Showing 144001 words to 147000 words out of 168002 words

Chapter 49 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

684

rasa, ka zubar da jini ba ?a??autawa har sai mutane sun fara jin fitsari a duk lokacin da aka ambaci sunanka.
Ka kame mutanen gefen al?aryar nan, ka mayar da su bayi, matansu ka mayar da su naka, mazansu su zama bayinka, ka yi amfani da ?arfinsu da fikirarsu ka gina al?aryar da babu wani mahaluki da zai iya Waga maka yatsa, kar ka gushe kana aikata hakan, har sai bu?ata ta biya.
Zaka kasance cikin sanyawar albarkar Aljanu, za su baka dukkanin goyon bayan da ka ke bu?ata kar ka saurarwa kowa"

Cikin damuwa mutumin ya kalli mai maganar ya ce "Ka sanya ni na kashe mahaifina da hannuna, yanzu ga wani abin ka sake zuwar mini da shi, kar ka manta ina da 'yan uwa maza, ba za su zuba mini ido, duk na yi wannan ba, na Wauki abin da ba nawa ba, alhalin su na gaba da ni ba"
Ji ta yi mudubin gurin yana wata irin ?ara tamkar zai tsage, a take ta ajiye littafin ta nufi mudubin tana kallonsa.
Wata irin wuta ta gani tana ci a cikin mudubin. Wutar mai matu?ar ban tsoro saboda yadda take ci. Wani mashi ta gani a soke a jikin wani ?warangwal, Waya gefen mashin an yi rubutu a jikin wani abu mai kama da takarda. Ta ?ara matsawa domin karanta mene ne a jikin takardar amma ta ga mudubin yana haya?i yana ba?i yana washewa.
A kusa da wutar ta ga wani abu mai kama da mutum, a lulluSe da wani mayafi yana zuba wani abu a cikin wutar wanda yake ?ara sanya wutar ?ara balbala.
Imam... ta iya gani a rubuce a jikin abin, mai kama da takarda, a gaban Imam Win akwai wani sunan, sai dai ba ta iya karanta sunan ba. A jikin wutar ta ga taswirar fuskar Sayyid yana jijjiga jikinsa na ?onewa yana kururuwa yana kiran sunanta.
Wata irin zabura ta yi ta kuma tunkarar mudubin gadan-gadan, mudubin ya yi wata irin tsawa ta ja da baya ta faWi ?asa.
A gigice Nana ta farka, ta haWa uban gumi ta yi sharkaf, ga wata irin ?ullewa da cikinta ya yi haWi da mararta. Ta yin?ura da ?yar ta tashi ta tafi banWaki, a zatonta fitsari take ji, ko kuma bayan gida, amma ta ji ba bayan gida take ji ba, ta fitsarin amma still mararta kamar an saka wani abu an Waure mata. Ta yi alawala ta koma Wakinta.
A zaune take salla saboda yanayin girma da nauyin da cikin ya yi. Ta kasa tuna abin da ta gani, sai iya wutar nan da wannan tsawar da mudubin ya yi su kawai take iya tunawa.
"Allahumma ajirni mina narr"
Ta maimaita da tuno yadda ta ga wutar nan. Ta ji sam mafarkin nan bai yi mata daWi ba, ko mene ne babu Alkhairi a tattare da shi sam.
Sai da gari ya waye, sannan ta samu afuwa daga wannan Waurewar da mararta ta yi da bayanta. Jikinta babu daWi, haka nan take lallaSawa ta daure kar Nene ta fuskanci wani abu.
Nana ta dama kunu da kanta, ta tashi tana tafe da kyar, Nene ta ce "Nana wai cikin nan naki wata nawa ne?"

Ta Wan yi shiru ta ce "Ina ga bakwai ne"
"Anya kuwa Nana, kalli yadda ya cure guri Waya ya cure guri Waya ya yi ?asa sosai a ce cikin nan na watanni bakwai ne kawai? Amma ban sani ba ko biyu ne. Yakamata ma mu je Asibiti a duba ki, ni wallahi na ma manta shaf ana zuwa awo. Ko danmu lokacinmu ba awon ake yi ba oho" Nana dai ta yi murmushi kawai tana jin yadda Wan yake ta motsi yana danno ta.

Da ba rufe cikakken sati, mijin Hajara bai zo gidan ba, dama yana fargabar kar Nana ta kasa zama da Nene, saboda faWanta, kuma cikin ikon Allah ya ga lafiya kalau suke zaune. Dan haka ya rage zuwa sosai.
Tun da Nana ta je gidan, Neme ba ta barin ta ta fita, saboda ta ce mata tana da aure, kuma tana yawan gaya mata, ba a son mace mai ciki ta din ga yawo jama'a su na kallonta, saboda baki da ido.
Ma'aikatan Nene duk sun saba da Nana, duk a tunaninsu 'yar uwatta ce, sai dai sukan tambayi Nana, ya aka yi hausarta ba irin tasu ba.
Wasu lokutan sai Nene ta cewa Nana ta zauna a Waki kar ta fito, dan haka babu inda Nana ta sani a garin.
Nana ta kwana huWu, tana fama da wannan ciwon a tsaitsaye.
Sai dai na yau ya fi na kullum, dan sam ba ta yi bacci ba, kuma ba ta gaya wa Nene ba.
Da safe kan Nene ta fito, Nana ta yi shara ta wanke banWaki, ta Wora abin karin kumallo.
Ta kuwa sha faWa a gurin Nenen, sai dai ita ko a jikinta.
Sun gama karyawa, Nene ta shiga Waki, ta ji Nana na kiran sunanta, cikin mawuyacin hali.
Nene ta fito da sauri ta ce "Nana lafiya?"

"Nene yoyon fitsari nake yi, ba na iya ri?e fitsari" gaban Nene ya faWi ta ce "Kamar yaya?"

"Ji na yi kawai fitsari yana bin ?afata, kin ga" ta yi maganar tana Waga wa Nene doguwar rigarta, ruwa na ta bin ?afafuwanta".

"Nana wannan ai kamar na?uda ki ke yi, anya ba ruwan mahaufa ba ne?"

Duk da ?o?arin da ta yi, za ta yi magana, sai ta kasa saboda wani irin gigitaccen ciwo da ta ji.

Har Nene ta fita suka samo abin hawa, Nana na cikin hal????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  in ciwo, ba ta iya gane komai.
Nene ta Waukko wa Nana wasu kayan, su ka fita suka tafi Asibiti.
A Asibitin ma, da aka tambayi Nana, cewa ta yi cikinta wata bakwai ne, sai dai da aka yi hoton cikin, ya nuna satin cikinta arba'in da biyu.
Likitan ya yi mata tambayoyi, yaushe ta yi al'ada na ?arshe, ta ce ita ba za ta iya ganewa ba, saboda Sari kawai take yi a jere.
Ya tabattar mata a cikin Sarin da ta din ga yi, tun da ba Asibiti take zuwa a duba ba, akwai wanda bai fita ba ya ci gaba da girma, dan haka na?uda take yi.

Gaba Waya Nene ta rikice, kamar 'yar ta ce za ta haihu, sai a lokacin ta fita, ta sayo kayan jariri da ba ta san ma na wani jinsi ba ne, da Wan abin da za a bu?ata.
Ma'aikata na tsaye a kan Nana, su na ?o?ari, duk ta galabaita ma ta kasa nishin can ta ce "Ya hayyu ya ?ayyum" ta yi yin?uri sai ga kan Wan ya fito. Ita dai ba ta san yadda aka ?arasa ba, ta ji kukan jariri ya cika Wakin.

Likita ta Wago mata jaririn ta ce "Kalli me ki ka haifa?"

Nana haushi ya kama ta, ta gama shan wannan uwar wahalar ga Wan a hannunta, kuma a din ga tambayarta me ta haifa.
Ta kalli yaron namiji ne, ta ga wani irin shirgegen Wa, kamar Wan wata biyu, sai ta hau mamakin yanzu wannan Wan duk girmansa a jikinta ya rayu, kuma ta Wan wannan gurin ya fito?
Wata irin zabura ta yi ganin fuskar yaron, ta mi?a hannunta gaba Waya tana ?o?arin karSe yaron daga hannun Likitar a kiWime.

Yana kan gadonsa na marasa lafiya a kwance, su ka ga ya yi wata jijjiga sai da gadon ya girgiza kamar an jona masa wani abu, kawai suka ga ya buWe idonsa.
A rikice suka kewaye shi, su na kiran sunansa, sai dai babu wanda ya amsawa sai bin su da yake da ido, kamar ya ga ba?in halittu.
Sultan ya ri?o hannunsa ya ce "Imam ka gane mu kuwa?"
Ya yi shiru yana bin Sultan da kallo.
Abduou ya ce "Ikon Allah, ka ga wannan karon bai tashi da ihun ba, sannu Imam"
Kawai ya yi shiru kamar sa?ago, sai ?wayar idonsa da yake juyawa.

Ayshercool
08081012143
Nana kuwa da sauri wata ma'aikaciya ta mayar da ita ta kwantar, ta ce "Kar ki tashi, ai mi?o miki shi za a yi"
Abin da ya razanata kuwa, bai wuce yadda ta ga fuskar Sayyid sak, a jikin ?aton jaririn nata ba, ga sumar kansa a cike har goshinsa. Ga shi jariri amma hatta girar sa da gashi, haka jikinsa ma akwai gashi sosai.
Aka Wora mata shi a ?irjinta, ta yi wata nannauyar ajiyar zuciya, tare da furta Alhamdillah.

Ta sanya hannayenta, ta zagaye shi, ta Wora hannunta a kansa ta din ga karanto masa addu'oi.
Ta din ga hasko irin murnar da Sayyid zai yi, da ya na nan aka haifi jaririn nan. Hawaye ya din ga gagangarowa ta gefen idonta.
Tana jin Likitan tana tsokanarta da har da kukan daWi, ba za ta bayar da jaririn ba sai an ba ta tukuici mai tsoka. Nana dai ta lumshe idanunta tana murmushi. Aka Wauke jaririn aka gyara ta, aka yi mata Winki, sannan aka kai ta Wakin hutu.
Bakin Nene ya ?i rufuwa, ta din ga kallon jaririn. Ta kira wayar su Hajara, ta gaya musu ba?uwar su Nana ta haihu.
Nana ta din ga kallon Nene, da mamakin yadda take ta murnar haihuwar nan, tamkar ita ta haihu.
Sai dai da Nana ta kalli fuskar jaririn sai jikinta ya yi sanyi, ta rasa abin da yake yi mata daWi, tana tsoron idan ba ta haWu da Sayyid ko 'yan uwansa ba, yaya za ta yi mene ne makomar yaron kenan? Ga fargaba da tsoron kar su ?aisar su yi masa wani abu, kar shi ma ya yi mummunan gado kamar yadda ta yi.
Haka dai ta Wan saki fuska babu yabo ba fallasa. Bayan awanni shida aka sallame ta daga Asibitin suka koma gida. Aka bata magungunan da suka dace ta yi amfani da su, duk Nene ta biya komai.
Nene ta shiga hidima da Nana sosai, ruwan wankanta da na jariri. Ga lafiyayyen Abinci, Hajara kanta idan za ta zo, sai ta yi girki.
Kowa ya Wauki jaririn Nana, sai ya burge shi.
Ita kanta Nana tasirin Addu'a ne ya sanya Allah ya kawo mata wannan Waukin da gaggawa, mutanen da ta haWu da su suke sonta.

Kwana na biyar da haihuwarta, ta Webo kuWi a cikin jakar gurin Sarkin baka, ta samu Nene ta ce "Nene kuWin nan za su isa a sai wa yaron nan abin yanka?"

Nene ta ce "Kar ki damu, mun yi magana da Auwwalu za a samo abin yanka in sha Allah"

Nana ta ce "A'a Nene, ko ke ki ka haife ni, wahalar da za ku yi mini kenan, kuWinki na sana'a ne. Ina son a saya masa kaya, a saya masa abin yanka, ko ba za su isa ba, a karSa a ?ara irin kuWin mahaifinsa ne, dan Allah kar ki ce a'a" Da ?yar Nene ta karSa.
Dan kuWin da yawa, aka sayo ?aton rago, Nene har da Wawainiyar yin girki, ta gayyaci ma?wabtanta suna.
Muhammad Muhsin, shi ne sunan da Nana ta sanya wa jaririn, Muhsin saboda sunan Wan gidan Alhaji Fatuhu da har abada ba za ta manta da mutuwarsa ba.

Ma?wabtan Nene da ma'aikatanta sun yi wa Nene kara, sosai suka tara mata abin alheri na kuWi, da kayan sakawa kasancewar Nene duk masifarta akwai kyauta, shi yasa take shiri da mutane.

Da daddare Nene ta yi wa Muhsin wanka, Nana ma ta yi ta ba ta jaririn ta shayar da shi. Ta fita tsakar gida ta ?arasa aikace-aikacenta. Kukan jaririn ta din ga ji, Nene ta ce "Nana ya ne, ki kula da shi mana"
Amma Nana ba ta amsa ba, sai kukan jaririn da ta ci gaba da ji. Ta koma Wakin ta Waga labule, kawai ta tarar da Nana, ta saka jaririn a gaba tana ta uban kuka.
Hankali tashe ta shiga Wakin cikin damuwa ta ce "Ke lafiya, kukan me ki ke yi?" Nana ta kasa magana, ta ci gaba da kuka, ga jaririn a kan cinyarta amma ta kasa ri?e shi. Nene ta ?arasa ta Wauke jaririn ta ce "Ba za ki illata Wan mutane ba, maza yi ta kukan, idan kin gama kya kula da shi" Nene ta goye shi a bayan ta, ta ci gaba da sabgoginta ta ?yale Nana.
Ba ta sake kula Nana ba, sai da ta yi kuka mai isarta ta gaji.
Nene ta gyara shimfiWarta, ta kwantar da Muhsin da ya yi bacci.
Ta koma gurin Nana, ta zauna. "Nana" ta kira sunanta.
Nana ta Waga kai ta kalle ta.
"Ki gaya mini tsakaninki da Allah, yaron nan ta hanyar aure ki ka haife shi ko kuwa? Na san tambayar nan tana ba?anta miki rai, amma ha?uri za ki yi da ni"

Nana ta share hawayenta ta ce "Nene ni ba ?arya na yi miki ba, ina da aure wallahi Wan sunna ne"
"To Alhamdillah, dama jira nake Allah ya sauke ki lafiya, idan ta kama da kaina sai na je Nigeria, na mayar da ke gaban iyayenki Nana, wannan zaman naki kina yarinyar mace, ba kamace ki ba"

"A'a ba zan koma ba Nene"

"To saboda me?"

Hawaye na ambaliya a fuskar Nana ta ce "Sai na haWu da Babansa, ko danginsa. Ai sun san na taho neman sa"

Nene ta ce "To a wane garin baban nasa yake?"
Ta girgiza kai ta ce "Nima ban sani ba"

"Kamar yaya? Meye sunansa da garin da yake ko hotonsa, sai a taya ki cigiyarsa" Nana ta sake girgiza kanta ta ce "Ban sani ba"

"Wacce daga cikin tambayar ce ba ki sani ba?"

"Nene ban san garin su ba, ban san sunansa ba, kuma ba ni da hotonsa"

Nene ta ce "Ke kar ki raina mini wayo mana, na kwaWe ki, ta yaya za ki auri mutum ba ki san sunansa ba, ba ki san sunan garinsu ba kawai ki ka kamo hanya ki ka taho? Me ki ke Soye mini ne?"

Nana ta Wan yi shiru ta numfasa ta ce "?addara ce ta haWa ni da shi muka yi aure, ban san sunansa na gaskiya ba, ni ba shi sunan Sayyid. Ba shi da cikakkiyar lafiyar ?wa?walwa kuma." Nan Nana ta warware mata komai da ya danganci aurenta da shi, duk da ba komai ta gaya mata ba.
Nene ta yi shiru sannan ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah, dama shi ne Sayyid Win da ki ke ambata idan kina bacci? Amma Nana iyayenki sun yi ganganci. Ke yanzu ko hotonsa ba ki da shi.
Kawai Nana ta Waga mata kai alamar eh.
"To ai Nana zama guri Waya a haka, ba zai sanya a gano shi ba, dole sai an taSuka wani abin, wane ?abilar ne ko shi ma ba ki sani ba?" Nana ta yi shiru ta rasa ma me za ta cewa Nene.

Nene ta ce "To shikenan, amma ba kya ganin yakamata gidanku su san kin haihu?"

"Nene babu bu?ata goben jaririn nan nake hange"

"Haka ne, to Ubangiji Allah ya kyauta, amma wannan lamarin naki akwai sar?a?iya Nana. Amma ba komai Allah ya ta?aita"

Nana ta amsa da Amin.


Baba yana tsakar gida yana shan kunu, sai ga Suwaiba ta fito, gaba Waya ta zama wata iri kamar shiri-shiri. Ta kalli Baba ta cake a ?ofar Waki ta ce "Nana fa ta haihu" ba shiri ya ajiye ludayin kunun ya kalli Suwaiba ya ce "In ji wa? Waye ya gaya miki?"

"Nanan ce ta gaya mini"

"Ke a ina ki ka ganta?"

"Ina bacci a Waki, na ganta da jaririn, ta ce mini haihuwa ta yi"

Wani uban tsaki Baba ya ja, saboda jin shiritar da Suwaiban take faWa. Dan da fari ya zata ma da gaske take yi.

Alhaji Zailani ne tare da Malam Gambo, su na zaune fuskarsa Wauke da damuwa.
Malam Gambo ya ce "Wai duk me yasa ka damu ne har haka? Ka na tsoron ?ungiya ta sake cewa ka kawo jininka ne?"
Alhaji Zailani ya numfsa ya ce "Abu na farko burukana biyu, Waya ya cika na dur?usar da Fatuhu. Amma samun yarinyar nan ya zame mini bala'i, ?arewa ma da yake azzaluma ce mai ba?in hali, wai ta tafi Nijar. Ban kuma san ta yadda zan yi na same ta ba.
Babu yadda ban yi na samu yarinyar nan ba, amma duk lokacin da na yi wani yin?uri a kanta, sai hankalina ya gushe. Yanzu babban tashin hankalina wannan jarababbiyar Sa'a, ashe ita ma ?o?ari take yi, ta mallaki jinin yarinyar nan.
Ga shi na rasa dalilin da ya sanya Shukura take ta zargin likitan da yake yi mini aiki, da kisan jaririnta."

Malam Gambo ya numfasa ya ce "Ka tattara nutsuwarka guri guda, nasara na bu?atar kasada a kowane lokaci. Ita waccan yarinyar ka jingine batunta a yanzu tukuna, tun a wancan lokacin ai na gaya maka tana Wauke da wani shu'umin aljani ne mai taurin kai a kanta ba zai taSa barin burinka ya cika ta daWin rai a kanta ba. Ba kai kaWai ba koma waye kuwa. Sannan ?ungiya idan ta sake bu?atar jini, sai ka bayar da na Waya daga 'ya'yanka ko namijin, ko kuma ita yarinyar taka a bar jaririn nata ba shikenan ba. Kawai ya zuba wa Malam Gambo ido, idanunsa suka yi jawur sai dai bai ce komai ba ya tashi ya fita.


?angaren Sagir kuwa, sosai yake sintiri tsakanin Kano da Abuja, saboda Yusra, saboda soyayyar da suke yi ma a yanzu, ba su yi ta a lokacin da suke saurayi da budurwa ba.
Wata irin muguwar sha?uwa suka yi, da shaiWan ke barazanar shiga cikin lamarin nasu, ga shi ya rasa ta inda zai tunkari Hajiyarsa da batun, domin ba son Yusra suke yi ba. Shukura tuni ta daWe da gano inda ya dosa, amma ta zuba masa ido ta ga ina ne ?arshen alewar zai kasance.


Kwanci tashi asarar mai rai, Nana ta yi wata guda da haihuwa, Nene ta tattara ta daina fita gurin sana'arta.
Sai aikin kula da Nana, ga shi kullum da sassafe kan ta ci komai, ake kawo nonon ra?umi fresh Nana ta sha, sannan ta ci Abinci.
Nana tana kwance tana bacci da azahar, saboda yadda Muhsin ba ya barin su bacci da daddare, saboda ba ya Waga wa Nana ?afa da tsotso, ga kuka sai dai Nene ta taya ta ri?onsa.
Yana gabanta yana bacci, ita ma ya Wauke ta, ta Waga kai ta ga ya shigo ta ?ofar Wakin. Tana kwance ba ta motsa ba ta ga ya ?araso ya zuba musu ido, daga ita har Muhsin, ya sanya hannunsa ya shafa gashin jaririn, ya dur?usa ya sumbaci gishin yaron. Sannan ya kalli Nana idanunsa cike da hawaye.
"Sayyid, yaushe za ka zo ka ganmu? Mu na bu?atar ka a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login