Showing 141001 words to 144000 words out of 168002 words

Chapter 48 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

682

da shi.
Kin san waye mutum na farko da na fara bayarwa?"
Jamila ta girgiza kai alamar a'a.
"Babban yayanmu, da iyayensu su ka mayar da mu saniyar ware a gida"
Jamila ta jinjina kai a Wan tsorace ta ce "Sai kuma ki ka ba da wa?"
Hajiya Sa'a ta yi murmushi ta ce "Zan ?arasa miki nan gaba kaWan, yanzu bari mu ?arasa gida, akwai abin da nake son yi"
Jamila ta jinjina kai tana satar kallon Hajiya Sa'a.

Hajiya Sa'a ta ajiye Jamila, sannan ta ja motar ta tafi. Tana tafe ta kira layin Alhaji Zailani.

Sai da ta kusa katsewa, sannan ya Waga tare da yin sallama.

Ta ce "Ai na zata ba ka Waga ba ne"

Ya ce "A'a ina tu?i ne? Lafiya?"

"?alau, tambayarka abu zan yi"

Ya ce "Ok, ina jin ki"

"Ashe kwanaki da aure zaka yi?"

Ya ce "Yaushe?"

"Kwanakin baya mana, za ka auri wata yarinya Nana"

Kamar tana gabansa ya tsuke fuska ya ce "Waye ya gaya miki"

"A'a ba sai ka ji wanda ya gaya mini ba, zancen Duniya ba ya Suya ai, sai dai ka sani na san da abin da ka ke nema, ni ma shi nake farauta"
"Sa'a ban fahimci abin da ki ke nufi ba fa, ki yi mini bayani gwari-gwari "

"Za ka fahimta ne, ka je ka nutsu ka yi nazari" ta kashe wayar ta ajiye ta ci gaba da tu?inta.

*

Yana zaune a takure a gurin, ya yi shiru tamkar mai jiran tsammannin wani abun, aka buWe ?ofar Wakin da yake . Wasu ti?a-ti?an murWaWWun maza suka shigo. Ba su yi wata-wata ba, suka yi sama da shi, suka fito da shi daga gurin da yake zaune.

Wani Wakin aka sake kai shi, sai dai yana shiga ya yi turus, ganin mutumin da yake zaune a cikin Wakin.
?artin suka juya suka fice, suka bar shi daga shi sai mutum biyu a Wakin.

"Bismillah ka zauna mana" cike da tsoro ya ?arasa ya zauna yana rarraba ido, ya sunkuyar da kansa.

"Mahmudu, Wagowa za ka yi ka kalle ni ai"
Ya Waga kai ya saci kallon mutumin, ya mayar da kansa ya sunkuyar.

"Na san wannan zaman takurar ya ishe ka zuwa yanzu, kasancewarka mutum da ya saba da 'yanci a baya.
Ina son ka buWe kunne ka saurare ni da kyau, tambayoyi nake son na yi maka, muddin ka gaya mini gaskiya ka bani amsa, zaka iya samun sassauci, ko ma na yi umarnin a sake ka, ka yi tafiyarka gaba Waya"

Ya jinjina kai ba tare da ya Wago ba.
Mutumin ya sauke rawnain fuskarsa ya ce "Na san an yi maka wannan tambayoyin an kum a baya, yanzu ma zan sake jaddada maka su, me yasa ka sace Imam ka kai shi Nigeria, da ka kai shi kuma me ka yi masa?"

Kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya girgiza kai ya ce "Ban sace shi ba, kuma ban yi masa komai na cutarwa a Nigeria ba"

"To me yasa ka tafi da shi Nigeria ba ka sanar da kowa ba?"

Mahmudu ya ce "Wannan wani sirri ne da ba zan iya tona shi ba, ko da za ku salwantar da rayuwata, wani abu wanda daga ni sai shi Imam"

Abduou ya jinjina kai ya ce "Da amincewar sa ku ka tafi Nigeria kenan?"

"A'a hasalima bai san komai ba, ba wani da zaSi ne da ya rage, sai abin da na aikata Win"

"Mahmudu, na fuskanci zama da maWaukin kanwa ya sanya maka farin kai. Rayuwa da Imam ya sanya ka koyi ba?in taurin kai irin nasa. Amma ka snai, kama da wane ba ta wane, kuma? ina fatan ka san da tun da aka Waukko shi daga Nigeria har yau ba ya hayyacinsa, bai yi magana da kowa ba?"

Mahmudu ya girgiza kai ya ce "A'a ranka ya daWe. Rashin gane kowansa ba shi da nasaba da zuwansa Nigeria"

"Saboda me?"

"A can Win ma ba gane kowan yake yi ba"

Abduou ya Wan yi shiru sannan ya ce "Zoben Azurfarsa fa guda Waya da baya hannunsa, ina fatan ka san inda wannan yake?"

A zabure Mahmudu ya kalli Abdou matawalle, jin abin da ya faWa.

"Ka daina zaro mini ido, kwanaki biyu kawai ka ke da su, ka faWi inda zoben yake, ko kuma ka rasa rayuwar ka baki Waya, zaSi ya rage naka"

Abdou ya mi?e, ya ja rawaninsa ya rufe fuskarsa ya fice daga Wakin.

Cikin matsanancin tashin hankali, ya bi bayan matawalle da kallo. A Nigeria babu wanda ya san ma'anar zobunan da suke hannun Imam. Kuma ya yi iya ?o?arinsa gurin ba shi dukkanin kariya, balle ya ce wani ya san muhimmancin su ne ya karSa.
Matu?a ya ji yana son ya ga Imam, ya gana da shi, sai dai ya san ko mai zai yi babu mai ba shi wannan damar. Ga shi ya ji Abdou ya ce tun da aka dawo da shi, bai farfaWo ba balle ya yi magana. Gefe guda kuma yana jin tsoron kar a koma a Nigeria a bibiyi Nana, saboda za ta shiga matsala ba kaWan ba.
Koma a wani hali take ciki yanzu? Ya tambayi kansa yana jin wata irin damuwa ta mamaye zuciyarsa, tare da Wora wa kansa laifi amincewa da auren Imam da Nana, ya kuma Soye mata komai a kan Imam Win. Ya dafe kansa da yake jin tamkar zai tarwatse dan damuwa.


Nana ta nutsu da zaman gidan Nene, duk Nenen akwai faWa kamar yadda Hajara da mijinta suka din ga faWa, amma sam hakan bai damu Nana ba, dan ba ta yi mata abin da za ta yi faWan.
Nana ta fuskanci Nene sana'ar Abinci take yi, wasu lokutan tun safe idan ta fita sai daf da magariba take dawowa. Ta kan dawo tar e da yaran da suke yi mata aiki, su fara rage aikin Abincin sayarwar da za a yi washegari.
Nana tana jin yadda Nene take yi musu bala'i bisa kuskure kaWan. Nene ta din ga gwada Nana, da ajiye kuWi ko ina ta ga dama, ko ma ta fita ta bar Wakunanta a buWe, amma ko allura ba ta taSa rasawa ba.
Kullum sai ta ba wa Nana Abinci, na safe kan su fita na sayarwa ta ba ta na rana, idan sun dawo ta ba ta na dare, har da ma tsaraba ta masu ciki.
Ma'aikatan Nene sun Wauka ma, Nana 'yar uwatta ce.
Idan sun dawo Nana kan fito ta ce za ta taya su aiki, Nene ta yi ta faWa ta ce ba za ta yi ba. Sai dai hakan ba ya hana Nana kama musu wasu ayyukan.
Nana ta shafe kusan wata guda a gidan Nene, ta ga kullum sai Nene ta ba ta Abincin nan sau uku, ba ta taSa nuna mata ta gaji da ciyar da ita da take yi ba, wasu lokutan har tambayarta take yi, ko tana son cin wani abin ne daban.
Da daddare ta kira Nana, Nana ta fito ta zauna a kusa da ita. Ta buWe takarda fal kifi ta ce "Nana ga kifi ko za ki iya ci, idan ?arnin ba zai dame ki ba".

Nana ta dube ta ta ce "Nene, dama ina son mu yi magana ne"

Nene ta ce "To ina jin ki"

"Na ga kullum sai kin bani Abinci sau uku a rana, na ce ko za ki ba ni wani aikin na din ga yi miki, a maimakon Abincin da ki ke ba ni, ko gurin sayar da Abincin sai na din ga bin ki, ko wanke-wanke na din ga yi miki"
Ta dubi Nana, sannan ta numfasa ta ce "Ni kuwa duk rashin imanina, da wannan tsohon cikin sai na saka ki aiki, dan dai abin da za ki ci sau uku ba zai gagara ba. Ban san takamaiman abin da ya kawo ki ?asar nan ba, ban san kuma lokacin komawar ki ba, amma ba na tunanin abin da za mu ci ni da ke zai gagare ni. Ba zan Soye miki da fari ban so zamana da ke a gidan nan ba, saboda ba na son matsi da takura ko kaWan, da su Auwwalu sun matsa ne, dan kora da hali na so yi miki. Amma yanayin ki ya nuna mini ki na Wauke da damuwa mai nauyi a zuciyarki. Ba ?aramin dalili ne zai sanya yarinyar mace, mai ?anan shekaru kamar ki, ta baro gida ta taho uwa Duniya ba ga juna biyu. Kuma ki na yawan zama ki yi shiru, fuskar ki Wauke da damuwa. Na kuma jarraba ki ta Sangarori da dama, ban ga alamar rashin nutsuwa a tare da ke ba, shi yasa na ji zan iya zama da ke. Amma Nana tsakaninki da Allah wannan juna biyun na ki, na halal ne? Kuma da sanin iyayenki ki ka taho nan?"
Tambayar Nene ta yi wa Nana mugun zafi a ?irjinta, amma sam ba ta ji haushinta ba, dan kowaye dole ya yi irin wannan tambayar. Sai da ta ji hawaye ya cika mata ido, da tuna ire-iren waWannan tambayoyin dole ta ci gaba da amsa su, a cikinta da abin da za ta haifa, muddin ba gano inda Sayyid yake ta yi ba.
Ta haWiye wani irin yawu mai zafi ta ce "Nene cikina na halal ne, ni matar aure ce, ban kuma gaya wa iyayena zan taho nan ba, sai da na riga na yo nisa da gida"

"To saboda me, kuma ina mijinki?"

Kawai Nana ta fashe da kuka, ta ce "Shi na fito nema, mijina da danginsa"
Nene ta ce "Shikenan, ya isa haka ki kwantar da hankalinki, mu bar maganar ma yi wani lokacin. Amma sai dai ki yi ha?uri, dan dole sai mun ?arasa wannan maganar Nana, saboda ni uwa ce, dole na mu'amalance ki na yi miki nuni da abin dai-dai da akasin haka. Ban ga alamar ki na magana da wani a can gida ba, ko ta tarhon hannunki ce ba. Mahaifiyarki tana raye?" Nana ta jinjina kai tana share hawayenta.
Nene ta ce "Shikenan, share hawayenki mu ci kifin"

Ta girgiza kai ta ce "?arnin hawa kaina yake yi na ?oshi" daga haka Nana ta tashi, ta koma Wakinta. Sai dai ta din ga kuka, saboda ita kanta ba ta san ta ina al'amuran za su warware ta cimma abin da ta fito nema ba.

Shukura ta rasa gane kanta da kanta, saboda rashin lafiya da take ta fama, ga Sagir ya rage ba ta kulawa, duk da yana ta Soye-Soye amma tuni ta daWe da gano shi, sai dai ta maze ita ma ba ta nuna masa ba.
Hajiya Amina ce ta je gidan, Shukura ta ji daWin zuwanta sosai da sosai, a nan Hajiyar take gaya mata batun Nana.

Cikin damuwa Shukura ta ce "Wallahi Mami, tun da aka yi auren nan, nake jin tausayinta, gaba Waya ban ga riba a abin da babanta ya yi mata ba. Babu bincike babu komai a ce an aura mata mutum, wasu lokutan na kan rasa ina tunanin mutanenmu yake tafiya"

"Ke dai a yi sha'ani kawai, amma na jinjina batun ni kaina"

"Shikenan an saka rayuwarta a gagari, ga ?arancin shekaru" suka ci gaba da jajanta lamarin. Hajiya ta fuskanci yanayin Shukura kamar ba ta da cikakkiyar lafiya, ta kira Doctor Sharif ya zo ya duba ta.
Shukura ba ta so ba sam, dan ko ?aunar ganin Sharif Win ba ta yi, amma tuna ta yi wa Hajiya Al?awarin komai ya wuce, ta yi tawakalli ta dangana ya sanya ta ha?ura.
Ya zo har gida ya yi mata gwaje-gwaje, ya kuma tabattar mata da tana da juna biyu.
Hajiya Amina ta din ga murna, a duk lokacin da aka ce ga wata mace da ciki, sai ta yi ta murna, ta ji dama ita ce.
Shukura ba ta wani yi murna ba, saboda ita gaba Waya haihuwar ma ta fita daga kanta.
Da yamma Hajiya Amina ta koma gida, saboda tsabar zumuWi, tana zuwa ta tarar da Alhaji Zailani a gida, ta hau ba shi labarin Shukura wani cikin ne da ita. Wata irin mummunar faWuwar gaba ce ta ziyarce shi, yana tsoron a wannan karon ma, kar a nemi ya bayar da wani abu da ya danganci iyalinsa.

Hajiya Amina ta din ga jin wani irin bacci, tana idar da sallar isha'i, ta Sungire a gurin ta hau bacci.

Ita da Nana ta gani a falo, a zaune suna hira, kamar yadda suka taSa yi kwanaki lokacin Nanan, na zuwa gidan rainon Haidar.
Ta ce "Hajiya, kin kuwa ci gaba da bibiyar Likitoci a kan matsalar rashin haihuwar ki?"
Hajiya Amina ta ce "Nana ai ni na ha?ura ma na bar wa Allah, yanzu shekaruna sun wuce na haihuwa"

Nana ta ce "A gurinki ba, a gurin Allah yana bayar da falalarsa a inda ya so, da kuma lokacin da ya so ne. Ki daina biye wa wannan mijin naki, ya din ga sarrafa rayuwar ki yadda yake so. Ki nemi mafita a kan matsalolinki.
Kuma Shukura ta dage da Addu'a, kar wannan Wan ma ya sake raba ta da shi"

Maganar Alhaji Zailani ce ta tashi Hajiya Amina daga mafarkin da take yi, tana kallonsa kawai ta ji gabanta ya faWi"

"Lafiya ki ke kwance a ?asa haka ki ke bacci?"

Ta ce "Bacci ne ya Wan Wauke ni ban sani ba"

Ya ce "To ki tashi ki koma gado mana, kar wuyanki ya yi ciwo" Ta yin?ura ta tashi ta canza kaya ta hau gado ta kwanta, sai dai ta din ga jin mafarkin da ta yi da Nana a jikinta, tamkar a zahiri ya faru.

Fadila ce zaune a kusa da Alhaji Fatuhu, gefenta kuma jaririnta ya yi wayo, yana ta bacci.
Ta mi?a masa lemon da ta haWa masa a kofi, ta zuba masa ido, yana sha a hankali.
A ranta take faWin "Ubangiji Allah ka bawa wannan bawa naka lafiya, albarkacin ayoyin Alkur'ani'
Ta kalle shi tsaf, ya yi rama ta ban mamaki, dan ma yanzu ya Wan ciko, ba kamar da ba" ya shanye ya mi?a mata kofin, ta karSa ta ajiye a gefe. Ta matsa kusa da shi tana Wan ?ara gyara masa filulluka.
Ya ce "Na gode sosai, Allah ya yi miki albarka, ya raya miki Muhsin"

Ta ce "Amin Daddy"

"Da lafiyata ?alau, da mun yi sauri, nan da wata wata taran, ki kuma haifo mana wani" Murmushi ta yi ta ce "Allah ya baka lafiya ya tashi kafaWunka" ya amsa da Amin yana ri?e hannunta cikin nasa da ya yamuste kamar na tsoho.
Hajiya Suwaiba ta ce ta shigo Wakin, Fadila ta Wan zabura ta ja da baya.
Hajiyar ta ja tsaki ta ce "A hakan ma da kake wani abin ka ke ?o?arin yi, ai sai ku rufe ?ofa kar yara su faWo, a lalata mini tarbiyyar yara"
Fadila ta ce "Haba Hajiya, abu na ba shi ya ri?e hannuna, and laifi ne dan ya ri?e hannuna wani abin ki ka ga na yi?"

"Kar ki yi mini rashin kunya dai? Idan ma yin ku ke, ku ?arata ku da Allah"
Ran Fadila ya yi mummunan Saci, ta yin?ura da niyyar, ta Wauki Wan ta ta bar Wakin, amma ya ri?e hannunta, ya hana ta tafiya. Hajiya Suwaiba ta gama bala'inta ta tafi ta bar su.
Idan ya ce Suwaiba ba ta ?o?ari a kan rashin lafiyarsa ya yi ?arya, tana iyakar ?o?arinta amma wasu lokutan tana da saurin ?osawa gashi haryanzu azababben kishi na Wawainiya da ita.


Gidan Maijidda kuwa, Iliyasu bai taSa tsammanin,? ? Maijidda na da taurin kai haka ba. Gaba Waya ta tarkata shi ta yi watsi da shi. Iyakarta da shi, ta girka Abinci ta ba shi, idan bu?atarsa ta tashi, ya yi kiWansa ya yi rawarsa. Gaba Waya ta sanya damuwa a ranta, ta rame sosai da sosai, dan ko Abincin kirki ba ta iya ci, kusan kullum cikin kuka take, ko ta zauna ta yi shiru. Ga shi ya lura 'yan uwanta sun fara gajiya da sinturin kai ?ararta da yake yi, ba yau ba gobe.

"Anya ka na ganin haka rayuwar Imam za ta ci gaba, duk lokacin da ya farka sai ihu da fizge-fizge, sai dai a yi ta yi masa allurar da zai yi bacci? Idan aka bar shi a haka rayuwarsa fa ta nakasa kenan har abada"

Sultan ya ce "Abdou, ni kaina ala'amarin nan yana damuna, na rasa yadda zan yi. A Sangaren ?wa?walwar ma, babu wani gamsashshen bayanin abin da ya faru da shi. Ta Sangarenka ma babu wani nagartaccen bayani daga bakin shi yaron, balle mu ji ko wani abin Win aka yi masa".

"Sultan, ka ?i bayar da dama a sanya 'yan doka, su maguza yaron nan, ya faWi gaskiya ko ya ?i Allah"

Sultan ya girgiza kai ya ce "A'a, duk ranar da Imam ya samu lafiya, muddin ya ji labarin an cuzguna masa, zai yi fushi, kuma zai ji babu daWi kai ka san irin ala?ar da take a tsakaninsu."

"Amma yanzu ai yanzu a kan gaSar bincike a ke Sultan. Amma tun da haka ka ce Shikenan, za a ci gaba da bin komai sannu a hankali"

Sultan ya amsa da "Yauwwa"

BAYAN WATA ?AYA
Sabo turken wawa, rashin ganin ?aisar da Nana ta daina yi, ya sanya ta din ga tunanin ko wani abin ne ya faru da shi.
Sai dai yau kwatsam cikin barcinta, ta ganta a cikin Librarynsa. Sai dai ta gurin ?walam babu litatafai babu kayan rubutunsa sai mudubin da yake nuna mata abubuwa a cikinsa.
Ta waiwaya ta lelle?a, amma babu ?aisar babu alamunsa.
Wani littafi guda Waya tal, ta hango a kan teburin rubutun ?aisar, ta ?arasa ta nufi teburin ta Wauki littafin.

Bangon littafin na fatar wata dabba ne. Dan har da gashi-gashi a jiki. Yanayin bangon littafin ya sanya ta yi tunanin, ko mene ne a rubuce a littafin ba yanzu ya faru ba, ya kwana biyu da faruwa. Littafin ba wanda ta karanta tarihin su Lanti ne a ciki ba, wani ne daban.
Hoton wata al?arya ce, da ke tsakanin duwatsu, da aka rarake aka samar da katafariyar daula.
Ta buWe littafin shafin farko, ta fara karantawa.

"Tushiya..." Shi ne abin da ke rubuce a shafin farko na littafin.

"Ka sani,har abada da Wan Gari a kan ci gari. Kuma ba a cimma buri da tausayi ko jin ?ai. Wannan mataki na farko kawai ka cimma, na sharar fagen cimma nasararka.
Ka na bu?atar sanya wa mutane tsoronka, da shakkarka domin cimma burinka, kuma hakan ba zai taSa yiwuwa ba sai ka zubar da jini, duk wanda ya biyo ta hanyarka ka datse rayuwarsa, kar ka damu da adadin rayukan da za a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login