Showing 54001 words to 57000 words out of 168002 words

Chapter 19 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

646

je masallaci "
Ta ce "To shikenan, a yi mini addu'a"
Ya Waga mata hannu, tare da jinjina mata kai, ita kuma ta shiga cikin gidan.

Sallama ta yi, Nasiru yana tsakar gida yana goge takalminsa, yana ganin Nana ya tashi da gudu ya nufe ta.

Nana ta rungume shi tana murmushi, "Nasiru ya garin?"

"Lafiya ?alau"

"Ina mutanen gidan ne?"

"Mama ta Wan fita, Baba kuma ya je masallaci"

Nana ta ce "Samo mini tabarma na zauna a nan, ina su Jamila?"

"Jamila daga warkewarta ta tafi yawo, Suwaiba ma ba ta nan"

"Ohh ya jikinta kuwa, mu ka yi waya da Ummi, ta ce mini tun da ku ka dawo ba ta da lafiya "

Nasiru ya ce "Eh, amma ta warke, Mama ta ce wai me magani ya ce Aljani suka yi wa laifi. Aka yi sadakar ?osai, aka dafa zakara aka bin...

"Ammm ya jikin Baba kuma" Nana ta katse maganar Nasiru.

"To ga shi nan dai, yanzu zai shigo ai ki gan shi"

Nana ta Waukko wayarta ta ce "Nasiru ga wayata, ga kuWi ka yo mini turin fina-finai dan Allah" ya karSa ya mi?e tsaye tare da faWin an gama yanzu kuwa.

Nana ta tashi ta fara tattare tsakar gidan, saboda yadda aka bar shi kaca-kaca. Ta gama sharewa Baba ya yi sallama, ta Wago ta kalle shi. Da ?yar yake taka ?afarsa yana bin bango. Ya tsaya sororo ya ce "Ke me ki ke yi a gida kuma?" Duk da Nana ba ta ji dadin tambayar da ya yi ba, saboda ta san yana tunanin ko auren ya samu matsala ne, amma ta yi murmushi ta ce "Baba duba ku na zo yi" Ta yi maganar tana gyara masa tabarma a tsakar gida.

Ya ?arasa ya zauna da ?yar, Nana ta koma gefensa ita ma ta zauna ta ce "Sannu ya jikin naka?"

"Jiki ga shi nan mu na lallaSawa abu ya ?i ci, ya ?i cinyewa"

Ta kalli ?afafuwan nasa ta ce "Wacce ce take ciwon a ciki?"
Ayshacool
Ya ce "Duka, sai dai wannan ta fi ciwon" ya yi maganar yana nuna mata ?afarsa ta hagu.

"To Baba ka je Asibiti?"

"Da wane kuWin zan je Asibitin? Na gargajiya zan koma, ina fatan dai ba wata matsalar ba ce ta dawo da ke gidan nan?"

Nana ta yi murmushi mai ciwo tana buWe jakarta, ta fito da leda tana faWin "Baba idan matsala ta dawo da ni, ba zaka karSe ni ba ko? Ai ka yi mini addu'a ka ce Allah ya bani zaman lafiya, in sha Allah matsala ba za ta kawo ni ba sai alkhairi" ta yi maganar tana Sare dafaffen ?wan da ta fito da shi daga leda.

Ta gama Sare ?wan, ta mi?a wa Baba, ya saka hannu ya amshe, yawun bakinsa na tsinkewa.

"Baba na san ni mai laifi ce a gurinka, na Sata maka rai a kan abubuwa da dama, mussaman na bijirewa auren waWanda ka so na aura, amma ina son mu saka a ranmu cewa, dukkanin su Allah bai ?addara akwai mijina a cikin su ba. Ni yanzu babban fatana ka daina yi mini kallon mutuniyar banza, na san dole na fuskanci tuhuma na abin da ya kai ni Wakin su magadi, amma ba abin da ka ke tunani ba ne Baba, da zan lalace da ban kawo wannan lokacin ban lalace tun a baya ba." Tuni hawaye ya wanke mata fuska, zuciyarta na wani irin tafasa da raWaWi. Baba bai ce mata komai ba, sai karSe ?wan da yake yi yana lamushewa.
Ta goge hawayen ta, sai da ta Sare masa dafaffen ?wan nan guda biyar, ta Webo ruwan randa ta kawo masa ya karSa yana sha.

Ta Waura alwala ta yi sallar azahar, bayan ta idar, Nasiru ya shigo gidan yana faWin "Nana ga wayar ki, an ciko miki ita da fina-finai fal"

Ta yi murmushi ta ce "Na gode yaron kirki"

Mama ta yi sallama ita da Suwaiba, sai da suka Wan yi turus ganin Nana a gidan babu tsammani.

"Lafiya dai na ganki a gida? Ba dai auren ne ya samu matsala ba"

Nana ta waiwaya ta kalle ta, ta yi murmushi ta ce "A'a ganin ku na zo yi, na gaishe ku, aurena bai samu matsala ba" Mama ta kwaSe baki tana rataye mayafinta a kan igiya.

Nana har kallon Mama take yi, tana mamakin wai ita ba ta san ?arara a fili take nuna ?iyayyar da take yi mata ba.

Nana ta ce "Suwaiba ya ku ka zo gida?"

"Lafiya ?alau wallahi, mu na dawowa Jamila ta kwanta rashin lafiya"

"Haka Ummi take gaya mini, shi yasa yau na yin?uro na fito. Nasiru duba idan ya idar da salla, ya shigo ya duba Baban mu tafi, ban yi girki ba"

Nasiru ya ce to.

Suwaiba ta ce "Nana wai waye yake ba ku Abinci? Gidan da ku ke aikin ne suke ba ku?"

Nana ta yi murmushi ta ce "A'a wanda ya ajiye ni ne yake kawowa, ba kuna nan ya kawo muku fura ba"

Nasiru ya ce "Yana waje, na yi masa magana bai kula ni ba"

Nana ta yin?ura ta ce "Bari na yi masa magana"

Yana zaune a wani dakali da yake kallon gidan su Nana.

Yana ganin ta fito ya mi?e tsaye yana kallon Nana.

Ta ?arasa ta ce "Sayyid, zo mu je ku gaisa da Baban"

"Wai in shiga?"

Ta ce "Eh, ku gaisa da Babana ka duba shi"

Nana ta yi gaba ya bi bayanta,

Gaba Waya suka zubo masa ido, sai dai kansa a sunkuye, har suka isa gaban Baba.

"Sannu" ya furta a hankali yana tunanin ko haka ya kamata ya ce?

"Yauwwa sannu, ya iyalin?"

Ya ce "Alhamdilillah"

Baba ya ce "To madalla"

Nana ta ce "Sayyid, ga ?anwata wadda su ka zo ranar, ga mamana, ga kuma Nasiru da suka zo a tare"

Bai kalli inda Mama take ba, ya ce "Sannu"

Yanzun ma kwaSe baki ta yi ta ce "Ji wata irin gaisuwa, haka ake gaida sirikai?"

Nana ta ce "Ki yi ha?uri, ba hausa sosai ne"

Buzu dai bai tanka musu ba, ya mi?a hannu ya Wora a kan ?afar Baba, ya ce "Allah ya sauwwa?e"

"Amin na gode" ya Wan jima yana kallon ?afat, sannan ya Wauke hannunsa, ya saka a aljihunsa, ya ciro kuWi ya ajiye wa Baba a gefen ?afarsa ya tashi tsaye.

Nana ta bi kuWin da kallo, ba tare da ta san ko adadin nawa ba ne ba.

Baba ya ce "Duk wannan haka, to na gode sosai Allah ya yi albarka"

Nana ta ce "Baba bari mu tafi gida, Allah ya baka lafiya ya ?ara afuwa, dan Allah a gaida Jamila idan ta dawo"

Sayyid tu ni ya yi waje, domin shiga gidan su Nana ji ya yi tamkar ya yi tsirara, gaba Waya idanun mutanen gidan da bai saba da su ba ya ji ya takura masa.

Suwaiba ta ce "Ke Nana wai mijin nan naki kamar dodo, baya sauke wannan takunkumin na fuskar shi, ko ba shi da ha?ora ne?"
Ayshacool
Nana ta yi dariya ta ce "Biyo ni waje na saka ya sauke miki rawanin ki gan shi. Baba Allah ya sauwwa?e idan Jamila ta dawo a yi mata sannu" Nana ta ja takalmanta ta yi waje.

Tana fita waje, ta yi karo da Gaddafi. Turus Nana ta tsaya cikin tsoro, sai ma ta rasa me za ta ce masa.

"Nana me ki ke yi a gida?"

"Zuwa na yi duba Baba, ina wuni?"

"Lafiya ?alau, ya ki ke ya gidan?"

"Lafiya ?alau, ashe ka dawo"

"Eh na dawo shekaranjiya" Nana ta yi tsuru-tsuru, tana hango Sayyid da ya tsaya yana kallon ta, ya tsuke fuska tamkar ya fashe.

"Amm ai tare ma muke da shi" ta faWa cikin kame-kame.

Gaddafi ya waiwaya, ya kalli Buzu ya mayar da idonsa kan Nana ya ce "Amma babu wata matsala dai ko?" Nana ta jinjina masa kai.

Gaddafi ya saka hannu a aljihunsa ya Waukko kuWi ya mi?a mata ya ce "Ga wannan, kya sai wani abun"

Ta saka hannu biyu ta karSa, tana mamakin yadda duk Gaddafi ya canza.

"Nana duk yadda za a yi, ki ri?e auren ki, ki ?addara wannan shi ne zaSi mafi alkhairi da Allah ya yi miki, kin san zaman gidan nan namu ba daWi ne da shi ba"

Nana ta jinjina kai ta ce "Na gode sosai da sosai Yaya"

Ta nufi inda Sayyid yake, idanunsa kawai suka tabattar mata da a hasale yake.

Har suka je gida bai sake tanka ta ba.

Su na zuwa a gurguje Nana ta yi sallar la'asar, ta Wora girki, dan ba su ci komai ba.

Shi kuwa tuni ya haWa kayan shayinsa, yana ta tafasawa yana sha.

Ta Waga labule ta ce "Sayyid, na gama girki, ka zo ka ci" ya Wago ya kalle ta ya mayar da hankali ya ci gaba da shan shayinsa.

Sai da ya gama jan ajin, sannan ya shigo Wakin, ya Wauki nasa abincin ya fara ci.

*

Mutumin yana zaune a kan kujera, a wani katafaren falo, ya ?are wa Jamila kallo ya ce "Wannan ce yarinyar?"

Hajiya Sa'a ta ce "Ita ce ranka ya daWe"

"Kuma kin tabattar za ta ri?e amana? Ba za ta tona asirin ?ungiya ba?"

"?warai kuwa, na yi mata duk abin da ya kamata"

Ya yi dariya ya ce "Babu laifi, wannan Shekarar da ita za mu yi taronmu na shekara"

Ita dai Jamila ba ta iya cewa komai ba, sai tsananin mamaki, ganin daular da ba ta taSa tunanin akwaita ba.

Bayan Hajiya Sa'a sun gama magana da mutumin, ta Wauki Jamila su ka fita.

"Hajiya yanzu dama haka garin Abuja yake? Lallai na zaune bai ga gari ba, kalli gidaje"

Hajiya Sa'a ta yi dariya ta ce "Jamila kenan, a garin nan gidajane sun fi huWu, akwai arziki Jamila, muddin za ki yi biyayya ki ri?e sirri, to za ki samu arzikin da sai ya kankare ba?in talaucin da yake bibiyar zuriyar ku. Dan ma mun kasa samun jinin yayar ki ne, da tuni ta fashe mana tana da taurarin arziki amma ba ta san yadda za ta yi amfani da su ba ne ba"

Cikin shau?i da zumuWi Nana ta ce "Kai in sha Allah, zan ri?e amana da sirri babu wanda zai ji komai"

"Yauwwa yarinyar kirki, wannan yana Waya daga cikin shugabannin ?ungiyarmu, tun da ya amince da ke, tare da ke za mu je taron shekara, ina saka ran a karSe ki a ?ungiya"

*

Har wajen ?arfe goma na dare, bai shigo Wakin ba, Nana ta kashe fitila, ta Waga labule, ta hange shi a zaune a kan benci yana ta kore sauro, yana shan shayi.

Kawai ta girgiza kai ta nemi guri ta zauna, ta yi addu'oin kwanciya bacci, ta kwanta.

Ta kai a ?alla mintuna arba'in, tana tunanin yadda rayuwa za ta ci gaba da juyawa a haka. Zama da mutumin da ba ta san ma waye shi ba.

Tana kallon ?ofa, ta ga ya shigo, ya ajiye kayan shayinsa ya tafi banWaki. Ya jima a ciki sannan ya fito daga ciki, ya rataye kayan da ya cire, ya nufo kan katifar.

A ranta take jinjina ?arfin hali na maza, da a ?asa yake zamansa, ko ya kwana a waje a kan benci, amma yanzu kansa tsaye yake Warewa katifa.

Ba ta gama tunanin ba, ta ji shi a jikinta.

"Me yasa ki ke kallona?"

"Ya aka yi ka san ina kallon ka a duhu?"

"Na sani, tun da na shigo ki ke kallona"

"Shi ne tun da mu ka dawo, ka ?i kula ni"

Ya Wan yi shiru kamar ba zai yi magana ba sannan ya ce "Ba na son na ga wani yana yi miki magana, zuciyata na yi mini ciwo. Ba na son kowa ya kalle ki, ba na son kowa ya ji muryar ki, ba na son wani ya raSi inda ki ke, sai nikaWai ban san dalili ba amma ina jin kamar zuciyata za ta tsaya ne, ba na so"
Ayshacool
"Amma wanda ka ganmu tare, Yayana ne fa, babanmu Waya da shi" Ya yi shiru bai yi magana ba.

Ita ma ta Wan yi shiru sannan ta ce "Sayyid a ina ka samu kuWi ne? Na ga ka bawa Haidar, ka bawa Baba, kuma ka na sayo mana abubuwa"

"Allah ne ya bani"

"Eh na sani, amma waye yake baka?"

"Habu" ya amsa kai tsaye.

"Shi ba shi da nasa bu?atun zai din ga kashe mana kuWi har haka?"

Ya yi shiru bai amsa mata ba.

A hankali Nana ta ce "Sayyid"

"Husnahh"

"Dan Allah ya ake yi ka ke yin wasu abubuwan, ka san na ce maka, ba ni da cikakkiyar lafiya wasu lokutan gaba Waya a rikice nake ba na tantance ainihin zahiri da mafarki, amma sai na ga kana abubuwan da mutane normal ba sa iya yi"

"Kamar me?"

Ta ce "Ammm ka na shigowa cikin mafarkina"

Kawai ta ji ya yi dariya "Dama wani na shiga cikin mafarkin wani ne? Ba mafarkinki nake shiga ba, ruhina ne yake rayuwa a cikin naki, kuma naki yake rayuwa a nawa. Na fuskanci hakan a ranar da na fara ganin ki, zuwa ranar da aka Waura mana aure"

"Ban gane ba, ka yi mini bayani sosai"

Ya yi ajiyar zuciya ya ce "?irjina ya fara nauyi"

"Saboda me?"

Ya yi mata shiru.

"Amma Sayyid.... "Shhhh zan yi bacci"

Ta ce "Tambaya Waya zan yi maka dan Allah"

"A'a"

"Allah fa na ce"

"Na ce A'a"

Ta Wan ja numfashi ta ce "To amm... Tsit ta yi dalilin bakinsa da ta ji a nata.

Ya ri?e hannunta a nasa yana matsa nata a hankali.

"Dan Allah ka bari yau mu samu isasshen bacci, ni dan Allah ka ?yale ni"

Ya ce "Idan ma kin yi baccin, zan biyo ki har cikin baccin naki. Na gaya miki ruhinki a cikin nawa yake rayuwa, ko fushi ki ke yi a cikin jikina nake ji".

Haka ya yi ta tsaro maganganun, da suka ci gaba da dagulawa Nana lissafi, da birkita mata ?wa?walwa, wanda ba ta gama warwarar su ba, har ya nufi inda yake son zuwa.

*

Tun bayar tafiyar Nana, da Shukura ta ga mahaifinta ta ji gabanta ya faWi, ta kalle shi cike da tsoro da?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? razani.

Cikin kulawa ya ce "Sannu Auta, haka ki ka koma? Ya jikin naki?"

A tsorace ta ce "Daddy dama yau zaka dawo, Mummy ba ta gaya mini ba"

Cikin damuwa ya ce "Ina can hankalina ya ?i kwanciya, na ce bari na zo na ganki, na kira Sharif ya ce mini jikinki da saura, shi yasa na ce gara na zo na gan ki"

Ta dai yi shiru, gabanta na ci gaba da faWuwa, ya gama yi mata sannu ya tashi suka fita tare da doctor Sharif.

"Sharif "

"Na'am ranka ya daWe"

"Muddin yaron nan zai rayu, ka yi duk mai yiwuwa a cire shi kawai, a matsa nake"

"Zan yi iya ?o?arina, amma ka san wannan sabga ce mai haWarin gaske, sai an yi taka tsantsan yadda ba za a bar duk wani trace da za a gane wani abu ba, zan yi setting date da komai da yadda abin zai kasance"

"Better" Alhaji Zailani ya furta yana yin gaba.

Gidansu Nana har ?arfe goma na dare Jamila ba ta dawo ba, Baba yana tsakar gida yana yi wa Mama bala'i.

"Yanzu Rabi sakarcin naki har ya kai Jamila ta kai bayan goma a waje? Gidan uwar wa ta tafi haka?"

"Wai dan Allah Jamila za ta gudu ne? Na ga dai ba yarinya ce ?arama ba, na ce maka za ta dawo"

"Za ta dawi gidan uban ta je? Goma na dare ta riga ta wuce, me take yi a waje a wannan lokacin?"

"Dan Allah ni kar ka Waga mini hankali, na ga dai yarinyar nan ba sauke hakkin da Allah ya Wora maka ka ke yi ba, abinci ma ba bamu ka ke yi ba, sai ma dai ta samo ka ci"

"Da ba na sana'a sai na zuba ido su lalace? Sana'ar uwar me take fita?"

"Ni fa 'ya ta ba lalacewa ta yi ba, na ga dai nan Nana take nata yawo, ba ka yi magana ba"

"Ai Nana na san me take fita yi, Jamila fa, na san dai tana yawon ma?ota, bayan wannan uwar me take yi?" Sosai su ka ci gaba da jayayya tsakanin Mama da Baba, sai sha Waya da rabi na dare, sai ga Jamila ta yi sallama, hannunta ni?i-ni?i da ledoji.

Duk da ledojin hannunta, sun Wauki hankalin Baba, amma ya dake ya fara tuhumar ta daga ina take.
Mama ta kankane, ta hana Jamila magana, ta din ga karewa.

?arshe sai ha?ura ya yi, ya rabu da su.
Ayshacool
Ita kanta Suwaiba jiki a sanyaye take kallon kayan da Jamila ta zo da su, tana fargabar Allah ya sa ba kauce hanya 'yar uwarta ta fara yi ba. Sai dai Mama ko a jikinta, musamman da Jamila ta ce mata, Hajiya Sa'a ce ta saya mata, wai gidan 'yar uwatta ta raka ta.

Wajen Sha biyu na dare, Jamila na ta bawa Suwaiba, labarin abin duniyar da ta gani.
Suwaiba ta yi tsuru da ido tana kallon Jamila, daga bisani ta ce "Ni dai Jamila na fara jin tsoron matar nan, anya haka kurum take yi miki wannan Wawainiyar. Jamila kar ki kai kan ki ga halaka, idan rayuwar ki ta lalace ba ki da wata makoma wallahi"

Jamila ba ta yi magana ba, Gaddafi ya faWo Wakin ya kalli Suwaiba ya ce "Bar Wakin nan" Jamila ta mi?e ita ma a tsorace tana kallon sa"

"Fita na ce" ya yi wa Suwaiba tsawa.

Jamila na ?o?arin fita, ya danna ?ofar Wakin ya saka sakata, ya fito da wani irin dan?o na injin markaWe, ya kalle ta ya ce "Gidan uban wa ki ka je, ki kai yanzu ba ki dawo ba?"

Jamila ta rikice jikinta yana tsuma, amma ta kasa magana.

"Ba magana nake yi miki ba?"

"Babu inda na je?"

"?arya ki ke yi, uban waye ya sauke ki a mota?"

"Hajiya Sa'a ce"

"Babar ki ce ita? Meye tsakanin ki da ita?" Jin ta tsaya inda inda, ya sanya ya fara zuba mata dan?on nan a jikinta.

Cikin kururuwa Mama take dukan kofar Wakin, tana neman agajin mutane, kar Gaddafi ya kashe mata 'ya.

Ya zuba wa Jamila dan?on nan, ya fi sau sha biyar, sai da ya zamana daga ita sai underwear.

Sai da aka taru aka yi ta yi masa magiya, sannan ya buWe ?ofar Wakin ya yo ball da ita waje.

Mama hankali a tashe ta nufi Jamila tana salati, saboda wahala ko kukan ba ta iya yi, sai wani yawu da yake fita daga bakinta.

Baba ya ce 'Haba Gaddafi, ba kowane lokaci duka da zuciya yake aiki ba, yanzu idan ka illata ta fa, mace ce fa"

Gaddafi bai saurari Baba ya ce "Wallahi ta sake sai na karairayata, ba za ta Sata mana suna a banza ba"

Cikin ?araji Mama ke faWin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login