Showing 39001 words to 42000 words out of 168002 words

Chapter 14 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

629

goge mata, bayan ta gama sai ga wani saurayi mai kama da matar ya shigo, da gayyar abokansa.

Bayan Nana ta gama da falon ?asan, matar ta ce "Dan Allah taimaka ki karkaWe mini falon saman ma"

Nana ta ce "Babu damuwa" ta hau saman benen, sai dai hawanta ke da wuya, ta ?ara jin jikinta babu daWi, kamar za ta fita hayyacinta. Sai ta fara sauri ta yi ta kammala, ta kammala kafin wani abin ya faru.

Ga mamakinta ta ga wata matashiyar budurwa, za ta Wan girme mata, ta fito daga wani sashi na Wakunan saman benen, tsiga-tsigal da siraran ?afafuwanta ta saka mini skirt sai vest a jikinta.

Nana ta kalle ta ta ce "Sannu ina kwana" Sai a lokacin ta kula da Nana ta ce "Yauwwa" ta nufi wata ?ofa.

"Siyama" matar ta kira sunanta. Cak ta tsaya ta waiwayo ta ce "Na'am"

"Wai Yusra ba za ta fito ta karya ba ne?"

Siyama ta Wan Wage kafaWa ta ce "I don't know"

Matar ta Wauki wayar ta, ta danna sannan ta kara a kunnenta.

"Ki fito falo, ina son ganin ki" ta ajiye wayar, tana mita ?asa-?asa. Nana a ranta ta din ga mamakin, da mata kamar wannan a gida, amma a ce saboda babu mai aiki an yi sati ba a yi shara ba.

Nana ta nemi guri ta yi zamanta a kan carfet, tana kallon t.v. sai dai har ta shafe lokaci a zaune, ba ta ga wadda aka kira Win ta fito ba.

A?alla Nana ta kai awa biyu, tana kallon film a MBC2 na divergent. Sai da aka gama ta yin?ura ta tashi ta ce "Na tafi"

Matar ta ce "Har za ki tafi? Duba dining akwai ragowar bredi, ina ga har da sauran dankali ma ko za ku yi amfani da shi"

Nana ta yi murmushi ta ce "A'a Hajiya na gode sosai, idan na tafi da shi sai dai na ajiye, a ?oshe muke sai anjima" ba ta ma jira mai Hajiyar za ta ce ba, ta yi waje abin ta, tana jinjina rainin hankalin matar, dan wula?anci ma ita za a bawa ragowar buredi.

A harabar gidan ta hango shi yana ta kaiwa yana komowa, ita tun da ta samu kallo ma har ta manta da shi. Wani irin kallo ya yi mata da sai da ta Wan tsorata. A hankali take takawa tana satar kallonsa, har ta wuce bai kula ta ba, bai kuma bi ta Wakin ba.

*Ayshacool
Alhaji Fatuhu ne yake zaune yana kallo, ya Wan kalli matarsa Fadila ya ce "Kin an yi wa malamr su Muhsin aure kuwa?"

Ta ce "Haba dai?"

"?arya na yi kenan?" Ta dafe bakinta da sauri ta ce "Afuwan"

Ya ce "Haka na ji a bakin Yaya Sa'a, ashe wai ta santa"

Fadila ta ce "Haka na ji ranar da ta zo gaisuwa, amma ba ta kyauta ba, abin babu gayyata"

"Ni tun kwanaki ta ce mini za ta yi auren ai, na ma zata tuni an yi fa, ashe sai kwanan nan aka yi, amma duk da haka zan bayar da wani abun a bata"

"Gaskiya yakamata, ni ma zan bayar, ina fatan Allah ya kawo rabo, ta yi yaronta takwara"

Ya Wan yi murmushi yana tuna yaron nasa.

Ta ce "Yauwwa Daddy, ya ciwon kan kuwa?"

Ya Wan Sata fuska ya ce "Ke dai a yi sha'ani kawai, daurewa nake yi amma duk da haka Alhamdilillah"

"To sannu Allah ya ?ara afuwa"

"Amin babyna" ta yi murmushi tana Wan yi masa fari da ido.

*
Yunwa ce ta ishi Nana, ita ba azumin ba, amma ba ta ci komai ba, ta Wora girki, sai dai fafur ya ?i shigowa Wakin.

Muryar Habu ta ji yana ta kwaWa sallama, ta saka hijjabi ta le?a, ta ga Buzu ba ya gurin. Ta amsa sallamar ta ce ya shiga.

Ya shiga yana sake sallama, ta amsa masa ta ce "Ina ga ya Wan fita ne"

Cikin damuwa ya ce "Ya fita kuma, ina yaje?"

Nana ta ce "Nima ban sani ba, amma ai dama yana fita"

"Duk da haka, kar ya din ga nisa, ki din ga hana shi fitar, kin san ba shi da cikakkiyar lafiya"

Nana ta ce "Ta yaya zan hana shi fita, ni ka zo gaSar da nake son a zo. Ni fa mutumin nan tun da aka yi auren nan, ko sunansa ban sani ba, kullum na tambaye shi sai ya ce mini sunan shi Buzu. Yakamata na san waye shi, a ina ku ke a ?asar ku? Kuma yaushe za mu je na ga danginku. Tun da a haka tawa ?addarar ta zo."

Habu ya numfasa ya ce "Kin yi gaskiya Amarya, shi yasa na yi ta ce miki ki yi ha?uri, ki karSi ?addara, sai a yanzu na ?ara tabattar da wannan ?addarar ce ta haWo mu baki Waya.
Magana ta gaskiya, ban san waye Buzu ba, a sahara na tsince shi cikin mawuyacin hali, mai kama da gushewar hankali da Wimuwa. Yanayin kamaninsa ya sanya na san Wan uwa ne buzu, kuma buzyen ma kala-kala ne, na ji yana iya hausa ya kuma iya French, shi yasa na tabattar da Buzun Nijar ne. Na yi yin?urin tafiya da shi Nijar, saboda idan na bar shi a saharar nan, zai iya rasa ransa, ban kuma san da wa zai haWu ba, dan haka na yi nufin tafiya da shi Nijar, domin neman ahalinsa. Sai dai da na yi yin?urin nufin komawa Nijar da shi, sai guguwar sahara ta taso, ta rufe hanyar baki Waya. Dole na canza hanya na nufo Nigeria, jikina ya bani akwai wani abu, domin duk wata hanya da zan bi mu koma Nijar na kasa samun ta.
Ina da wasu abokai a Nigeria, su na kira suka karSe ni, da niyyar a taimaka mini, a samo masa magani. Saboda duk abin da na tambaye shi game da shi bai sani ba, sunansa, waye shi, daga ina yake, ina za shi duk bai sani ba. Wasu lokutan zai yi miki abu lafiya kalau na cikakken mai hankali, sai dai ba zai taSa iya ce miki waye shi ba. Wasu sai ya burkice, ba magana yana ma iya daina gane mutane gaba Waya. Ba ya son magana ko da yana normal, sannan wasu lokutan ya kan burkice ya din ga jijjiga. Duk gurin mai maganin da muka je a Nigeria sai a ce ba za a iya ba shi magani ba. Shi yasa tun da aka yi auren nan, za ki ga kusan kullum ina zuwa, ina kawo muku abin amfani, wallahi ina matu?ar tausayinsa ne. Ba shikaWai ba har da ke ma"

Jikin Nana ya mutu murus, ta ce "Yanzu shikenan ba ku san kowa na shi ba? Me na aura kenan?"

Cikin kwantar da hankali Habu ya ce "Akwai dalilin da Allah ya sanya ya haWa ku, da babu wanda ya sani sai shi. Ni kaina na fuskanci ?alubale baro ahalina na taho Nigeria nema wa wanda ban sani ba magani. Idan ki ka saka hannu ki ka dafa mini a kan wannan jihadin, Allah ne kawai zai biya mu. Idan ba ki amince ba kuma shikenan babu dole, sai na wuce gaba a raba auren, dama mahaifinki ne ya matsa ya sanya aka yi auren dole".

Ba su ankara ba kawai su ka gan shi a cikin Wakin, ya ajiye abin dafa shayinsa, da kayan dafa shayin, ya juya zai bar Wakin.

Habu ya tashi da sauri yana faWin "Tun Wazu na zo ai, ba ka nan ga kayan dahuwar shayin nan na kawo maka"
Ayshacool
34



Habu bai yi zuciya ba, ya sake bin bayan Buzu, ya juya yare, ya tsaya yana yi masa magana, ya din ga zuba babu ?a??autawa.

Nana kuma mamaki ne ya ishe ta, ganin Yadda Habu ha rikice gaba Waya, kuma ita ba ta ga abin da ya yi na ba daidai ba, da zai yi wannan rikicewar kamar mara gaskiya ba.
Ita wasu lokutan har mamaki yake bata, kamar tsoron buzun yake ji, shi da yake taimakonsa amma ba ya ?aunar ya ga Sacin ransa ko kaWan.

Nana ko a jikinta, ba ta ma san yadda suka ?arke ba.
Sai dai ta yi ta jujjuya maganganun da Habu ya gaya mata. Yanzu shikenan haka za ta ci gaba da rayuwa da mutumin da ba a ma san suwaye danginsa ba? Ko a daWe ko a jima dole tana bu?atar sanin waye shi, kuma suwaye ahalinsa.
Ba ta taSa jin lallai tana son ganin ?aisar ba sai a wannan lokacin. Ba shiri ta kwanta ta hau bacci, ko za ta gan shi, amma ba ta ga komai ba, har ta gama baccin ta tashi.

Bayan farkawarta ta ga wayarta a gefenta, a lokacin yamma ta yi sosai da sosai. Da sauri ta Wauki wayar, ta kira lambar Ummi, dan tun da suka zo, ba ta ji ya suka je gida ba.

Sai da ta kusa katsewa, sannan Ummi ta Waga.

Nana ta yi sallama, Ummi ta amsa ta ce "Kai, Nana a ina ki ka samu waya?"

Nana ta ce "Dama ina da ita, kin san lambar ki na haddceta, saboda ke ce line 911 Wi na"

Ummi ta yi murmushi ta ce "Eh lallai kam, ya ki ke ya mai gidan?"

"Alhamdilillah, ya ku ka je gida, ban samu na kira ku ba, bayan tafiyar ku na Wan yi rashin lafiya ne"

Ummi ta ce "Alhamdilillah, mun je gida ?alau. Kai Nana daga zuwa sai rashin lafiya, a dai ciki ba ne ko?"

Nana ta kwashe da dariya ta ce "Dan azaba auren kwanaki sai ciki?"

"Eh mana, tun da ina jin fitsarar da ki ke yi, ranar da mu ka zo"

Nana ta ce "Wallahi kawai cika baki ne, ji na yi za su raina mini hankali ne. Kuma ba na fatan ko alama, a ga Saraka a tattare da aurena"

Ummi ta ce "Allah sarki Nana, in sha Allah auren nan, sai ya baki kwanciyar hankalin da ba ki taSa tsammani ba. Ke Jamila fa babu lafiya fa"

Nana ta dafe ?irjinta ta ce "Babu lafiya kuma? Me ya same ta?"

"Oho, ni mun yi waya da maman, ban gama gane kan zancen ba. Wai tun da mu ka baro gurin ki, washegari ta tashi ba ta iya tsayuwa, wani abu duk ya feso mata a jikinta".

Nana ta girgiza kai ta ce "Hmm na san cewa aka yi ni ce ko?"

"A'a wai sun je gurin wani mai magani, aljani ne yake hawa kansa ya bayar da magani, ya ce musu wai wani aljani suka yi wa laifi" Kan Nana ya sara, ta yi shiru tana son tuna wani abu, amma ta gagara tuna komai.

Ummi ta ci gaba da cewa "Shi ne ya basu magani, wai ya sha sannan a yi sadakar ?osai mai zafi da la'asar"

Nana ta ce "Ita sadakar ?osan ta mece ce, sharaWin mene ne? Kin ga Mama ba za ta din ga kiyaye irin wannan yawace-yawacen ba ko? Wane irin sadakar ?osai mai zafi da la'asar?"

"A'a ni ina zan sani, tun da ba ni na ba su maganin ba, ina gefe labari aka bani"

Nana ta numfasa ta ce "Sadaka mahaWin Addu'a ce, amma wannan sharuWWan da ake sakawa ne, ni ba na gane kansu"

"To ni ya za ni tsitsiye ni, labari kawai na ji, ban ma je na duba ta ba"

Jikin Nana a sanyaye ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, Allah ya sauwwa?e ya jikin Baban?"

"To da sau?i, ni rabona da gidan tun biki, amma sun ce yana jin jiki, ?afar nan tana yi masa ciwo sosai"

Nana ta ce "To shikkenan, zan samu na je na duba su baki Waya, in sha Allah, amma jikina ya yi sanyi, na san ciwon Jamila cewa za a yi nice"

"Ke rabu da su dan Allah, ni wallahi na jiye miki daWin auren nan, Allah ya sanya shi ne mafi alkhairi, amma da zaman wannan gidan namu, ba gara auren ba, kullum cikin bala'i. Ko banza Wakin ki a cike yake da kayan abinci"

Nana ta Wan yi shiru, kamar ta gaya wa Ummi halin da ake ciki, na rashin sanin dangin mijinta, amma ta basar. Ta ce "To Allah ya sa mu dace"

na gode sosai ki gaida yaran"

Suka yi sallama, Nana ta tashi ta Wan yi gyare-gyaren ta, ta Wauki magic coal Win sa da yake haWawa da gawayi, ya kunna wutar dafa shayi, ta kunna turaren wuta. Ta Wauki wayarta ta kunna karatun Alqur'ani.

Fafur ya ?i shigowa Wakin, sai bayan isha'i.
Ayshacool
Ya shigo da 'yar ledarsa, ya Wauki kwano ya zazzage fruit, ya je ya wanko abin sa, ya dawo ya zauna a gurin zamansa, ya fara ci a hankali.
Nana ta na kallon sa, zuciyarta Wauke da tunani daban-daban.

Ta dake zuciyarta, ta tashi ta tafi kusa da shi ta zauna.
Bai ko Waga kansa ba, balle ya nuna ya san tana zaune a gurin.

"Ba za ka ci abincina ba ne, ka je ka sayo fruit ka ke ci?" Sannu a hankali yake tauna apple Win bakinsa, bai kula ta ba.

"Ni mamaki ma nake yi, idan ka je da yaya ka ke sayayyar, magana ka ke yi musu, ko kuma ni ce kawai ba ka kulawa?"

Ya Sare ayaba zai kai bakinsa, ta ri?e hannun, ta sauke shi ?asa a hankali. Ya Wago idanunsa yana kallon ta. Ta yi saurin sauke nata ta yi murmushi ta ce "Na san na yi maka laifi, bai kamata abubuwan da na gaya maka ba, ka yi ha?uri ina cikin damuwa ne, amma ka yi mini afuwa ba zan sake ba" ya sunkuyar da kansa ya yi shiru.

"Ka yi magana mana" ta yi maganar a raunane.

Ture ta ya yi daga kusa da shi, ya tashi ya bar mata Wakin. Abin ya yi wa Nana ciwo, sai dai ta tuna bayanin Habu daki-daki, tabbas wasu abubuwan da yake za ka san ba normal yake ba.

Ta tashi zuciyar ta cike da damuwa,? sai dai a zuciyarta ta ?uduri aniyar jure kowane irin ?alubale, tun da ba duka yake ba, ba kuma zagi yake yi ba, gara zamanta a nan da shi sau dubu, a kan ta koma gidan su.

Ta kunna gas ta Wora ruwa, domin ta yi wanka kafin ta kwanta, garin akwai yanayin hadari, dan haka akwai sanyi.
Tana Wan dube-dube, da goge kan mududinta, ta ga Wan littafin da yake yawo da shi, ko ta ga yana karantawa, da biro a cikin drower mudubi.

Ta Wauka ta buWe, ta ga kyakyawan rubutunsa, wani da French, wani da hausa.

"A ba ni kankana, da ayaba na dubu biyu. A bani buredi mai kyau babba guda Waya. Ina son wannan jan abin, na kuWin da na bayar" sai da Nana ta yi dariya, wato duk a rubuce yake sayen abin da yake zuwa da shi. Tana shirin buWe wani shafin, ta ji wutar gas Win na fita da yawan gaske, tukunyar kai na wata irin tafasa kamar ta diro daga kan gas Win.
A gigice ta nufi gas Win ta sauke, abin ya ba ta mamaki, dan ko mintuna biyar a yi da Wora ruwan ba, yake wannan tafasar.
Ta juye ruwan a flask, ta sake Wora wani.

Yana tafasowa ta haWa ruwan ta shiga wanka, sai dai bayan ta shiga banWakin, ta ji ruwan ya yi mata zafi sosai, maimakon ta kunna famfo, ta ?ara sirkawa, sai ta jingina da bango tana jiran ya huce. Shiru ta yi tana ta tunani daban-daban a zuciyarta.

?angaren buzu bayan ya dawo Wakin, ye nemi Nana ya rasa, ya ga littafin sa a kan mudubi. Ya Wan yi jimm ko zai ji motsinta amma shiru.
Kusan mintuna goma bai ji ko zubar ruwan famfo ba, balle ya yi tunanin tana banWaki.

Gaba Waya hankalinsa ya tashi, kamar yadda ya tashi Wazu, da ya dawo ya tarar ba ta nan ashe tana cikin gidan nan ba ta gaya masa ba.

Kasa jurewa ya yi ya nufi banWakin kawai ya buWe ?ofar.

Zabura Nana ta yi, ta saki ?ara, domin ?o?arin cire zanin jikinta take yi ta yi wanka.

Cak ya tsaya yana kallonta, ta saka hannu ta ri?e zanin da hannu Waya, hannu Waya kuma ta kare ?irjinta da shi.

Sannu a hankali take jin sanyi, ?irjinta kuma ya fara bugawa.

Ta sake Waga ido, suka haWa ido, ko a jikinsa ya ci gaba da tsare ta da ido. Ta yin?ura da niyyar magana, amma ta ji ta kasa furta komai, ta sake sunkuyar da kanta ?asa.

A hankali ta ji ya rufe ?ofar toilet Win, wata irin ajiyar zuciya ta yi, jiki a sanyaye ta yi wanka, sai dai ta kasa fitowa saboda kunya.
Da kyar ta iya fitowa, amma ta ga baya Wakin, cikin hanzari take shiri, domin kwanta, kafin ya sake shigowa.

Gari sai wal?iya ake yi, da wata irin tsawa hadari yana tasowa.

Tana gama zura rigar ta ya shigo, bai ce komai ba, ya rufe taga sai dai yana juyowa gaba Waya kamaninsa sun sauya, ya koma wannan tsohon.

Kallon kallo suka yi da ita, ta tsaya tana yi masa wani irin kallo, mai cike da tsoro da razani, a take fitilar Wakin ta Wauke, Wakin ya gauraye da wani irin matsanancin duhu, ?ofa da tagar Wakin su ka din ga bugawa da ?arfin gaske.
Ayshacool
Wata irin wal?iyya ta haska Wakin, ta ganshi sanye cikin wannan fararen kayan da take ganinsa da su, hannunsa ri?e da sandar sa, idanunsa ba?i ?irin wani ba?in haya?i na fitowa daga cikin su.

Ya hangame bakinsa, ya fara fito da wuta.

"Allahumma ajirni fil musibati, wa aklifni kharin min ha" ta yi maganar tana sanya hannunta, ta Wora a kanta.

"Meyafaru?" Ta ji muryarsa. Ta buWe idonta ta kalle shi a hankali. Fuskarsa Wauke da damuwa yake tambayarta. Da sauri ta ja da baya tana girgiza masa kai.

"Kar ka sake zuwa kusa da ni, ka yi mini duk abin da za ka yi mini, na gaji me na yi maka ne?" Ta yi maganar cikin kuka.

Cikin mamaki yake bin ta da kallo, yana tunanin me ya yi mata take wannan kururwar.

Ya taka ya ?ara matsawa kusa da ita, amma ta din ga ja da baya, tana maimaita "kar ka matso kusa da ni, ba na bu?atar ka, kar ka zo inda nake".

"Kalli ni mutum ne ba abin tsoro ba, babu abin da na yi miki, le regard kalli" ya yi maganar yana nuna mata hannunsa domin ta taSa ta tabattar.

Cikin fita hayyaci Nana ta ce "Ka fita ba na son ganinka, ba za ka haukata ni a banza ba, ka fita ba na son ganin ka" ta yi maganar jikinta na tsuma da karkarwa. Cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login