Showing 105001 words to 108000 words out of 168002 words

Chapter 36 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

679

Da la'asar bayan Ummi ta yi salla, ta ba wa Nana kuWin barkononta da aka sayar, ta yi ta mata nasiha da kwantar mata da hankali, sannan ta yi musu sallama.
?an gidan Uwani ya Wauke ta a kan babur, ya tafi da ita.

Nana ta ?arasa gaban Sayyid, da ya zuba mata idanu tamkar bai taSa ganinta ba.

Ta ri?o hannayen sa ta ce "Sayyid, duk da ban san wace irin rayuwa ka yi a baya ba. Amma wadda muka yi, mun yi ta ?ar?ashin kulawar su Habu, ba mu taSa neman abu mun rasa ba. Amma Allah shi ne abin godiya. Wannan yanayin da muke ciki, ba zai dauwama ba in sha Allah. Ina fatan Allah ya baka lafiya, ya kuma baka ha?uri da juriyar a yanayin da muka tsinci kanmu a ciki".

Ya sanya tafukan hannayen sa biyu, a fuskarta laSSansa na rawa, amma magana ta gagara.

Ta girgiza masa kai tana murmushi, ta ce "Ruhinka yana cikin jikina, kar ka damu kanka lallai sai ka yi magana. A jikina ina jin abin da ka ke son faWa" Wan guntun murmushi ya yi, duk da yadda yake matu?ar son ya furta wani abu.

Da daddare Uwani ta aiko musu da tuwon dawa, da miyar karkashi, ta sha daddawar kalwa har Waurin yajin daddawa.
Ta san ba lallai ya iya ci ba, ta ba wa yaran da suka kawo kuWi, ta ce su sayo mata buredi da shayi, na gurin masu sayarwa, da kuma maganin sauro, saboda azabar sauron da ke Wakin.
Sai dai ya ?i shan shayin, buredi kawai ya ci ya kwanta. Nana jikinta na rawa ta ci tuwon, saboda yadda ranta ya biya, amma ?arshe amai har ta hancinta sai da ta yi shi.

Kan su kwanta, ta kunna maganin sauro, ta gyara masa shimfiWa ya kwanta. Ita ma ta hau katifar ta tofa masa Addu'a, sannan ta kwanta a kusa da shi, tana yi masa fifita.

Ta daWe idonta biyu, kafin bacci Sarawo ya sace ta. Sai dai kamar a zahiri, kuma kamar a mafarki ta fara jin hayaniya a kanta. Ba ta gama tantance hayaniyar mece ce ba, ta ji wani abu na wucewa ta saman roofin Wakin. Idan abin ya daki kwanon Wakin da abin da yake takawa, tamkar kwanon zai buWe ya faWo musu a ka.

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
https://chat.whatsapp.com/KJoPVAmFgseJj2f8Y9wQqg?mode=ac_t

Free class Free class Free class
Imagine a ce za,a koyar da ke kayan mata masu kyau da inganci kyauta Sannan kuma ace Zaki samu horun daga kwarariyar Mai kayan mata nan ta jahar sokoto wato maman Maryam organic aphrodisiac sokoto yar uwata mi kike jira maza kama wurin zamanki kafin ajin ya cika domin samun damar dogaro da Kai ko hutar da kanki wurin sayen kayan mata.




Wata irin yin?urawa Nana ta yi, cikin azama da tashin hankali ta kifa a kan Sayyid, saboda kar abin da yake takun koma mene ne, ya faWo masa a ka.

"Ma vie" ya furta da ?yar can ?asan ma?oshinsa. Ta Wago ta fara laluben fuskarsa a cikin duhu.

"Sayyid, ba ka ji wani abu zai faWo mana ba?"

"A'a"

Ta sake cewa maganar ta dawo "Maganar ta dawo?"

"Eh"

"To sannu" ta furta a hankali cikin tsoro, ta mayar da kanta kan ?irjinsa a tsorace. Sai dai kamar dole, ta ?arfin tsiya, wani baccin ya sake awon gaba da ita, tana cijewa da ?o?arin hana idonta sake yin bacci, amma abu ya ci tura, baccin ya kuma awon gaba da ita.

Ganinta ta yi a tsaye a tsakiyar Wakin, itakaWai babu Sayyid. Ana ta cigaba da hayaniyar da ba ta gane me ake faWa. Ta din ga waige-waige tana tunanin ina ya shiga haka? Sai dai ba ta gama tunanin ba ta ji muryoyi daban-daban suna faWin "Lale da manyan ba?in garin Buda. Barka da zuwa." Sai kuma ta ji ana dariya tare da ci gaba da hayaniya.

Idonsa biyu, yana jin yadda ta yi wa hannayensa wata irin muguwar dam?a, ta nutsa faratanta a jikin fatarsa, dan tuni ya karaya jini ne yake fita daga fatar tasa. Ta din ga juya kanta a kan ?irjinsa tana kuka tana faWin "A'a, mu ba ba?in ku ba ne ba, ba gurinku muka zo ba, mu ba ba?inku ba ne" jin ta fara Waga murya, ya sanya ya murginata gefensa, ya zame hular kanta yana shafa gashinta a hankali, tare da hura mata iskar bakinsa a kunnenta. Daga haka sai ta yi shiru, ta ci gaba da bacci.

****
Barira sai da ta sha jini leda biyu a Asibiti da allurai da magunguna, amma tana komawa gida, abu ya ?ara rikicewa. Domin kuwa babu damar ta sanya ha?ar?arinta a ?asa ta fara bacci, wannan jibgegiyar magen za ta bayyana, su hau kokowa da ita. Duk sai magen ta yayyage mata fuska da jikinta. Idan ta tashi sai ta ji jikinta na yi mata wani irin zugi da raWaWi.
Ta cewa mijinta ita fa ba za ta koma wannan gidan ba. Ya sanar mata an tashi su Nana, daga su sai su Sajida a gidan kamar da, amma ta hau kujerar na?i ta ce gidan ne ba za ta koma ba. Shi kuma ya ce sai dai ta yi ta zama a gidansu, dan ba shi da kuWin kama wani gurin.

Shukura ce tare da Hajiya Amina, suke hira. Ta je yi mata sannu da zuwa dawowar da ta yi daga umara. Alhaji Zailani ya yi sallama ya shigo falon.

"Daddy sannu da zuwa"

Ya ?are mata kallo ya ce "Yauwwa, mara tawakalli da ba ta san ?addara ba" Ta yi shiru tare da sunkuyar da kai. Duk irin kashedin da nake yi miki, da rarrashin da na yi miki, ba ki ji ba abin har ya kai ki dizga bawan Allah nan, a gaban mutane kina cewa yana kashe mutane, idan ya yi ?arar ki kina da shaida a kan haka?"

Ta yi shiru ta sunkuyar da kai. "Tambayarki nake yi" Ta girgiza kai alamar a'a.

"Amma ki ke wannan i?irarin, maimakon ki mayar da hankali a kan fatan Allah ya raya na gabanki, ya ba ki wani. Ba ki kyauta ba" Hajjya Amina ta yi ta kallon Shukura ko za ta ba shi ha?uri, amma ta yi mursisi.

Ko da ya shiga Wakinsa, babbar rigarsa ya cire saboda azabar gumin da yake yi. Dan tun da Doctor Sharif ya gaya masa ga yadda suka yi da Shukura hankalinsa ya yi mummunan tashi. Ya kuma sake jaddada wa Sharif, muddin wani abu ya fita to babu hannunsa a ciki. Kuma likitan ya yi masa bayanin process Win da ya bi, abu ne mai wahala a gano. Ya yakice gumi ya nemi guri ya zauna.

Hajiya Amina ta ce "Me yasa ba ki ba shi ha?uri ba, kina kallon yadda ya yi fushi?"

"Mummy, duk wannan abubuwan kamata ya yi a tsaya a saurare ni, a kuma fahimce ni. Da hankalina fa ta yaya zan din ga i?irarin an kashe mini Wa haka kurum.
Ayshacool
Mummy ranar da za a yi mini aiki, kina bacci cikin dare, na kasa bacci saboda damuwar da nake ciki, aka buWe ?ofar Wakin, aka zo aka kama hannuna aka laluba cannula, aka yi mini wata allura a cikin duhun nan. Tun da aka yi mini allurar nan. Na ji kaina ya fara juyawa, ina neman na fita hayyacina, duk iya ?o?arina na kasa, na ji jikina na ?amewa kamar zan yi jijjiga. SaSanin da da idan za a yi mini allura cikin dare, za a ?wan?wasa Wakin, sai kin tashi kin ce a shigo tukuna, a kunna ftila a yi mini"
Mummy ta Wan yi shiru, cike da mamakin me yasa tuntuni ba ta faWa ba, amma domin kawo ?arshen maganar, sai kawai ta kawo gigin ciwo ne ya sanya ta ga haka a lokacin. Dan haka ta ce "Duk da haka wannan ma ba hujja ba ce, ke da ki ke fama da ciwo ina za ki tantance wani abu ma. Dan Allah ki bar zancen nan"
Shukura ta yi murmushi ta ce "Shikenan, na bar shi"

Sai kuma ta sake cewa "Mummy, Nana shiru, ni yakamata ki kwatanta mini gidan da suke na kai mata Haidar"

"Gidan Alhaji Garba giwa ne fa, kuma fafur babanku ya hana ni zuwa ban san dalili ba" Dummm! ?irjin Shukura ya buga, ta ce "Saboda ne ya hana ki zuwan?"

"Ban san dalili ba, za ki je ne? Sabon gidansa nan Kano"

Shukura ta ce "Wace matar ce a gidan?"

"Halima ce, uwar gidan sa"

Shukura ta girgiza kai ta ce "Ba zani ba, gidansu tsohuwar matar Sagir ce"

Mummy ta waro ido ta ce "Ke haba? Dama 'yar Halima ce matar Sagir Win?"

"Eh mana"

"Ikon Allah, da na ce wa Daddy, ya taimaka musu, a samo wa mijin Nana, gurin da zai yi gadi, su samu su zauna, shi ne aka samo gidan"

Shukura ta ce "wai canza masu gadi ku ka yi ne?"

"Ina fa, ina nan cikin gida, daga baya ma Yusuf yake gaya mini. Wai zuwa aka yi da motoci da alama daga ?asar su ne ma, motocin duk rubutun fransanci aka kwashe su kaf, kuma babu wanda aka yi wa bayanin me yasa"

"Ikon Allah, kuma ba laifi suka yi ba?"

"To ina zan sani, ina nan cikin gida?" Suka ci gaba da tattaunawa da jajanta lamarin. Har wayar Nana suka jarraba kira, su ji ko ita nata mijin yana nan, ba a kama shi ba amma wayarta ba ta shiga sam.

****
Da safe Nana ta tashi, ta fara alwala sannan ta zuba wa Sayyid ruwan da yara suka Webo musu jiya, dan gidan babu ruwa. Ya yi alwala a ?ofar Wakin, sannan suka koma ciki ya yi salla. Sai dai bai ga alamun ta san abin da ta yi cikin daren jiya ba.
?arfe tara da rabi, Uwani ta aiko yara da kunu da 'yar tsala aka kawo wa su Nana.
'yar aiken ta ce "Uwani ta ce idan kin gama karayawa, wai ki je"

Nana ta ce "To, zan zo a ce mata mun gode sosai da sosai, Allah ya biya ta"

Ta koma ta zauna a gaban Sayyid ta ce "Sayyid, ka ga kunu ne da 'yar tsala za ka iya ci, ko na nemo maka wani abin?" Ya girgiza kai.

"To za ka iya cin wannan Win?" Ya gyaWa mata kai.

Kunun tsamiya ne, na daka ba ni?a ba, ya sha kayan ?amshi, sai dai babu suga ko kaWan a ciki, ga tsamiyar nan cau har ka.
?uli-?ulin 'yar tsalan, ya sha barkono, ta zuba masa a kofi ta ba shi. Ya saka hannu ya karSa.
Tun da ya yi kurSa Waya, ya yi shiru. Nana ta ce "Za ka iya sha kuwa?" Ya jinjina kai ya ci gaba da sha, saboda Nana.
Ya haWa da 'yar tsalan nan, duk da ba son Abincin yake yi ba.
"Sayyid, idan ba zaka iya cin Abincin nan ba, ka bari na nemo maka wani"

Ya Waga kai ya kalle ta, sai dai ba baki, dan haka ya harare ta, ya ci gaba da cin abincin.
Ta yi murmushi ta ce "Ni ka ke harara ko, aishike?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? nan"

Ya gama karyawa, ta saka Wankwalinta, ta goge masa bakinsa da hannunsa. Ta ce "Bari na je kiran da Uwani take yi mini, daga nan na saka a raka ni, na Wan yi mana sayayya, dan na san dole za ta daina bamu Abinci yau da gobe sai Allah"
Bai ba ta amsa ba, ya jingina da bango, saboda yadda yake jin daWin hakan, yana lumshe ido.

"In je?" Ya yi mata shiru, kuma ya?i yi mata wata alamar, da za ta gane ya amince ko a'a.

Cikin shagwaSa ta ce "Sayyid" ya kawar da kansa gefe, ya ?i buWe ido.

"Duk da maganar nan Waukewa take yi, amma dai tun asalinka miskili ne, ina ta magana ka ?i kula ni, ni ce fa rayuwartaka guda ka ke wa haka?"

Murmushi ya yi, tare da saka hannunsa a cikinta, yana shafawa a hankali.
Ayshacool
"Wai ba za ka kalle ni ba?" Ta yi maganar tana juyo da fuskarsa. Ya ?ara rintse idanunsa, wai ba zai kalle ta ba. Nana ta din ga dariya.

Ya ja jikinsa a hankali, ya kwanta a kan cinyarta, ya zuba wa cikinta ido, tamkar zai gano abin da yake cikin.

"Idan na haihu na ga yadda za a yi, da kai da jaririn wa zai bar wa wani cinyar nan" Ta yi maganar tana shafa gashin sa.

*

Hajiya Sa'a ce take cin abinci, tana kallon Jamila, da take ta cakala kaWan-kaWan.

"Jamila ya ne? Ki saki jiki ki ci abinci mana" Jamila ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba.

"Ko dai haryanzu abin da ya faru Win ne yake damun ki? Tun wuri ki ajiye wannan abin, ki ci gaba da rayuwar ki cikin kwanciyar hankali. ?an ?aramin abu ne fa, ranar da aka ce ki bayar da jini kuma ya zaki yi? Ki na gani Safiyya ta tafi Dubai ma sarin kaya, kuma duk harka ce ta ?ungiya ta Waukakata haka. Har gara ke ma da ba ki da aure, Safiyya da aurenta, amma kalli yadda ta kama ?asa, mijin ma ita yake yi wa biyayya, ki saki jikinki dan Allah ki daina wannan damuwar.
Ki ?arasa cin abincin, Talatu ta gyara gidan, idan an zo ana son kaya, kin san gurin da suke, zan je sake duba Fatuhu ne, daga nan na je a gyara mini kaina"

"To Mummy a dawo lafiya"

"Yauwwa Daughter Allah ya sa"

Ta gama abin da take yi ta fita, bayan fitar ta, Jamila ta tashi ta nufi harabar gidan, tana kallon flowers Win da aka ?awata harabar da su. Jibga-jibgan motocin Hajiya Sa'a uku na hawa. Ga na Wanta Abba biyu. Iya harabar gidan abar burgewa ce, ta yadda duk mai rai zai yi fatan ya samu wannan wadatar. Sai dai kash, hanyar da aka bi gurin tara dukiyar, duk wanda ya ji muddin yana da imani, sai ya gudu da ?afafuwansa.

Ji ta yi kamar wani abu yana bin wuyanta, ta juya a hankali ta ga Abba ne a tsaye, yana saka abin fulawa a wuya.
Ta yi guntun murmushi ta ce "Yaya Abba"

"Na'am ?anwar Abba. Ya na ganki nan lafiya dai ko?"

"Lafiya ?alau, ba ka fita ba?"

"Yau ba zan fita ba, ba na jin daWi ne gaba Waya, dan da zazzaSi ma na kwana wallahi"

Cikin tausayawa ta ce "Kash, sannu Allah ya ba ka lafiya. Ka je Asibiti mana"

Abba ya Wan numfasa ya ce "Na sha magani already, dan haka ba sai na je ba, zo mu je mu zauna ki yi mini hira, na san zazzaSin zai sauka gaba Waya" Dariya ta Wan yi ta ce "Ai ni ban iya hira ba"

"Ba wani nan, amma ki na yi da Mummy ai, gaskiya mu je sai kin yi mini" Tana dariya ya wuce gaba ta bi bayan sa. Sanyin halin Abba ya fara tasiri a zuciyar Jamila.

*
Alhaji Fatuhu na zaune, Hajiya Suwaiba ta gama gyara jikinsa, fuskarsa Wauke da damuwa, ya kalli uwar 'ya'yan nasa ya ce "Haryanzu Fadilan ba ta haihu ba?" Ta taSe baki ta ce "Tana can ba ta haihun ba tukuna."

"Allah ya sauke ta lafiya" ta yi shiru ba ta amsa ba.

"Yakamata a sallame ni na koma gida haka, na gaji da zaman Asibitin nan gaba Waya"

A hasale ta ce "To mu koma gida mu yi yaya ne? Nan Win ba dai magani ake baka ba ana kula da kai, komai sai ka nuna kai ba a kyauta maka ba, ba a iya ba haba dan Allah"

Jiki a sanyaye ya ce "Yi ha?uri, Allah ya baki ha?uri" daga haka ya sunkuyar da kansa.
Sai kuma jikinta ya yi sanyi, ta zauna a kusa da shi, tana tunanin ta yi magana. Ta ga yana share hawaye.

Cikin damuwa ta ce "Alhaji kuka ka ke yi? Dan Allah ka yi ha?uri raina ne a Sace, amma dan Allah ka yi ha?uri"

Ya yi mata shiru, gaba Waya ta rikice ta rasa abin da za ta ce. Raudah ce ta turo ?ofa hannunta da towel ta ce "Daddy guess what?" Ta mi?a masa narkeken jaririn da Fadila ta haifa.

Hannunsa na karkarwa ya ri?e jaririn ya ce "Another Muhsin" ya yi maganar yana murmushi.

Ya din ga yi wa jaririn kiss, yana shafa shi kamar ba a taSa yi masa haihuwa ba.

****

Fafur Sayyid ya hana Nana zuwa ko nan da can, har aka yi azahar.Uwani ta sake aiko musu da dambu, ta ce a cewa Nana ba za ta zo ba, sai ta zo da kanta.

Cikin damuwa ta ce "Sayyid dan Allah ka bari na je, na ji kiran me take yi mini" fafur ya sha kunu ya tsuke fuska.
Ayshacool
Babu yadda Nana ta iya, ta zauna ta ?i fita. Ta zazzage kayansu, tana ?ara gyara musu, ta fito da kayan wankin gashinsa, da turarrukansa da duk wata sai su Habu sun sayo sun kawo. Ta Waga kai ta ga ita yake kallo, ta Wan yi murmushi ta haWe su a guri Waya da combs Win sa na taje gashi.

Sai yamma bayan sallar la'asar, ta yayyafawa tsakar gidan ruwa, ta share shi.
Ta yi shimfiWar tabarma a tsakar gidan, ta saka wa Sayyi fululluka ta kamo hannunsa zuwa waje.
Ya zauna, ta Waukko mayafin rawaninsa ta yafa masa a kansa.

Babu jimawa sai ga Uwani ta zo, tana faWin "Tun da ba za ki zo ba, ni ga ni na zo da kaina"

Nana ta ce "Ba ?in zuwa na yi ba Uwani, yanayin jikinsa ne sai a hankali, shi yasa ban fito ba"

"Koma dai mene ne gani na zo ai" Ta kalli Sayyid ta ce "Sannu ko" ya jinjina mata kawai.

"Dama kiran ki nake yi, na ji idan akwai wani abu da ku ke bu?ata?"

"Eh, ina son yin sayayya ba mu da fitila sai ta waya, da kuma 'yan kayan bu?atu"

"To da kin sanar, ai da na saka yara sun raka ki, dama zan ce miki kuma idan an kwana biyu, yakamata ki zo a Wan zagaya da ke cikin dangi, su san kina garin nan, tun da dama ba zuwa ku ke yi ba, dui ba sanin ku aka yi ba"

Nana ta jinjina kai ta ce "To in sha Allah"

"Wai ni Nana ina Mai jidda kuwa?"

"Tana can Bauchi inda take aure"

Uwani ta ce "Kuma tana zuwa?" Jiki a sanyaye Nana ta girgiza kai.

"Ai dama na san babu lallai ta zo, ko dan saboda ba?in halin Isa. Ai ya bamu mamaki. Ita ma tun da suka rabu ba ta sake zuwa garin nan ba. Kuma yakamata mu je

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login