Showing 216001 words to 219000 words out of 241367 words

Chapter 73 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1567

ba, amma jikinta kan yayi sanyi sosai ba kadan ba, ji tayi ya kamo hannunta murya can kasa yace "Kin yi shiru Housemate, say something pls" Kasa kallonsa tayi, idonta a kan hannunsa dake nata tana jin heartbeat dinta na karuwa, a hankali ta zame hannunta daga nasa tana murmushin karfin hali cikin sanyin murya tace "Amma baka tunanin hakan da zaka yi zai ja issues a family din naku?" Jay yace "I don't care, as far as Mami is in support of me i really don't care ko me za ace, idan naga ran Mami ya bace da decision dina shine kadai hankalina zai tashi, cause i love my mom so dearly...." Khaleesat still couldn't look at him in the eyes, after some seconds a hankali tace "Menene yayi triggering din canza decision da kake kokarin yi all of a sudden, bayan a farko ka riga kayi masu accepting zaka aureta?" Jay ya Wan yi murmushi yana kallonta, kamar bazai ce komai ba sai kuma yace "Look at me in the eyes Halysaah" Khaleesat felt like she is melting cause his intonation was something else, gaba daya ta kasa kallonsa, underneath his breathe yace "Look at me Halysaah" Da kyar tayi karfin halin daga manyan idanuwanta ta saka cikin nasa....


*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*

Ur evidence 07087865788


https://chat.whatsapp.com/I5vo38MH2jH8pDvzVF0Q4w


Tun kan Jay yace komai Khaleesat ta kasa ci gaba da kallonsa ta sunkuyar da kanta tana jin kamar ta nutse a wajen, bata taSa jin tana kunyarsa ba kamar wannan lokacin, ta kasa gane wani irin kallo ne wannan yake mata da yake sa ta kara jin kunyarsa, shi ko bai fasa kallonta ba yana admiring kunyanta, she became so uncomfortable lokaci daya a wajen, taji Wan composure din nata na neman guduwa ya bar ta, yayi kasa da murya yace "Halysaah..." Bata yarda ta sake kallonsa ba, speaking with calmness yace "Ban taSa sanin akwai lokacin da zai zo inji wata daban nake so ba Hadiyah ba, i never saw that coming, and i can't help it...." Shiru Khaleesat tayi har sannan taki yarda su hada ido, a hankali yace "Kin yi shiru Housemate" Tayi murmushin karfin hali, sai kuma ta fara kame kame tace "To ai ni ban ma san me zan ce ba, the issue is too big for me to give out any advice, it's ur family matter, or better still kawai kayi addu'an abinda yafi zama alkhairi a gare ka, just pray about it, pray for the best...." Yace "Is that all u have to say, ke da ake neman shawara a wajen ki" Tayi shiru for the second time, sai kuma ta samu kanta da cewa "To idan zaka iya masu adalci sai ka hadasu duk biyun ai ba haramun bane" Bata san sanda furucin ya fito bakinta ba, sai kuma ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake babu ko kiftawa, sunkuyar da kanta tayi da sauri, a hankali yace "Haka kike ganin yafi?" A takaice tace "Nima ban sani ba" Yace "But you suggested it" Kin cewa komai tayi tana wasa da edge din veil dinta, shiru Jay yayi kamar wanda ya fada duniyar tunani, after a while Khaleesat ta daga kai ta kallesa, suna hada ido ta dauke nata idon, slowly yace "Ohk then, i will think about that, but..." Kafin ya karasa Khaleesat ta dau handbag dinta tace "I think hadari ne a garin, kar ruwa ya sauko" Yace "Yea akwai hadari, i can perceive it too" Mikewa tayi without looking at him, yace "To saurin me kike sai kace a kafa zaki koma gidan" Ta Wan yi yake tace "Gobe fa akwai jarabawan da za mu yi kuma ko karatu ban yi ba" yace "Ai ke Genuis ce...." Khaleesat dai bata ce komai ba amma taki komawa ta zauna, a hankali yace "Kin kawo Suggestion kuma kina fushi da Suggestion din naki Housemate" Khaleesat ta zaro ido tana kallonsa, bata san sanda tace "Ban gane ba" Murmushi yayi ya mike yace "To mu je kar ruwa ya sauko" Sosai ta sha jinin jikinta da furucinsa ta kasa motsawa a inda take tsaye har ya wuce ta, after clearing the bills ya dawo kusa da ita yana kallonta yace "Let go Housemate, ko baki koshi bane let's place another other" Ta wani kallesa, dariya yayi yace "To mu je in ba dai wani abincin kike son ci ba" Kamar warce aka zare ma laka take biye da shi a baya tana tafiya a hankali har zuwa gun motarsa, ko da suka fito an fara yayyafi amma ba da yawa ba, ya bude mata front seat bayan ta shiga ya kulle motar ya zaga ya shiga mazaunin driver, yana fara driving wayarsa ya fara vibrate, Khaleesat ta kalli screen din wayar, Hadiyah ta gani, ta dauke idonta, ya kai hannu yayi silencing wayar gaba daya sannan ya kifar ta yanda ma bazai dinga ganin hasken wayar ba, ita dai bata sake kallon inda wayar yake ba, the ride back to her apartment was silent, ga yayyafin da ake sosai, ko wannensu da tunanin da yake a ransa, ita kam gaba daya farin cikin da take ciki as at 15 mins ago duk ya bace kamar bata yi sa ba, kawai taji zuciyarta ya tunkushe babu abinda yake mata dadi a rai, sai da suka kusa gida ya Wan kalleta a hankali yace "Amma idan kun gama Exams za ki je Nigeria ko?" Khaleesat tayi shiru, ita har tana da choice din cewa zata je Nigeria ko bazata je ba, abinda ba ita zata ma kanta kudin jirgin ba, murya can kasa taji yace "Kin yi shiru Housemate..." Murmushi tayi ta buda masa hannu alamar ita ma bata sani ba, yace "Za ki je in sha Allah, ko 2 weeks sai kiyi kafin ayi resuming summer and final semester din ku...." A hankali tace "To Allah ya kai mu" Yace "Ameen" Ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna takwas da rabi yace "Idan nayi dropping din ki zan je wajen abokina ne da ya shigo garin nan daxu, he will be leaving early tomorrow, ko mu je dake ku gaisa? He is looking forward to meet you" Khaleesat ta girgiza masa kai a hankali tace "Ruwa ake yi, kuma ina son zan yi karatu" Shiru yayi idonsa akan titi, can yace "Ohk then, may be some other time sai ku gaisa, he is my very good frnd, a Nigerian also" Khaleesat dai bata ce komai ba, duk ta kagu ta ganta a apartment dinta taje tayi sallah ta kwanta ko zata samu nutsuwan da ta rasa ga zuciyarta dake a tunkushe, dai dai garage din apartment din nata yayi parking yana kallonta yace "But cikin ruwan nan zaki fita Halysaah, kar ruwa ya taSa ki kiyi mura" Khaleesat ta kirkiri murmushi tace "The rain is not heavy ai" Yace "Give me the key idan na bude sai ki sauko..." Bude jakarta tayi ta ciro makullin ta mika masa ya amsa yana kallonta, sai kuma ya sauke ido yace "Before then i have something little for you" Ita dai kallonsa kawai take har ya dauko wani karamin box a nan cikin motar ya bude yana mika mata, kallon zoben dake cikin box din yana ta kyalli kawai take, sai kuma ta kallesa taga kallonta yake, yayi murmushi yace "Haska da wayarki ki gani, i hope you will love it" A hankali Khaleesat ta ciro wayarta a handbag dinta ta ajiye handbag din gefe, sannan ta kunna fitila tana haska siririn diamond ring din dake wani kyalli, sauke idonta tayi ta ma rasa me zata ce, ya ajiye mata a cinya sannan ya bude motar ya fita cikin ruwan, da ido ta bi sa har ya isa kofar apartment din ya bude, jiki a sanyaye ta dau box din zoben ta kashe fitilar wayarta sannan ta bude motar ta sauka, zuwa sannan ruwan ya fara karfi, yana tsaye bakin kofar yana jiranta har ta karaso ya mika mata makullin apartment din yana kallonta yace "Good night Halysaah" Hawaye ya gani idonta, ta amshi makullin zata yi magana ya daura fingers dinsa a lips dinsa ya girgiza mata kai sannan ya juya ya koma gun motarsa ta bi sa da kallo tana son ce masa ko zai yi spending night din a apartment din nata because the rain is getting heavy, amma tuni ya bude motarsa ya shiga, a hankali ta dinga goge hawayenta, ta shiga parlon ta kulle kofar ta wuce sama, gefen gado ta zauna ta kife kanta da pillow wasu hawaye masu zafi na zuba idonta, bata san da ta fashe da kuka ba bayan ta tuno maganar da yayi mata na Hadiyah, tafi minti goma a haka taji an danna bell din gidan, mikewa zaune tayi ta kalli wayarta da ke hannunta, dawowa kuma yayi cikin ruwan nan, sai a sannan ta tuna ta bar Handbag dinta a motarsa, ko jakar ya kawo mata, ta kalli agogon wayarta dake hannunta, sai kuma ta mike ta bude kofar dakinta a hankali ta sauko downstairs, sake danna bell din aka yi making it the 3rd time, ta karasa har bakin kofar ta bude a hankali, kiris ya rage numfashinta bai dauke ba bayan tayi ido hudu da wanda ke tsaye bakin kofar, bata gama recovering daga matsanancin shock din da ta shiga ba kawai taga ya shigo parlon yana kallonta, wani kara tayi duk da babu me jinta saboda ruwan da ake, ya tura kofar speaking calmly yace "Listen to me Khaleesat" Bata sake yarda ta hada ido da shi ba tsabar rudewa sai ta nufi kitchen maimakon ta gudu sama, shi dai ya bi ta da kallo yana tsaye inda yake, sai da ta shiga kitchen din taga babu makulli jikin kofar, hannunta na rawa ta shiga call log dinta tana neman number Ajay tayi dialing, don tasan tsayawa kiran Housemate dinta ma will be a waste of time, he might not even see the call balle yayi picking, jikinta na rawa ta dinga addu'an Ajay ya daga kiran, rikicewa tayi ganin sa a kitchen din ya biyo ta, ya karasa har gabanta ya amshe wayar hannunta yana kallonta ya kashe wayar gaba daya ya ajiye saman cabinet din kitchen din, cikin sanyin murya yace "Listen to me Khaleesat, i promise you I am not here to hurt you" Kuka kawai Khaleesat take ta rakube jikin bango har lkcn jikinta na Sari tana kallonsa, he look so lean kamar ba Abdul din da ta sani ba, sai dogon hancinsa da haske da ya kara, daxu tana zaune department dinsu a schl taji exactly kamshin turaren da yake using wanda hakan sai da ya sa ta tsorata ta rasa nutsuwarta, does it mean bibiyanta yake ta yi kenan all this while? How did he even know her apartment? Ta shiga uku ta lalace, Muryarsa taji a hankali yace "Kiyi hakuri na shigo maki apartment without permission Khaleesat, i know it's not right, bani da courage din tare ki a hanya don ban san yanda zaki yi reacting ba cikin mutane, i have no choice shi yasa har kika gan ni a nan this late, kiyi hakuri don Allah" Sai a sannan Khaleesat ta samu kwarin gwiwan hade rai ganin how calm and soft he was speaking to her, cike da karfin hali tace "Pls i don't want to report you to the cops, ka fita ka bar min apartment dina tun wuri" A mugun tsorace ta dake take masa maganar, instead sai taga ya sauke idonsa, a hankali yace "Zan fita, amma kafin nan ina son kiyi hakuri ba don ni ba kar ki sanar ma bodyguards dinki i badged into ur house, plss kar ki gaya masu Khaleesat.... Ni ba tashin hankali bane ya kawo ni i promise you.... nasan you are soft Khaleesat, ke mace ce me raunin zuciya sannan ke me yafiya ce, i am not using ur good characters to blackmail you Khaleesat, i am just saying the fact about you, ki dubi girman Allah da soyayyar da kike yi ma ma'aiki ki yafe min sannan ki tsaya ki saurareni ko na minti biyar ne...." She was so shock ganin ya duka a gabanta ya sauke idanuwansa daga kallonta cikin muryarsa da baya fitowa sosai yace "Ki duba alkhairina gareki ki saurareni ba don halina ba Khaleesat, i am begging you to pls give me a listening ear, na maki alkawarin ba dadewa zan yi ba zan fita...." Khaleesat ta dauke idanuwanta daga kallonsa tana jin hawaye na zuba idonta, alkhairansa da yace ne kawai ke ringing a kanta amma duk da haka ta dake zuciyarta, cikin rawan murya tace "Ni dai don Allah ka rufa min asiri ka fita in kulle apartment dina bani da lokacin sauraron ka ko na minti daya wallahi, i am begging you plss ka fita" Kamar zai mata kuka yace "Baza ki saurareni ba kenan Khaleesat?" Muryarta na rawa tace "In saurareka akan me? Bani da lokacin sauraranka, ka tashi ka fita before it's too late" Cikin sanyin murya yace "To zan fita, amma kiyi hakuri kar ki gaya masu i am here, i came with a pure intention not otherwise, plss do not tell them i am here" Duk don ta samu ya fitar mata a gida tace "Na ji, ka tashi ka tafi" Mikewa yayi ya juya ya nufi kofar kitchen din ta bi sa da kallo hawaye masu zafi na zuba idonta, sai kuma ta bi bayansa da sauri don tabbatar da fitan zai yi ko akasin haka, yana sa takalmansa dake bakin kofar parlon, Khaleesat ta karasa window da sauri ganin haske a labulen parlon, tana dubawa taga motar Ajay yayi parking a garage, ta juya da sauri ta kalli Abdul, zuciyarta na bugawa tace "My call went through, kuma gashi ya xo..." Abdul ya bude labulen dai dai sanda Ajay ya fito daga motar, kallonta Abdul yayi and she could see the panic in his eyes, ita kanta jikinta rawa yake don ko kadan bata son ayi wani tashin hankali a gabanta, muryarta na rawa tace "Ni ban san ta inda zaka fita ba, just go upstairs before he comes in...." sama ya nufa, within a blink of an eye ta dena hangosa, ta karasa tsakar parlor da sauri zuciyarta na bugawa ta zauna hawaye na zuba idonta, dai dai sanda Ajay ya bude kofar parlon, tsaye yayi bakin kofar yana kallonta, ita dai taki yarda su hada ido da shi wasu hawayen na zuba idonta, ya karasa cikin parlon still looking at her yace "Why did you call my line?" Kin cewa komai tayi tana goge sabbin hawayen dake sauko mata, ya hade rai yace "Kee, baki ji na ne? Me yasa kika kirani?" Muryarta na rawa tace "Nima ban sani ba" Tana fadin haka ta fashe da kuka sosai tana kallonsa, ya cire takalmansa going closer to her yace "Ban gane baki sani ba, What happened?" Tana shesshekan kuka ta bude masa hannu alamar ita fa bata sani ba, bin parlon ya dinga yi da kallo, nan taji gabanta ya fara faduwa sosai, cikin rawan murya tace "May be i was just hallucinating...." Sai kuma ta rakube jikin kujera ta kwantar da kanta tana wani sabon kukan, shi dai kallonta kawai yake, can ya zauna kan kujera that is near to her yace "What did you see?" A hankali tace "Abubuwa da yawa" Ya dinga kallonta kafin yace "Abubuwa kamar me?" Ta bude masa hannu alamar bata sani ba, yace "Ina wayarki? And why did you switch off the phone after calling me?" Ta fara kalle kallen parlon a hankali tace "Nima ban sani ba ai" Yace "Ina kika ajiye wayar da kika kirani?" Hanyar kitchen ta kalla tayi shiru, ya kalli kitchen din sannan ya mike ta bi sa da kallo zuciyarta na tsananta bugawa har ya shiga kitchen din, sai gashi ya fito yana rike da wayarta dake a kashe, tuni ta lumshe ido da sauri don kar ma su hada ido yayi mata wani tambayar, ya karasa har gabanta, ita dai idonta na lumshe tana sauke ajiyar zuciya a hankali, dukawa yayi gabanta ya kai hannu forehead dinta to feel if she is running temperature, amma yaji temperature dinta is normal, kawai with the way she is breathing zaka gane a tsorace take, ta bude ido a hankali tana kallonsa, sai kuma murya can kasa tace "Bacci nake ji" Yace "Why won't you hallucinate, wani kika ba ma contract din ya dinga maki Azkar din ki?" Ta sauke idonta bata ce komai ba, mikewa yayi ya koma kan kujera ya zauna yana ?are ma parlon kallo, a hankali ta mike ta kwanta saman dogon kujera ta takure waje daya tana jiran taga ya tashi ya tafi, shi dai Ajay bai ma san wani tunani zai yi ba, ta kirasa yana jin kukanta a background and before you know it kuma yaji an kashe wayar gaba daya, he tried reaching her but to no avail, tunani ya fara yi ko tana da jinnu ne, ya sake juyawa ya kalleta, ita dai idonta a lumshe yake, a haka bacci ya dauketa bata sani ba. Khaleesat bata yi minti sha biyar tana bacci a kan kujeran ba ta farka a gigice bayan tayi mafarkin Ajay ya ga Abdul a gidan ya kamasa yayi ta duka, kawai daga karshe ya harbesa da bindiga, rikicewa tayi bayan ta fado daga kan kujeran ta dinga nanata "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" jikinta na rawa, Sai bayan da ta tabbatar mafarki ne ta daga kai har lkcn jikinta na rawa tana kallon Ajay da ya durkusa gabanta yana tofa mata addu'o'i, jinginar da kanta tayi jikin kujera tana jin hawaye na zuba idonta, after almost 10 minutes, speaking calmly yace "Ta shi ki tafi sama kiyi alwala ki kwanta" Make masa kafada tayi tana shesshekan kuka tace "A'a ni tsoro nake ji, zan kwanta a nan" Tana fadin haka ta mike ta sake kwanciya kan kujeran, shi dai kallonta yake, tun da bacci ya dauketa yake tsaye jikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login