Showing 27001 words to 30000 words out of 168002 words

Chapter 10 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

636

?ara tabattar da taSin hankalin nasa. Duk da ma ba wannan ba, hankalinta ya fi karkata ga son sanin ainihin waye shi.

Ya shafe tsawon lokaci a banWakin, dan sai da Nana ta manta da shi ma, sannan ya fito. Jikinsa sai tsuma yake yi.

Ya nufo kan katifar da Nana take kai tsaye, bai ce mata uffan ba, ya zazzageta ya janye bedsheets Win da yake shimfiWe a kan katifar ya du?un?une a ciki.
Galala ta saki baki tana kallonsa.
Lallai babu alamar hankali a nan" ta faWa a zuciyarta. Sai dai ta lura da yadda jikinsa yake ta tsuma da rawar sanyi.

Ga garin babu sanyi sam, ita gumi ma take yi, amma ta ga yana ta tsuma. Ya jima sosai a haka, daga bisani ya tashi tsaye, ya nannaWe bedsheet Win ya ya jefe mata a ka, ya wuce gaban mudubin.

"Ya haka, me yasa ka jefo mini?"

Waiwayo wa ya yi mata wani mugun kallo, ya juya ya ci gaba da abin da yake yi.

TaSe baki ta yi, ta tashi ta Waukko wani zanin, ta shimfiWa ta zauna. Hannunsa Wauke da robar mai, ya nufo ta.

Ya ajiye man a gefenta, ya zauna ya juya mata bayansa.
?uri ta yi wa bayansa da ido, daga bisani ta ce "Me za a yi ne?"

Ya Wauki robar man, ya saka mata a hannunta, ya nuna mata bayansa da hannunsa.

A Wan tsorace ta ce "Wai taSa ka zan yi?"

Ya juyo gaba Wayansa ya zuba mata ido.

Nana ba ta taSa ?are masa kallo ba, sai yanzu. A hankali ta fara jin sanyi yana ratsata, bugun zuciyar ta ya fara ?aruwa.

Cikin sauri ta ce "To juya" ya juya mata. Ta Waga robar man ta na kallo, duk rubutun jiki da french ne, ba ta iya gane komai ba.

Ta tsiyayo man, sai ?amshi yake yi, hannun ta har rawa yake yi, ta kai hannunta bayansa. Sai dai tana Wora hannunta ta ji tsigar jikinta ta tashi, sanyi na ?ara ratsa ta.
Ayshacool
Ta ture gashinsa gefe, ta fara shafa man a bayansa, sai dai tana shafa masa, yanayinta yana canzawa zuwa wani abu, da ta kasa tantance mene ne.
Tsayar da hannunta ta yi a guri Waya, ta ?i gaba ta ?i baya, jin zuciyarta na rayo mata wani abu a game da shi. Haushin kanta ne ya kama ta, kawai ta ja da baya ta haWe rai. Ya sake waiwayo wa ya kalle ta. Kamar wanda aka yi wa dole ya ce "Sanyi nake ji"

MurguWa baki ta yi, ta ja jikinta lungun katifa, ta yi masa shiru. Ganin ba ta da niyyar sake taSa shi, ya sanya ya tashi ya nemi guri ya kwanta a ?asa.

Shiru ta yi tana zancen zuci, iya tsawon rayuwarta, ita ba ta taSa kai hannunta jikin wani namiji tana sane ba. Kuma ba ta taSa jin abu makamancin irin haka ba, a tattare da wani ba.

'ki shiga hankalinki Nana, kar wannan farar fatar ta ruWe ki" wata zuciyar ta gargaWe ta.

Guntun tsaki ta yi, ba tare da ta shirya ba.

"Ya dai?" Muryar ?aisar ta dawo da ita tunaninta.

Ta kalle shi, yana ta haWa wasu abubuwa a cikin kwalabe.

"Kai ne ko?" Ta yi maganar a Wan ?ule.

"Na yi me?" Ya yi maganar ba tare da ya kalle ta ba.

"Ka fi ni sani ai"

?aisar ya girgiza kai ya ce "Sanin gaibu sai Allah ai, ban san me na yi miki ba"

Nana ta ce "Ka sani"

Ya Wan kalle ta, kawai ya bushe da dariya ya tashi tsaye yana faWin "Kar ki damu, yanayi ne da bil adama su kan kasance a ciki, ai ba ki yi wani abu ba, ba abin damuwa ba ne ba. Kuma ni bani da hannu a wannan lamarin. Sai dai ina tunatar da ke, kafin ki yi aika-aika ki tabattar da wane ne shi"

Banza ta yi masa, ta nufi wata ?ofa da take buWe.

A hankali ta buWe idonta, tana kwance a kan katifarta, ta kalli gurin da yake kwance, yana nan kamar yadda ya kwanta. Ya dun?ule jikinsa guri guda, jikinsa ko riga babu. Ta shafa jikinta ta ji gumi take yi, amma shi alamu suka nuna sanyi yake ji.

Ta yin?ura da ?yar ta tashi, ta Waukko bargonta a saman wardrobe, ta nufe shi.

"Ka tashi ga bargo ka rufa"

A hankali ya buWe idonsa, ya kalle ta, kawai ya mayar ya lumshe. Ba ta ha?ura ba ta sake cewa ga shi ka rufa tun da sanyi ka ke ji. Ta yi maganar tana ajiye masa bargon. HankaWe bargon ya yi gefe a zuciye, yana ?o?arin gyara kwanciyarsa.

"Me ya sa zaka jefar mini da abu, idan ba ka so sai ka jefar mini, haka Wazu ma ka jefa mini bedsheet a kaina, ni ka daina yi mini haka. Kawai ya tashi zaune. Me Nana za ta gani, kamaninsa sun koma na tsohon nan da take gani a tare da shi. Ihu ta kurma da ?arfi ta suma a gurin.

*

Sanye take da doguwar rigar bacci shara-shara blue black, ta yi mata kyau sosai, ga tsohon cikinta, tana gefen gado tana shan abu a cikin kofi.

Da sallama ya shigo Wakin, ta amsa masa, ya zauna a kusa da ita. Ta ce "Ya yi baccin?"

Ya ce "Ya yi da kyar, ban da labarin Anty Nana, babu abin da yake yi mini, yana ta biya mini abin da take koya masa. Babu yadda za a yi ta dawo gidan nan ne ta ci gaba da kula da shi?"

Ta kwaSe baki ta ce "Ta ina? Na gaya maka an yi mata aure da buzayen da suke gadin gidanmu"

Ya ce "Ikon Allah, to dama buzaye na auren wasu wanda ba irin su ba ne?"

Shukura ta ce "Waye ya san musu ma? Abin ne dai ga shi nan"

"Allah ya kyauta, ni dai Haidar nake ji, da alama sun sha?u, wai me ki ke sha a cikin kofin nan ne?" Ya yi magana yana karSar kofin.

Magani ya gani a ciki, ya tsuke fuska ya ce "Wai me yasa ba kya ji ne? Na hana ki shan wannan abubuwan, ya za a yi ki na da tsohon ciki ki din ga shan wannan abubuwan? Sai kin yi wa kan ki illa?"

Shukura ta Sata fuska ta ce "Ba fa da yawa na sha ba, kuma ai duk dan kai nake yi"

"Kuma ni na ce miki ina bukatar wannan abin? Fruit bai ishe ki ba me ki ke nema kuma? Kawai sai kin illata mini yaro? Wallahi na kuma ganin kina shan wannan abubuwan sai ranki ya Saci" ya tashi ya fice ya bar mata Wakin.

Haushi ne ya ishe ta, kawai ta nemi guri ta kwanta.

Girma da nauyin cikin jikinta, bai hanata yin gudun ceton ranta ba, tana gudun tana waiwaye, ga numfashinta na neman barin huhunta, saboda tsananin gajiya.
Karo ta yi da wani mutum sanye da farar riga, mi?a masa hannu take yi, tana faWin "Dan Allah ka taimake ni"
Ayshacool
Lokaci Waya abin da yake cikinta, ya yi wani irin dun?ulewa, ya na danno ta. Cikin gigita ta tsaya tare da dur?usawa a kan gwiwoyinta, tana jin nishi.

Mutumin da yake bin ta ya ?araso gabanta, ya saka hannu ya cire abin da ya rufe fuskarsa da shi.

Cikin tashin hankali ta ce "Daddy"

"Ki yi ha?uri Shukura, ni za ki taimaka, ki sadaukar mini da abin da yake cikin ki"

Jan jikinta ta fara yi, tana girgiza kanta, cikin kuka da azabar na?uda take faWin "A'a Daddy, dan Allah ka bar mini jaririna, na baka tawa rayuwar amma ka bar mini jaririna dan Allah"

Ya girgiza kai ya ce "Ba na bu?atar rayuwar ki Shukura, yaron nan kawai nake bu?ata"

Mutumin nan mai farar riga, ya buWe fuskarsa, sai ta ga doctor Sharif ne. Cikin kuka take ce masa "Dan Allah Doctor ka taimake ni, ka ba shi ha?uri".

Bai saurare ta ba, ya dur?usa ya yi mata wata allura, take ta yi wani irin nishi, jaririn ya faWo.

Ya Wauke shi har mabiyiyar, ya mi?a wa Alhaji Zailani.

Alhaji Zailani ya ciro wata 'yar wu?a, ya Waga jaririn kansa a ?asa, ?afafuwan sa a sama.

Ihu take iya ?arfin ta, tana yi masa magiya, amma ya Waga wu?ar nan zai caka wa jaririn, bai kai ga caka masa ba, ta ji an kira sunanta. Tana Waga kai ta ga Nana.
Nana ta jefa mata wata sharSeSiyar wu?a, a rikice Alhaj Zailani ya yi kan Shukura, cikin sa'a ta caka masa wu?ar da Nana ta jefo mata.

"Shukura lafiya? Me ya same ki? Me ya samu jaririn naki?" Ta buWe idonta a hankali ta kalli fuskar mijinta da ke Wauke da matsananciyar damuwa.

"Meya faru?" Ya sake tambayarta.

Jikinta ne kawai yake karkarwa, tana zare ido cike da matsanancin tsoro da tashin hankali.
Ba ta iya yi masa magana ba, sai godiya da ta din ga yi wa Allah a zuciyarta, da ya zamana mafarki ne ba gaskiya ba.

*

Da safe Nana na ta karkaWe Waki tana gyarawa, ko gaishe shi ba ta yi ba, dama ba amsawa yake yi ba idan ta gaishe shi. Sai dai fes take tuna abin da ya faru jiya da daddare, yadda fuskarsa ta canza baki Waya. Sai dai haryanzu tana ji a ranta, sharrin ?aisar ne ya sanya take ganin wannan abubuwan a tattare da shi.

"Zan yi wanka" ta ji muryarsa tana tsaka da gyara Wakin.

Ta kalle shi ta ce "To banWakin zan biyo ka ko ya za a yi?" Ta yi maganar cikin tsiwa.

Bakinta ya bi da kallo, rasa me zai ce mata ya yi, a wannan karon ma, ba ta gane abin da yake nufi ba, kawai ya wuce banWakin. Yana shiga ta dira mitar abin da yake yi mata.

"Wai zai yi wanka, ko bin sa zan yi na yi masa wankan, ni ban gane ba"

Ta ci gaba da aikinta, yana fitowa bai tsaya wata-wata ba, ya sake yaye bedsheet Win da ta gama shimfiWawa ya rufa yana rawar sanyi.

A hanzarce ta Wago a ?ule ta ce "Lafiya, meye haka wai?" Ta yi maganar kamar ta fashe da kuka, saboda a lokacin ta gama sanya zanin gadon.

Jin ta tsaya masa a ka, saboda ya Wauki bedsheet ya sanya ya mi?e, ya watsar mata da shi a gurin.

Ya Wauki kayan da zai saka ya shiga toilet ya canza, ya fito ya bar mata Wakin. Cikin hantsi ya fita ya zauna ya takure jikinsa, Wumin ranar yana taSa shi.

Nana ta ci gaba da mita tana ?ara gyarawa.

Muryar Habu ta jiyo, ta le?a ta taga, ta gan su tare a zaune. Yadda Habu ya yi shiru ya nutsu ne, ya sanya ta gane mijinta magana yake yi, amma muryarsa ?asa-?asa, ba a jin tasa sai dai ta Habu ake iya ji.

Ta saki labulen ta nemi guri ta zauna, Habu ya yi sallama a ?ofar Wakin. Ta amsa masa. Ya ce "Na shigo?"

"Eh bismillah" sai ta ga ya shigo shikaWai.

Nana ta ce "Ina kwana?"

"Lafiya ?alau Alhamdilillah. Ya rayuwar?"

Nana ta yi murmushi, haryanzu hausar su wasu lokutan sai a hankali, ta ce "Lafiya ?alau"

"Ga wannan" ya yi maganar yana ba ta leda.

Jiki a sanyaye ta ce "Malam Habu, abin da ya faru Allah ne ya ?addara, wannan Wawainiyar ta isa haka, kullum sai kun kawo mana Abinci, ga Wawainiya da ku ke ta yi. Zan fara girki in sha Allah"

Ya yi murmushi ya ce "Kar ki damu, ai dolen mu ne mu kula da ke. Kayan miya ne a ciki da sauran kayan amfani. Duk abin da babu, akwai lambata a rubuce a gurin mijin naki, sai ku kira ni" Nana ta jinjina masa kai.
Ayshacool
Sai kuma Habu ya yi murmushi ya ce "Amm amarya, mutumin fa ya kawo mini ?arar ki, ya ce ki na yi masa rashin kunya, ki na Waga masa murya. Dan Allah kamar yadda na gaya miki ki yi ha?uri da shi dan Allah. A hankali za ki fuskanci yadda za ki zauna da shi, na san abin zai yi miki wahala amma dan Allah ki yi ha?uri hakan tamkar jihadi ne, ke ma Allah ya kawo ki mu yi tare"

Nana ta haWiye maganganu da tambayoyi da ta so yi wa Habu, ta daure ta ce "Hmm ?ara ta ma ya kawo ko? To shikenan na daina"

"Ki yi ha?uri amma, yanayin ciwon nasa ne ba ya son hayaniya, shi yasa"

Nana ta ce "Babu damuwa in sha Allah, ina son ma na yi maka wasu tambayoyi, amma sai ka kuma dawowa"

Gyaran muryar sa su ka ji, Habu ya mi?e. Buzu ya juya yare ya yi masa magana, Habu ya jinjina kai.

Ya zo ya wuce ya buWe wardrobe, ya Webo kayansa masu datti, da ya nannaWe ya bawa Habu.

Habu ya karSa, ya yi musu sallama, ya tafi.

Nana ta din ga kallonsa, bakinta fal magana, amma ya ?i kallonta.

"Shi ne ka ce ina yi maka rashin kunya ko? To me na yi maka na rashin kunya? Dama ashe ka na magana ni ce ba ka kulawa ko?" Ya lumshe idanunsa yana kaWa ?afar sa.

"Idan ba ka yi mini magana, ba zan san na yi maka laifi ba, ko na san abin da ka ke so ba, da wanda ba ka so" ta gama surutunta, ganin ba shi da niyyar tanka mata ya sanya ta kama wani abin.

Kayan miyar da Habu ya kawo, ta zauna ta gyara tsaf, ta yi greating Win su. Ta Wora a kan gas. Tana jin yadda yake tari, saboda zafin attaruhu. Ta dafa taliya da miya.

Ya din ga bin ta da ido, har ta gama.

Ta zuba masa ta ajiye masa komai, ta tashi ta je ta yi alwala, ta dawo ta tayar da sallar azahar.

Ta idar ta yi azkar, ta ninke dadduma, ta gan shi ya haWa gumi, yana cakalar abincin, fuskarsa ta yi jawur, sai gumi ne yake tsatstsafo masa.

"Lafiya ya na ga ka na gumi, abincin babu daWi ne?" Ya ja numfashi ya kalle ta, hannunsa ri?e da cokali mai yatsu.
Babu irin tambayar da ba ta yi masa ba, amma bai ba ta amsa ba, har ta gaji ta rabu da shi. A haka ya cinye abincin.

Nana ta rasa abin da ya sanya shi haWa wannan uban gumin. Idonta ne ya sauka a kan wayarta. A take tunanin mahaifiyarta ya ?ara faWo mata. Jiki a sanyaye ta ?arasa ta Wauki wayar tana kallon screen Win.

Jiki a sanyaye ta buWe wayar, ta shiga gurin kira, ta shigar da lambobin kamar yadda ta haddace su, cike da fatan Allah ya sa wayar ta shiga.

Babu zato babu tsammani, ta ji wayar ta shiga. Gyara zamanta ta yi tana fatan Allah ya sa ta ji abin da take tsammanni. Sai dai akasin haka ta ji muryar namiji, muryar mutumin da ta tsana a rayuwarta.

Cikin dakiya ta ce "Baba ina wuni?"

"Lafiya kalau wace ce?"

Cikin sanyin murya ta ce "Dan Allah me wayar nake nema"

Ya ce "To wace ce ke Win?"

Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Baba Nana ce, mamana nake nema" ta yi maganar cikin rawar murya, idanunta na cika da hawaye.

"Ai dama na sani, wallahi na sani, na san ba ta fasa bibiyar tsohon mijinta ba, wallahi zan gauraya da ita"

A ruWe Nana ta ce "Dan Allah Baba ka tsaya ka ji, wallahi ba sa waya da Babanmu, lamba ta ce, dan Allah ka haWa ni da ita ko muryarta na ji, dan Allah.. ?it ya kashe wayar ba tare da ta gama faWar abin da za ta faWa ba.

Wata irin tafasa zuciyarta ta din ga yi, cike da Sacin rai da tashin hankali. Wasu irin hawaye masu raWaWi suka fara biyo fuskar ta.

Ta Wauki wayar ta yi jifa da ita, caraf ya cafke wayar.

Ya kalli yadda hawaye yake fita daga idanunta.

Kawai ya ga ta taso za ta fita daga Wakin, jikinta yana rawa.

Har za ta gota shi, ya dan?o hannunta ya yo baya da ita, yana ?arewa ?aisar kallo da ya bayyana a gefenta yana huci!.

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
Page 31


Bai kula ?aisar ba, ya ja Nana zuwa kan katifa, ya zaunar da ita, idanunta a lumshe, har a lokacin kuma fitar da hawaye suke yi, babu ?a??autawa. Ya taSa tafukan hannayenta, ya ji sanyi ?alau kamar an ciro ta daga ?an?ara.

Ya ?ura mata ido yana nazarin ta, a take ya tuno ranar da ta shiga Wakinsu, tana kiran Haidar, su na haWa ido ta ja da baya ta ?wala ihu ta faWi.
Haka jikinta ya ?andare, ta din ga karkarwa, ya ga wani narkeken ba?in muzuru ya bayyana a Wakin, yana ta zagaye ta.

Ya sauke numfashi, ya sanya yatsunsa biyu, ya danna bayan kunnenta. Ya mi?e ya bar kusa da ita. A hankali jikinta ya daina rawar, ta buWe idonta, sai dai tun da ta buWe idon, ba ta tashi daga gurin ba balle ta ci abinci.
Ya din ga satar kallonta, amma ba ta tashi daga in da take ba, balle ta ci abinci. Yana son ya yi magana amma ya rasa me zai ce mata.
Ta tashi zaune da ?yar, ta haWa kai da gwiwa, ta yi kuka mai isar ta. Sai da aka kira la'asar sannan ta tashi ta yi alwala, ta tayar da salla.

Bayan ta idar tana zaune ta yi shiru, ya dawo Wakin, ya duba gurin da ta gama girkin, babu alamar ta ci abinci.

"Ba za a ci abinci ba?" Ta ji maganar sa babu tsammani.

Ta Waga kai ta kalle shi, kamar mai jiran ?iris, kawai ta sake fashewa da kuka. Ya yi zuru da ido yana bin ta da kallo, bai ce ta yi shiru ba, har ta yi mai isar ta yi shiru.

Duk ya damu ganin ba ta ci abinci ba, ya rasa me zai ce mata, ga shi yanayinta ya fahimci rigimammiya ce.

Jin motsi a waje ana taSa gate, ya sanya ya tashi ya rufe fuskar sa, ya fita ya duba waye.
Tsayawa ya yi yana kallon su, mata ne su uku, da ?anan yara sai wani Wan matashin saurayi.

"Sannu malam, ko kai ne mijin Nanan?" Ya tsaya tsuru yana kallon su.

"Gurin Nana mu ka zo tana nan?" ya nuna musu Wakin su.

Suka wuce, Ummi tana cewa "Na yi ?o?ari fa da na iya kawo mu gidan nan"

Bayan Jamila ya bi da kallo, jikinsa na ba shi wani abu a game da ita.

Wata irin zabura Nana ta yi ta rungume Ummi, ba ta taSa tsammanin ganin su ba. Ta rungume Jamila cikin farin ciki ta ce "Dama za ku zo ba ku gaya mini ba?"

Ummi ta ce "Mu ki bamu guri mu zauna"

Nasiru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login