Showing 69001 words to 72000 words out of 168002 words

Chapter 24 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

654

dariya ba, jikinsa yana tsuma.

Tsorata ta yi, ta ?ara ja da baya, kawai ta ji ya ri?e wuyanta.

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
Idanun Nana suka yo waje, ta ji numfashinta ya yi sama, ta saka hannu ta rirri?e nasa tana kakari.

Da ?yar ta kalli fuskarsa, gaba Waya ta canza naman fuskarsa sai rawa yake yi. Tsohon nan ta ga ya bayyana a gefensa, ri?e da sandarsa yana kallon ta yana dariya.

Jikinta ne ya saki a hankali, ta sauke hannunta. Ya yi jifa da ita kan katifa ya yi baya, yana jin tamkar ana jan kansa.

Tana dur?ushe tana wani irin tari, haWi da kakari, tana ta yin?urin amai, amma babu abin da yake fita daga bakinta sai wani irin yawu mai yau?i. Ta ja jikinta da ?yar ta jingina, ta lumshe idanunta ta buWe a hankali. Ta ga ?aisar ya zura mata ido.

Ya gyara zamansa ya ce "Yanzu da ki ka fara WanWana kuWarki, wata?ila za ki yarda da abin da nake gaya miki. Laifi na biyu kenan da ya aikata mini, zan kuma taSa shi a inda ba ya zato".

A wahale Nana ta ce "A'a ?aisar,? koma dai mene ne, ni ya yi wa dan Allah ka rabu da shi, wannan tsohon na gani a tare da shi, kuma idan ka ce za ka yi masa wani abu, kai ma wannan tsohon wahalar da kai yake yi."

"Ba ke za ki gaya mini abin da zan yi, ki rufe mini baki. Kuma kuskure mafi girma da ki ka aikata, bayan ?in amincewa da bu?ata ta, shi ne Waukar cikin da ki ka yi, ba zan taSa lamunta a samu zuriya ta tsatsonki ba, na ci gaba da ?untata rayuwata ina wahalar banza a kan mutane marasa ala?awri kamar ku ba"

Nana ta kalli cikinta ta kalle shi ta ce "Ciki kuma?"

"?warai, ga Wan tayi nan a cikin ki, tun a ranar farko da ku ka kasance tare. Kin Wauki abin da ke kan ki ba ki da tabbacin wane jinsi ne"

"Mutum ne, Sayyid bil'adama ne, da aljani ne ba zai iya tarayya da ni a zahiri ba, sai dai a cikin bacci, ko ta hanyar amfani da gangar jikin Wan Adam "

"Ko?"

"Eh" ta ba shi amsa.

"Yaro yaro ne. Kin tabattar bil adama ne, daga ina? Daga wace nahiyar? Wane shiri ki ke da shi, a kan sanin waye shi da inda ya fito? Har ki ka sakankance ki ka amince da Waukar ciki?"

?o?arin juyawa Nana ta yi a kan katifar, amma ta ji jikinta a WaWWaure kamar an yi mata duka. Ga wani irin azabar sanyi da yake ratsata ko ta ina, tamkar an ajiye ta a cikin ?an?ara. A cikin kunnuwanta kuma take jin yadda zuciyarta ke bugawa da ?arfi da kuma sauri. Ga wani irin nauyi da kanta ya yi mata tamkar an Wora mata. Ga azababben ciwo da yake yi mata, tamkar zai rabe.

Ta juya da ?yar tana numfarfashi, tana son lalubar abin da za ta rufa, wani irin huci ne ya daki fatarta, ta buWe idanunta da ?yar, ta kalli gefenta.

Yana kwance jiginsa na ta jijjiga, yana numfarfashi.

Ta din ga jan jikinta a hankali, ta matsa ta hau kan ?irjinsa ta kwanta, ba tare da fargabar zai sake yin?urin cutar da ita ba.

A hankali ta ji zafin jikinsa, ya fara ratsa ta, ta fara rage jin sanyin da take ji, wani wahalallen baccin ya sake yin awon gaba da ita.

"Asmy" ta ji ya kira ta da wani sunan kuma.? Ta buWe idonta da ?yar ta kalle shi.

Garau da shi kamar babu abin da ya faru.

"Salla" ya faWa a ta?aice, jikinsa duk danshin ruwan alwala, ya fice ya tafi masallaci.

Da ?yar ta tashi, tana daddaga bango, ta shiga ta yi alwala, ta dawo ta yi salla a zaune, ta kwanta.

Ganin ba ta tashi da wuri ba, ya sanya shi fara rage aikace-aikacen Wakin, amma ya ga babu alamar za ta tashi balle ta Wora girki. Ya matsa kusa da ita ya tashe ta. Ta tashi zaune da ?yar, kanta kamar ana buga mata guduma.

Ya ?ura mata ido ya ga duk ta canza, sai dai ta yi masa kyau a ido sosai, ?anan kitson kanta, sun dace ba ?in gashinta, ga hannunta lalle ja da ba?i ya yi mata kyau sosai da sosai.

Ta saukko daga kan katifar, ta Wauki wata roba, ta Waukko lemon tsami ta yanka, ta fara matsawa a bakinta. A hankali tashin zuciyar da take ji, ya fara raguwa. Shi dai ya zuba mata ido.

Ta gama ta sake ?o?arin kwanciya.

"Ki ci abinci, ga ?osai" ya yi maganar yana nuna mata ledar da ke kusa da gas.

Ta girgiza masa kai ta nemi guri ta kwanta.

"Kin yi mini laifi ki na fushi da ni kuma? Na ce kar ki yi abu kin yi, kuma kina fushi?"
Ayshacool
Ta kalle shi idonta fal hawaye ta ce "Kuma shi ne sai ka sha?e ni? Har na yi maka laifin da za ka yi yin?urin kashe ni, dama ba so na ka ke yi ba" A rikice ya zaro ido ya kalle ta ya ce "Ni? A'a ban sha?e ki ba. Me yasa zan sha?e ki kuma? Raina ya Saci ne, zuciyata ta kama da wuta, sosai da sosai amma ban sha?e ki ba. Kamar bacci ma na yi daga lokacin"

Idonta fal hawaye ta ce "Bayan ga shaidar faratanka a wuyana"

Kamar ya yi kuka ya ce "A'a, kin manta kin yanke mini farce, amma ban taSa ki ba ma, kalli hannuna" ya yi maganar yana nuna mata yatsun sa.

Ya mi?a hannunsa wuyanta, dan ya duba shaidar faratan da ta ce, amma ya ji jikinta zafi rauuu.

Sake rikicewa ya yi ya ce "Ma vie. (Rayuwata) tu as de la fi?vre ? (ZazzaSi ki ke yi?" Ya yi maganar a rikice.

Ba ta kula shi ba ta kwanta, tana jin yadda jikinta yake Waukar zafi, cikin ta yake yamutsawa.

Wayarta ya Wauka ya danna, ya kara a? kunnensa. Da French ya yi magana, ya ajiye wayar a kan mudubi, ya dawo inda take ya ce "Tashi ki saka kaya, na kira Habu"

"Sayyid da ba ka kira shi ba, zan warke fa"?

"A'a jikin ki ya yi zafi sosai"

Ya nemi guri ya zauna a musa da ita, yana ci gaba da kallonta cikin damuwa.

*
Sannu a hankali yake jujjuya wayar hannunsa, yana sake karanta sa?on da ya shigo wayarsa.
An shirya tsige shi, daga shugabancin 'yan kasuwa, bisa zargin sa da yin sama da faWi da wasu kuWaWe, na ?ananan 'yan kasuwa.

Tabbas akwai kuWaWen wasu a hannunsa, har da wanda kuWinsu bai kai ba, da zai yi wa ciko ya ba su bashin kaya. Kuma ya tattara kuWin ya yi order kayan, sai dai sun ?ara wata guda a kan lokacin da yakamata su zo, shima yana ta bibiya ne. Amma ya yi wuri a ce an Wauki wannan matakin, duk da ba yau ya saba yi wa ?ananan 'yan kasuwan irin wannan tallafin ba, har ma da manyan, amma ba a duba hakan ba.

Fadila ce ta nufo shi, hannuna da Wan ?aramin tray, Wauke da fruit, ta nemi guri ta zauna.

Ta ce "Daddy, ga fav Win ka, banana, ga kuma smoothie na yi maka, na ga kamar a gajiye ka ke"

Ya yi murmushin ya?e ya karSa ya ce "Na gode sosai da babyna"

Jiki a sanyaye ta ce "Daddy" ya kalle ta ya ce "Na'am"

"Me yake faruwa ne?"

Ya ce "A ina?"

"Damuwa ce a fuskarka, dan Allah gaya mini, meyafaru?"

Ya yi murmushi ya ce "Tsabar gajiya ce kawai, kin san yanayin harkokin namu, babu hutu"

Fadila ta ri?o hannunsa ta ce "Na san wata?ila har da damuwar kayan nan, da suma suka yi delay, amma dan Allah ka yi ha?uri ka daina damuwa, yadda wancan suka kuSuta, wannan ma da yardar Allah za su tsira. Kar ka damar mini kanka dan Allah"

Maganganun nata sun Wan ba shi ?warin gwiwa, shi bai damu da batun tsige shi daga shugabancin ba, shi ha??o?in mutane da suke kansa, su ne suka dame shi. Yana jin daWin tattauna matsalolin sa da Fadila. Duk da ba ta kai uwargidan sa shekaru ba, amma yau shekara bakwai da auren Fadila, ta tattara duk ta tsane shi, tana ganin ya ci amanarta, sun yi wahala tare ya ?aro aure. Duk da duk wani abu na jin daWi na hakkinta yana sauke mata. Ko ya gaya mata damuwarsa, sai dai ta taSe baki kawai ta ce Allah ya kyauta, ko ma ta ce masa alhakinta ne.
Fadila kuwa ko sun samu saSani, da ya shiga damuwa, take ruWewa har sai ya samu mafita, sai dai a wannan karon, ba zai iya gaya mata ba, saboda ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba ita ma.

****

"Husnah" ta buWe idonta ta kalle shi, lokacin agogon Wakin ya nuna ?arfe sha Waya da rabi na safe.

"Tashi ki saka kaya, ga Habu can ya zo, za mu je a duba ki"

"Na ce ka daina gaya musu, mu daina saka su Wawainiya"

"Tashi ki daina yi mini jayayya" ya yi maganar, yana tsuke fuska.

Ta tashi da ?yar, ya taimaka mata ta saka kaya, ta saka hijjabi, a harabar gidan suka tarar da Habu. Ya yi mata sannu suka fice.

Tun da ya kira Habu ya sanar masa, dama da adaidaita sahu ya zo. Wani ?aramin asibiti suka je. Buzu yana tare da Nana, Habu ya yi ta shiga yana fita.

Ya sayo kati aka duba ta, aka ba ta gwaje-gwaje. Sun Wan jima a gurin Waukar jinin, ta gaji da zaman, ta zame tana ?o?arin kwanciya a gurin, amma ya ri?o ta tsam a jikinsa.
Ayshacool
Suka koma gaban likita da sakamakon, ya duba ya kalli Nana ya ce "Yaushe rabon ki da Al'ada?"

Tamkar ya sokawa Sayyid mashi, ji ya yi ina ruwansa da zai yi mata wannan tambayar? Amma ya dake bai yi magana ba.

Nana ta gaya masa, ya ce "Ok, to akwai ciki ne, sai kuma malaria++ bai kamata a ce, ga juna biyu ba kuma ga malaria ki na fama ba. A kula sosai. Zan rubuta ruwa da allurai a saka miki, za ki Wan ji ?warin jikin ki in sha Allah"

Ya yi rubuce-rubuce ya basu, Sayyid ya karSa suka fito.

Ya mi?a wa Habu katin, aka nuna musu inda za su kai Nana.

Habu ya kalle shi ya yi masa magana da yaren su, ya cewa Habu "Tsaya" ya saka hannu a aljihunsa ya Waukko kuWi ya ba wa Habu"

Habu ya kalli kuWin ya kalle shi, ya ce "Da can kuWin yi wa Nana amfani da su.

Wani ma'aikaci ne, ya shigo ward Win zai sanyawa Nana cannular. Nana ta mi?a masa hannun, ya kai hannu zai kama ya saka mata Buzu ya ri?e hannun Nana.

Ma'aikacin ya ce "Allurai zan yi mata, zan saka mata cannula ne" ya yi shiru ya ?i magana. Nana ta kalli yadda launin idonsa ya canza. A ranta ta ce "Allah ya yaye maka wannan azabar kishin Sayyid"

Habu ya yi gyaran murya, ya "Ka yi ha?uri, a saka mata, ka ga tana shan wahala sosai.
Ya yi mursisi, ya murtuke fuska, ya ri?e hannunta gam, ya ?i saki.
Sai da Habu ya zauna ya din ga yi masa bayani da yarensu, cikin tattausar murya. ?arshe ma'aikacin gefe ya koma, ya zubawa sarautar Allah ido.
Tamkar gunki ya yi gum, ya ?i motsi kuma ya ?i magana.

"Ni idan ba zai yarda a saka mini ba, dan Allah ku mayar da ni gida, na je na kwanta na gaji" ta yi maganar a raunane, cikin yanayin rashin lafiya.

Da ?yar ya saki hannun Nana, sai dai ya kawar da kansa gefe, saboda yadda zuciyarsa ke tafasa da ganin ya kama hannun Nana ya saka mata ruwa.

Har huWu su na Asibiti, sai dai ta ji dadin jikinta, zazzaSin ya sauka.

Aka gama saka mata ruwan, sannan suka tafi gida. Ba ya jin nauyi ko kunyar Habu, haka yake rungume da Nana yana shafa ta, kamar zai lashe ta ya mayar da ita cikin sa.

Suka koma gida, Nana ta samu ruwa ta yi wanka, ta saka kankanar da ya saya mata a gaba, ta din ga sha, saboda itakaWai ce ta ji ta yi mata daWi.

Suna harabar gidan, Habu yana yi masa magana, sai ga babar su Yusra ta ?araso.

"Kai mai gadi, ina ka tafi baka yi wa kowa bayani ba? Zamu kai Siyama wankin ?onuwar da ta yi, amma ka yi tafiyarka yawon ka?"

Habu ya ce "Ki yi ha?uri Hajiya, mai Wakin nasa ce babu lafiya, ba a nuste yake ba, hankali tashe mu ka tafi Asibiti ki yi ha?uri dan Allah"

"Ni ma tawa 'yar babu lafiya ai, ba sai ya yi bayani ba. Tun da idan zai je wani guri yana rubutawa Jamil ba, sai Jamil ne ya buWe mana muka tafi, ?onuwar na ta jini"

Habu ya sake cewa "Ki yi ha?uri dai dan Allah"

Ko Waga kai bai yi ya kalle ta ba, balle ya kula ta, ko ta saka ran zai ba ta ha?uri, ya bar ta ita da Habu.

"Sannu"

Ta jinjina kai ta ce "Sayyid da ka sani ka ba ta ha?uri, ba na son wannan faWan da ake yi maka"

"Ya jikin? Kin daina jin zazzaSin?"

"Amma ka san mun yi laifi, bai kamata mu tafi ba su sani ba"

"Da suka buWe ?ofar sun mutu ne?"

Nana ta sauke numfashi ta ce "Aishikenan, idan ka janyo aka kore mu, ka nemo mana inda za mu zauna ai" ya yi shiru, bai kuma cewa komai ba.

Daga bisani ya ce "Me za ki ci?"

"Ba komai, ba na son komai, kankanar nan ta ishe ni".

A hankali ya kai hannunsa, ya shafa gashin ta, ya saki murmushi ya ce "Kitson nan ya yi kyau sosai, ya dawo da hannunsa kan hannunta, ya jujjuya hannun, ya kai bakinsa ya sumbata ya ce "Kin yi mini kyau"

Ta kalle shi galala ta ce "A hakan da na fita hayyacina. Tun jiya na so ka kalla ka yaba ba, ka share ni ka yi ta yi mink faWa"

"Idan na ce kar a yi, to a bari ne kawai, ba na so. Me yasa zan ce kar ki je guri ki je?"

Jiki a sanyaye ta ce "Na san na yi laifi, ka yi ha?uri. Za su ga kamar wula?anci ne, sun gaya mini abu na tashin hankali, amma na kasa yi musu jaje. Sayyid ban ji ka ce komai ba, a kan abin da aka ce"

"Wanne?"

"Da likitan ya ce... Sai kuma ta yi shiru.

"Ya ce me?"

"Ina da juna biyu, tsoro nake ji" ta yi maganar tsoron na bayyana ?arara a kan fuskarta.

"Tsoron me?"
Ayshacool
Abin da ta so furtawa daban, amma ta kauce faWar hakan, kar ta tayar masa da hankali ta ce "Ban ga ka yi murna da hakan ba"

Ya gyara zamansa ya dubi Nana a tsanake ya ce "Wata irin wutar zafin, ganin wani ya taSa ki ne, take ci mini zuciya. Amma wallahi ina cikin murna zamu ?ara yawa, nima Ahalina zai cika, ki haifi namiji mai kama da ni. Ko kuma mace mai kama da ke"

Murmushin dole Nana ta yi, ba dan ya kai zuciyarta ba ta ci gaba da tauna kankanar bakinta a hankali.

*

Yanayin yadda aka banko ?ofar gidan, sai da Baba ya tsorata kamar ya zura da gudu. Ya dai tsaya ya ce "Kai wani mara hankalin ne ya ke yi mana wannan banzan bugun haka?"

Bai yi magana ba, sai ganinsa Baba ya a tsakiyar gida, tamkar ya faWo daga sama.

"Uban me ya kawo ka gidana?"

"Gidan Ubana ne" ya faWa yana Wan rarraba ido yana kallon gidan.

"To uban me ya dawo da kai? Nan ka saka 'yan sanda suka din ga yi mini sintiri a gida, ka kai Gaddafi ?ara, kuma ka gudu, da yake kai duk inda ka tsuguna babu alkhairi tsiya ce take biyo baya. Ka bar mini gida kafin 'yan sanda su zo neman ka"

"Ni fa ban kashe kowa ba wanda suka yi abin ma an kama su, kawai ka wani din ga kora ta, idan na gama abin da nake yi da kaina zan bar maka gidan ai. Ka yi ta wani gidanka kamar wani gidan arziki"

Baba ya ce "Tun da ba na arziki ba ne ba, zo ka fice"

Imarana ya ce "Wallahi ba zan tafi ba. Ina Nana? Ke Nana"

Nasiru ne ya yi sallama a gidan, hannunsa ri?e da ledar kayan miya, yana ganin Imarana ya tafi da gudu ya rungume shi.

Imarana ya ce "Nasiru, na ga kana nema ka kamo ni a tsawo. Wai ina Nana ne?" Baba yana ?iftawa Nasiru ido, amma tuni ya kwatsa wa Nasiru bayani.

"Ai an yi mata aure"

Turus Imrana ya yi ya ce "Kamar yaya? Uban waye ya yi mata auren ban sani ba?"

"Ni ne nan ubanta, idan kuma kai ka haife ta da sai an sanar da kai sai na ji"

"Kut.. aure fa, wa ka aura mata, ina fatan ba wannan ajawon bane Salisu yake ko wa?"

"Ba Saleh ba ne, wani Buzu ne mai gadi" Nasiru ya sake ba wa Imrana amsa.

Kai tsaye ya ?undumo ashariya ya ce "Wane irin Buzu kuma? Kai ina ne gidan da aka kai ta?"

Baba ya ce "Wallahi ka taka ka je gidanta ban yafe maka ba. Kar ka kuskura ka je ka yi mata hauka ka kashe mata aure"

"Wallahi sai na je, dama kula ka ke da ni, shi ne za ka yi mini Allah ya isa ta kama ni, amma tun da ni nake kula da kaina ba za ta kama ni ba. Kai Nasiru wuce mu je ka raka ni"

Baba ya ce "Nasiru idan ka raka shi, sai na yi maka dukan tsiya"

"Kai mu je zan baka dubu biyu"

Nasiru ya waiga yana kallon Baba, ga batun kuWi ya ji, ya maze ya bi Imarana suka fice, Baba na ?wala masa kira amma ya fifita dubu biyu a kan kiran Baba.

Su na tafe a hanya, Nasiru yana ba wa Imarana labarin, abin da ya faru da yadda aka yi auren Nana. Ba ?aramin fusata Imarana ya yi ba.

Mussaman da ya gaya masa, gadi Buzu yake yi.

"Uban me mai gadin zai tsinana mata,? Allah na tuba mu dai ba mu yi dacen uba ba wallahi? mu dai kawai ya kawo mu Duniya yana neman maraba da mu."

Sayyid na zaune yana shan shayi, a harabar gidan ya ji an taSa gate. Ya rufe fuskar sa da sauri, ya tashi ya je ya buWe, ya tsaya yana kallon Imran, saboda tsananin kamnninsa da Nana.

Babu jiran komai,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login