Showing 120001 words to 123000 words out of 168002 words

Chapter 41 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

631

Bismillah ta fara shafa masa wannan ruwan. Tun daga cikin kansa.
Girgiza kai ya fara yi, yana ture ta da lafiyayyen hannunsa, yana toshe hancinsa. Ya din ga girgiza kai jikinsa yana karkarwa bakinsa yana rawa, ya din ga wani irin gunji yana mi?a. Amma sai da Nana ta ji?e shi da ruwan nan tsaf.
Ta kunna kiran salla a wayarta. Ta kawo tazargade, da habbatussauda da ganyen magarya ta zuba su a kan garwashin nan, haya?in ya turnu?e Wakin, ta ajiye shi a nesa da shi kaWan. Ta fice daga Wakin ta kulle shi a ciki. Ta tafi ta din ga wanke hannunta. Wani irin jiri ya din ga Waukar ta, ga matsanancin ciwon kai, Sari Waya da ya sanya take jin, tamkar kan zai yi bindiga ya rabe.
Ta samu guri ta zauna a tsakar gida, ta dafe saitin zuciyarta da yake ta bugawa da sauri.

Bayan wasu mintuna, ta tashi ta je ta le?a ta window, ta hango shi a kwance a ?asa. A tsorace ta buWe shi, ta nufe shi da sauri tana kiran sunansa.
Gaba Waya ?wayar idonsa ba?ar ta Wauke sai farar, ta dur?usa a kansa kawai ya mi?o hannu zai sha?e ta, amma ta ri?e hannunsa. Hannun ya din ga rawa, ya sauke shi a hankali.

"Sayyid" tana ambatar sunansa, ?wayar idonsa ta dawo ya kalle ta.

"Sannu Shugaba" hararta ya yi ya juya mata baya. Dariya ta fara yi ?asa-?asa.
Ta ce "Haba Shugaba, ya ka juya mini baya, juyo ka kalle ni" ya ?i juyowa. Ta tashi ta buWe labule saboda yadda warin ita ma ya fara damunta.
Ta Waukko tsumma, ta hau goge masa jikinsa, saboda ya daina warin miskin nan ita ma ba ta so.
Ya tashi zaune, tana goge masa. Ta ce "Ko a yi wanka?" Ya Waga idonsa yana hararta, jikinsa ya koma jawur kamar wanda ya ?one.
Ta din ga Soye dariyarta, ta yi masa wanka, ya din ga sinsuna jikinsa yana yamutsa fuska.
Ya shafa fuskarsa ta ce "Ka yi ha?uri, magani ne, ina son ran Ubangiji Allah ya kawo mana afuwa" Ya ture ta daga jikinsa. Amma ta manne masa ta hau cinyarsa ta zauna tana dariya.

Ta juyo da fuskarsa suna kallon juna, ta lumshe ido ta buWe ta ce "Sannu shugaba" Ya jinjina mata kai. "In zubo Abinci ne?" Ya girgiza kai.

"Sai an yi salla?" Ya gyaWa mata kai.

Ya yi sallar magariba da isha'i, ta zubo masa Abinci.

Washegari ma da sassafe, ta kuma rutsa shi tana shafa masa ruwan nan. Yau ma ture ta ya din ga yi yana girgiza mata kai. Ta kunna masa haya?i, ta gudu ta rufe shi a Wakin. Haka ta sake tarar da shi, ya koma ja ya haWa uban gumi. Ta yi masa wanka. Ta ba shi Abinci ya karya.
Allah ya dafa wa Nana, ba su taSa rasa abin da za su ci ba. Kuma haka take ta jujjuya kuWin.

Sai da ta gama yi masa duk abin da zai bu?ata, sannan ta tashi za ta yi wanka, tana tsaye daga ita sai bra da zani a ?ugunta, sai cika bakinta take da aya mai gishiri, ga cikinta ya Waga sosai.
Ta waiwayo suka haWa ido. "Ya ake kallona haka?"

Ya yi mata alama da hannunsa mai lafiya ta zo.
Ta ?araso gabansa ta dur?usa ta ce "Gani" ya nuna mata cinyarsa.
Ta ce "Ina da nauyi fa, jiya ma dan na tsokane ka na zauna, ka ga baka da lafiya" ya saka hannu ya janyo ta, ta hau cinyar tasa tana dariya.
Yatsansa ya saka ya Wan latsa cikinta, ya kalle ta yana murmushi. Ita ma murmushin ta yi ta ce "Kullum sai ya ce ko ta ce tana gaishe ka" Da hannunsa yake tambayarta yaushe za ta haihu?

"Nima ban sani ba, amma dai bai fi wata? huWu ba, saura wata biyar in Allah ya sa mu na raye. Idan ka samu lafiya sosai, za mu je mu ?ara dubawa idan su Habu sun dawo, idan ba su dawo ba sai mu tafi Nijar. Duk da na san da sun dawo zuwa yanzu za su neme mu" Ya yi shiru yana ci gaba da kallon cikinta, da lokaci lokaci yake dan harbawa.
"Zan je na yi wanka"

Da hannunsa ya yi mata alamar, su je ya yi mata.

"Kana fama da kanka za ka yi mini wankan? Wato a ramawa kura aniyarta ko? To na yafe idan Allah ya baka lafiya sai ka yi mini Rayuwata" Cikin murmushi ya sunkuyo da kanta ya sumbaci goshinta ta da laSSanta. Hira yake so ya yi da ita, amma ya kasa sai dai ya kalle ta yana murmushi ko kuma ya din ga yi mata nuni da hannunsa.

Ya Wauki wayarta, ya kunna wa?ar da take yi masa, yana yi mata nuni da ta yi masa. Ta ce "A'a karatu za mu ji ba wa?a ba, a wannan yanayin da muke ciki, ai ba mu ga ta wa?a ba Sayyid" Ya tsuke fuska yana hararta. Ta ce "To shikenan, bari a kashe wa?ar, sai na raira maka da bakina ko?" Kawai ya tsare ta da ido yana wani lumshe ido.

Tana dariya ta ce "Wai Sayyid ni fa ban gane maka ba kwana biyun nan, rigima ka ke ji, amma Alhamdillah alamun sau?i ne da nasara.

Aka shiga kwana na huWu, tana shafa masa tofi tana kunna masa haya?i ta gudu ta bar shi a Waki. Yau sai dai ta gama shafa masa, za ta gudu ya ri?e ta gam. Duk yadda ta so guduwa ta kasa. Ya kalle ta yana murmushin mugunta. Aikuwa jikinta ya fara tsuma ta saka masa kuka, jin yadda gaba Waya duniyar take juya mata, tana shirin fita hayyacinta.
Har dare ya yi suka kwanta, ba ta kula shi ba, dan gaba Waya jikinta ya mutu murus, babu abin da yake yi mata daWi.
Can cikin bacci ta ji ya yi magana"Ma viee"

"Sayyid"

"Na'am"

"Magana ka yi?"

"Eh, yanzu na ji ta zo"

Ta tashi zaune cikin murna tana taSa shi ta ce "Alhamdillah Sayyid, Allah ya ?ara lafiya"

"TaSa ni na ji, ko zan ji wani abu"

Ta ce "Ga shi ina taSa ka"

Ya ce "Ba wannan ba" ya yi maganar yana rungumota da duk hannayen sa biyu.

"Sayyid hannunka ya warke?" Ta tambaye shi a kiWime cikin farin ciki.

"Eh" ya amsa a ta?aice yana ?o?arin yin wani abin daban.

"Bari na lalubo waya na haska ka na gani"
"Kar ki haska ni"

"Me yasa ganinka fa zan yi, hannun zan gani"

"Kar ki haska ni" ya sake maimaitawa.

A Wan tsorace ta ce "Anya kai ne?" Ya yi dariya ya ce "A'a ?aisar ne. Idan ma ba ni ba ne, ai kina ganewa"

Ta yi dariya ta ce "Wai Sayyid ya haka ne? Ka tsaya mu yi murnar ka samu sau?i"
Ruf ya rufe bakin Nana, bayan ya tabattar da lafiyarsa ta dawo. Duk da ya yi farin ciki da mi?ewar da hannunsa ya yi, wanda farkawa ya yi daga bacci kawai ya ji hannun ya saki, duk da ya yi masa wani iri babu daWi.

Bayan wani lokaci, ya saka hannunsa ya Waukko fitila a gefen Nana, ya kunna ya haske ta. Rufe fuskar ta ta yi, ta juya bayan ta da sauri.
Ya kwanta a jikinta yana yi mata raWa a kunnenta. "To tashi ki haska ni ki ganni, kin ga hannun" Nana ta ?are rufe fuskarta a fulo, ta ?i Wagowa.
"Kin ga" ya yi maganar yana taSa ta da hannun. Shi wannan abubuwan da take yi ma, ba ?aramar dariya take ba shi ba.

Da ?yar ta tashi, tana kallon hannun nasa da take ganin, tamkar almara ya mi?e.
Ta ja hannun ta ga ya mi?e, ta ce "Kuma ba ya ciwo?"
Ya girgiza kai yana taSa hannun ya ce "Ba ya yi"

"Allah ya ?ara maka lafiya mai Worewa"

"Amin. Na gode. Na gode" ta rufe bakinsa ta ce "Ya isa haka. Allah za mu godewa"

"Alhamdillah. Amma ya zama dole na yi godiya, kuma na jinjina miki, saboda" bai ?arasa maganar ba ta cije shi a kafaWarsa, kamar yadda ya kan yi mata, idan yana jin raha.
Kamar ba su ne cikin zullumi da damuwa ba, suka koma shagalinsu. Dare ya tsala amma tamkar rana a gare su, ?arshe ma zaman hira suka zauna. Da anjima sai ta tattaSa hannun nasa, dan ta tabattar lafiya kalau yake bai kuma ma?alewa ba.
Haka suka kwana cikin nishaWi, da kewar juna.
Da safe ta gama abin da take yi, ta shigo da maganin da take shafa masa, ya kalle ta ya ce "Wallahi ki ka zo kaina da wannan abun, sai na yi miki wanka da shi, ke ma na kulle ki a Wakin, ki ji abin da nake ji" Ganin yadda ya haWe rai ya sanya ta rabu da shi.
Wunin yau ma lafiya suka yi shi, babu damuwa, duk da jikinsa babu ?arfi sosai.
Ya ci Abincinsa ya yi sallolinsa babu wata matsala. Sai dai yau ma Nana ba ta samu rintsawa yadda yakamata ba, sai da ta san ya warke. Wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.
Wani mutum ta gani a tsaye a jikin bishiya, ya lulluSe jikinsa da mayafi. Ta yi tsuru tana son ta ga waye haka.
Yana Waga mayafin ta ga fuskarsa, ta ja da baya, ta tsorata. Tsohon nan ta gani, jikinsa yana ta fitar da wani irin ba?in abu, fuskarsa ta yi ba?i ?irin, ga haya?i na fitowa daga cikin bakinsa da hancinsa gaba Waya siffarsa ta yi muni babu kyawun gani.

Sai da Nana ta ja da baya, cikin tsoro da razani.

"Kin tafka kuskure yarinya, kuma za ki san kin taSa Giyaz bin Jaddul Jinn. Babu wanda ya taSa karya alkadarina, abu ya yi tasiri sosai haka a jikina. Dan a duk lokacin da aka yi yin?urin illata ni, barin guri nake yi. Sai dai kash kina Wauke da abin da aka yi mini tarko da shi a wancan karon." Ya jefo mata wani littafi jikinta ya ce "Ga shi nan, littafin da ki ke ta bibiya sai kin ji ?wa?waf, ki ?arasa karantawa kafin na je na yi jinya na dawo. Amma ki sani dawowata ba za ta haifar miki da Wa mai ido ba. Domin illar da ki ka yi mini sai na ninka wa mijinki, wahalar da ki ka sha ba ki ga komai ba." Kawai ya Sacewa ganin Nana.
Nana ta kalli littafin hannunta, na gurin ?aisar ne, da take ta bibiyar sai ta karanta hanata.
Da kansa littafin ya buWe, a daidai shafin da tsaya da karantawa wancan karon.
Jiki na tsuma ta ci gaba da karantawa.

Jama'ar da suke gurin girkar, wasu suka watse a dalilin gakin sarkin Aska ya bayyana a gurin, kar ya gansu ya hukunta su. Bayan musayar yawu a tsakanin Duna da uban du?usa, Sarkin Baka ya yi girgiza ya Sace.
Uban du?usa ya saka aka Wauki kakan Lanti, a ka kai shi gida. Ita ma Lantin tana zuwa gida ta faWi ?asa.
Ba ta sake farfaWowa ba sai washegari. Sai dai bayan farfaWowarta, ta tarar da kakanta cikin mawuyacin hali, wanda hakan ba ?aramin Waga mata hankali ya yi ba.
Cikin damuwa mijinta ya ce "Lanti sai da na gaya miki ina jin tsoron wannan abun, ki ka ce babu komai, ina tsoron kar rikici ya Sarke a garin nan"
"Babu rikicin da zai Sarke, ka kwantar da hankalinka, ni dai kawai fatana na kawo ?arshen Sarkin Aska."

Kakan Lanti da ya yi tari, sai aman jini, dama ga jikin tsufa, ya zamana ko tashi baya iya yi saboda buguwar da ya yi. Kwanaki huWu da faruwar lamarin, Lanti tana yi masa haya?i da ganyen Saure. Ya ri?o hannunta ya ce "Ya ke jikata, ki sani na yi miki Girka da babban Aminina, kuma ya Waukar mini al?awarin ba ki duk wata kariya, da zama mai hidima a gare ki, kuma ya yi al?awarin bawa zuriyarmu kariya daga cutarwar miyagun Aljanun cikin su. Dan haka a duk lokacin da ki ke bu?atar ganawa da shi, ki sanya kayan sa?in ki, ki Waura gurunki. Sai dai kar ki kira shi a guri mai ?azanta, ba ya son zama a guri mai ?azanta, kuma ba ya zama a guri mai najasa. Sannan 'yar ki Duna ne ya shafe ta, kuma ga wannan abu da ya faru, abu ne mawuyaci ta warke, sai dai idan uban du?usa ne ya samo mata magani. Ni na san ba zan rayu ba, Duna ya riga ya yi mini illa, dan haka ki kula da mutanen Buda. Yana gama faWin haka wuyansa ya karye. Lanti ta fashe da kuka, ya buWe baki yana son ya yi mata magana amma ya kasa, har ya daina motsi ya mutu.
Nana ta yi kuka ba kaWan ba, da mutuwar Kakanta.

?aisar ne a tsaye a kan wani dogon tsauni, gabansa kuma Giyaz ne, da yake kamannin da shi sak, tamkar ya yi kaki ya ajiye.

"A kan me za ka je ka aikata wannan shirmen da ka yi? Ko har ka manta da cewar fansarmu za mu Wauka a kan abin da mutanen nan suka yi mana?"

"A'a Giyaz, mutanen nan ba su ne ainihin waWanda suka fara rigimar nan ba, kuma Sarnar da aka yi musu ta yi yawa. Babu amfani rashin zaman lafiya da tashin hankali. Kuma ka duba irin cutarwar da abokinka Duna ya haWa kai da sarkin Aska yake yi wa mutanen garin nan. Yakamata a zauna lafiya, haWa kai da bil'adama ana cutar da jinsinsu ba zai haifar da Wa mai ido ba."

"Rufe mini baki ?aisar" ?aisar ya kalli mahaifinsa jin ya kira shi da sunansa na yanka, saSanin sunan da yake masa kara da shi, na uban du?usa wanda da shi ake kiransa saboda kara ga mahaifinsa. Dan duk cikin bataliyar 'ya'yan da ya haifa, ya fi ?aunar sa. Ya Wora da cewa "Kar ka manta abin da suka yi wa Mahaifina Jaddul Jinn wanda yake kaka ga duk wani Aljani da yake nahiyar nan, da yadda ake girmama shi, sai mene ne dan a azabtar da su. Dan mene zaka hau kan bil'adama a matsayin bawa, duk da kasancewar ka ?asaitaccen matashin aljani da ake ji da shi a jinsinmu" ya yi maganar cikin Waga murya, muryarsa na amsa kuwwa a ilahirin dajin.

"Zaman lafiya da kwanciyar hankali, mu rayu mu da su babu cuta babu cutarwa. Lalata musu amfanin gona, sanya musu rashin lafiya da makamantansu duk ba zai sanya ku huce ba, tun da waWanda suka yi laifin na sun mutu basa nan"

"Uban du?usa yanzu ka fifita bil'adama a kan ni mahaifinka?"

"Ko Waya, sai dai ka san muna mutunta yarjejeniya. Mun yi yarjejeniya da abokina, zan ci gaba da bawa zuriyarsa kariya, zan kula 'yar sa zan din ga kawo mata magunguna tana bayarwa. Kuma ya yarje mini ci gaba da yi wa zuriyarsa hidima, da bayar da magani ta hanyar waWanda aka haifa da tauraron 'yar sa Lanti"

"?arya ka ke yi ?aisar. ?ana ba zai zama bawa ga gajiyayyun halittu kamar bil'adama ba, ka sani yadda suke yi mana kallon halittu ma?aryata, haka su ma ba su da cika al?awari. Ka tuna kai makaranci ne, manazarci kuma marubuci. Ka karanta litattafai da ni kaina ban san adadinsu ba. A Wakin karatun ka akwai litattafan da aka rubuta dubbanin shekaru kafin zuwanka Duniya. Ka yi yawace-yawace a Duniya domin neman abubuwan rubutawa, kuma ina da tabbacin ka karanta tarin kashedin da magabantanmu suka yi mana a kan bil'adama. Dan haka ba zan bari iliminka da soyayyar da nake yi maka, su ?are a kan yi wa biladama hidima ba, ba ma su su yi maka ba. Sai dai ka zaSa, zama da mu ko kuma hidima ga bil'adama!"

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
Sai da ta shekara biyar, tana aikin jakar nan, tare da ji?ata da magunguna daban-daban. Ban da zanen hatimai kala-kala da yake cikin jakar.
Ta haWa kai da Wan uwan Sarkin Aska, baya nan ya je ya ajiye masa jakar a ?asan abin kwanciyar sa. Kuma ?aisar ya Satar da sahun sa, ta yadda babu wanda ya gane a cikin aljanun da suke yi masa hidima. Tun da ya kwana a kan jakar, Aljanun da suke yi masa aiki, suka watse suka bar shi, ya kamu da matsananciyar rashin lafiya da sai da ta yi ajalinsa. Yana mutuwa kuma aljanun suka fantsama kan 'ya'yansa da jikokinsa, sai dai aka rasa wanda zai gaje shi gurin ci gaba da aikin zaluntar al'ummar da yake yi. Sosai mutanen gari suka yi murna da mutuwar sa. Babban Wan sa da suke bokancin tare ma, cewa ya yi ba zai iya ba.
?in samun wanda zai gaje shi, ya sanya aljanun fara sanya wa iyalansa cututtuka. Wasu kuturta wasu suka makance, har da waWanda suka haukace. Aka din ga Wauki ba daWi da Lanti, a kan sai ta warkar da su. ?aisar ya gargaWe ta a kan babu ruwanta ta rabu da su.
Lanti ta shafe shekaru Ashirin da bakwai, tana aiki tare da ?aisar tana harkokinta na bori da bayar da magani, haka zalika ita ma ta yi wa mutane da dama girka, masu sha'awar harkar bori. Akwai bikin 'yan bori da ake gudanarwa da nuna bajinta duk shekara, wanda a nan ake yi wa masu so girka, ake bikin bajekolin abubuwan ban mamaki, na gidaje daban-daban.
Maharba su yi na su, wanzamai, 'yan bori da dai sauran su.
Domin bayan mutuwar Sarkin Aska an Wan samu zaman lafiya, tun da dama shi yake assasa duk wata fitina da rashin zaman lafiya. Sai dai aljanu ba su fasa cutar da su da razana su ba, duk da Lanti tana iya kokarinta. Sai dai ita ma bayan wannan shekarun ta koma ga Allah.
Sai dai kan ta mutu, a cikin jikokinta an samu guda Waya da take da irin tauraronta.
Dan haka bayan mutuwar Lanti, aka ci gaba da ba ta kashi tsakanin mutanen garin, da Aljanun da sarkin Aska ya yi aiki da su, har ma da waWanda ba 'yan asalin garin ba ne.
Sai dai babu yadda ?aisar zai yi, a lokacin jikar Lanti ba ta kai lokacin da za ta iya bayar da magani ba. Kuma har a lokacin ba a fasa yi masa magiyar ya rabu da bil'adama ba. Gaba Waya ya nesan ta kansa da Ahalinsu.

Bayan jikar Lanti ta fara tasawa, ?aisar ya fara bijiro mata, domin yin gadon kakarta, sai ta kasa Wauka sai ma taSin hankali da ta samu, duk da ta Wan taSa bayar da maganin amma ba sosai ba. A hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login