Showing 36001 words to 39000 words out of 168002 words

Chapter 13 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

647

ta shiga banWaki ta duba, ta ga ta samu tsarki, ta yi wanka ta yi alwala ta fito. Ta kunna fitilar Wakin, haske ya gauraye Wakin, ba ya cikin Wakin. Duk da wasu lokutan idan ta kwanta bacci ba ta iya tantance mafarki ko kuma zahiri, amma ba ta tunanin da idonta ta taSa ganin ya kwana Wakin. Ko dai ya kwanta a farkon dare, tsakiyar dare ta neme shi ta rasa, ko farkon dare baya nan, cikin dare ta ganshi kafin asuba ta neme shi ta rasa.

Har ta doshi ?ofar Wakin, da niyyar ta Waga labule ta duba, ta gani ko yana waje, amma ta fasa da tuna abin da ta gani a wancan karon. Babu tsammani iska ta kaWa labulen, ta hango shi a kan benci a kwance ya takure, yana bacci.
Sai ta ji tausayin da ya kama ta.

Ta tayar da salla, ta yi nafila raka'a biyu, ta zauna ta din ga istigfari da salatin annabi Sallallahu alaihi Wasallam.
Bayan ta gama ta Waga hannayenta ta din ga tasbihi duk wanda ya zo bakinta yi take yi. La'ilahaillalahul azimul halim
La'ilahaillalahul jalilul jabbar
La'ilahaillalahul kabirul mut'al
La'ilahaillalahu muWWali'i sittar
La'ilahaillalahul khali?ul laili wa nahar.
Allahu Allahu rabbi, la ushriku bi hi shai'an.
Ayshacool
Allahumma inni as'aluka bi anni, ashhadu annaka antal ahadussamadu lazi lam yalid wa lam yulad, wa lam yakun lahu kufwan ahad.
Sai da ta gama tasbihin kaf, sai kuma ta rasa abin da za ta ro?a. Ta sauke hannunta a hankali ta yi shiru, kawai daga bisani ta rufe da sayyidul istigfar, dai-dai lokacin an kira sallar asuba.

?arar zubar ruwan famfo ta ji, ta dake ta je ta le?a, ta hango shi a dur?ushe yyana alwala. Ya idar ya zare sakatar gate ya fice.

"Abin mamaki, mutum mai taSin hankali ya san salla, ya san addini anma kuma a ce ba shi da lafiyar ?wa?walwa anya kuwa?" Ta tambayi kanta.
"Zan ci gaba da tunzura ka, da ?o?arin ?ure ha?urinka, har sai na tantance ainihin jinsin ka, sai na gano ko kai waye!" Ji ta yi an bushe da dariya mara daWin ji, gaba Waya Wakin ya Wauki sautin.

AYSHERCOOL
08081012143
Ayshacool
Page 33


?o?arin dai-daita nutsuwarta ta yi, ta tattara hankalinta guri guda.
Ta fara jin sanyi yana ratsa ta, ta din ga nanata Innalillahi wa innalillahi raji'un. Sai kuma Wif tamkar an yi ruwa an Wauke, ta daina jin sautin dariyar.
Ta tafi banWaki, ta sake yin alwala, ta zo ta yi raka'atanul fajari, sannan ta yi sallar asuba.

Ta zauna a kan daddumar, tana kallon wardrobe, tana son ta je ta Waukko Alqur'ani, amma ta kasa tashi.
Ta yi ?o?arin yin karatun Alqur'anin da ka, ta karanta abin da ta sani, amma ta ji tamkar an tattare komai daga cikin kanta an kwashe bar mata fanko.

Ba ta san me ya ci gaba da wakana ba, ta ji an taSa hannunta. Ta buWe idonta ta Waga kanta ta kalle shi. Ta ganta zaune a kan daddumar, sai dai gari ya yi haske sosai, da alama takwas ma ta wuce.

Ya nuna mata ledar hannunsa ya ce "A zo a karya, ga abinci" ?amshin soyayyen ?osan ya daki hancin Nana yawunta ya tsinke. Duk son ta da ?osai ta girgiza masa kai.

Ya ce "Me yasa?"

"Azumi na Wauka"

"Da izinin wa?" da fari shirin tashi take yi, babu shiri ta koma ta zauna, tana bin sa da ido. Mamaki take yi har ya san sai da izninsa za ta yi azumi?.

Ya kamo hannunta, ya juyo cikin tafukan hannun ya ce "Kalli, kin zubar da jini sosai, ta ya ya za ki Wauki azumi? Ki ci abinci"

Ta no?e kafaWarta ta ce "Ni ba zan karya ba, na riga na yi niyya, ka bari daga wannan idan zan kuma yi zan gaya maka in sha Allah"

A fuskarsa ta ga alamar ya ji haushi, saboda yadda y tsuke fuskar, kawai ya gyaWa kai ya ce "sai ki yi na gani" ya tashi daga gabanta. Ta bi bayansa da kallo, yana tashi ita ma ta tashi, ta haye katifarta saboda bacci kanta har wani nauyi ya yi mata.

*

Jamila fatar jikinta, ta warke, amma da ?yar take tafiya tamkar tsohuwa. Hatta banWaki sai an kai ta, komai a du?e take yin sa.

Babu shiri Mama ta Wauki Jamila, ta kira ?anwarta ta raka ta zuwa gurin wani mai magani, tana ta bala'in daga zuwa gidan Nana wannan masifar ta afka mata. Ta din ga faWan ba yadda ba ta yi da su ba, a kan kar su je gidan Nanan, tun da dai alkhairi babya bibiyar ta, amma suka nace su ka tafi.

Ko da suka je gurin mai maganin, ya ?are wa Jamila kallo ya ce "Gaskiya wannan ya fi ?arfina, sai dai na nemo Ibrahima wakilin rafi, ya duba ta. Idan da wani abu ma duk zai yi muku bayani"

Mama ta ce "Waye hakan? Kuma a ina yake?"

Ya ce "Kar ki damu, yanzu za ki gani, ba a nesa yake ba, yana nan kusa"

Mama ta ce "To madalla, mun gode sosai da sosai "

Mutumin ya tashi, ya din ga tattara shirgi a Wakin, da tsummokara ya cika gurin da su, kamar Wakin mahaukaci. Sannan ya buWe wasu manyan randuna a sha?e da ruwa, ya barbaWa wani magani a ciki. Ya buWa wata jaka, ya kwaso wasu tarkace, ya Waura wani guru a damtsensa, sannan ya saka yaronsa ya kawo masa, garwashi a cikin kasko, ya turare Wakin da wani irin haya?i mai warin gaske, sannan ya nemi guri ya zauna a tsakiyar shirgin nan da ya baje.

Ya sunkuyar da kansa, ya din ga karanto wasu abubuwa da ba a iya gane me yake cewa, saboda ba yaren hausa ba ne, yana yi yana kaWa kansa.
Can bayan wani lokaci ya Wago kansa a hankali.

Gaba Waya kamaninsa sun sauya, fuskarsa duk ta wani tattare tamkar tsoho, jikinsa kuma sai karkarwa yake yi, kamaninsa sun canza.
Ba Mama ba hatta Jamila, a tsaroce suka ja da baya, su na rarraba ido.

Ya ?ure Jamila da ido sannan ya ce "Wannan ai wani aljani ne yake jinya a jikinta" Ba Jamila hatta Mama cikin bala'in kiWima da tashin hankali, ta kalli mai maganin ta ce "Aljani yake jinya a jikinta kuma, na shiga uku na lalace, ta yaya?"

"A'a ba ki shiga uku ba, uban du?usa su ka yi wa laifi da alama, ya hukunta su ne, su duka daga ita har shi a haka"

Cikin rashin fahimta ta ce "Wa kenan?"

"Wani aljani ne shi ma"

Cikin damuwa ta ce "Ya za a yi Jamila ta ga aljani ta yi masa wani laifi?"

"To wannan kuma wani abu ne daban, ba na son dai yin doguwar magana, balle dogon jawabi, amma idan ta nutsa ita ta san ta yi laifin. Yanzu dai zan baku magani, na sha da shafawa, sai kuma wanda za ta din ga she?a kafin ta kwanta bacci.
Ayshacool
Daga nan sai kuma a samu ?osai mai zafi, a yi sadakarsa bayan la'asar. Amma iya ?anan yara wanda ba su kai shekaru goma ba, su za a bawa. Za ta mi?e gaba Waya, ta warke. Sai kuma a nemi saurayin zakara, a yanka a fige shi a sulala, da almuru idan an gama rabawa yaran ?osan, a tona rami a binne zakaran. Zai bar jikinta ya yi jinya a wani guri. Wanda kuma su ka ba ta aikin. ta yi musu su za su Wauki ragamar ba wa uban du?usa ha?uri. Ni ba ma shi nake ji ba, an riga an nakasta aljanin har abada. Ya ?one sosai daga feshin wutar da aka yi masa. Wata ?ila ya yafe mata gaba Waya, wata?ila kuma shi ma ya ce sai ya rama, duk da babu lallai ya samu damar hakan ?ungiya ba za ta ba shi wannan damar ba"

Cikin tashin hankali ta ce "Ni fa duk ban fahimta ba, ka na maganar ?ungiya, bayar da ha?uri, duk me ya kawo wannan zancen?"

Ya ce "Ki bar shi a haka kawai yadda na gaya miki "

Cikin damuwa "Ni dai malam ka taimake ni dan Allah, ka da yarinyar nan ta nakasa ita ma. Yayarta ta nan haka take ta fama da aljanun nan, da ?yar ta yi aure tamkar za ta haukace, daga zuwa gidanta ta gamu da wannan masifar"

"Kar ki damu, ba wani abu" Ya Waga hannunsa sama, ya dun?ule ya watsowa Mama wani ?ulli guda uku, ya ce "A je a yi mata wanka da shi, za ta ware, na ba?ar takarda shi ne na shan, sai na sha?ar"

Bayan ya basu maganin ya sallame su.

****

HaWuwa da kuma ?asaitar Wakin, ya sanya Nana sakin baki tana ?arewa Wakin kallo, tare da tunanin yau kuma a ina take?.
Sai dai yanayin adon da aka yi wa Wakin, ba wai ado ne irin na wannan zamanin da muke ciki ba. Ta Waga kai ta kalli rufin Wakin, sai ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?dai ga mamakinta, sai ta kasa tantance wani irin rufi ne, gini ne dogo mai matu?ar tsawon gaske. Sai da ta kalli wani sashi na jikin Wakin, sai ta ga ya yi kama da cikin dutse,, ba wai gini ne na bulo ko ?asa ba.
Wani irin ?amshi ya karaWe ilahirin Wakin, amma shi ma ?amshin sai ta ji bai dace da wannan zamanin ba.
A hankali ta kalli gadon da take kai a zane, ta shafa saman gadon, wani irin laushi na ban mamaki, bayanta ga fululluka a ajiye. Jin motsi ya sanya ta zabura ta waiwaya zuwa inda take jin motsin. Sai a yanzu ta hango wani sashi da ta sani a gurin. Gurin da ta gan ta jiya tana taje masa gashin kansa ne. Gadon ya tunkaro da kofin shayi a hannunsa yana takawa a hankali, jikinsa sanye da wata doguwar riga fara ?al.
Sai da ya zo gaban gadon sannan ya ajiye kofin a gefe, ya taka wani abu ya hawo gadon.
Kallonta yake yi yana wani irin murmushi mai ?ayatarwa, ya sumbaci bakinta ya ce "que se passe-t-il?"

"Ban iya ba" ta bashi amsa tana kallonsa ta ?asan idonta.

Ya yi dariya yana rungume ta a jikinsa ya ce "Me ya faru na ce" ya yi maganar yana shafa gefen fuskarta.

Ta Wan tura baki ta ce "Ni sanyi nake ji" ta yi maganar kamar za ta yi masa kuka.

Ya Wan girgiza kai ya ce "Ai ina kusa da ke, kwantar da hankalinki yanzu zan ba ki Wumin da ya dace da yanayin jikinki, wanda ba zai cutar mini da une ame(Soul/ruhinki ba). Ni ma ki bani wanda ya dace da ni, ni sanyin nake bu?ata". Ya yi maganar yana rungumeta a jikinsa, cike da shau?i.

Tamkar almara haka Nana take ganin abubuwan da suke faruwa a tsakanin ta da shi, Kasa saita kanta ta yi a dalilin yadda jikinta yake wata irin tsumar da tun da aka haife ta, ko a duniyarta ta zahiri ba ta taSa tsintar kanta a makamancin wannan yanayin ba. Ita duk yadda take tsintar kanta a mabanbantan yanayi, da gurare ba ta taSa mafarki makamancin wannan a rayuwarta ba. Ga shi ya fi kama da zahiri ba mafarki ba.
Amma duk da haka, ta bar wa zuciyarta mafarki ne, babu tunanin komai take biye masa, tamkar masoyan da suka shafe tsawon lokaci, cikin matsananciyar soyayya da ?aunar juna.
Bayan wani lokaci a hankali ya buWe idonsa, ya ?ura mata ido idanunta a lumshe. Ta buWe nata suka yi ido huWu.
Ta Wan zaro masa ido, tare da murguWa masa baki ta ce "Meye?"
Ayshacool
Ya yi murmushi ya ce "Komai ma, je suis heureux (Ina cikin farin ciki) na samu farin ciki amma ba cancan ba saura sex... Hannu ta saka ta toshe masa baki tana hararsa. "Kai ba ka jin kunya ne? Ka ke faWar irin wannan maganat?"
Dariya ya yi, yana ?o?arin cizon hannun nata. Ya ce "Yanzu ma ai ba mu ji kunyar ba, tun da...
Ba ta bari ya ?arasa ba, ta yin?ura ta kama kafaWarsa, za ta cije shi, ya mirgina ta yana dariya.

"Haryanzu ka ?i ka gaya mini sunanka" ta yi maganar tana lumshe idonta

"?asair" ya furta a ta?aice.

"?aisar kuma?" Ta furta a zahiri bayan da ta buWe ido, ta ga yadda take ?an?ame da pillow.

Juyowa ya yi daga inda yake zaune, da wani Wan ?aramin littafi a hannunsa, suka yi ido huWu. Kawai ya yi wani irin murmushi yana Wan kaWa kai ya ci gaba da kallon Wan ?aramin littafin.

Ta tashi tana ?arewa kanta kallo, tana jin abin da ya faru a tsakanin su a jikinta, dan hatta ?amshin turaren da yake yi, shi take ji haryanzu.
Ita dai ba gwanar nannauyan bacci ba, balle ta ce ko abin ya faru a zahiri tana bacci. Ko da tana gurin ?aisar da an taSa ta take tashi. Wasu lokutan ko tsayuwa aka yi a kanta, sai ta farka.
Sai dai ba ta gama razana ba, sai da ta ji ta ba a daidai ba gaba Waya. Da sauri ta tashi ta tafi banWaki, cikin damuwa. Sai dai ko da ta duba, ta sha mamakin abin da ta tarar. Abin da ya faru a mafarki ta gan shi a zahiri, azumin ya karye Wungurungum, kamar yadda ya gaya mata.

Ta jingina da bangon banWakin, al'amuran sun fara ba ta tsoro, ta yaya mutum zai biyo ta cikin mafarki, har ya aiwatar da abin da ya ce? Yaya aka yi ta iya biye masa haka, babu kunya babu jin nauyin sa, duk al'amarin ba?i ne a gare ta, kuma ta farka sun haWa ido yana murmushi, kamar dai ya san abin da ya faru.
Maganganun ?aisar su na ta ?ara tabatta ba ta tunanin Wan Adam ne Buzun nan. Jiki a matu?ar sanyaye, ta yi wanka.

Ko da ta fito ba ya Wakin, ba ta ko yi yin?urin gyaran Wakin ba, ta zauna zaman jiransa.

*

Mama ce take zaune a Waki, tana ba wa Suwaiba labarin yadda aka yi a gurin malamin nan.

"Ni anya ma kuwa Suwaiba, idan Jamila ta warke, ba gurinsa za mu koma ba, ya haWa muku maganin farin jini, tun da wannan karon na ga kamar maganin malam ?ayyabu bai yi ba".

Suwaiba ta ce "To mama, a bari dai a fara ganin yanayin jikin nata, amma na yi mamaki da aka ce wai aljani ta yi wa laifi. Ni na fara zargin Nana wallahi".

"Ai idan na faWa wasu lokutan haushi ku ke ji, a zo a sayo mini waken da zan soya a yi sadakar nan, anjima kaWan na je na sayo zakaran nan. Kar rana ta take an ce ?osan da zafinsa ake so a bayar"

Nasiru ya ce "Mama shi ?osan ne zai ba ta lafiya? Allah kawai za..

"Rufe mini baki kafin na ragargaje ka a gurin, dama yadda ka ke shishshige mata kafin ta tafi, duk ka ko yi miyagun halayen ta".

****
Nana ko karyawa ba ta yi ba, ba kuma ta da niyyar Wora komai, ta zauna zaman jiran dawowar sa.

Ba a yi mintuna talatin ba ya shigo, hannunsa ri?e da ledar buredi.

Ya ajiye mata a gabanta, bai yi magana ba zai juya, ta ri?o rigarsa ta tashi tsaye.

"Ina son na san waye kai? Me na aura? Na kasa fahimtar abubuwan da suke faruwa ka yi mini bayani" ta yi maganar numfashinta na fita sama-sama.

"Waye ni?" Ya yi maganar cike da mamaki, yana kallonta.

Ta ce "Eh shi nake son sani, ba na gane abubuwan da suke faruwa, ka yi mini bayanin waye kai? Daga ina ka ke? A ina danginka suke? Saboda na samu nutsuwar zuciya da kwanciyar hankali ka gaya mini"

"je ne sais pas (ban sani ba) ni ma haryanzu ban san waye ni ba"

Ta buWe baki za ta yi magana ya riga ta ta hanyar cewa "Ki yi mini magana cikin girmamawa, ki daina Waga mini murya"

"Ni ba ni da nufin Waga maka murya, amma ka yi mini bayani, ba na gane kan yadda al'amura suke faruwa, ta yaya za ka din ga bi na cikin mafarki kuma... Sai kuma ta yi shiru, ganin yana sauraren ta da mamaki a fuskar sa.

"Kuma me?"

"Ka din ga tsorata ni" ta ?arasa a sanyaye.

Ayshacool
"Ni kuma? Ta yaya zan bi ki mafarki? Mafarki ba gaske bane ai, kuma wani ba ya shiga baccin wani. Kuma me na yi na.." sai kuma ya yi shiru, ya kasa ci gaba maganganun da yake son yi, suka tsaya a iya ?irjinsa da ma?ogwaronsa.

A ?o?arin sa na ya yi maganar, kawai sai ya fara tari, ba tare da maganar ta fito ba. Sai kuma Nana ta rikice ta fara dana sanin abubuwan da ta gaya masa. A take ?aisar ya faWo mata. Ta san babu abin da ba zai iya aikatawa ba, duk domin ta amince da abin da yake so.

"Sannu, ko na baka ruwa?" Ya girgiza mata kai ya fita.

Kawai ta zauna ta tattara hannunta, ta zabga uban tagumi ta ma rasa mene ne abin yi, a tsakanin shi da ?aisar waye yake raina mata hankali.

Tun da take ta taso, ta fara ganin ?aisar a siffofi daban-daban, bai taSa yin?urin yin makamanciyar wannan ala?ar da ita ba, ko a farke ko kuma a bacci. Ita hasalima idan ana irin wannan zantukan har mamaki take yi, ba ta taSa jin wani abu mai kama da feelings ba, sai da aka yi mata wannan auren, ta fara rayuwa inuwa Waya da wannan Buzun.
Sai dai yadda mafarkin nata ya kasance, tamkar zahiri ba mafarki ba, tun da har ta farka ta tarar sakamakon abin da ya kwana a zahiri.
Guntun tsaki ta ja, ta tashi da ?yar ta fara gyaran Wakin.

Da ta gama ta shirya cikin hijjabi ta fito harabar gidan ba ta gan shi ba, kawai ta yi shigewar ta cikin gidan.

A falon gidan ta tarar da matar, tana mopping, Nana ta gaisheta. Ta Wan saki fuska ta amsa ta ce "Kwana biyu ba ki shigo ba"

Nana ta ce "Ba ni da lafiya ne, kawo na yi miki"

"A'a ba komai, kar ki damu zan goge" Nana ta ?arasa ta karSa ta ce "Bani zan goge. Masu aikin naki ba su dawo bane?"

"Wallahi tsoron su nake ji ne, tun da suka yi mini sata ne, su ka gudu sar?o?inmu na gold kaf suka sace. Shi yasa yanzu nake ?o?arin mu yi komai da kanmu falon ma sai a yi sati ba shara, tun da ba yara"

Nana ta karSi mopping, ta goge Wakin tsaf, sai dai ta din ga jin jikinta wani iri babu daWi.

Har su Tv duk Nana ta karkaWe ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login