Showing 93001 words to 96000 words out of 241367 words

Chapter 32 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1599

her plss" Shi dai kallonta kawai yake, Calmly yace "Where in Lagos?" Tace "Zan kira in tambayeta, amma bani da numberta ne" Ya ga alamar gaba daya she is confuse and in fear, yace "Ta yaya zaki kirata baki da numberta?" Wayarsa ta dauka da sauri ta shiga call logs dinsa tana duba number Baaba Gaje, dialing tayi yana fara ring Baaba Gaje ta daga, da sauri Khaleesat tace "Baaba Gaje don Allah number Aunty Farida za a duba a wayarki sai a turo ta wannan layin" Baba Gaje tace "Har kun je wajen kare hakkin Wan Adam din?" Khaleesat tace "Ki dai turo min don Allah yanxu Baaba" Baaba Gaje tace "Toh bari in je makota kin san ban san kan wayar ba ai" Khaleesat ta gyada kai da sauri tace "To ina jira" Katse wayar tayi ta jinginar da kanta jikin kujera tana sauke numfashi, wani dishi dishi take gani tsabar kuka, Shi dai Ajay idonsa na kan titi alamar dai kansa ya gama kullewa, ya kalli agogon wrist dinsa yaga karfe biyu ya gota, driving motar ya ci gaba da yi da tunani iri iri a ransa ya nufi wani eatry ya sauka ya shiga ciki, Khaleesat ta dinga bin haraban wajen da kallo sai kuma ta rufe fuskarta da Hijab dinta da sauri zuciyarta na bugawa, incident din jiya ne kawai ke dawo mata a kai as if she is hallucinating, sai taga kamar yanzu incident din ke faruwa yanda Abdul yayi parking ya fita daga mota ya shiga eatry, kan kace me ko ina na jikinta ya fara rawa taji kamar numfashinta zai dauke, ba a dau lokaci ba Ajay ya fito daga gidan cin abincin da leda a hannunsa, yana shiga motar ya ajiye ledan da sauri yana kallonta yace "Me ya faru??" Ta dago kanta hawaye caba caba a fuskarta, sai kuma ta kamo hannunsa gam tace "I just want to leave here plss, don Allah mu bar nan" Gaba daya ta dawo kamar warce ta zauce, ya fara bin area din da kallo tunaninsa ko Abdul din ta gani, can ya sake kallonta bayan ya ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????zauna cikin motar, cikin nutsuwa yace "Look, stay calm.... You are safe" Ya gyara mata kujeran motar a hankali ta yanda zata Wan kwanta yana kallonta, sai da ya jira for almost 10 mins yaga ta Wan nutsu tana sauke numfashi a hankali, lkci lkci yake kallon agogonsa saboda flight din da yayi booking, after a while ya Wan duba fuskarta yaga kamar ta fara bacci, tada motar yayi ya bar wajen, still sai da ya kara tsayawa a pharmacy ya siya mata magunguna, ko kashe motar bai yi ba don kar ta ma san yayi parking, har yaje ya dawo kuma bacci take, ya ja motar ya dau hanyar airport hoping jirgin bazai tashi kafin su isa ba, suna isa airport din bayan yayi parking yaga saura minti sha biyar kawai jirgin ya tashi kamar yanda suka sa a ticket, tapping din kujeran motar yayi gently don har lkcn bacci Khaleesat take, a tsorace ta farka kamar yanda tayi daxu a eatry tana ganinsa kuma tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, ya bude ledan abincin da ya siya ya ciro mata takeaway din ya bata yace "Take a little before ur flight..." Ba musu ta amshi abincin tana kallonsa a hankali tace "Lagos din zan je?" Yace "In kin je zaki gani" Sai da ya hade mata rai sannan ta ci abincin cokali uku da kyar tana hadiyewa kamar magani, ya bude drugs dinta ya bata ta amsa ta sha da ruwan goran hannunta, without looking at her ya mika mata wayarsa yace "Saka min number mutumin nan" Zaro ido tayi tana kallonsa, yace "Ko bakya ji na ne?" Kamar zata yi kuka tace "Kiransa zaka yi?" Yace "Amsa ki sa min number sa nace" Hannunta na rawa ta amshi wayar ta saka masa lambar Abdul don tana da shi a kanta, ya amshi wayar yana kallon number sannan ya ajiye wayar yace "Dama an mashi alkawarin aurenki ne?" Ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace "Um, tun shekara hudu da suka wuce" Shiru Ajay yayi yana kallonta, but because of how cautious he is with time kar tayi missing flight dinta kawai ya ciro Eye drop din da ya siya mata ya mika mata ta diga a idonta, tsoro ya sa ta kasa digawa don bata san wani kalan azaba zata ji ba, daga karshe ya fixge eye drop din babu yabo babu fallasa ya diga mata a cikin idon, tuni ya sauka daga motar yana jiran in ta gama kururuwan da take ta sauko, daga karshe ta sauko daga cikin motar tana rufe idon da Hijab dinta, dayan wayarsa ya mika mata wanda ticket dinta ke ciki, daga ita sai handbag din ta da wayarsa ta nufi cikin airport din tana waige waige kamar iska zai kadeta ta fadi, kana ganinta kasan ba dai dai ta ke ba, she is traumatized and stressed, tsoron Abdul kuma ya gama shigarta sosai, shi dai yana tsaye jikin motarsa yana kallonta har ya ga shigarta cikin airport din, komawa cikin motarsa yayi yana duba full name din Abdul ta true caller, wani number yayi dialing yana fara ring aka daga yace "Zan turo maka wata number yanxu, ina son kasa a bincika min location dinsa a cikin garin kano, i will be waiting for feedback" Bayan ya katse wayar ya ajiye ya jinginar da kansa da kujeran motar, yana nan zaune har bayan 20 mins just to be sure bata yi missing flight dinta ba kafin ya bar airport din, Khaleesat ta dinga bin cikin jirgin da kallo kamar idanuwanta za su fito jin anyi announcing za su tashi zuwa garin Abuja, Abuja kuma? Ita wa ta sani a Abuja? Hawaye ne ya cika idonta ta dinga waige waigen cikin jirgin, me yasa ya mata booking ticket din Abuja.
[5/28, 8:42 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Khaleesat na zaune hall din da jama'a ke jiran Luggages dinsu a Arrival, duk da bata da kayan da zata jira amma rashin sanin inda ta nufa yasa ta zauna wajen tana bin kowa da kallo, tun 15 mins ago jirginsu ya sauka Abuja, daurewa kawai take don wani bacci take ji tare da gajiya, vibration taji a jakarta dake cinyarta alamar ana kiran waya, a hankali ta bude jakar ta ciro wayar da AJ ya bata tana kallon screen din, har ya katse bata daga ba don number kawai ta gani ba ayi saving ba bata san ko ta daga ba ko kar ta daga, kiran wayar da ake ta yi continuously ne yasa tayi picking tayi shiru tana sauraron me magana taji namiji ne, ta amsa sallaman da yayi mata, sannan yayi introducing kansa ya sanar mata shi ne ya zo daukanta Airport, a hankali Khaleesat tace "Ohk" Mikewa tayi ta fita daga Arrival din tana kalle kallen inda yace mata yake a Airport din, sai ga shi ya nufota bayan ya gane ita ya zo dauka, gaisheta yayi da ladabi yace "Babu kaya ko Hajiya?" Khaleesat ta gyada masa kai kawai, yace "Bismillah, Motar na can nayi parking" Tana biye da shi suka isa inda motar yake, ya bude mata back seat ta shiga ya kulle sannan ya zaga ya shiga driver seat, Ita dai Khaleesat ji tayi kawai yana sanar mata sun iso, bata san for how long suka yi tafiyar ba don bacci ne ya dauketa throughout the journey, gyara zama tayi tana kalle kallen compound din gidan da suke ciki, ta kalli Drivern da ya bude mata back seat, ta sauko a hankali tace "Nagode" Gida ne babba irin na zamani, tana biye da shi ya kai ta har zuwa Entrance din shiga babban parlon gidan ya danna bell, ba a dau lokaci ba aka bude kofar wata budurwa ce warce bazata wuce ta ba ta gani tsaye, da ladabi Drivern yace "Bakuwar da na dauko Airport ce Hajiya" Yarinyar ta Wan yi murmushi ta koma gefe tana kallon Khaleesat tace "Sannu da zuwa sister, come in" Khaleesat ta shiga parlon yarinyar ta kullo kofar tana nuna mata kujera ta zauna, bayan Khaleesat ta zauna yarinyar na kallonta tace "I am Inteesar" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalleta tace "Sunana Khaleesat" Yarinyar tace "Welcome Khaleesat, bari in ma Ammin mu magana" Daga haka ta juya ta bar parlon, after a while sai ga ta sun shigo parlon da wata dattijuwa that is in her middle 50, zamowa kasa Khaleesat tayi a hankali tana gaisheta, da fara'a matar da ake kira da Ammi ta dagota tace "A'a, koma kiyi zamanki kan kujera diyata" Khaleesat ta koma ta zauna kan kujeran, Matar ta zauna kusa da ita tace "Sannu da zuwa, ya hanya?" Khaleesat tace "Alhmdlh, ina yini" Ammi tace "Lafiya lau, ya kika baro mutan gidan?" Khaleesat tace "Suna lafiya lau" Ammi tace "Ai na zata tare da Yariman ku ke, ashe ke kadai ce" Ita dai Khaleesat ta sunkuyar da kanta tayi shiru tana wasa da gefen hijab dinta, Ammi ta kalli Inteesar tace "Inteesar ki kai ta daki ta huta" Inteesar tace "Ohk" Tare suka tafi dakin Khaleesat na biye da ita, Ammi ta bi su da kallo. Wajen karfe takwas na dare Khaleesat na zaune daki tare da Inteesar da ta mayar da ita Television, ita dai a hankali take cin fruit salad din gabanta, tun zuwanta gidan in dai ta kalli Inteesar by mistake zata ga kallonta kawai take, da sun hada ido kuma sai Inteesar ta mata murmushi, Khaleesat wasn't bothered da kallon don farkon haduwarsu da Sophie haka ita ma take mata, tayi ta kallonta a makaranta ko gajiya bata yi kuma da sun hada ido sai ta mata murmushi, bayan sun zama best of friends ne Sophie ke gaya mata she is soo beautiful shi yasa bata gajiya da kallonta, sai bayan sun zama kawaye Sophie ta dena mata maganar kyanta, kuma dama da wuya taje waje bata ga mutane na kallonta ba, ba maza ba hatta yan uwanta mata haka suke kallonta, muryar Inteesar taji a hankali tace "You are Beautiful Khaleesat" Khaleesat ta Wan kalleta sai kuma ta mayar mata da murmushin da take mata kawai, Inteesar tace "Sosai fa" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "And you too Inteesar" Inteesar tayi dariya tace "A'a gaskiya ba kamarki ba, ni dai ina son mu zama frnds in baza ki damu ba, Ya Prince yace gobe zaki tafi Lagos da safe, don Allah ki bani numberki mu dinga zumunci ta waya, probably baza ki sake dawowa gidanmu ba" Sosai Khaleesat taji wani relieve ya zo mata bayan taji Inteesar tace zata tafi Lagos da safe, dama gaba daya hankalinta yayi gun kanwar Ummanta, Allah ya gani daurewa kawai take amma ita kadai tasan me take ji both mentally and physically, tana cikin tashin hankali sosai but she is trying her best to act normal, Khaleesat tace "Ohk amma nayi misplacing wayana ban yi welcome back, idan nayi zan amshi lambarki gun sa" Inteesar tace "Ohk to ba damuwa, amma zaki dade a lagos ne in kin je?" Khaleesat tace "Zan Wan yi kwana biyu a can in sha Allah" Inteesar tace "Akwai sisterna dake aure can, idan baza su dawo gida for New year ba in sha Allah zan je Lagos din so that i will meet with you there" Murmushi Khaleesat tayi tace "Toh shikenan Allah ya kai mu lafiya" Inteesar ta tashi ta bude press ta dauko mata kayan baccinta don dakinta ta kawo Khaleesat, bayan ta ajiye kayan gefen gado tace "You can change to this idan kinyi wanka, i will be back later" Khaleesat tace "Alright, thank you so much" Bayan few minutes da fitan Inteesar Khaleesat ta tashi a hankali ta tafi bandaki, da ta tuna auren Abdul dake kanta tashin hankalinta ninkuwa yake, sai da ta ci kukanta me isarta sannan tayi wanka ta fito daga bandakin, ta gama saka kayan da Inteesar ta bata kenan tana kokarin daure gashinta sai ga ta ta shigo dakin, Inteesar ta wara ido tace "Waow is all that ur hair Khaleesat?" Khaleesat dai ta mata murmushin karfin hali tana ci gaba da daure gashinta, Inteesar that was looking at the hair with fascination tace "Bari in baki Hair net" Hair net dinta ta dauko ta ba Khaleesat, Khaleesat ta amsa tace "Nagode sosai" Washegari karfe tara da rabi na safe Khaleesat ta gama shiryawa tana jiran Drivern gidan, kayan Inteesar ne jikinta da yake yanayin jikinsu daya babu me cewa ba kayanta bane, tana zaune gefen gadon Inteesar duk da Hijab ne har kasa jikinta amma sanyi take ji sosai, ga AC dake dakin a kashe amma she is shivering, tun da ta tashi da asuba tasan she is not feeling okay, breakfast din ma da kyar ta sha shayi kawai, ko irish din bata ci ba balle bread, she is trying all possible best to look alright don kar ayi cancelling tafiyarta zuwa lagos yau, Mai aikin gidan ce ta Kwankwasa kofa ta sanar mata driver yana jiran ta, Khaleesat ta tashi da kyar ta dau handbag dinta ta fita daga dakin zuwa parlor, nan ta tarar da Ammi zaune, Khaleesat ta karasa ta duka kusa da ita tana mata godiya don sosai suka sake mata kamar da can sun taba saninta, daga karshe dai Inteesar ta bi su har Airport don rakiya, haka kawai jininta ya hadu da Khaleesat, ita kanta Khaleesat don bata cikin nutsuwarta ne amma she so much appreciate Inteesar's care toward her, a haka dai suka rabu kamar sun jima da sanin juna, Khaleesat ta shiga cikin airport din ta amshi boarding pass dinta don Ajay ya tura mata ticket ta Email din wayar da ya bata hade da hoton National ID dinta da yayi snapping tun karfe bakwai na safe, bayan ta amshi boarding pass dinta ta nufi Departure Lounge. Karfe sha biyu saura suka sauka garin Lagos, Khaleesat ta sauka a jirgi da taimakon wata mata don zazzabi ne sosai ya rufeta but she is still pretending to be fine, a haka suka fito Airport din daga Arrival matar na tambayarta za a zo daukanta ne ko Taxi xata hau, Kafin Khaleesat tace komai ta hango wani kamar AJ tsaye jikin wata mota yana danna wayarsa, sai da ta kifta ido ta bude to be sure he is the one she is seeing, ta kalli matar kusa da ita da kyar ta sanar mata yayanta ya zo daukanta, a haka suka rabu da matar, Khaleesat ta nufi inda ta hango Ajay, sae da ta iso kusa da motar ya daga kai ya kalleta, ta sunkuyar da kai a hankali tace "Ina yini" Calmly yace "Ina wayar da na baki?" Jakar hannunta ta nuna masa tace "Yana ciki, na sa silent ne" Driver seat ya bude ya shiga sannan ya bude mata daya side din motar, zagawa tayi ta shiga ta jinginar da kanta ta lumshe ido, ya tada motar suka bar Airport din, Google map yayi ta using after almost 45 mins ride Khaleesat ta fara gane inda za su, amma kuma sae ko ina yayi mata sabo a area din ko don she is not stabilize ne bata dai sani ba, ta juya ta kallesa shi dai driving dinsa kawai yake with the assistant of his google map, at last suka shigo wani unguwa yayi parking ya dau wayarsa yayi dialing number, muryar Aunty Farida taji bayan anyi picking, Khaleesat taji kamar an yaye mata ?aso tamanin cikin damuwarta jin muryar kanwar Ummanta, bayan few minutes sae ga ta ta fito daga cikin wani gate, tun da AJ ya hangota daga nesa ya fahimci da ita yake waya don kana ganinta ka ga Khaleesat, yayi driving din motar har zuwa dai dai kofar gidan da ta fito, yana parking Khaleesat ta bude motar da sauri ta sauka da sauran last strength dinta ta nufi Aunty Farida ta fada jikita, Aunty Farida ta rikota da sauri kafin ta kai kasa, wata makociyarta ce ta taimaka mata suka rike Khaleesat suka shiga da ita cikin gidan, shi dai AJ na tsaye kusa da motarsa yana kallonsu har suka shiga ciki, sai kuma ya jingina da motarsa yana kallon yara dake wasa few houses away, wayarsa ya ciro jin yana ringing ganin me kiransa ya daga yace "Ya ake ciki?" Daga daya bangaren mutumin yace "Ranka shi dade sai daxu ya kunna wayar tasa, an kuma duba location din nasa yana cikin garin Abuja yanxu haka" AJ yayi shiru kafin yace "Ohk, i will get back to you nagode" Daga haka ya katse wayar ya mayar aljihunsa, sai ga Aunty Farida ta fito daga cikin gidan, yayi ?asa da kansa ya gaisheta, ta amsa cikin sanyin murya tace "Sannu da kokari fa, Allah ya saka da alkhairi, mu shiga ciki sai mu yi magana ko" Bai ce mata komai ba ya bi bayanta zuwa cikin compound din, Compound ne me dauke da apartment uku self contain each, AJ ya tsaya daga balcony din apartment din bai shiga ba har sai da Aunty Farida ta kara lekowo ta masa magana sannan ya cire takalmansa ya shiga parlon ya zauna saman kujera yana kallon Khaleesat da ta juya baya kan 3 seater din da take kwance, Aunty Farida ta tafi kitchen dauko masa ruwa, ya ciro wayarsa yana dannawa absentmindedly, Sai ga Aunty Farida ta fito kitchen ta ajiye masa ruwan a kusa da shi sannan ta zauna, da damuwa tace "Sannu da kokari Junaid, Allah ya saka da alkhairi, mun gode sosai" AJ ya daga kansa ya kalleta yace "Amma dai kince bai san inda kike a lagos ba ko Aunty?" Aunty Farida tace "Gaskiya bai san nan gidan ba, tsohon gidan da na baro ne dai ya sani, shi ma wani lokaci ne da ta zo Lagos dubani bani da lafiya, ta zo da kwana uku sai ga shi shima ya zo, to yau wata hudu kenan da barina wancan Unguwan na dawo nan" Ajay dai yayi shiru idonsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login