Showing 57001 words to 60000 words out of 241367 words

Chapter 20 - Halysaah Book One Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

1618

karatu a kasar nan, dama tun 3 weeks ago da muka zo muka kawo maki abinci da ni da Y Mustapha ta kara kullatata ta kara tsanata tunda har yau tayi tunanin da akwai wani abu tsakaninki da Mustapha, ko ga maciji fa bama yi da ita a gidan" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta kamo hannunta tace "Ki dai dinga hakuri plss Sophie wataran sai labari, da ni ce ke ma wallahi bazan dinga biyeta ba a gidan nan" Safiyyah tace "To ai ba kowa ke da matattciyar zuciyar da kare ya lashe irin taki ba, amma wallahi tayi kadan in ki biye mata, tana ce min kule zan ce mata casss don ubanta, an gaya mata ita ta isa ta shiga tsakanina da Mustapha? Cousin dina ne fa, Uwarsa ce ta sha nono ta bar ma uwata, Babansa kuwa Cousin din babana ne halaq malaq, ina ga bai taSa zaunar da ita ya mata bayanin nan dalla dalla bane, kuma ya ci sa'ar bana kai karar abinda matsiyaciyar matarsa ke yi min gida, don wallahi da tuni an dau mataki, amma dai bari mu yi hutu in koma Nigeria" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "Zancen gaskiya ke ma fa kina da naki Safiyyah, babu ta yanda za ayi kina zaune da mata ko Wan wanke wanken nan da shara baza ki ke taya ta ba a gidan, Abinda fa idan an mana mun san baza mu ji dadi ba to kar mu yi ma wani, she is also human, kuma at times bacin rai ne ke triggering wani mugun halin mutum, kece kika yi triggering din halinta a gidan, babu ta yanda zaki ji dadi wataran kanwar mijinki ta zo gidanki ta zauna bata taya ki aikin komai sai dai in kinyi girki ta deba ta ci ta ajiye maki plate, ki duba wannan lamarin fa, mu mata muna da son kanmu wani lkcn..." Safiyyah ta dakatar da ita tace "Ohh wato goyon bayanta ma kike kenan Khaleesah? you are trying to say duk abinda take min yayi dai dai ko?? To nagode, dama ke baki taSa goyon bayan mutum a duk halin da yake ciki, in dai mutum zai kawo maki damuwarsa to ya kara dulmiya kansa cikin damuwa ne, ni kuma ban taSa kin supporting dinki ba no matter the situation, ko Abdul da nake zagi kullum kamar Wa na nake goyon bayanki an gaya maki kema baki da naki ba?in halin ne wani lkci? Dama mistake nayi ma na zo gidan nan asirina a rufe da gidan Sandra na wuce da ba a kara bata min rai ba" Tana fadin haka ta mike ta figi jakarta ta nufi kofa kamar zata tashi sama, Khaleesat ta mike tace "Safiyyah" Banza da ita Safiyyah tayi har ta fice daga parlon ta kullo mata kofa, Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta zauna, a hankali tace "Ae shikenan"


07087865788
' [5/15, 7:17 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Read My Book "HALYSAAH" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6



('(' HALYSAAH('('





By _Khaleesat Haiydar_
'




19....

Ranan friday wajen karfe sha daya na safe Khaleesat ta gama Laundry da take a kitchen ta fito, a reading nook din parlon ta tarar da Housemate dinta yana duba textbooks dinsa, cikin few seconds ya dau wanda zai dauka ya dawo cikin parlon yana kallonta yace "Har kin gama kenan" Kai kawai ta gyada masa ta fara tidying din parlon, rana na farko kenan da ta fara ganinsa yayi shiga irin ta Hausa cikin fararen kaya, Taji yace "Hope you are studying well Halysaah" kai kawai ta gyada masa, yace "Alright, till later" Ta Wan kallesa tace "Are you Nigerian?" Ya buda ido yace "Why do u ask?" Tace "Kawai nayi zatan ko daga Chad kake, or Niger" Dariya yayi yace "Hope it's fine now tunda kin rama?" Hanyar dakinta ta nufa ba tare da ta basa amsa ba, ya dau makullin motarsa ya nufi kofar parlon, sai bayan da ya fita sannan ta dawo cikin parlon ta tafi gun window ta Wan bude drapery din jiki tana leka garage, ganin har ya tafi ta ci gaba da aikin da take yi a parlor. Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat na kitchen tana girki at the same time suna waya da Abdul, tun 40 mins ago ya kirata suke magana har sannan, duk kwanan nan dai lafiya suke waya da shi, ya kuma Wan rage mata wasu abubuwan da yake mata, he is being a little caring these days, a rana sai su yi waya sau biyu wani lkcn har sau uku har hakan na bata mamaki kamar dai ba shi ba, yanzun ma shi ne yayi encouraging dinta ta tashi ta fara girkin da take yi don bata yi niyyar girki ba, for weeks now kullum Housemate dinta ke masu takeaway na dinner wani lkcn har lunch, this made her soo lazy to go to the kitchen, breakfast dama tea and cookies take ci yawanci ko kuma ta ci da bread idan Housemate dinta ya siyo, wani lkcn ta ci french fries da kwai ko ketchup, kwankwasa kofar parlor taji ana yi, ta Wan zaro ido sanin bazai wuce Housemate dinta ba, kilan ya mance makullinsa ko kuma yayi misplacing dinsa as usual, ta kalli wayarta dake ajiye a kan kitchen cabinet har sannan Abdul was on the line kuma a handsfree ta sa wayar, tana Wan kame kame tace masa "Can u excuse me pls, i will call u back in the next 2 minutes pls" Abdul yace "Why? Me zaki yi? Is the call hindering you from doing anything?" Da sauri tace "Noo" don bata son tayi laifi, sai kuma a hankali tace "Just want to round up the cooking ne, na kusa gamawa ai" Yace "But my call isn't preventing you from doing so, wayan ba a ajiye yake ba? Continue with ur work kawai" Knocking ta sake ji, ta ma san Housemate dinta ne cause haka yake knocking dinsa, ta kalli wayarta tace "Ohk then" Abdul ya ci gaba da maganar da yake mata, a hankali ta dau wayar ta fita daga kitchen din almost tiptoeing kamar tana tsoron yaji sound din tafiyarta, ta nufi kofar parlon ta bude at the same time tana kokarin yi ma Housemate dinta alamar da yayi shiru ta hanyar dora finger dinta daya a lips dinta, lkci daya taji komai nata ya tsaya cak, a hankali ta zame finger dinta daga lebbenta tana kallonsa bata ko kiftawa zuciyarta na bugawa, ta cire wayar dake kunnenta looking speechless and Surprise at the same time, Calmly yace "Ko in koma ne?" Ta zaro ido cikin in ina tace "No, no, not at all, i... i was just being surprise, sannu da zuwa" Da sauri ta koma gefe zuciyarta na bugawa da karfi, Ya katse wayar dake kare kunnensa sannan ya shiga parlon, ta bi sa da kallo still shocked, gani take kamar she is daydreaming, ta kikkifta idanuwanta ta bude to be sure but still she is still seeing him, har sai da ya karasa cikin parlon ya zauna sannan ta bi bayansa, a hankali ta duka kusa da shi tana ya?en karfin hali tace "Wai dama all this while kana garin nan ne? I am so confuse" Yace "Gashi kin gan ni, in baki yarda ba sai ki taSa ki ji don ki tabbatar" Still feigning smile tace "I am seriously surprise, this is the least thing i expected today wallahi..." Sai kuma ta tashi da sauri tace "Let me get u water" Kitchen ta tafi zuciyarta na bugawa, sai da ta jingina jikin cabinet ta dafe kirjinta a hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku" Tasan at anytime Housemate dinta zai iya shigowa gidan don yamma yayi sosai, cikin hanzari ta bude fridge ta dauko masa ruwan gora da drink with glass cup sannan ta fita da sauri, tana kirkiran murmushi ta durkusa gabansa ta ajiye masa tace "Tun yaushe kake garin nan amma?" Ya dau ruwan goran yana kallo yace "You are buying expensive water now? Sannu er gayu" Tayi dariyar karfin hali tace "Not at all, miyar ma ya kusa yi sai in zuba maka abincin, ko dama shi sa kace sai nayi girki?" Kawai murmushi yayi bai bata amsa ba, ta mike ta koma kitchen, gaba daya she is confuse on what to do, ta fara dube duben wayarta ta tuna ta ajiyesa kan kujera a parlor, fitowa ta sake yi ta tarar Abdul yayi picking din kiran da ake masa ta waya, cikin dubara ta dau wayarta ta nufi dakinta da sauri tana kallonsa ta gefen ido taga attention dinsa na kan wayar da ya fara, bandakinta ta shige ta kulle tace "Na shiga uku" Da ta tuna bata ma da lambar Housemate din nata ta sake jin mugun tashin hankali, yanzu ya zata yi? Da sauri ta fara dialing number Salem, ai ko yana fara ring ya daga, murya can kasa ta gaishesa without waiting for his full reply tace "Plsss how can i get in contact with my Housemate? ina son zan masa magana ne urgently" Salem yace "Ohk, muna ma tare, gashi nan" Bata san sanda ta sauke wani irin ajiyar zuciyar relieve ba, taji muryar Housemate dinta yace "Hello Halysaah, is everything alright?" Ta girgiza masa kai da sauri kamar yana ganinta tace "Plss i am sorry amma kar kace zaka dawo yau, my fiance is around, he just came without notice" Yace "Tohhhh, haka kuma aka yi ashe?" Ta wani turo baki kamar yana ganinta, yayi murmushi yace "Alright Halysaah, keep ur cool, duk sanda ya tafi sai ki sanar min" A hankali tace "Thank you" Yace "Not a problem" Shi ya fara katse wayar, ta kalli screen din sannan ta sauke ajiyar zuciya ta fito da sauri bayan ta bar wayar a dakinta, har sannan ta tarar Abdul bai gama wayar da yake ba, da alama business call ne, Khaleesat na tafiya a hankali ta tafi kitchen don saka masa abincin da ta girka, har sannan she is shock, babban damuwarta yanzu kasantuwarsu su biyu kadai a gidan, a da bata jin tsoron kasancewa da shi guri daya and that was almost 4 years back, but not anymore, he is complete changed all of a sudden in just a year, da tunanin nan ta fito daga kitchen, ta karasa har gabansa ta ajiye masa abincin, yana kallonta yace "How about ur Housemate, bata nan ne?" Ta Wan yi murmushin karfin hali tace "Yeah bata nan" Ta mike ta koma edge din kujera ta zauna kamar bakuwa a gidan, a hankali tace "Ya su Momy da Aunty Hafsah?" Yace "Lafiya lau" Bata sake cewa komai ba, Ya kalli abincin da ta ajiye masa yace "I am full, ki rufe sai dai anjima" A hankali tace "Ok tafiya zaka yi da shi?" Yana dubanta yace "In tafi da shi ina?" Ta kirkiri murmushi tace "A'a ai tambaya kawai nayi" Yace "Na riga nayi lodging out of the hotel, i was in Maryland since morning" Khaleesat was speechless, bata gane yayi lodging out of the hotel ba, to ina zai kwana ko kuma wani hotel din zai kama? kai bata ma yarda ba don in yayi lodge out to ina trolley din kayansa yake, Tana murmushi da kyar tace "To ina akwatin ka?" Yace "Tana cikin mota" Ta hadiye abu da kyar tace "Motar wa?" A takaice yace "Ban sani ba" sunkuyar da kai tayi bata sake cewa komai ba, yace "Ko kina da plans ne yau? Naga kinyi mamakin zuwana da gaske" Ta zaro ido tace "Not at all wallahi, ai kai ma kasan daga schl babu inda nake zuwa, kawai dai nayi mamakin muna ta waya tun daxu ashe kana garin nan" Ya mike yace "To ki dena mamaki tunda ba ke kika siya min ticket din ba" Ta sunkuyar da kanta tayi shiru, dakinta ya nufa yace "Let me take a shower" Khaleesat ta gyada masa kai kawai ta bi sa da kallo, a very tall and masculine guy he is, just like her Housemate, and they are all handsome in their own different ways kamar su suka yi kan su, sai dai ita tafi ganin kyan Housemate dinta ko me yasa, a zahiri duk macen da ta samu Abdul in dai mayyar kudi ce kuma tana son namiji me tsantsan kyau ga kuma qualities na cikakken namiji pertaining to body structure not behavior... to duk walakancin da Abdul zai dinga mata zata jure tayi ta shanyewa don mijin nuna ma sa'a ne shi din, that is if behavior isn't included, amma Khaleesat dai dai da rana daya qualities din nan biyu na Abdul bai taSa dada ta da kasa ba, a haka stepsisters dinta ko ga maciji basa yi da ita all because of Abdul, kiri kiri suke nuna mata jealousy dinsu daga su har iyayensu a fili, ba su kadai ba hatta wasu daga sa'aninta a anguwa sun dena kulata saboda shi, basu san ba?in cikin da take kunsa day by day ba, she wish zai koma ma daya daga stepsisters din nata da ita kam ta huta, kwantar da kanta tayi jikin kujera tana jin hankalinta na kara tashi, yana nufin kenan bazai tafi anytime soon ba? kilan ma yace nan zai kwana fa? Sosai hankalinta yayi mugun tashi da tunanin hakan, after a while ta mike a sanyaye ta dau abincin da ta zubo masa ta tafi da shi kitchen ta rufe, ana haka har lkcn sallan magarib yayi bai fito daga dakinta ba, Khaleesat dake ta zaune a parlor kamar bakuwa a gidan ta kalli kofar dakin nata a sanyaye, sai kuma ta tashi walking slowly ta nufi dakin, a hankali tayi sallama sai da ya amsa sannan ta bude, ta samesa zaune saman darduma alamar sallah ya idar yana danna wayarsa, gaba daya dakin ya cika da kamshin turarensa, murmushin karfin hali ta kirkiro ta dau hijab dinta tace "Sallah zan yi" Sai kuma ta juya zata fita yace "Ina zaki yi sallan?" Ta sake juyowa cikin sanyin murya tace "Parlor" Mikewa yayi ya bar kan darduman yace "Pray here, dama kin saba sallah a parlon ne?" Ya koma gefen gado ya zauna still pressing his phone, da kyar ta karasa kan darduman ta fara sallan, bayan ta idar ta dinga addu'ar Allah ya taSa zuciyarsa ya tashi ya tafi ya bar mata gidan ita dai, muryarsa taji yace "Make me a cup of hot chocolate" Ta gyada masa kai tace "To" Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita zuwa kitchen, abinda yace tayi ta masa sannan ta koma dakin rike da mug din, bedside drawer ta ajiye masa tace "In kawo maka abincin?" Yace "Aa bazan ci abinci ba, me yasa kike yawo da Hijab kamar matar liman" Tana murmushin karfin hali da kyar tace "Aa ina jiran lkcn isha ne" Yace "Cire Hijab din nan" Ba musu ta cire a hankali ta linke ta ajiye, yace "Ke kin ci abincin ne?" Duk da bata ci ba ta gyada masa kai don gaba daya ta nemi appetite dinta ta rasa, gun reading material dinta ta tafi ta zauna ta kunna laptop dinta tayi kamar karatu take, ya gama danne dannensa a waya ya dau chocolate dinsa ya fara sha, gaba daya Khaleesat bata fahimtar me take dubawa a laptop din gabanta, sun kusa awa daya a yanda suke, ita dai har sannan tana gaban laptop taki tashi, ta gefen ido ta kallesa ganin ya mike daga inda yake zaune, taga sallan isha zai yi, sai da ya idar sannan ita ma ta tashi ta tafi tayi sallan, nan ma babu kalan addu'ar dabata yi ba kan Allah ya taSa zuciyarsa ya koma hotel dinsa, after a while ta mike ta dauke darduman ta linke ta ajiye, ya mike ya kamo hannunta yana kallonta yace "Why are you uncomfortable kamar kina tare da stranger a gidan nan ne Khaleesat?" Tayi dariyar yake tace "Stranger kuma Ya Abdul? Ai kai ba stranger bane, kai yayana ne, kuma da ai ka sha kwana gidan nan farkon da na zo kasar, kana kwanciya a parlor ni kuma in kwanta a daki" Yace "Kinsan da haka kike dari dari?" Ta sunkuyar da kanta ganin kallon da yake mata, zuciyarta ya dinga bugawa, har ji take kafafuwanta suna neman kasa daukarta, ya matso da ita dab da shi har tana iya jiyo breathing dinsa, calmly yace "Kinsan menene yasa nake kwanciya a parlor a sannan?" Ta girgiza masa kai without looking at him don she is soo uncomfortable with him drawing her closer to himself, yayi kasa da murya yace "Saboda u were still a baby sannan" Ta daga idanuwanta da kyar ta kallesa amma ta kasa cewa komai, yace "Yanzu kuwa ke ba baby bace, how old are you?" Ta kasa basa amsa, ya Wan mata tsawa yace "Tambayarki nake?" Ta hadiye wani abu da kyar tace "I am 20" yace "To a sannan ina keeping distance between us because i was still grooming you" Ta kauda kai seeing how closer he was coming to her, juyo da kanta yayi yace "Meye haka?" Muryarta na rawa tace "This is against the teaching of islam Ya Abdul, ni ba muharramarka bace" Yace "Oh really? Dama wani ne zai aure ki ba ni ba ashe?" Ta kasa ce masa komai lkci daya hawaye ya cika idonta, duk tsiyar da yake mata da yaga hawaye idonta yake calming down, ya jawota jikinsa yayi kasa da murya yace "Kin zata ke irin matan da zan yi using inyi dumping ne Khaleesat? You are diff from them, ke matar da zan aura ce" Ta kasa basa amsa hawaye na zuba idonta, ita kanta tasan Abdul so na aure yake mata, a shekarun da suka yi tare iyaka yakama mata hannu babu dadi babu kari, amma daga 2 years back labarin ya sauya har bata son ya zo inda take don sai ya mata wasu abubuwa dake damunta, in ya tafi ta sha kukanta kuma ta kan yi kwana da kwanaki bata dawo dai dai ba, amma bai taSa attempting saninta ba, muryarsa ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login