tare da yi masa sallama, after few seconds tace "Ohk to" Daga haka ta katse wayar tana kallon Khaleesat tace "Yana waje" Ita dai Khaleesat ta kasa dago kanta ga wani faduwa da gabanta yayi.
[7/4, 8:51 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Safiyyah ta gama saka Jacket dinta da neck warmer tana kallon Khaleesat da ta kasa tashi daga inda take zaune tace "C'mon Khaleesat, yana fa waje yana jira, and the weather is very cold outside, don Allah ki tashi mu je" Da kyar Khaleesat ta tashi tana jin bugun zuciyarta na tsananta ta dau Veil din Abayan jikinta ta yafa kanta a hankali, gaba daya jikinta a sanyaye yake don bata san ta yaya zata fara hada ido da Jay ba, Safiyyah na kallonta tace "Baza ki saka rigar sanyin ki ba?" Khaleesat ta girgiza mata kai kawai, Safiyyah tace "Saboda room heater ne fa yasa kike jin kamar ba sanyi sosai a garin, amma wallahi azababben sanyi ake a waje idan kika fita" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba don bata ma san me Safiyyah ke cewa ba, duk tunaninta ita dai da wani idon zata kalli Housemate dinta, Safiyyah ta tabe baki ganin Khaleesat taki tanka mata kamar ma bata san me take cewa ba, Safiyyah ta nufi kofa Khaleesat ta bi bayanta tana tafiya a hankali kamar mara lafiya, a haka suka fito parlor, Safiyyah bata ko kalli Surayyah dake zaune parlor tana ba yaronta abinci ba ta nufi kofar fita, ita dai Khaleesat na bin ta a baya walking slowly fuskarta dauke da damuwa, Surayyah ta bi su da wani shegen kallo har suka fita daga parlon, Khaleesat na hada ido da Housemate dinta dake jingine da motarsa ya rungume hannunsa taji wani kuka na neman taho mata from no where, amma ta dake ta sunkuyar da kanta tana biye da Safiyyah har suka iso dai dai inda yake tsaye, sau daya ya kalli Khaleesat ya dauke idonsa ya mayar kan Safiyyah dake gaishesa, ya amsa gaisuwanta da murmushi fuskar sa yace "Ya hanya?" Safiyyah tace "Hanya Alhamdulillah" Ita dai Khaleesat gefe ta koma ta tsaya har sannan ta kasa hada ido da shi tana wasa da veil dinta, nan kuma daurewa kawai take kar ta fashe da kukan dake cin ta, bayan sun gama gaisawa da Safiyyah, ya juya ya kalli Khaleesat for the second time, calmly yace "Housemate" Kamar jira take ta fashe masa da kuka sosai, ya sauke idonsa yayi shiru, after some seconds... walking slowly ya karasa har inda take tsaye yayi kasa da murya yana kallonta yace "Ina Jacket din ki?" Ta kasa cewa komai tana kuka a hankali tana girgiza masa kai, cire tsadadden rigar sanyin jikinsa yayi yana kallonta ya zaga ta bayanta yace "Wear this, the weather is cold" Ta gyada masa kai kawai wasu hawayen na sauka idonta ta amshi Jacket din nasa ta saka, lokaci daya kamshin turarensa da ta dade bata ji ba ya cikata ta ko ina ga kuma warmth din jikinsa from the Jacket, ji tayi kamar an yaye mata duk wani damuwar dake tunkushe a ranta, Ita dai Safiyyah na tsaye tana kallonsu, har cikin ranta take jin tausayin Khaleesat don tana jin ta ne kamar er uwarta ta jinin, Jay ya cire neck warmer din wuyansa ya daura mata kan Jacket din, ita dai Khaleesat ta kasa barin su hada ido, taji daddaden kamshin turarensa na kara mata wani irin nutsuwa da relieve??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????, Ya juya ya kalli Safiyyah yace "Za mu je tare da ke can apartment din nata yanxu ko?" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Ohk, let me get her luggages" Daga haka ta juya ta koma cikin gida, ya bude ma Khaleesat gaban motarsa yana kallonta, ita dai ta kasa hada ido da shi wasu hawayen na taruwa idonta ta shiga motar ya kulle gently, after some minutes Safiyyah ta fito da akwatin Khaleesat guda biyu ya bude booth ya saka a ciki, Safiyyah tace "Let me get the rest" Daga haka ta juya ta koma cikin gidan ta dauko sauran kayan su ma ya amsa ya saka a booth, Safiyyah ta shiga back seat sannan ya zaga ya bude driver seat ya shiga, the ride was so silent ga snow da aka fara yi, after almost 20 minutes suka iso sabon Apartment din da Jay yayi renting ma Khaleesat, parking yayi a garage din apartment din yayi shiru, sai kuma ya jinginar da kansa da driver seat ya lumshe ido bayan ya tuna makullin apartment din na can gida ya bar sa, after some seconds ya Wan shafa kansa yace "Sorry... i think na mance makullin apartment din a can gidanmu" Reverse ya fara yi bayan ya fita garage din ya dau hanyar gidansu, ita dai Safiyyah tayi murmushi kawai bata ce komai ba, dai dai sanda wayarta ya fara vibrate ta duba taga Mustapha ne ke kiranta, hade rai tayi, tayi silencing kiran sannan ta kife wayar a cinyarta, wato ya dawo yaga bata gida shi ne zai fara doka mata kira, Jay na isa gidansu yayi parking a waje ya juya ya kalli Khaleesat da tayi nisa tunanin da take, yace "Let me get the keys Housemate" Bata bari sun hada ido ba ta gyada masa kai kawai, ya bude motar zai fita, ta kalli snow din dake sauka sai kuma ta kallesa, da sauri ta fara kokarin cire Jacket dinsa dake jikinta tace "Should i give you the Jacket? Naga akwai sanyi" Ya juya ya kalleta, sai a sannan suka hada ido all this while, taji kamar kasa ya bude ta shige tayi saurin sauke idonta, ya Wan yi murmushi yace "Don't worry, i will get another one idan na shiga gida yanxu" Daga haka ya sauka daga motar ya shiga gidansu. Bayan kusan minti goma sai ga shi ya fito daga cikin gidan yana sanye da wata rigar sanyin, Khaleesat dai kallonsa kawai take, ganin ya tsaya bakin gate din gidan nasu yana kallon direction daban yasa ta kalli direction din da yake kallo, sunkuyar da kai tayi bayan ta hango Ajay yana tahowa tare da katon karensa Legend yana rike da Leash din karen, Safiyyah tayi kasa da murya tace "That is Ajay, and ya kamata ki gaishesa gaskiya Khaleesat" Khaleesat ta Wan kalli Safiyyah, a hankali tace "Baza ki gane ba Sophie wallahi kunya nake ji" Safiyyah tace "To ya za ki yi? Dole dai haka zaki ajiye kunyan ki sauka ki gaishe sa, ni dai nasan baxai taSa barin Jay yayi duk wannan hidimar da yayi maki shi kadai ba, tunda kan su a hade yake, nasan dole Jay zai yi shawara da shi before anything, Kuma tare za su yi komai..." Khaleesat ta kasa cewa komai amma har cikin ranta she is so ashame of speaking to him, har yau maganganun da Abdul yasa tayi masa ta waya na yawo a kanta, Safiyyah ta hade rai ganin Ajay ya kusa inda Jay ke tsaye tace "Pls Buckle up kiyi abinda ya dace Khaleesat, ni na tsani wannan halin kauyancin da kike yi wallahi, to meye a ciki gaishesa fa kawai zaki yi, ai ko ba komai kokarin da shi ma yayi maki ya kamata ki gaishe sa, abinda ya faru ya riga ya faru so forget that and do the needful" Jiki a sanyaye Khaleesat ta kai hannu zata bude motar, amma Ajay ko kallon inda suke bai yi ba ya wuce Jay dake tsaye yana jiransa yayi shigewarsa cikin gida, Jay ya bi bayansa, a sanyaye Khaleesat ta fasa bude motar ta juya tana kallon Safiyyah, Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya tace "He is still angry at what you did to them, nasan zai huce definitely" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, after some minutes sai ga Jay ya fito daga cikin gidan ya bude driver seat ya shiga yace "Sorry for keeping u waiting, makullin apartment din na aljihun jacket dina ne, and Ajay wore the Jacket out for a walk" Safiyyah na murmushi tace "It's fine" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, wajen karfe biyar da rabi suka iso sabon Apartment din, ya kashe motar yana kallon Khaleesat a hankali yace "This is ur new apartment Housemate, i hope you will love it" Daga haka ya bude motar ya sauka, Safiyyah ma ta sauka tana kallon gidan tana murmushi don sama da kasa ne, Khaleesat ta goge hawayen dake makale idonta sannan ta sauka daga motar, bude masu kofar apartment din Jay yayi ya jira suka fara shiga sannan shi ma ya shiga, yayi switching din light din parlon da Heater, Safiyyah na murmushi tana bin parlon da kallo ganin yafi na tsohon Apartment din girma tace "Waow, this is soo beautiful" Jay ya zauna kan kujera yana duba wayarsa dake vibrate alamar kira, Safiyyah ta bude kofar da ta gani a parlor taga kitchen ne, ita dai Khaleesat na tsaye bayan kujera tana kallon Jay ta kasa cewa komai, Safiyyah ta fito daga kitchen din ta nufi sama zata duba dakunan gidan, after some seconds Jay ya gama sending message din da yake a wayarsa ya juya suka hada ido da Khaleesat, sauke idonta tayi tana wasa da gefen Veil dinta, Calmly yace "Housemate" Da kyar tace "Um" Ya mike ya dawo gabanta ya tsaya yana kallonta, a hankali yace "You like the new apartment?" Ta gyada masa kai tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba, bai sake ce mata komai ba don yana kallon fuskarta yasan kuka zata fara masa, Safiyyah ce ta sauko downstairs tace "Ya Jawwad wallahi gida yayi kyau Maa sha Allah, Allah Ubangiji ya saka da alkhairi yasa kafi haka, my frnd is really grateful ba ma ta da bakin yi maka godiya shi yasa nake magana on behalf of her, mun gode sosai, Allah Ubangiji ya kare ka da sharrin mahassada, thank you so much Housemate we are really grateful" ?an murmushi yayi bai ce mata komai ba, Khaleesat ta goge hawayen da taji ya silalo idonta, Safiyyah tace "Toh ni zan tafi yanxu, yayana sai doka min kira yake, ya kirani yafi sau goma ban dauka ba" Jay yace "Ohk, to bari in yi dropping din ki" Da sauri Safiyyah tace "A'a wallahi ba sai ka ba kanka wahala ba Yaya Jawwad, har nayi order din Lyft gashi nan zuwa" Yace "Ohk then, my regards to everyone back home Safiyyah" Safiyyah na murmushi tace "In sha Allah" Sai kuma ta kalli Khaleesat tace "Toh mu je ki rakani kawata" ta kama hannun Khaleesat suka fita daga parlon, suna barin apartment din Safiyyah ta kalleta tace "If you like kar ki dena wannan kukan ki bude baki kiyi masa godiya sosai, shi yasa ma nace ki rakani don nasan halinki in kika fara kuka ba lallai ki masa godiya ba, in mutum yayi kukan sau daya ba shikenan sai ya rungumi kaddara ba yayi abinda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login