Showing 21001 words to 24000 words out of 168002 words

Chapter 8 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

639

take yi a kansa, amma abu ya gagara, ta ji gaba Waya kanta ya toshe.

Ta yin?ura ta tashi, ta tafi banWaki domin ta yi alwala ta yi sallar isha'i.
Sai dai bayan ta yi alwala da ?yar ta baro banWakin, saboda duk taku sai ta ji tamkar zuciyarta za ta fashe.
?afafuwan ta su ka gaza Waukar ta, a dole ta zauna ta kalli gabas, ta tayar da salla. A zaunen ma jiri take yi, da haka ta yi salla.

Shi dai bai kula ta ba, bai kuma tashi daga gurin da yake a zaune ba, kamar gunkin budda.

Ta idar da sallar, ta koma jikin bango ta matse jikinta, ta rasa abin da yake yi mata daWi, ji take kamar ta kurma ihu, ga sanyin nan da take ji ?aruwa yake yi, tsigar jikinta sai tashi take yi.

"Allah ka dube ni, dan Allah ?aisar kar mu yi haka da kai, ni hauka shi hauka ta ya ya za a yi wannan zaman" ta furta hakan a hankali.
Ayshacool
Sun shafe dogon lokaci, kamar babu halitta mai motsi da ta wanzu a gurin, Nana tana ta tufka da warwara a zuciyarta, kawai ta ga ya tashi tsaye. Zuciyarta ta ?ara tsinkewa da tsoro da razani, tare da hakaito mata miyagun abubuwa, yanzu idan ya yankata a gurin nan ya gudu fa? Mussaman wannan takobin da take gani.
A hankali yake tafiya, ya tafi gefen wardrobe Win Wakin, da aka kafe abin rataye kaya. Ya cire takobin ya rataye ta. Ba tare da ya waiwayo ba, ya fara kwance rawaninsa. Kasancewar ya juya mata baya, ya sanya ta zuba masa ido ko ?iftawa ba ta yi. Ya kwance rawanin gaba Waya, ya ninke Nana ta zuba wa sarautar Allah ido, ganin kansa Wauke da gashi ba?i wuluk, ya tufke shi tamkar an yi wa kan bahauhishiya saloon.
Ya saka hannu ya zare rigar jikinsa, da sauri ta sunkuyar da kanta, tana kallon gefe, kamar mara gaskiya.

A hankali ta ?ara Wagowa, ta ganshi da dogon wando, da shirt, ya ninke rigar da rawaninsa, ya buWe wardrobe Win ya saka kayan a ciki.

Ba ta san ya aka yi ba, kawai sai gani ta yi sun haWa ido. A take ta tuno ganin da ta yi masa, har ta suma a Wakin su.

Da wata irin azama ta tashi, duk da bugun zuciyar da take ji da kuma jiri, ta ja da baya ta tsaya cikin tsoro da razani.

Ya ci gaba da kallonta, ba tare da ko ?ifta ido ba.
Kawai Nana ta fashe da kuka, ba tare da sanin dalilin da ya sanya ta kukan ba.

Gani ta yi Wakin yana juya mata, ya kawar da kansa daga kallonta, ya fice daga Wakin. Fitarsa ke da wuya ta silale a gurin ta faWi.

A hankali ta fara juyi tana tari, a cikin kunnuwanta take jin bugun zuciyarta, ta ja jikinta ta tashi da ?yar. Ta karkaWe hannunta saboda ?ura, ?aisar ta gano sanye ba?ar riga tana jan ?asa, yana shirya litattafan sa, yana goge su.

Da ?yar tarin ya Wan lafa mata ta ce "?aisar"

"Ya aka yi?" Ya amsa ba tare da ya kalle ta ba.

"Tsoro nake ji, ji nake yi kamar zan mutu. Ba ka ji yadda zuciyata take bugawa ba"

"Ina jin yadda take bugawa mana, ai mutuwar ma za ki yi idan ba ki yi wasa ba, tun da ke dai kin ?ware a taurin kai. Wannan mutumin ?ila shi zai yi ajalin ki. Ki kan ji bugun zuciya da sanyi ne, idan ina guri to me yasa ba na gurin daga ke sai shi ki ke jin bugun zuciyar?" Ya jefo mata tambayar.

Nana ta Wan yi shiru, sai kuma ta ware ido, amma ta kasa magana. Ya ce "Eh, ai na gaya miki ba ki da tabbacin abin da ki ka aura, mutum ne ko kuma jinsinmu" yana gama maganar ya yi gaba. A rikice Nana ta bi shi tana faWin "Dan Allah ka tsaya ka saurare ni, yanzu ya zan yi dan Allah?"

Ya waiwayo ya kalle ta ya ce "Au tambayata ma ki ke yi ya ya za ki yi? Shirka fa ki ke ?o?arin ko kin manta?"

Nana cikin kuka ta ce "Ba haka nake nufi ba, amma wallahi tsoro nake ji idan na ci gaba da rayuwa da shi, zan iya mutuwa"

?aisar ya ce "Ai da da na gaya miki ba ki yadda ba" ya juya zai tafi, ta ri?o rigarsa"

"Zan watsa ki ta waje, idan ki ka kuma bi na"
Za ta yi magana ya ce "Sai kuma ki yi" kawai ya Sacewa ganinta.

Kawai ta koma gefe ta tsaya tare da fashewa da kuka.

Yana zaune a gefen Wakin nasu, ya na shan hantsi, sai ga Sule ya zo da kwandon kayan abinci.

"Ango har ka tashi? Ya mari?e Win ?"

Ya nuna masa Wakin, alamar tana ciki. Gaba gaWi Sule ya nufi Wakin da kwandon Abincin cikin hanzari Buzu ya mi?e ya tsaya a ?ofar Wakin.
Sule ya ce "Au yi ha?uri, bari na zauna daga nan" ya nemi guri ya zauna a gefensa.

Nana kuma ta buWe idonta, ta ganta kwance a kan katifar, jikinta babu naWin lafayar da aka kawo ta da shi, sai riga da skirt Win ta na ciki, kanta ko Wan kwali babu. A razane ta dubi jikinta tana tambayar kanta, ko ya yi mata wani abin ne?. Ta kalli gefen katifar ta ga lafayar a ninke a ajiye. Da azama ta yin?ura ta faWa banWaki, amma ba ta ga alamar an yi mata wani abu ba.
Ta yi tsarki, ta yi alwala tana ta istigfari ta yi sallar asuba, cike da jin kunyar Ubangiji, yadda lokaci ya ja gari ya yi haske ba ta yi salla ba.

Bayan ta idar tana jiyo Sule yana ta zuba da yaren su, shi dai ba ta ji maganar sa ba. Ta yi mamakin abin da ya sanya Sule kasa yin zuciya ya ci gaba da surutu ba tare da ana kula shi ba.
Ayshacool
Babu tsammani ya shigo Wakin, ba tare da ko sallama ba. Aikuwa ta zabura ta ja da baya tana kallonsa.
Kai tsaye ya nufo ta, ya ajiye mata kwandon Abincin a gabanta. Ya nemi guri ya zauna ya zuba mata ido, da kwandon kayan abincin a tsakiyar su.

Nana ta sunkuyar da kanta, sanyi na ratsa ta.

"Zan ci abinci" ta ji muryarsa kamar daga sama, Waga kai ta yi ta kalle shi, ji ta yi kamar ta ce masa to ya ci mana, sai kuma ta tuna ashe fa wai yanzu mijinta ne. Mamaki ne ma ya kamata, dan har a lokacin tana mamakin idan ba kurma ba ne ba.

Ta janyo kwandon ta sassuke abincin, ta fara ?o?arin zuba masa, kawai ta ga ya tashi ya fita. Sai ga shi ya dawo da abin da suke hura wutar dafa shayi, har da butar shayin ma, da alama abin da suke yi a wajen tun Wazu kenan, shan shayin.

Ya buWe cikin kayansa, ya Waukko turaren wuta, ya zuba a kan sauran garwashin. Take Wakin ya karaWe da ?amshi mai daWin gaske. Ya samu guri ya zauna, ya karSi abincin, ya koma gefe ya sauke takunkumin rawaninsa ya hau ci.

Nana kuwa kasa cin abincin ta yi, ta yi tsuru sai satar kallonsa da take yi, ya gama ci ya Wauki kwanukan da ya ci, ya fita waje ya wanke ya dawo ya ajiye mata. Ya tsiyayi sauran shayinsa na butar, ya shanye abin sa.

Ya kewaye ta, ya Wauki pillow ya koma can gefe ya ajiye ya kwanta. An shafe tsawon lokaci, na zaune ba tare da sanin abin yi ba. Jin yunwa ta uzzura mata ya sanya ta Wan zuba abincin ta fara ci. Tun tana cakala har ta saki jiki, ta ci gaba da zurawa kawai suka yi ido huWu, tana ta loma. Sai kuma ta yi sak, ta ci gaba da ci ta kasa kamar wadda ta aikata rashin gaskiya, kuma ya ?i daina kallonta. ?arshe sai ha?ura ta yi da cin abincin, kallon da yake yi mata duk ya sanya ta damu.

*
Gidan su Nana tun a ranar kowa ya watse, dan baba faWa ya yi ta yi, yana cewa duk wanda ya kwana sai dai ya nemi abin da zai ci, shi ba shi da abin da zai sake bayarwa a bawa mutane.

Suwaiba ta ?arewa Wakin su kallo ta ce "Ohhh abin tsiya, ko tsinke ba ta bari ba, duk ta kwashe komai balle mu gada."

Mama ta ce "Au ke har wata tsiyar ki ke saka ran gada a gurinta? Me za ki gada banda gayyar masifa, ai gara da tarkata komai ta tafi, ma sake mu mi?e ?afa mu huta mu ma"

Jamila da ta shirya tsaf za ta fita ta ce "Aikuwa dai"

"To kafin hankali ya dawo kan ku, Ubangiji Allah ya kawo muku mazaje na gari 'yan uban uban su, wanda kowa sai ya koka a tashi kan munafukan unguwa da na family"

Suwaiba har da tsalle ta ce Amin Mamanmu maganin kukanmu.

Jamila ta yi murmushi ta ce "Ni dai sai anjiman ku"

Mama ta ce "To a sauka lafiya"

*

A tsanake take kallon yadda mai gidan nata, yake Wan yamutsa fuska bayan ya kammala cin abinci.

A hankali ta ce "Daddy"

"Na'am baby"

"Ya dai? Jikin ne ko garin? Na ganka so silent"

Ya Wan yi mi?a ya ce "Pressure ce ta Wan yi mini yawa wallahi, ina shirin tafka asara ne, kwana biyun da ban je kasuwa ba, har an yi mini Sarna wallahi. Ga kaya sun iso Nigeria na gama clearance amma coustom sun ?i sakar mini kayan"

"Subhnallah, in sha Allah ba za ka yi asarar ko naira biyar ba. Allah zai warware komai, bari mu du?ufa da addu'a in sha Allah ba wani abu"

Ya yi murmushi ya ce "Sweetheart, Allah ya amsa mana, Wan duba mini paracetamol idan ki na da shi, kaina yana ciwo, ina so na je asibiti ma a duba ni ko bp na ne ya hau"

Cikin damuwa ta ce "In sha Allah ba shi ba ne ba ya hau, dan Allah ka kwantar da hankalinka, mu na bu?ar lafiyarka just recently fa kai ne ka ke yi mini nasiha a kan yadda da ?addara"

Ya girgiza kai ya ce "A'a ba ma damuwar na saka a raina ba, kawai jikina ne babu daWi"

Ta tashi ta ce "Bari na Waukko maka" ta nufi bedroom Win ta.

*

Alhaji Zailani ne zaune a gaban malam Gambo, sai gumi yake yi kamar ya yi wa sarki ?arya.

"Na rasa gane abin da ya faru gaba Waya, ni dai na san mun yi da kai za mu yi magana da wanda ta aura Win, na ba shi kuWi ya sake ta, sai dai ban san meyafaru ba na kira shi Win a zahiri, ban kira shi ba na kasa tunawa, ni dai kawai na ganshi a mafarki ban ma san meyafaru ba kawai na farka na ji tamkar an sha?e ni, da ?yar nake numfashi"
Ayshacool
Ta tashi ta kwance kayan da Ummi, ta yi mata sayayyar su.
?an kayan shafe-shafe ne, da turaruka sai under wears, duk da masu arha ne Nana ta ji daWi sosai da sosai.
Duk da tana jin haushinta, amma ta san idan ba Ummin ba, babu wanda zai tsaya tsayin daka ya yi mata wannan abin. Ta haWa da na gurin Hajiya Amina, duk ta jere. Ta janyo drower mudubin, ta ga burshes ne da comb a ciki. Ta mayar ta rufe.

Ta janyo jakar kayanta, ta buWe wardrobe Win, ta ga Sangare Waya sha?e da kayansa, sai da abin ya bawa Nana mamaki.
?angare Waya ta jere kayanta, ta tsaya tana kallon kayan, duk da galibi wanda hajiya Amina ta ba ta ne, ba ta san lokacin da murmushi ya suSuce mata ba. Ta daWe tana burin ganin kayanta a cikin wardrobe. Dan a gida, a wata tsohuwar adakar kakar su take zuba su, ?arewa wataran talauci ya ishi Baba ya ce ta zazzage kayanta, ta ba shi. Haka ta ba shi ya sayarwa 'yan gwangwan ya sayo mata viva ya bata wai ta zuba kayan a ciki, tun da tsummokaran nata ba su da yawa. Daga baya ta koma zubawa a kwalaye, daga ?arshe dai Jamila ce ta samo mata ghana must go ta bata, take saka kayan ta a ciki. Amma yau ga kayanta a wardrobe, kuma kaya kusan set goma sha uku, sababbi da tsofaffi, ga atamfofinta uku da ba a kai ga Winkawa ba.
Ta ninke bargonta, da bedsheets da Shukura ta bayar a bata, ta saka su a saman wardrobe Win.
Drower ?asan wardrobe Win kuma, ta saka takalmanta guda biyu, da jakar gidan sarkin baka, da pad Win ta. Ta gyara kan katifar ta Wame ta da bedsheets. Ta tashi tsaye tana kallon katifar, ita ma tsawon rayuwarta a kan wani tsohon bargon Baba take kwana, shi ma dai na kakar ta ta ne, bargon nan tamkar ya koma audigarsa saboda tsufa, amma yau albarkacin aure, ga ta da ?atuwar katifa.

Wani murmushin ne ya sake suSuce mata, ta juyo kawai ta yi karo da shi a tsaye a bayanta.

Ba ta san lokacin da ta ?wala ihu ba, dan sam ba ta ji alamun mutum a bayanta ba.
Kuma kasancewar ta ?ure da jikin katifar, razanar da ta yi, sai ta faWa kan katifar.

Taku Waya ya ?ara, ya tsaya a kanta yana kallonta.

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
29

?ara rikicewa ta yi, ta kasa tantance abin da take gani daga cikin idanunsa.

Ya sauke rawaninsa, ya saka hannu a aljihunsa, ya Waukko wayarta ya ajiye mata a gefen ta. Tashi ta yi zaune tana kallon wayar, gaba Waya ta manta ma tana da wata waya, a ina ya samu wayata? Ta tambayi kanta.

Ta bi wayar da kallo, ta kasa taSa ta. Ya sake zura hannunsa a cikin aljihunsa ya ciro wata roba, ya ajiye mata, ya juya ya fita. Sai da ya fita ta Wan samu ta nutsu, ta kai hannunta ta Wauki wayar ta duba ta ga a kashe take, sai ?amshi take yi. Ta kalli robar da ya ajiye mata, dabino ne fal a cikin robar lubiya.

Gefe kuma ga kwanukan abinci, fulasan kawai ta kalla ta san daga gidan Hajiya Amina suke.

Tana cikin tunani, ta ji sallamar mace. Ta amsa tare da kallon ?ofar Wakin. Wata mata ce ta shigo, Nana ta yi mata maraba, ta shimfiWa mata sallaya ta zauna.

Bayan sun gaisa Nana ta ce "Ban gane ki ba"

"Eh ai ba ki sanni ba, a nan baya muke, aka ce ai an kawo amarya na ce bari na zo mu gaisa"

Nana ta ce "Allah sarki, dama da mutane a nan haka? Shiru nake jin unguwar duk da jiya na zo"

Matar ta ce "Eh, ai a nan baya nake, sunana na Haulat, amma kin je kun gaisa da mutanen gidan"

Nana ta girgiza kai ta ce "Ai ban san da mutane a gidan ba"

Haula ta ce "Ai ba su fiye zama bane ba, kullum cikin yawo suke, amma yau ko gobe za su dawo."

Zuwan Haulat sai ya Webe wa Nana kewa, su ka yi ta hira.

Sun daWe su na hirar, sannan ta yi wa Nana sallama, ta rako ta har bakin ?ofar Wakin ta ce "Idan na fara fita, nima zan kawo miki ziyara"

"To shikenan, ai a nan baya muke"

Nana ta ce "Kuma da gidaje a gurin? Na ga duk kangwaye ne?"

Haula ta ce "Gamu kuwa, akwai gidaje a gurin"

"Allah sarki, to na gode sosai ki gaida gida"

Yana zaune a kan benci, yana shan shayi a cikin Wan ?aramin kofin nan nasu, Nana ta jima tana mamakin kofin da suke shan shayin nan, tamkar wasan yara. A ganinta sai mutum ya sha goma bai ?oshi ba.
Tana hango shi su na fitowa da Haulat, ya rufe fuskarsa.
Ta zo za ta fita ta tsaya tana gaishe shi, amma ya yi shiru, kuma bai Waga kai ya kalle ta ba, ta fita.

Sai da Nana ta ji babu daWi, haryanzu ita ba ta ga wata alama ta hauka a tare da shi ba, kuma jiya ya yi magana ba kurma bane ba, tsagwaron wula?anci ne ya sanya sai a yi masa magana amma ya yi shiru.

Da daddare ma, zuwa ya yi ya saka ta a gaba, yana kallonta yana kallon kwanukan abincin da ba ta san waye ya kawo ba, ta san dai na gidan Hajiya Amina ne.

Haka ta zuba masa ya ja gefe ya sauke rawaninsa ya ci abinsa, sai dai da ya gama ci, yake Waukar kwanon da ya ci abinci ya fita ya wanko ya zo ya ajiye. Abin da ta lura da shi, shine mutum ne mai tsafta sosai.
Ita dai tana gefe sai dai ta saci kallonsa, sai dai ?asan zuciyarta tana mamakin yadda yau ba ta jin bugun zuciyar, sai dai sanyi da take ji.

Bayan ya ajiye kwanukan, ya tashi ya kwance rawanin sa, duk da wayarta take Wan dannawa, sai da ta saci kallon gashin kansa, kawai ta ji tana son ya ware shi, ta ga adadin tsawonsa.
Ya rage kayan jikinsa, ya Wauki radion sa, da kayan shayinsa ya fice daga Wakin.
Yana fita ta ja ajiyar zuciya, ta tashi ta shiga banWaki, ta yi wanka ta wanke bakinta, tayi alwala, ta fito ta shirya ta kwanta.

A iya saninta, wayarta take Wan duddubawa tana tunanin yadda aka yi ya samu wayarta.

"Amarya ba kya laifi, ko kin kashe mai gida?"

"Meye haka wai?"

"A ina?"

"Ni fa yanzu matar aure ce, ya zaka din ga kawo ni nan, duk lokacin da ka ga dama?"

Ya ajiye littafin hannunsa ya ce "Ina ruwana da auren ki? Auren jeka na yi ka? Auren da haryanzu ba ki da tabbas a kansa? Haryanzu ba fa ki san me ki ka aura ba, kuma kamar an ce ma mahaukaci ne ko?"

A ?ule Nana ta ce "Ko ma dai mene ne ina ruwan ka? Zan gano da kaina, koma wane ne, idan ma mutum Win ne ko akasin haka"

?aisar ya ce "Jiya fa ki ka zo nan ki na yi mini kuka, ki dai san iya abin da yakamata ki yi, da inda yakamata ki tsaya kar allura ta tono garma"

"Eh, haushi ka ke ji na yi aure, ba tare da tsammaninka ba, balle ka sake hanawa"
Ayshacool
Kawai ?aisar ya bushe da wata irin dariya, da sai da ta tsorata ya ce "Ke haryanzu ba ki san ina ki ka dosa ba, ni ba jinnil ashi? bane da zan hana ki aure, na baya ma mazan naki ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login