Showing 84001 words to 87000 words out of 168002 words

Chapter 29 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

683

magana ta what's app. "?anwata, shi ne tun da ku ka sauka, ba ki neme ni ba ko?"

"Ba haka ba ne, ba ni da data ne"

"Kuma ba ki gaya mini ba, bari na saka miki. Ina Mummy?"

"Ta fita"

"Wai ina ku ka je ne a Abujan?"

Jamila ta yi masa reply da "Ban san sunan gurin ba, wani gida ne dai mai kyau sosai"

"Ok, to dan Allah ki kula da kan ki sosai da sosai, Allah ya bayar da nasarar abin da aka je nema, na ji ta ce taron kasuwanci ne ko?"

"Wallahi dai ban sani ba tukuna"

"Haka ta ce mini ni, ta tafi da ke ku ka bar ni a gida, ai shikenan" har za ta rufe data ta ga 10gb na data. Sai ta washe baki ta ce "Har 10gb na gode sosai da sosai"

Abba ya ce "Babu godiya tsakanin, Yaya da ?anwarsa, ki kwanta da wuri ki yi bacci. Ki yi addu'a kuma, sai da safe"

"To yayana na gode sosai da sosai" suka yi sallama, ta rufe laste seen Win ta da online, ta tafi kallon videos a tiktok.

Hajiya Amina ce ta shigo Wakin, ta ce "Jamila ba ki yi bacci ba?"

"Eh Mummy, kin dawo?"

"Eh zan sake zuwa wani gurin ne, babu lallai na dawo da wuri, za mu yi meeting, ki yi kwanciyar ki"

"To shikenan, sai kin dawo"

"Yauwwa amma ba kya bu?atar wani abu, ko jin yunwa ko?"

Ta ce "A'a a ?oshe nake"

"To sai na dawo" Hajiya Sa'a ta fice, ta rufe wa Jamila ?ofar.

****

Nasiru tun ranar da ya je gidan Ummi, su Nana suka tashi, ya koma gida ya ba wa Baba labari. Baba ya ce "To shikenan ma, ta kwana gidan sau?i, tun da sun samu mafita.
Ni na san babu yadda za'a yi ma a kore su haka kurum, dan mijinta ba shi da lafiya akwai dai abin da suka aikata.

"Dama wasu Buzaye abin yarda ne, kalli kayan da suka kawo mata fa, Allah ka dai ya san mugun abin da suke aikatawa, har aka kama su. Kai Nasiru to ya gidan da suka koma yake?" Cewar Mama cike da son jin ?wa?waf.

Nasiru na tauna rake ya ce "Normal dai gida ne, amma da wasu a gidan, wancan gidan da suka baro ya fi. ?akinsu ya fi kyau da girma, banWakin har da famfo ga wuta, wannan kuwa gaskiya bai yi kyau ba"

Ta sake cewa "Kuma da gaske mijin nata ba shi da lafiya?"

Ya Waga kai ya ce "Kai, sosai yana daurewa ne kawai, idan ya yi magana haki yake yi fa, wannan karon na ga ya yi magana sosai. Da an yi abu sai ya ce mata Rayuwata, ki yi a hankali ki zauna ki huta"

Sai ta sake zabura ta ce "Au rayuwata yake ce mata"

"Kai Mama dan Allah ki rabu da ni, haba wannan tambayoyin kamar a kabari"

"Kai a gidan uban wa ka san kabarin, sai ka yi saSo tukuna" ya yi mata shiru, ya tashi ya Wauki rakensa da yake sayarwa a ?ofar gida, da wu?a ya fice.

*
Tun da garin Allah ya waye, Nana take tashin sa, amma ya ?i tashi, irin wannan baccin da ta farka ta ga yana yi dai shi yake yi.
Gaba Waya ta tsorata, ga dai numfashi yana yi, idan ta taSa zuciyarsa tana bugawa da ?arfi jefi-jefi.
Ta saka shi a gaba, ta ma rasa abin da ya kamata ta yi. Ummi takira ta a waya, ta tambaye ta babu matsala babu wani abu da take bu?ata, ta ce mata eh.
Har sha biyu na rana Nana ta rasa abin yi, ta kunna karatun Al?ur'ani a wayarta, ta ajiye masa sai dai bai fi mintuna talatin ba wayar ta Wauke. Ji ta yi ana bubbuga ?ofar Wakin nasu. Ta yin?ura ta tashi ta saka hijjabi, ta je ta buWe.

Sajida ta gani a tsaye, ta Wan saki fuskarta su ka gaisa. Sajida ta ce "Mun ji shiru ne, ko ?ofa ba ku buWe ba, shi ne na ce bari na ?wan?wasa ko lafiya?"
Ayshacool
Nana ta ce "Lafiya ?alau Alhamdillah, ba ma jin daWi ne daga ni har shi, shi yasa ba mu fito ba, amma lafiya ?alau muke"

"Ok Allah sarki, ko dai amarya ce ne, haryanzu ba a gama cin amarci ba?" Ta yi maganar tana kallon Nana.

Nana kawai ta yi murmushi, ta koma Wakin, ta buWe ?ofar ta saki labule. Dama ta gyara komai a Wakin. Ta dafa shayi da habbatussauda, da citt, kanumfari, kimba, na'ana'a kamar yadda yake dafawa, ta zuba a flask ta rasa me za ta dafa, dan ba ta son cin komai.

Tana nan zaune, sai ga 'yar gidan Ummi ta zo, Islam. Ta kawo wa Nana faten doya da wake, ya sha alayyahu. ?amshin attaruhun da ya daki hancin Nana, sai da ta haWiye yawu. Ta ba wa yarinyar wayarta, ta mi?a mata caji.

Ta Wan zuba abincin tana ci, ta zuba masa ido, tana tunanin ko Asibiti za ta nemo mota su tafi, amma kuma sai ta tuna abin da ya yi jiya ba shi da ala?a da ciwon Asibiti.
Tana ta tunanin mene ne mafita, kuma ba ta son waWannan maganannun matan, suk san halin da suke ciki ita da mijinta.
Tana nan zaune tana bin sa da kallo, ta jiyo hirar Sajida da Barira, da wasu ma?wabta. Barira ta ce "Sajida, jiya da daddare, kin ji kamar ana nishi cikin dare?"

Sajida ta ce "Wani irin nishi kuma? Ni ban ji ba"

"Wallahi nishi, kamar ana kokowa kamar wani gurnani, ga Amiru ya yi bacci, na din ga jin tsoro na kasa bacci, na ce ko gamo na yi da aljanu"

"Ba wasu aljanu, ba wani aljani da yake razana mutum, da wani sauti ko wani abu, duk ?aryar banza ce"

"Kai ni dai na tsorata, kuma daga nan haka na din ga jiyo sautin, wajen nan" ta yi maganar tana nuna Wakin Nana.

Sajida ta yi magana ?asa-?asa, Nana ba ta ji me su ka ce, sai ji ta yi sun tuntsure da dariya. Ta yi ajiyar zuciya, ta fara tunanin ko dai wani gidan za su kama, ta san idan suka ci gaba da zama a gidan nan, asirin su na iya tonuwa, wanda ba za ta so hakan ba.

Babu tsammani ta ga ya tashi zaune, ta tashi da sauri ta nufe shi cikin kulawa ta ce "Sannu Sayyid, ka tashi?" Shiru ya yi yana bin ta da kallo, tamkar ya ga wata ba?uwar halitta daban.

"Sannu ya jikin naka?" Yanzun ma bai yi magana ba, ya ci gaba da bin ta da ido. Ta yi ta magana ya yi shiru, tamkar kurma. Can kuma ya tashi ya shiga banWaki ya fito ya nemi guri ya zauna.

"Sayyid, za ka yi sallolin da ba ka yi ba, Asuba da kuma Azahar, duk ba ka yi ba" ya yi mata shiru, ya kawar da kansa gefe. Ta tsiyayo ruwan shayi a kofi, ta zo gabansa da cokali ta zauna ta ce "To Wan sha tea Win, sai ka ci abinci ka yi sallar" ya kawar da kansa ya yi mata shiru. Ta ?ara matsawa kusa da shi, kawai ya hamSare kofin ruwan zafin ya kware mata, a wuyanta zuwa jikinta. Wata irin zabura ta yi, ta ja da baya tana tsuma, saboda yadda zafin ya ratsa fatarta. Ko kallon inda take bai yi ba, ya ja gefe ya ci gaba da huci.

Ranta ya yi mummunan Saci, amma ta kalli fuskarsa, ta tabattar da yana hayyacinsa, babu yadda za a yi ya yi mata haka, dan haka ta yi shiru ba ta ce komai ba, ta tashi ta cire kayan, ta saka wasu.

Haka suka wuni a Wakin, bai yi salla ba, bai ci abinci ba, kuma bai yi magana ba.
Ana yin sallar magariba, ya haura kan katifa ya kwanta.
A jikin mudubi ta tsaya, tana haska ?irjinta, yadda inda ruwan zafin ya zuba a ?irjinta, ya Wuri ruwa.
Ta hasaka kan katifar, ta ga ya ci gaba da wannan baccin, mai rabin idonsa a buWe, ta nemi guri a ?asa lungun wardrobe ta kwanta. Sai dai yau ta kwanta cike da fargaba da kuma zullumin abin da zai faru, kar ta je ya sake sha?e ta.
Sam ta kasa bacci, da ta fara sai ta razana ta buWe idonta, dama a kunne ta bar fitila ba ta kashe ta ba.

****
Shukura ce tare da Sagir a zaune a cikin mota, ta zuba wa ?ofar gate Win Asibitin ido. Ya ce "Ya dai? Ki shiga ki fito ina nan ina jiran ki"

"Wallahi haka kurum gabana yake faWuwa, ko hanyar Asibitin nan ba na son na ni an faWi sunan ta"

"Shukura duk saboda da Wan ki ya rasu, ban taSa ganin mutum mara tawakkalli kamar ke ba"

"Ba haka ba ne, wallahi yanzu ma ban da Mummy ta matsa, ba zan zo ba, bari na je na dawo"

Sagir ya ce "Tom ki yi masa sannu, ni na zo na duba shi dama" ta jinjina kai ta fice daga motar.
Ayshacool
Tana shiga cikin Asibitin, ta din ga jin kamar a lokacin ne, za a yi mata aiki a cire Wan cikinta, wata irin fargaba da yanayi mara daWi ta din ga ji a jikinta.

Ta ci gaba da jan ?afafuwanta, jiki babu ?wari ta nufi Wakin da Hajiya Amina ta kwatanta mata. Sai da ta yi knocking sannan ta tura ?ofar ta shiga. Fadila na zaune a gefen gadon kusa da Alhaji Fatuhu, ga cikinta ya yi wani irin girma, tamkar tana yin?urawa Wa zai faWo. Sai dai gaban Shukura ya yi mummunar faWuwa, ganin yadda Alhaji Fatuhu ya koma. Dogon mutum mai jiki, mai hasken fata, ya koma ba?i ?irin ya yi wata irin mahaukaciyar rama, jikinsa tamkar fata kawai aka yafa wa ?ashi. Ta ji kanta ya sara, wani irin abu ya soki zuciyarta. Wani irin wari Wakin yake yi, tamkar na mushe, ga shi dai babu ?azanta a jikinsa, ga Wakin a share a goge yana ?amshin turaren wuta, amma ita warin mushe ta din ga ji, da ba ta san daga ina yake fitowa ba

Fadila tana yi mata sannu da zuwa, amma ba ta kula ba, ta ?arasa kan gadon, ta zaune. Yana daga zaune, ya kalle ta ya yi murmushi tamkar mai raWa ya ce "Shukura"

"Daddy, haka jikinka ya koma?" Ta yi maganar cikin matsanancin tashin hankali, da tuni hawaye ya wanke mata fuska.

Ya ce "Alhamdillah, ai na ji sau?i ko Maman Muhsin?" Fadila ta jinjina kai hawaye na zubo wa daga idonta ita ma.

"An ce mini kin haihu Wan ya rasu, ban zo na duba ki ba, na haWu da wannan larurar"

Cikin kuka ta ce "Dan Allah ka yi ha?uri ban zo na duba ka a kan lokaci ba. Ban zaci abin ya kai har haka ba"

Ya yi murmushi yana jinjina kai, aka turo ?ofar Wakin,gaba Waya suka waiwaya Doctor Sharif ne ya shigo, tare da wata nurse.

Yana ganin Shukura ya yi murmushi ya ce "Hajjaju kwana da yawa, ni da na yi zaton zuwa yanzu ma, kin dawo mana awo? Ya gida ya mai gidan?"

"Lafiya kalau" daga haka ta ja baki ta tsuke. Sai da ya sha jinin jikinsa, da irin amsawar da ta yi masa.

Ya kalli Fadila ya ce "Uwar biyu, ya mai jikin?"

Fadila ta ce "Alhamdillah mun gode Allah"

"Ma sha Allah. Na ce ki je a duba ki, idan inducing Win ki za a yi, idan ma tiyata ya kamata a yi miki to. Amma kin ?i"

"Kar ki soma yarda, a kashe miki Wa, gara ki je wani Asibitin" tsit suka yi baki Waya, suka waiwayo su na kallon ta.

Jikinsa ne ya yi wani irin sanyi, wani irin tsoro ya ziyarci zuciyarsa. Cikin damuwa ya ce "A kashe mata Wa kuma Shukura"

"Nawa ba a hannunku ya rasu ba?"

"Kuma ai ba kya ce za a kashe mata Wa ba, nakin ma, Allah ne ya kawo ajalinsa"

Shukura ta ce "Ba zan dai sake zuwa Asibitin nan na haihu ba. Daddy Allah ya ?ara afuwa. Maman Muhsin sai anjima Allah ya raba lafiya"

Fadila ta ce "Amin, mun gode sosai da sosai Shukura, ki gaida gida. Mummy ma an ce ta tafi Umara ko?"

"Eh wallahi. Allah ya raba lafiya" har Shukura ta fice, jikin Doctor Sharif tsuma yake yi, amma ya dake tare da Soye hakan.

*

Jamila na tsaka da bacci, ta ji ana tashin ta. Ta buWe idonta ta ga Hajiya Sa'a a tsaye amma fitilar Wakin a kashe.

"Hajiya lafiya kuwa?"

"Lafiya ?alau, tashi ki saka wannan rigar mu tafi"

Cikin mamaki ta ce "Ina?"

"Ki saka sai mu je ki gani. Ki cire komai na jikinki ki saka ta"

Bakinta fal tambayoyi, amma babu damar yi. A duhun ta karSi rigar ta saka, kanta babu ko Wan kwali, Hajiya Sa'a ta kama hannunta suka fice. Sun yi doguwar tafiya sosai, su na ratsa guri-guri, sai dai duk a cikin duhu ne. Jamila ba ta san ina suke bi ba, da kuma inda za su je ba.

Aka buWe musu wata ?ofa suka shiga, ta ja ta tsaya. Yanayin gurin babba ne yana da girma sosai. Sai dai da mutane a ciki, galibinsu maza ne. An kunna kyandira a gurin. A haka ta lura kayan jikinsu jajaye ne da ba?a?e.
Sun kewaye wata ?atuwar tukunya a tsakiyar Wakin, fuskokin su a rurrufe.
Hajiya Sa'a ta ja ta suka samu guri suka zauna.
Wani irin gurnani mutanen Wakin suke yi, su na wasu irin maganganun da ba ta fahimtar abin da suke faWa. Da alama Waya daga cikin su ne yake jagorantar abin da suke yi, mai kama da ibadar bautar wani abin.

"Mun yi ba?uwa a gurin nan" cewar mutumin da yake zagaye tukunyar, yana faWar abin da yake faWa suna yi masa amshi.
Ayshacool
Hajiya Sa'a ta ce "Eh, ba?uwar mu ce, da na sanar da zuwan ta wannan bugiren"

"Ita ce aka kasa samo jinin 'yar uwatta, uwar gijiyar uban du?usa?"

"Eh ita ce"

"Mu na yi mata maraba da zuwa ?ungiya, za ta samu abin da take so. Idan duniya ce kun same ta kun gama. Babu wani abu da zai gagare ku. Can kuma wannan matsalar ku ce, ku neme ta ku rasa nan, ko ku nemi nan can kuma sai abin da hali ya yi. Mu na yi wa wanda ba su bayar da sadaukarwar su ta wannan shekarar ba, idan lokaci ya yi za su ga abin da ba su zata ba. Wanda suka riga su ka yi, mu na taya su murna da ?ara tabattar musu sun samu duniya, su taka wanda suka so, babu mai ganin bayansu, masu neman Waukaka za su samu, masu neman ilimi za su dace. Masu neman kuWi sun samu, haka ma masu neman madafun iko. Mu na sake jaddada muku dokokin ?ungiyarmu, babu fita bayan an shiga. Babu tona asirin ?ungiya. Duk wanda ?ungiya ta bu?ata za ka bayar, babu jayayya babu musu. Akasin haka jininka ya zama mallakin dodon ?ungiya".

"Mun yarda, mun yi mubayi'a, mun bi dodon ?ungiya, mun bi sarkin ?ungiya, ranmu da jukkunanmu fansa ne a gare ku, muna son duniya, mu na son tabattuwar duniyarmu" suka haWa baki su na maimaitawa. Jamila bin su kawai take yi da kallo, jin abin take yi tamkar a mafarki, kuma kamar wani film. Wani irin sauti mara daWin ji ya karaWe ilahirin gurin.
Mi?ewa mutanen suka yi, suka risuna tamkar za su yi sujuda. Su na ci gaba da karanto wasu irin abubuwa. Wani abu mai kama da guguwa, ya kashe kyanduran gurin. ?arar sautin abin, da surutun da suke yi ya karaWe gurin, baka iya gane komai. Can bayan wani lokaci kuma, sai gurin ya yi tsit hasken kyanduran ya dawo. Suka Sarke da wata irin shewa. Hasken ya haska gurin sosai da sosai, sai dai ba ta iya gane suwaye a gurin, kuma ta nemi Hajiya Sa'a ta rasa a gurin. Sai daga baya ta fahimci ashe akwai mata a gurin ba wai maza ne kawai ba.
Aka din ga raba wani abu a cikin kofi, aka zo kanta a ka ba ta, ta karSa ta sinsuna ta ji wani irin ?arni mara daWin ji ya daki hancin ta. Ta kawar da kanta yawu na taruwa a cikin bakinta. Ji ta yi an dam?i hannunta, an nufi wata ?ofa da ita. Tana ta ?o?arin gane waye, amma abu ya faskara ta kasa gane waye.
Su na shiga ?ofar ta ga duhu ya ?ara gaurayewa, amma ta ji sanyin AC na ratsa ta.
Ta ji an sha?e mata wuya, an toshe mata hanci, ta fara kiciniyar ?wacewa amma abu ya gagara, ta buWe bakinta za ta yi numfashi ta ji an zuba mata wani abu, da ya fi ruwa kauri kaWan, mara WanWano. Tana gama haWiyewa ta ji wannan ?arnin ya mamaye mata hancinta da bakinta. Take ta yi yin?uri ta fara amai, sai dai ba ta gama aman ba, ta ji jiri ya kwashe ta.

****

Bangaren Nana kuwa, aka shiga kwana biyu, ba tare da ko ruwa Sayyid ya saka a cikin sa ba. Balle Abinci, ba wanka babu salla balle ya sha magungunan sa na matsalar zuciya. Ga shi kuma bai daina haki ba. Idanunsa sun yi jawur tamkar gauta. LaSSansa sun yi wata irin bushewa. Ga gashin nan butsu-butsu a hargitse babu gyara, ya koma mahaukaci sosai da sosai. Ga shi da ta tunkaro inda yake, ko ya hankaWe ta, ko ya sha?e ta. Ko kallonsa ta fiye yi, sai ya hau huci yana zabure-zabure tamkar zai kai mata duka. Ta yi iya ?o?arin ta, babu wanda yake shigar mata Waki.
Ga laulayin ciki ya saka ta a gaba, ita kanta lallaSawa kawai take yi. Ba ta yi da yawa ba a rana ta yi amai sau goma, tun cikin dare take farawa. Tun tana sha'awar ta ci wani abu har ta daina. Daga shayi sai ruwa, ko juice Win lemon tsami. Idan ta ga jikinta ya bushe ne, sai ta aika a sayo mata ruwan gishiri ta haWa ta sha. Ga ranar da za su koma follow up, na Asibiti ya yi amma yana cikin wannan yanayin, a dole ta rabu da shi, ta ci gaba da addu'a.
Sai dai yau gaba Waya Jamila ce take ta kaiwa tana komowa a ranta. Sannan ?asan zuciyarta kuma haka kurum, take tunanin abin da ya sanya ta daina ganin ?aisar kwana biyu.

"Allah ya sa dai lafiya" ta furta a fili, sai kuma ta yi saroro bayan wata zuciyar ta ce "Ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login