Showing 90001 words to 93000 words out of 168002 words

Chapter 31 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

655

Ta ?ara saurin da take yi, amma ya cimma ta. "Nana dan Allah ki saurare ni".

Rikicewa ta yi, gani take a kowane lokaci za ta iya ganin Sayyid, ba ta san da wani yaren za ta yi masa bayani ba ya fahimta.

"Nana ki tsaya ki ji mana"

"Wallahi zan yi maka ihun kwarto, wace irin jaraba ce wannan ina ruwan ka da ni ne?" Ganin tana Waga murya, kuma Akuyarsa ta yi kuka a unguwar, ya sanya sum-sum ya koma da baya.

Tana zumbuWa sauri, ta je gida, ta san yana can yana jiran ta. Kawai ta ci karo da shi a wani lungu, yana zaune a kan wata sokawe, ya jingina da jikin bango, shikaWai ?wal a layin. Sai da ta razana, ta waiwaya bayan ta, cike da tsoron ko Saleh ya biyo ta.

"Sayyid me ka ke yi a nan kuma, ba ka shiga shiga gida ba?"

"Ba zan iya shiga nikaWai ba" Ta mi?a masa hannu ta ce "Taso mu tafi" ya mi?a mata hannunsa. Sai dai tun da ya saka hannunsa a nata, sai da ya kalli fuskar ta.

Da suka je gidan, dan?am da mata, ana ta hayaniya. Ya rufe fuskarsa Nana ta yi sallama. Gaba Waya suka yi tsit, suka zubo wa su Nana ido, musamman ganin hannunta ri?e da na Sayyid.

Kawai ta ja hannunsa, suka nufi Wakin su.

"Nana kun dawo" Sajida ta yi maganar, tana kokowa da zaninta tana fitowa daga Wakinta, saboda kar su wuce ba ta gan su ba.

"Eh sannun ku" daga haka ya tura ?ofar ya fara shigewa. Suna shiga Wakin matan suka saka shewa, Waya ta ce "In dai Namiji ne, yarinya za ta gama wannan iyayin ne"

Nana su na shiga Waki Sayyid ya tsare ta da ido ya ce "Nana ba ki da gaskiya"

Gabanta ya faWi cikin tsoro ta ce "Me na yi?"

"Gumi ki ke yi a iya goshin ki, da karan hancin ki. Kuma tafin hannunki ya ya sanyi, zuciyar ki na bugawa da ?arfi kuma da sauri. Kin yi wani abu da ki ke Soye mini ko?" HaWe rai ta yi ta fara ?o?arin ?wace hannunta daga nasa.

Sai kuma ya sassauta muryarsa ya ce "Ki daina fushi, ba zan iya barin, duk wani abu na ?i ya tunkaro rayuwata da ke ba, ki daina fushi"

"To sai ka din ga zargina da rashin gaskiya" ta faWa a hasale.

Ya girgiza kai ya ce "Ba zargin ki nake yi ba. Na tabattar da wani abu ya faru ne, da ba za ki so na sani ba, idan na sani zamu samu saSani. Kin manta mu ba kamar sauran mutane ba ne. Kuma ina iya jin abin da yake ranki, kin manta ne?" Ya yi maganar yana murmushi da shafo fuskarta. Dole ta saki murmushi.

Nana dai ta din ga yi wa Allah godiya, da ba ganta da Saleh ba.

Nana tana yi wa Allah godiya, ganin yadda jikinsa ya yi kyau. Duk da yana haki bai daina ba, amma yanzu yana cin abinci. Sayyid na matu?ar son zuwa masallaci salla, amma dole yake ha?ura. Saboda da gayya matan gidan suke wata shigar, duk da ba tsayawa kallon su yake yi ba. Ga shi ba ya son kallo, amma yana fitowa sai su yi shiru su zura masa ido.
Ita kanta Nana lamarin gidan ya ishe ta, ba ta ?aunar zaman gidan nan ko kaWan.
Maman Nana ta aiko mata da barkonon nan, har da awon kayan Abinci, tamkar ta san a halin da take ciki.
Ummi da kanta, ta je ta Wauki barkonon, domin kuwa Nana daina zuwa gidan Ummi ta gaba Waya saboda Saleh.
Ayshacool
Abu kamar wasa har zuwa wannan lokacin, Sayyid ya kasa gane kansa, abin ya fara damunsa sosai da sosai. Ga shi ya kasa cewa Nana komai a kan hakan. Ita ma kuma ba ta ce masa ba, sabgoginta kawai take yi.

Tun Yamma Nana, ke ?o?arin shirya duk abin da za su bu?ata, saboda washegari za su tafi Asibiti, kuma sammako take so su yi, saboda su ga likita da wuri.
Sai dai duk dauriya kawai take yi, wani irin zazzafan zazzaSi ne a jikinta, ta kasa cin abinci. Babu abin da take son ci, sama ds kazar da Habu ya kawo farkon auren su. Ga shi ba ta son yin duk wani abu da zai Waga wa Sayyid Hankali. Ta fuskanci ko saSani suka samu, ?aramar magana sai ta sanya ya fara haki, ya fara nema ya faWi.
Tana ?ofar Wakinta, tana soya miya, su Barira su na hira, tana yi wa wata ma?wabciyar su kitso. Suke zancen wata mata a bayan layin, wai sai mijinta ya neme ta ya rasa, sai a yi kwanaki ba a ganta ba, sai bayan wani lokaci a tsinto ta a wani gurin, ko a ganta a Waki.
Barira ta kada baki ta ce "Amma ta mayar da mijin nan tasono, ?arya take yi gantalinta kawai take tafiya. Meye matan auren ba sa yi yanzu?"

Sajida ta ce "A'a Barira, ki daina cewa ?arya ne"

"Ke wallahi, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, a gidan uban wa Aljani zai Wauke mutum ya kai shi wani gurin? Ke ni fa da ake cewa ana ganin aljanu, ko su tsorata mutum ban taSa yadda ba, iskanci ne kawai da ?aryar banza ce, ba wani aljan duk 'yan iska ne kawai.

Nana ta ji wani abu mai zafi ya soki zuciyarta, duk da ba da ita suke ba, kawai ta ?ura wa Barira ido, ko ?iftawa ba ta yi.
Tun Barira ba ta ankara ba, har ta lura, take ta ji tamkar an kwarara mata ruwan sanyi a jikinta, sai kuma ta Wan tsorata ta ce "Nana lafiya kuwa?"

Ayshercool
08081012143

Ayshacool
"Ni fa ba na son kurman ba?i, a masu shigowa ne mayun, ko kuma zaunannun gidan"

"Na ce ki zuba ido ki ga ikon Allah"

Bai fi mintuna biyar ba, wani irin haya?i, mai azabar yaji, ya turnu?e gidan.
Nana da take lafiya ?alau ma, ta fara tari.
Shi m tarin yake yi, numfashinsa kamar zai Wauke, ta Waukko mafici ta din ga yi masa fifita. Ta gaji ta tashi, da nufin ta je ta ga me ake ?onawa yake wannan uban haya?in haka. Amma ya ri?e hannunta ya hana ta. Haka suka wuni a galabaice. Sajida ma sai bala'i take yi, tana cewa Barira za ta kashe ta da haya?i.

"Wai Sajida ko ke ce mayyar nan ne?"

"Ke kama bakin ki, wallahi ki ka ce mini mayya, sai mun yi shari'a da ke"

Barira ta ce "Sai ki saurara mini, tun da dai ba ke ba ce" Haka suka wuni, Barira tana gana musu azaba, da wannan azababben abin da take zubawa a cikin murhu.
Washegari ma, azabar haya?in nan ce ta tashi su Nana, numfashin Sayyid tamkar zai Wauke saboda azaba.
Nana dai ta ci gaba da daurewa, amma yamma na yi, Barira ta sake cika kurfoti da gawayi, ta tayar da wuta ta afka haya?in nan.

A fusace Nana ta fita, ta tarar da ita tana ta girgiza kurfotin, tana zuba wani abu a ciki.

Nana ta ce "Barira, dan zatin Allah ki daina zuba wannan abin. Ina da mara lafiya a Waki. Yana da matsalar numfashi, jiya kwana muka yi babu bacci. Kuma da sassafe kin banka wani, kuma yanzu ma ga shi kina sake kunnawa"

Ta kalli Nana ta ce "Ai duk wanda ya hana uwar shi bacci, wallahi shi ma ba zai yi ba"

Nana ta ce "Kamar yaya kenan?"

"Kamar yadda ki ka ji"

"Ni dai koma mene ne, ki yi ha?uri idan ba ki yadda ba, zo mu je Wakin ki ga halin da yake ciki"

"Babu ruwana da halin da yake ciki, kurwata ce ta fi ?arfin duk wani maye wallahi"

Nana ta ce "Barira mu ne mayun da ki ke faWa dama? To Barira ko za mu ci mutum ma ci taki, jiki duk dauWa?"

"Ko ma duk uban mene ne, tun da aka kama ni aka lasa, an ji za?in kurwa ta, wallahi sai mutum ya ci ubansa, miyagun banza kawai"

"Mu ne mayun Barira?"

"Eh ku ne, ko na ce ke"

Nana ta ?arasa daf da Barira ta dam?i tsintsiyar hannun Barira ta ce "Ki ka ce ni mayya ce?" Barira ta yin?ura za ta fizge hannunta, ta yi bala'i. Kawai ta ji jikinta ya yi wani irin nauyi, kuma jikin ya yi mata wani irin sanyi, ta kasa motsa komai. Kawai ta silale ta faWi ?asa.

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
Tun da Jamila ta koma gida, jikinta a sanyaye yake, gani take yi, duk wanda ya ganta ya san abin da ya faru da ita. Mama kuwa baki ya ?i rufuwa, saboda Jamila ta zo da abin Duniya. Kuma kamar yadda ta gaya mata, sarin kaya ta raka Hajiya, babu wani bincike ta yarda da hakan ta amince.

Ta zo ba ta iya bacci sam, da ta kwanta bacc6, sai ta ga tamkar za ta buWe ido, ta sake ganinta, a wannan gurin da suka je da Hajiya Sa'a.

"Jamila" Suwaiba ta kira sunanta, ta waiwaya ta kalle ta.
"Wai ya na ga ki na abu kamar mara gaskiya ne?"

Gaban Jamila ya faWi ta ce "Me na yi na rashin gaskiyar, me ki ka gani?"

"To ai gani na yi kin kasa sukuni, ki na ta wani mutsu-mutsu gaki nan dai"

"Dan Allah Suwaiba ki ji da abin da yake damun ki, ni babu abin da ya same ni, lafiya ?alau nake "

Suwaiba ta ce "To ai shikenan"

****

Nana duk sammakon da suka yi, su ne na goma sha Waya, a gurin ganin likita.

Wajen sha Waya na safe aka zo kan su, Nana suka shiga, sai dai wannan karon wani likitan daban suka samu. Suka gaisa Nana ta yi wa likitan bayanin komai. Tare da ba shi takardun gwaje-gwajen da aka yi masa, da kuma katin da aka rubuta masa magunguna.

Ya karSa ya duba a tsanake, ya duba Bp Win Sayyid, ya duba ?irjinsa da stethoscope.

Nana ta ce "Doctor yaya jikin nasa? Me ka gani?"

Bai kalli Nana ba ya ce "Me yasa ba ku dawo follow up ba"

Ta ce "Ai ba a bamu lokacin dawowa ba. Dama ni ce naga yakamata mu dawo Win. mu na ta ?o?arin kuWin allurar su haWu ne, ko ba su haWu ba, zamu yi ?o?ari ko a anan Asibitin gwamnatin ne, sai mu yi booking a fara yi masa"

Likitan ya ce "Ki na ji na 'ya ta?"

Ta ce "Eh"

"Ai mijinki ne ko?"

Sayyid ya jinjina kai. "To a duniya babu wani abu da Allah ba zai iya ba, babu shi. Batun allura ki bar wannan a hannun Allah. Kuma dan babu kuWin allaura ba za a daina ganinsa ba. Zamu ci gaba da gwada shi, mu na ba shi magungunan da suka dace. Idan Allah ya yassare kwa zo a yi daga baya. Kuma jikinsa Alhamdillah da sau?i sosai da sosai. Jinin dai haryanzu bai sauka yadda ake so ba. Amma zai sauka da yardar Allah. Kawai ki din ga kiyaye damuwarsa da Sacin ransa. Idan kuma akwai wani abu da yake damunsa, ki zauna da shi ku tattauna ki ga ta ina za ku shawo kan matsalar?. Amma babu wani abu in sha Allah" Duk da ba lafiya likitan ya ba su ba, amma kalamansa akwai dattaku da ?warewa a kan aiki a cikin sa. Dan haka sosai Nana ta samu relief.

Ya rubuta musu lambarsa ya ce "Duk lokacin da za ku zo, ku kira ni, na baku ranar da nake aiki, ya zo ya din ga ganina." Nana ta din ga yi masa godiya da addu'a shi da iyayensa.

Sayyid ya ja wata takarda, ya yi rubutu ya mi?a wa likitan. Likitan ya karSa ya duba. Ya yi murmushi ya ce "Madam, ashe kema babu lafiya ya ce na duba masa ke"

Nana ta yi murmushi ta ce "Rashin lafiyata, ai ba komai ba ce a kan tasa, ni na fi damuwa da shi Win dai"

"A'a tun da ya nemi alfarma, ai dole a yi masa"

Ya duba Nana, ya yi wa Sayyid bayanin laulayi ne kawai yake damunta, ya rubuta mata abin da zai rubuta mata na magani. Ya kuma ba ta gwaje-gwaje. Sayyid ya ?i tafiya, sai da suka yi gwaje-gwajen.
Suka koma, ya tabattar musu da babu wata matsala, satin cikinta uku da kwanaki, ya rubuta mata magungunan da za ta yi amfani da su.

Suna tafe a adaidaita sahu, Sayyid ya kasa ri?e murmushinsa, ya kai bakin sa kunnen Nana ya ce "Saura kwana nawa ki haihu?"
Ta kwashe da dariya, ta ce "Ina na sani, ko cika wata Waya bai yi ba ma, mu dai ci gaba da addu'a Allah ya bar mana, ya bamu Wa na gari"

Ya amsa da "Amin."

A bakin titi, Nana ta yi sayayyar salak, saboda shi take sha'awar ci. Suka shiga layin gidan na su.
Su na zuwa gidan, Nana da sauri ta shiga banWaki, saboda fitsarin da ya cika mata mara. Sayyid tsayawa ya yi, yai shiru yana ?are wa Wakin kallo.

Nana ta fito bai ce mata komai ba, ta Wauki cylinder gas, ta ce "Sayyid gas ya kusa ?arewa, idan zaka iya fita in anjima sai mu je titi tare mu Wuro"

Ya ce "To"

"Bari na sake Wumama miyar"

Ta fito tsakar gidan kenan, Sajida ta ce "Nana, Allah ya taimake ki, da tuni da ke za a tafi bayar da shaida"

Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Shaidar me?"
Ayshacool
"Jiya hirar da ku ka yi, har ki ke yi wa Barira faWa, a kan matar nan. Daga jiyan nan zuwa yau magana har ta kai kunnen matar. Ta din ga kuka mijin ya ce ba zai yarda ba da 'yan uwanta. Da yyayyenta ne za su zo su zane Barira. Mijin matar ya hana aka kai ta police station. Tun bayan fitar ku tana can, duk sai da muka je bayar da shaida. Wata?ila dai kafin magariba a sako ta, ta dawo gida."

Nana ta numfasa ta ce "Gara da Allah ya sa ba na nan, dan babu inda zan je, shi yasa a rayuwa yake da muhimmanci mutum ya iya bakinsa. Wannan tara matan da ku ke yi, ku na surutai marasa amfani duk ba hanya ce mai Sullewa ba"

Sajida ta ce "Wallahi haka ne, shi yasa ki ke burge mu ma"

"Allah ya kyauta"

Har Nana ta yi haWin salak Win ta, ta fara ci, ya lura ba ta fahimci abin da yake faruwa ba, shi ma kuma bai gaya mata ba, ya ci abincin. Ta gama ci ta kalle shi ta ce "Sayyid, ka yi mini addu'a, Allah ya sanya kar na yi aman salad Win nan, na rufe sauran anjima zan sake ci"

"Kin cika yaji, sai kin yi ciwon ciki ko?"

Ta Wan waro ido ta ce "Dama ka gani?"

"Eh ina kallon ki"

Ta Wan yi murmushi ta ce "Idan babu yajin, ba zai yi daWi sosai ba. Amma yanzu ya ka ke ji a jikin ka?"

"Ba sau?i"
"Subhanallah, ba sau?i kuma?"

Ya ce "Eh, kin je ki na hira da likita a gabana"

"Amma ko ba komai, ya kwantar mini da hankali, bai ce mini zaka mutu ba, kalamansa sun bani ?warin gwiwar da yakamata na samu" ta yi maganar ?walla na cika mata idanu.

Ya girgiza mata kai ya ce "Kar ki bari su zubo".

"To ba kai ne ba, komai na yi sai ka ji haushi na?"

Murmushin sa mai matu?ar ?ayatarwa ya yi, ya ce "Ba haushinki nake ji ba, tsaro nake ba ki, saboda tawa ce nikaWai. sourire (smile) ki yi murmushi mana" ta no?e kafaWarta tana tura baki,ta juya masa baya.
Ya matsa bayan nata, ya sumbaci saman bayan ta, ya zagayo da hannunsa ta cikinta, ya kwantar da kansa a kan kafaWarta. Gaba Waya jikinta ya yi sanyi. Damuwa ce ya ziyarce zuciyarsa, jin yadda Nana ta saki jiki sosai da rungumar da ya yi mata, ko ba a gaya masa ba ya san abin da yake ranta, tuna cewar babu abin da zai iya tsinana mata, ya sanya a hankali ya raba jikinsa da nata, wani irin tausayinta na ratsa ilahirin jikinsa.

Ta maze cikin ya?e ta ce "Sayyid, ya na ji ka yi shiru ne?"

Ya girgiza kai ya ce "Babu komai"

"A'a akwai wani abu. Dama likita ya ce mu zauna na tambaye ka, ko akwai wani abu da yake damun ka, haryanzu fa jininka bai sauka ba Sayyid"

Ya Wan sake yin guntun murmushi ya ce "Damuwa ai akwai ta, ba na son Waga miki hankali ne kawai.
Haryanzu ina tunanin inda su Habu suka tafi, suka bar ki da Wawainiya, Kodayake ko suna nan ma, kula da ni ba dolen su ba ne. Sai wahala ki ke sha, wallahi idan ina tuna hakan, sai na ji tamkar numfashina zai Wauke a cikin damuwa nake sosai da sosai. Ba na son saka ki a damuwa ne kawai".

Nana ta tattara hankalinta ta matsa kusa da shi, ta ri?o hannunsa, ta kalli idanunsa da suka yi jawur. "Idan su Habu ba hakkinsu ba ne kula da ki. Ni yanzu ya zama ha??ina, na san ba a banza Allah ya haWa mu ba. Mu ci gaba da addu'a Allah ya kawo mana komai da sau?i. Amma ina fatan dan Allah ka daina damuwa, idan ciwon nan ya matsanta maka a jikina nake ji, ka daina ba na so" ta ?arasa maganar cikin shagwaSa.

KafaWarta ya ciza cikin wasa, yana rungume ta. Tamkar ba a cikin damuwa suke ba, suka ci gaba da raha, duk da yadda hayaniyar mata ta cika gidan, tamkar a na taro, saboda dawowar Barira, an cika gidan ana mayar da yadda aka yi.
Ana fara kiran sallar magariba, ta kai masa ruwan Wumi banWaki ya yi alwala.
"Za ka je masallaci ne?"

"A'a a nan zan yi"

"To yi sallar. Nima sai na yi muje mu Wuro gas, ko rabi ne sai kuma na sayo gawayi, Ummi ta bani kurfoti, na din ga haWawa da shi" Ya jinjina mata kai ya tayar da salla.
Yana kallon ta ta idar, ta buWe jakarta ta Webo sauran kuWin da suka dawo da su, ta nufi wardrobe ta haWa su da waWancan kuWin. Kawai ta ga kayan wardrobe Win a hargitse.
Mamaki ya kama ta, ta san Sayyid ba ya taSa mata wardrobe, kuma ita ba a haka ta bar wardrobe Win ba.
Ayshacool
Ta janyo jakar gidan Sarkin baka, ta duba ta ga kuWin nijar a ciki. Ta laluba ta Wauki ledar, da kuWin Nigeria ke ciki ta rasa. Ta watso kayan wardrobe Win gaba Waya, tana ?ara haskawa da fitilar wayarta.
Yana tsaye yana kallon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login