Showing 66001 words to 69000 words out of 168002 words

Chapter 23 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

649

da na ce miki rayukanmu na cikin na juna ba? Muddin ruhinki na yawo a doron duniya, ba zai taSa barin ruhina cikin nutsuwa ba, saboda abokan rayuwa ne"

"Sayyid"

"Duniyata"

Wani kyakyawan murmushi ne ya suSucewa Nana, ta ce "Kalaman ka na ?ara mini ?warin gwiwa, har ba na son na ji muryar ka ta Wauke ko sau Waya"

"Da gaske?"
Ta jinjina masa kai alamar eh. Ya sumbaci goshinta yana murmushi, mai ?ayatarwa.

Sai da zuciyarta ta motsa, wani irin shau?i ya mamaye ta, ji take tamkar ta furta abin da take ji a cikin zuciyarta, amma ta danne, sai kallonsa da take yi.

Ya ce "FaWi mana, ki furta"

"Me zan furta?"

"Abin da yake zuciyar ki, da ki ke son faWa" ta girgiza kai ta ce "Babu komai"

"A'a, ruhina ne a jikinki fa, ko in gaya miki abin da ki ke son cewa?"

Ta girgiza kai alamar a'a. Ya saki wani irin murmushi, mai cike da ?asaita yana kallon fuskarta.

Haka ya sakankance, ya tattara duk hankalinsa da lokacinsa a kan Nana, sai da ya mantar da ita damuwar da ta shiga, wani nannauyan bacci, ya sace ta.

*

Hajiya Sa'a ce take mita iya yin ta, "Wallahi Jamila, ban da yayan ki ne ya yi miki wannan dukan, da sai na rufe shi, wannan ai take ha??in Wan Adam ne. Tun da kin kai shekaru goma sha takwas, ai kin sa abin da ya dace da rayuwar ki".

"Wallahi haka Mama ma ta faWa, da police station za a kai shi, Baba ya yi ta bata ha?uri, nima na ce kar a kai shi, ta yi ha?uri"

"Saboda me ki ka hana a kai shi, ai gara a kai shi, ya san cewa ke da shi akwai bambanci yanzu"

Jamila ta ce "Kaii babban yayanmu ne fa Mummy"

"Shi Win fa, shi ba dukan ki ya yi ba?"

"A'a ai bai kamata ba, da kunya abun"

"Ke Jamila, kalle ni da kyau. Irin wannan lamarin, dole ki sakawa kowa tsoron ki idan ki na son ki zauna lafiya ki taka duk wanda ki ke so. Ba a tausayi ba kuma a tuna danganta kan ki kawai za ki kalla, ki gina rayuwar ki. Babu wani abu da dangantaka ke ?ara wa banda koma baya da hassada da fitintinu"

Jamila ta jinjina kai ta ce "Haka ne"

"Dan haka duk wanda ya yi yin?urin taSa ki, ki yi maganinsa kawai. Ni zan fita ba daWewa zan yi ba amma"

"To a dawo lafiya" Jamila ta yi maganar tana kashingiWa a jikin kujerar 3 seater da ke Wakin.

Har bacci ya fara Waukar ta, ta ji ana sallama, ta buWe idonta ya ce "Yi ha?uri na tashe ki, Mummy ta fita ne?"

Ta jinjina masa kai tana ?o?arin mayar da kai ta kwanta.

"Ta daWe da fita ne?"

"A'a"

Ya ce "Ok thanks " ta mayar da idonta, ta lumshe shi kuma ya Wan ?ura mata ido, kan ya fice.

****
Alhaji Zailani na zaune, yana jiran ta gama haWa tea ta ba shi, kiran wayar Hajiya Sa'a ya shigo wayarsa. Ya Waga su ka gaisa. Ta ce "Zailani, matarka ta fi ?arfin ta je duba Hanifah a Asibiti, har an sallame su sun koma gida"

"Dan Allah ki daina kamabama abu, wane irin fin ?arfi, ni na je, su Rauda su je, maman su ta je, duk bai isa ba? Ba ta da lafiya ne, mu na ta yawon asibiti"

"Ba ta da lafiya me ya same ta?"

Ya ce "We are expecting another Muhsin in sha Allah, cikin yana ta ba da matsala ne yana neman ya fita, so an bata complete bed rest ne, kin ga ba zai yiwu ta din ga yawo ba"

Hajiya Sa'a ta Wan yi jimm sanan ta ce "Yayi Allah ya raba lafiya"
Ayshacool
Uwargidan sa da ke ?o?arin haWa masa tea kuwa, ji ta yi tamkar ta kurma ihu. Da ta ji batun cikin Fadila, kuma wani namijin ne. Ita nata yaran biyar duk mata ne.

"Ya dai lafiya kuwa?" Ya yi maganar yana kallon ta.

Ajiye masa tea Win ta yi, ta bar falon saboda takaici, dan kuwa ji ta yi, tamkar ta watsa masa shayin a kansa.

Ya karya abin sa a nutse, yana yi yana communicating da mutane ta waya.

Tashi ya yi zai je ya duba Fadila, dan ba a gurin ta ya kwana ba, kuma ba ta jin daWi sosai. Sai dai ya ji tamkar an Wora masa dutse a kansa, kuma an saka igiya an Waure shi. Ya yi mi?a ko zai ji dai-dai, amma ya kasa jin ya dawo normal.

Ya lallaSa ya fita, kansa na sara masa ya nufi sashin ta. Ya yi iya ?o?arin sa, bai bari ta fahimci wani abu ba, saboda kar ya ?ara mata damuwa, ya zauna har su ka yi hira, sannan ya fita.

****
Ya na zaune yana kallon Nana, ta na ta fafutukar yin breakfast, saboda ?o?ari meatpie ta tsiri yi da safen.

Ta kammala ta zuba masa nasa, ta haWa masa tea. Ta zuba masa ido. Ya saka hannu ya Wauka ya kai bakinsa ya ci, ya yi murmushi ya sake kaiwa bakinsa.

Ta ce "Da daWi?"

Ya Waga mata babban yatsansa, alamar jinjina.

"To ka ce Allah ya yi mini albarka"

Murmushin sa ya ?ara faWaWa ya sumbaci goshinta, sannan ya shafa gashinta ya ce "Allah ya yi albarka"

"Amin Shugabana" ta yi maganar tana dariya.

"Ga Nonon can a kan mudubi, ki fara sha kan ki karya"

Ta tsuke fuska ta ce "Nonon ra?uma dai ba nawa ba" A tare su ka tuntsure da dariya, har ya kusa ?warewa, ta Waukko ruwa ta ba shi ya sha.

Ta ce "Ba ruwana, kar ka ?ware ka ce ni ce"

Duk da ba ta da cikakkiyar masaniyar dalilin ba ta Nonon ra?umin, amma ta fara jin daWin sa sosai da sosai a jikinta.

"Sayyid, bari na kaiwa ?awata ko za ta ci"

"Wa?"

"Yusra" ya jinjina kai. Ta fita ta shiga cikin gidan.

Ko da ta yi sallama, a falo ta tarar da Siyama, hannunta duk ya ?one, a Sare mata ?unar.

"Sannu ina kwana?"

Ta kalli Nana ta amsa ciki-ciki. Ba ta sake bi ta kan Siyama ba, ta haye benen. ?akin Yusra ta shiga da sallama.

Yusra ta Wago, amma ba ta amsa ba. Ta ganta a zaune a kan gado ta yi tagumi, amma tana ganin Nana ta saki murmushi.
Nana ma ta yi mata murmushi ta ?arasa ta zauna a kusa da ita ta ce "Yayata, kin tashi lafiya?"

Yusra ta ce "Lafiya ?alau"

"Abinci na kawo miki, ko kin karya?" Ta ce "A'a"

"To ga wannan" ta saka hannu biyu ta karSa ta ce "Na gode" Nana ta din ga yi mata hira, har ta cinye meatpie Win.

Ta Wan numfasa ta ce "Dan Allah Nana, kema ki na jin kin gaji da duniya, idan ki ka ga wu?a ki ji kamar ki cakawa kanki, ko ki faWo daga saman bene ki mutu? Irin duniyar babu daWi Win nan?"

Nana ta jinjina kai ta ce "Sosai, na taSa yin?urin kashe kaina ma, amma addu'a nake yi sosai da sosai. Ina ro?on Allah ya kiyaye ni. Kuma nake yin alwala sosai nake zama da ita"

"Kin tabattar idan na yi hakan zai daina ji, idan na yi addu'a Allah ba ya karSa, salla ma kamar ba daidai nake yi ba." Nana ta rufe mata baki ta ce "Ki daina faWar haka, nima da ina wannan tunanin amma na yi ta istigfari. Allah ya na karSar addu'armu, ba dan haka ba da wata?ila haukacewa zamu yi gaba Waya"

Yusra ta ce "Haka ne, wallahi na ji daWin zuwan ki gidan nan, duk kin san me nake ji, kuma kin san abubuwan da nake ji ba ?arya nake yi ba"

"Ai kamar yadda na gaya miki ne, mukaWai mu ka san abin da muke ji. Ki daina damuwa sai kowa ya san halin da ki ke ciki, an fahimce ki an daina cewa ?arya ki ke yi. Idan an kai ki gurin likita ya baki magani, ki din ga sha. A gefe kuma ki din ga addu'a ki na fatan Allah ya yaye miki"

Ta girgiza kai ta ce "Ba na son maganin likitan nan, bacci suke saka ni, kuma ba na iya baccin sam, sai dai jikina ya mutu, kuma damuwa ta ?ara yi mini yawa". Nana ta din ga rarrashinta da ba ta ha?uri.

Sun yi hira sosai, sannan ta ce za ta raka Nana bakin ?ofa.

Su na tafe ta ce "Kin ga Siyama ta ?one ko? Tana shiga kitchen za ta juye ruwa a flask, na she?e mata shi a hannunta. Nana ta tsaya cak ta ce "Saboda me?"
Ayshacool
"A'a kar ki yi kuka"

"To ni ka daina yi mini irin haka"

"To na daina" ya faWa yana kai hannunsa fuskarta.

"Kar ki yi kuka fa" jin yadda ya shiga damuwa nan da nan, ya sanya ta ci gaba da kunna shi, ta hanyar yin taSara iri-iri.

A ranta ta ce "Ohh, wai yau ni ce ba a son na yi kuka, da uban wa ya damu idan ma rijiya zan cika da hawaye?"

Ta ?arfin tsiya ta saka ya din ga rarrashinta, da Hausa da French.

Da Asuba kuwa sam bai tashi da alamar ma ya yi fushi ba, saboda kar ta yi kuka.

Bayan ya dawo daga salla, tana kwance a jikinsa ta ce "Dan Allah Sayyida ka bar ni na je a yi mini kitson nan, na je gurin 'yar uwata dan Allah"

"A'a"

"Dan Allah Sayyid."

"Idan kin tafi wa zai kula da ni?"

Ta yi murmushi ta ce "Zan ajiye maka duk abin da ka ke bu?ata, dan Allah ka bari na je Please. Ba dan kar na zaunar da kai ba, sai mu tafi tare ma, to ka ga bai kamata na bari ka na jira na ba"

"A dawo lafiya" ta zabura ta ce "Ka yadda na je?"
Ya jinjina kai. "Allah ya saka mini kai a aljanna na gode sosai Shugabana"

Ya yi murmushi ya ce "Sayyid yanzu kuma Shugaba"

"To ai duk abu Waya ne" kyakyawar sumbata ya samu a bakinsa, daga matarsa saboda tsananin farin ciki da ta shiga.

Da safe ta ya ?o?arin gama girki da wuri, ta Wora masa na rana, ta dafa ruwan zafi ta zuba masa a flask da duk abin da take sanya ran zai nema.

Ta yi wanka ta fara shiri, su ka yi waya da Hajiya Amina, take gaya mata kwana huWu kenan, an yi wa Shukura aiki yaron ya rasu. Nana ta ji ta damu sosai da sosai, ta yi mata jaje ta ce za ta je ta duba ta.

Ko da ta ajiye wayar, ta kalle shi ta ce "Sayyid, ka ji Shukura ta haihu yaron ya mutu, dan Allah zan biya na duba ta, sai na tafi gidan Ummi."

"A'a"

Ta marairaice ta ce "Dan Allah, kar su ga kamar wula?anci ne, an gaya mini abu ban je ba"

Ya kalle ta ransa a haWe, ya ce "Kar ki je gidan nan" ta tsuke bakinta, kar ta je gidan Ummin ma, ya hana ta zuwa.

Har bakin hanya ya raka ta, sannan ya koma.

Ta yi tunani ta ga yadda ya tsuke fuskar nan, babu lallai ya bari ta je, kuma Hajiya Amina ba ta cancanci haka daga gare ta ba. Duk da ba shiri suke yi da Shukura ba a baya, amma tana matu?ar tausayinta.
Kawai ta yanke shawarar ta je a gurguje, ta duba ta ta wuce gidan Ummi.

Habu ne ya buWe mata gate, yana ganin ta, ya yi murmushi suka gaisa ya ce "Ina mutumin?"

Ta ce "Yana gida, bai san zan zo ba, wata unguwar na tambaye shi, dan Allah kar ka gaya masa na zo"

"A'a kar ki damu, ba zan gaya masa ba, ina fatan duk ku na lafiya?"

Nana ta ce "Lafiya ?alau, ba ka zuwar mana kwana biyu"

"Ai na ga babu wata matsala ne, ku na lafiya shi yasa"

"Ko kuma shi ne ya hana ka zuwa, Sayyid kishinsa ya yi yawa"

Ya yi murmushi ya ce "Sayyid kuma?"

Nana ta jinjina kai ta ce "To na rasa da sunan da zan kira shi, amma dan Allah da wani sunan aka Waura mana aure da shi ne?"

"Kamar dai yadda na gaya miki ban san komai a kansa ba, kawai cewa na yi a saka Muhammad, amma ban san sunansa ba nima"

Ta jinjina kai ta ce "To da gaske kai ne ka ke ba shi kuWin da yake kashe mana? Na ga kuWin aikin gadin ba wani yawa ne da su ba"

Ya Wan yi dariya ya ce "Ai ainihi ba gadi ne sana'ata ba. Ina safarar dabino ne, da mazar?waila da cukui da sassan ra?umi, daga Nijar zuwa Nigeria na rarrabawa 'yan kasuwa. A garin haka ma na tsince shi. Na fara gadi ne saboda na samu na zauna guri Waya, a nema masa magani, amma haryanzu ba a dace ba, masu maganin sai su ce abin ya fi karfinsu"

"Amma Malam Habu, me aka ce muku yana damunsa?" Horn Win mota su ka ji, ya ce "Bari na buWe ?ofa"

Ta ce "Shikenan, nima bari na hanzarta"

Ta shiga cikin gidan, Jummai ta din ga murna da ta ga Nana, ta yi mata jagora har Wakin Hajiya Amina, inda Shukura take jinya.

Sosai Nana ta jajantawa Shukura, tare da ba ta ha?uri, da ?arfafa mata gwiwa a kan girma da muhimmancin tawakalli ga Musulmi.

Hajiya Amina har so take Nana ta zo, ko tana cikin damuwa, ire-iren wa'azinta, a kan tawakalli da dogaro ga Allah na ?ara mata ?warin gwiwa.

Nana ta tambayi ina Haidar, aka ce mata yana gidan kakarsa.
Ayshacool
Muryar Alhaji Zailani ta ji ya shigo Wakin, yana kiran sunan Hajiya Amina.
Gabanta ya faWi, ?wa?walwarta ta shiga fafutukar tuno mata, da abin da ta gani a mafarki amma ta kasa, duk da zuciyarta na raya mata mummunan abu ne, kuma kamar a zahiri ya faru. Saboda kaucewa zargi, Nana ta yi ta maza ta gaishe shi.

Shi kansa ya yi mamakin ganin Nana, ya daidaita nutsuwar sa, ya amsa mata ya ce "Ashe amarya ce ya mai gidan?"

"Yana nan lafiya ?alau. Hajiya bari na tafi ina sauri ne, sai na sake dawowa."

Cikin sauri ta Wauki jakarta ta yi waje, Shukura na ta yi mata godiya.

Ba ta tarar da Habu ba, kawai ta buWe gate Win ta fice. Ganin da ta yi wa Alhaji Zailani, ta din ga jin tamkar ta aikata wani mummunan saSo ne.

Tana ta sauri, unguwar shiru babu kowa, ta ga an sha gabanta da mota. Ta ja ta tsaya ?irjinta na dukan uku-uku.

Duk wannan saurin, na ki tsere mini ne? Idan na so kamo mini ke zan saka a yi, na yi duk abin da nake so, kuma babu wanda ya isa ya ce dan me, ko ya tuhume ni. Biyo ki na yi na ?ara tabattar miki da ina nan a kan baka ta, wallahi ba zan rabu da ke ba, sai bu?ata ta ta biya."

Cikin dakiya ta ce "Allah ko? A baya ban taSu ba, sai a yanzu ka ke tunanin zan taSu? To kar ka fasa, ka ci gaba da bibiyata da mugun nufinka, kar ka fasa" ta zagaye motar ?asan zuciyarta tana tsananta addu'a ta bar gurin.

Gidan Ummi ta tafi, Ummi ta yi farin cikin ganinta sosai da sosai, su na hira ana gyara Nana. Nana ta bata wasu daga cikin kayan da su Adda Saude suka kawo mata.
Aka wanke mata kai, aka yarfa mata kitso ?anana, ta yi mata dilka ta zana mata lalle ja da baki, ta turara ta da turarukan wuta.

Nana ta ce "Inyee ko ranar aurena ban samu wannan gatan ba"

"Ai biya za ki yi, ki je gida ki ce ya biya kuWin gyaran da na yi miki"

"Ba zamu biya ba Win" ta yi maganar tana dariya.

Ummi ta bata labarin yadda Saleh, duk ya shiga damuwa da tashin hankali, saboda auren da ta yi, ya tattara ya koma Lagos ma. Daga haka kuma suka koma tattaunawa a kan matsalolin gidan su, yadda Baba ya bar ragamar gida a hannun Mama, gantalin da Jamila take yi, har ta bata labarin dukan da Gaddafi ya yi mata, ga Imarana babu ma wanda yake cigiyarsa. Suka ci gaba da jajanta matsalolin na su, da a yanzu ba su san ma hanyar saita wannan gida na su ba. Gefe Wan gidan Yaya Atine ya ce yana son Suwaiba, Mama ta ce ba za ta bawa Fa?iri 'yar ta ba.
Sun daWe su na hira, Nana ta bawa Ummi kayanta da take so a WiWWinka mata.
Ummi ta duddubo mata wasu kayan kwalliya, da sauran 'yan kayan bu?atu ta rako ta titi, ta samu abin hawa ta tafi gida.

Ana ta kiraye-kirayen sallar magariba Nana ta isa gida, sai dai ba ta tarar da shi ba.
Ta yi salla, kasancewar ta zo da abinci daga gidan Ummi, ya sanya ba ta Wora girki ba, ta dai kunna gas ta Wora masa shayi.

Har aka yi sallar isha'i shiru bai shigo ba, sai kuma abin ya fara damunta. Ga shi shi ba waya ba, wayarta ma tana hannunsa, ba waya ta fita.

Tana nan tana kallon hanya, ta ji yana rufe gate. Ajiyar zuciya ta yi, ta jira ya shigo Wakin.

"Sayyid, duk na damu na ji ka shiru, ina ka tafi ne?"

Ko kallon gurin da take bai yi ba, ya wuce ta ya shiga banWaki. Sororo ta tsaya tana mamaki.

Ta koma gefe ta jira, ya fito. Ya sake nufar wardrobe. Ta bi bayansa ta na magana. "Sayyid wai meyafaru ne? Ina ta magana ka yi mini shiru"

Ya duba jallabiyar da zai saka ya kwanta. "Sayyid ka yi magana mana"

Ya ajiye jallabiyar, ya kalli Nana a tsanake ya ce "Me yasa na ce kar ki yi abu ki ka yi?"

Gabanta ya faWi, ce rauni ta ce "Me na yi?"

"Tambayata ki ke yi? Ban ce kar ki je gidan mutumin nan ba? Ban gaya miki ba?" Ya yi maganar cikin Waga murya.

Cikin sauri ta girgiza kai ta ce "A'a ban...

"Kar ki yi mini ?arya kin je, me yasa ki ka je?"

Ta girgiza kai tana tsuma, saboda yadda ya burkice mata.

Ya Kano hannunta Waya ya Wora a ?irjinta, ya kama Waya ya sanya a ?irjinsa, ta ji yadda zukatansu ke bugawa a tare.

"Haryanzu ki na tunanin ?arya nake yi, da n??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ace miki akwai ruhina a jikinki?"

Ya saki hannayenta, ya kuma tsare ta da ido, ya ce "Me yasa ki ka je bayan na ce kar ki je?"

Nana ta yi shiru ta ?i magana.
Ayshacool
"Magana nake yi miki" ya ?ara maganar yana Waga mata murya.

Ta Waga kai ta kalle shi, ta ga gaba Waya ya canza, fuskar sa kamar bai taSa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login