Showing 57001 words to 60000 words out of 168002 words

Chapter 20 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

685

"Wallahi ba zan yarda ba, sai na kai ka gurin hukuma"

Nasiru da yake gefe ya ce "Allah sarki, Nana na can, da yanzu an ce ta hana mutane bacci" babu wanda ya saurari abin da Nasiru yake faWa, suka ci gaba da hayaniyar su.

****
Ko da Nana ta fito daga wanka, yana tsaye a ?ofar banWaki yana jiran ta, ta murguWa masa baki, za ta wuce ya ri?e ta yana murmushi ya ce "Meya faru?"

"Ni rabu da ni, ka hana ni bacci, ga ji?a kai sai na yi ciwon kai"

"Ba dai fi na gashi ki ka yi ba" ya yi maganar yana taSa gashin nata.

Nana ta kalle shi ta ce "To yi mini gori" bakinta ya sake sumbata yana murmushi.

Ta gyara shimfiWa ta hau, shi ma ya haye yana buWe bargo.

"Ni gaskiya katifar nan ta yi mana kaWan"

Ya ce "Ya za ayi?"

"Ka saukar mini daga kan katifa, ai na ga ma ba a Wakin nan ka ke kwana ba"

"Na gama yi miki amfani dole ki kore ni, ba inda zan je" ya yi maganar yana kwanciya"

Nana ta ce "Na shige su, idan muka futa sai ka yi gumm, sai na yi ta yi wa mutane bayanin ka na magana, ba kurma ba ne ba, amma daga ni sai kai ka yi ta wasu maganganu"

Tana jin sautin dariyar sa, cikin nutsuwar sa, da ta fi kama da Iyayi ya ce "Asma'u ke duniyata ce, tun da na farka a cikin wannan duniyar, nake jin tamkar nikaWai ne ba?o, Habu yana iya ?o?arin sa a kaina, amma ba ya wadatar da ni. Fatana da burina na yi na gama mafarkin nan na tashi, na koma ainihin rayuwata.
Ba na jin daWin komai a wannan rayuwar, sai ranar da na fara ganin ki, tare da yayar ki da suka zo kun je gidan mai magani, har ki ka faWi. Ina ganin ki na ji kamar ina da wata ala?a mai ?arfi da ke."

"Ni Win? Yanzu dama kai na gani ranar da muka je?"

"Mun haWu a gidan sarkin baka ma."

A zabure ta ce "Sayyid ka san sarkin baka?"

Ya ce "Na sani, Habu sun kai ni, ko zan iya tuna ni waye. Ban taSa maganar awanni biyu cikakkiya a rana ba, ban taSa shafe sati guda ina iya magana ba. Duk sai bayan zamanmu a guri guda. Ni na ce Habu ya biya mini sadakin auren ki, tun ranar da na ganki kullum sai na yi mafarki da ke. Shi yasa da mai gidan da muke yi wa gadi ya ce na sake ki, zai biya ni na na ji kamar na kashe shi. Na san ni mahaukaci ne, amma mahaukaci bai kyautu a kyautata rayuwar sa ba.
Ayshacool
Ke Duniyata ce, a tare da ke nake iya doguwar magana, na ci abinci, na daWe hankalina bai gushe ba. Ba na son kowa ya raSe ki, ko ya kula ki, saboda ina jin tsoron kar na buWe ido na ga ba kya kusa da ni."

Ya kwantar da kansa a ?irjinta ya ce "Ke ce Ahalina, kuma Duniyata. Ke Duniyata ce"

Haka ya din ga maimaitawa har muryarsa ta fara rawa, tamkar zai fashe da kuka.

Nana ta saka hannu ta zagaye bayansa, ta rintse idanunta, sai dai ta kasa magana a dalilin sanyi da ta fara ji.

Sauti ta fara ji na tasowar guguwa, ta buWe idonta, ta gansu a cikin sahara tsakiyar dare, sai hasken farin wata da ya gauraye ko ina.

Tsohon nan ta gani a tsaye a kan su, hannunsa ri?e da sandarsa.

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
"La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin" Haka Nana ta rintse idanunta tana maimaitawa. Tana jin yadda yake sauke numfashi a jejjere, yana ?ara ?an?ame ta.

Ta sake buWe idanunta a hankali, ta gansu still a cikin saharar nan.

Tamkar wani zai ?wace shi, haka ita ma ta rirri?e shi, tana ci gaba da karanto addu'oin da suka sauwwa?a a bakinta. Zuwa jimawa ta daina jin sanyin,? ta buWe idanunta ta gansu a cikin Waki, jikinta ya gaji saboda yadda ya sakar mata nauyin shi gaba Waya a jikinta.

"Sayyid" ta kira shi a hankali. Amma shiru, sai dai tana jin yadda cikin sa yake Wagawa yana sauka a hankali alamar bacci yake yi. Ta motsa a hankali ta gyara kwanciyarta ta ci gaba da shafa kansa, tana tofa masa addu'a.

Wani irin nishi ta ji ya yi, ya yin?ura a gigice ya tashi zaune cikin Waga murya ya ce "Sultan"

Cikin azama Nana ta tare shi, duk da ya fi ?arfinta, ta ri?e shi gam.
Haki yake yi tamkar wanda aka biyo ya ?wace da ?yar.

Ta yin?ura ta kunna fitilar Wakin, ta dawo ta zauna a kusa da shi. Cikin sanyin murya ta ce "Sayyid. Me ya faru? Waye Sultan Win?"

Hannunta ya kamo, ya Wora a saitin zuciyarsa, ya ri?e hannun nata yana sauke numfashi.

"Sannu" ya jinjina kai.

Ya sunkuyar da kansa ya yi shiru, fuskar sa na bayyanar da matsananciyar damuwa da tashin hankali. Ta sanya Waya hannun nata ta dafa shi ta ce "Sayyid mene ne?" Ya Wago da ?yar ya kalle ta, ya buWe baki zai yi magana amma sai ya kasa.

Can tamkar an jefo maganar bakinsa ya ce "Wani abu ne yake damun zuciyata, ban san mene ne ba, amma ya yi mini nauyi, kamar zan bar duniya"

Ta ce "Ya isa, ya isa haka ka yi shiru, in sha Allah babu wani abu, ka yi ha?uri" ta yi maganar tana shafa gadon bayansa. Ga mamakin ta kawai ta ga hawaye na gangarowa daga idanunsa. Rikicewa ta yi cikin tashin hankali ta ce "Sayyid mene ne? Meye ya saka ka kuka?"

Ya girgiza mata kai alamar bai sani ba.
Tun yana yi a hankali, kukan nasa ya din ga ?aruwa, har da jijjiga. Ganin ta rasa abin yi kawai ta fashe da kukan ita ma, ta hau taya shi.

Ya janye ta daga jikinsa, ya kwantar da ita a kan pillow, shi ma ya kwanta a gefen ta, yana son ya yi mata magana amma tilas ya ha?ura ya kasa ce mata uffan.

*

Hajiya Amina na kwance tana bacci, a kan carfet, a Wakin da take jinyar Shukura, ita kuma tana kan gadon marasa lafiya tana bacci, ta ji an kama hannunta. Ta yin?ura za ta yi magana amma wani irin jiri ya Webe ta daga kwancen da take, duk yadda ta so ta yi wani yin?uri ko ta yi magana, ta kasa sannu a hankali jikinta ya yi sanyi, ya mutu murus, daga nan hankalinta ya gushe baki Waya.

*

Fuska Wauke da damuwa, Nana take kallon inda ?aisar yake ta haWe-haWen maganunansa, ba tare da ya dubi inda ma Nanan take ba.

"?aisar"

"Na'am"

"Karo na farko zan ro?i alfarmarka"

"Ina jin ki" ya amsa ba tare da ya kalli inda take ba.

"Abu na farko ina ro?on ka, dan Allah ka yi ha?uri, ka saki ?afar mahaifina, abu na biyu dan Allah ka bar ni mu zauna lafiya da mijina, ka daina wahalar da mu har haka dan Allah ka yi ha?uri."

Ya ajiye abin da yake yi, ya dawo gaban Nana ya zauna, ya kalle ta ya ce "Na riga na rantse sai na hukunta mahaifinki, mijinki ya shiga gona ta, ya kwance ?ullin da na yi wa mahaifinki a ?afa, zai WanWana kuWarsa zan nuna masa gaba ma akwai gabanta"

Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Ta yaya ya kwance ?ullin da yake ?afar Baba?"

"Oho ya dai kwance, kuma zai ga abin da zan yi a kai, sannan ki daina yi mini magiya a kan abin da yake faruwa, wannan wani abu ne da ki ka amince da shi da kan ki, dan haka dole ki jure duk abin da za ki gani. Sauran tambayoyin da ki ke son yi mini kuma ki adana abin ki, dan amsa miki su, dai-dai yake da amincewa da sharuWana"

Cikin kuka Nana ta ce "Dan Allah ?aisar kar ka cutar da shi, shi kansa bai san wasu abubuwan na faruwa ba"

?aisar ya mi?e tare da cewa "Allah ko?"

"Da gaske, bai san su na faruwa ba, dan Allah ka bar mu, mu ji da ?alubalen rashin lafiyarsa, da rashin sanin waye shi"

Wata irin guguwa ce, ta gauraye cikin Libraryn, da sauri ?aisar ya buWe rigarsa, ya kare Nana.
Ayshacool
Tsohon nan ne ya bayyana a cikin libraryn, ya tsaya yana kallon Nana.

?aisar ya tsaya a gaban Nana ya ce "Me ya kawo ka inda nake? Da izinin wa ka shigo gurin nan?"

"Ba na bu?atar izini, kafin zuwa inda farauta ta yake"

?aisar ya ce "Kar ka ?etare layin da ka iya kawo, gagarumin tashin hankali da rashin jituwa tsakaninmu"

"Hannun agogo za ka mayar baya, ka gyaro Sarnar da ka tafka, idan kuwa ba zai gyaru ba, to ba zaka hana ni, aikata abin da na yi niyya ba".

"Ka aikata duk abin da ka so, amma ka taSa uwar gijiyata a wannan karon ?arshen rayuwarka zan kawo a doron Duniya"

Jin tarin da Nana ta yi ne, ya sanya ta farkawa.

A ?asa ta hango shi, maimakon kan katifa, yana wannan jijjigar da ya yi.

A rikice ta tashi ta nufe shi, tana ambaton Allah.

"Sayyid jikin ne dai?"

Wayarta ta Waukko, ta kunna karatun Alqur'ani, sannan ta Wakko bargo ta lulluSe shi da shi, ta zauna ta saka shi a gaba, ta zura masa ido cike da damuwa.

Har gefin Asuba, sannan Allah ya sanya ya daina wannan rawar sanyin.

*

An kai ruwa rana da Mama sosai da sosai, kafin ta amince ta ha?ura, amma da rantsuwa ta yi a kanz sai ta kai Gaddafi gurin 'yan sanda. Ana bata ha?uri shi kuma ya ce "Idan ba ta kai shi gurin 'yan sanda ba, ba Hudu mai ice ne ya haife ta ba" wato mahaifinta.

Duk da Baba yana cikin wannan tashin hankali, amma ya lura da sau?in da ya samu, game da ciwon da ?afarsa take yi masa tun jiya. Sai dai damuwa da tashin hankali ya sanya, bai mayar da hankali a hakan ba, ya karkata ga son kashe wutar da ta taso a gidansa.

****

Hajiya Amina na tsaye cikin matu?ar damuwa, Doctor Sharif ya ce "Hajiya ki yi ha?uri, amma a daren nan, za mu yi mata tiyata domin a ceto ta, da abin da yake cikinta.

"Kuma Doctor babu wata matsala, babanta ba ya kusa, haka ma mijinta"

"To Hajiya ai ba zamu bar ta haka a cikin ciwo ba, ki na kallo ba ta hayyacinta dole mu ceto ta da abin da za ta haifa".

Jiki a sanyaye Hajiya Amina ta karSi consent form, ta saka hannu, tana mamakin yadda suka kwanta lafiya ?alau da Shukura, har likitan da ya ganta da yamma, yana faWin za a sallame ta washegari, a ce lokaci Waya ta rikice, duk da ba a tara sani da Allah, kuma babu kusa babu nesa a gare shi.

Haka tana tsaye aka turo Shukura a kan gado, aka shiga da ita tiyata. Ta koma gefe jikinta a sanyaye tana ta adduo'i daban-daban, tana fatan Allah ya sa ba abin da Shukuran take faWa ne, zai faru ba, da take cewa tana ji a jikinta kamar mutuwa za ta yi, ba za ta rayu ba.

Shukura a hankali ta buWe idonta, tana kallon likitoci a kanta, ba ta san me suke yi mata ba, ita dai tana jin ana girgiza ta.

Anesthetic Win ya ce "Kin farka?" Ta lumshe idanunta ta buWe alamar eh.

"?aga ?afarki sama mu gani"

"Ba zan iya ba" ta faWa a hankali.

Ya ce "To yauwwa, suma ki ka yi ne, shi yasa saboda kar a rasa ki, a rasa babyn, ake yi miki tiyata ba zai yiwu mu ci gaba da barin ki da shi ba, sai mu rasa ku, kuma ba mu sani ba sarkinmu ne na gobe ko shugaban ?asa" ya yi maganar da sigar wasa.

Ta kasa dauke idanunta daga kan Doctor Sharif, da ya haWa gumi suke ta ?o?arin ciro jaririn.

****

?arfe bakwai da rabi, Nana ta dafa ruwa, ta kai masa banWaki.

Ta zo kansa ta ce "Sayyid taso ka watsa ruwa, za ka ji daWin jikinka sosai da sosai"

Ya tashi ya zauna, ya Wan jima a zaune, sannan ya yin?ura, ta bi bayansa ta raka shi ?ofar banWakin, ta mi?a masa zanin hannunta ta ce "Idan ka gama ka lulluSa sai ka fito" bai karSi zanin ba, ya kalle ta, sannan ya kalli banWakin.

A take ta gane Abin da yake nufi, amma wani irin nauyin sa take ji, saboda ba su yi sabon da za a ce ta sake ta saba da shi haka ba. Amma ganin ya ja ya tsaya, ya ?i gaba ya ?i baya, ya sanya ta wuce shi, ta shiga banWakin.

Bayan ta ya biyo, yana bin bango, saboda jirin da yake ji, Nana ta din ga sinne kai, tamkar ta gudu saboda tsananin kunyar da ta lulluSe ta.
Ayshacool
Kafin a gama wankan, ita ma sai da ya ji?a ta jalaf da ruwan, tamkar Wan ?aramin yaron goye. Tana zuba masa ruwa a jiki yake zabura, kamar zai shiWe, sai ya rirri?e ta. Da dabara a hankali ta ci gaba da zuba ruwan a jikinsa. Ta gama ta goge masa jikinsa su ka fito.

Da ta kalle shi, sai ta ji zuciyarta ta karaya, amma ta din ga dakewa, tana mazewa.

Ta soya dankalin Hausa da suke da shi, ta dafa shayi, ta zuba masa ta ajiye masa a gabansa.

"Ko na baka a baki?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

Ta yi murmushi, ta saka hannu tana ba shi.

Ya ?ura mata ido, ko ?iftawa ba ya yi, ya Wage girarsa yana ?o?arin buWe bakinsa, sai dai leSensa ya din ga rawa.

Nana ta ce "Ai na san maganar ta Wauke, ba sai ka yi mini magana ba, na fahimta" ya sake kallon ta da mamaki.

Ta ce "Ka manta ka ce mini ruhinka yana rayuwa a cikin nawa? Shi yasa nake fuskantar yin?urinka ko ba ka furta ba"

Murmushi ya yi yana jinjina kai, ya haWa tafukan hannayensa biyu, ya Wago su daidai ?irjinsa, =?O? ya risunar da kansa alamar ya gode sosai.

Nana ta sauke hannun ta ce "Babu godiya tsakanina da kai, duk da ban san wace irin rayuwa ka baro a baya ba, amma kula da kai dolena ne Sayyid"

Idanunsa suka cika da hawaye, ya kamo hannayenta, ya din ga sumbata, ciki da waje. Tausayinsa ya ?ara mamaye ilahirin jikinta, cikin dakiya ita ma ta sumbaci hannunsa, ta ci gaba da bashi abinci. Sai da ya ?oshi, sannan ta saka hau kan katifar ya jingina, ta rife masa ?afafuwan sa da bargo.
Ta tashi tana gyara Wakin, horn Win mota ta ji, ya Wago ya kalli Nana. Ta ce "Ka zauna kar ka tashi" ta saka Hijjabinta ta fita waje.

Matashin saurayin nan da take gani a gidan, mai tara samari su na kallon Ball ta gani a cikin mota. Ta ?arasa inda motar take ya sauke gilashin motar ta ce "Sannu da fitowa"

Ya ce "Yauwwa sannu"

"Ka ga ba ya jin daWi ne, ba shi da lafiya, bari na buWe maka"

Ya dubi Nana ya ce "Subhnallah me ya same shi?"

"ZazzaSi ne yake damun sa"

"Allah sarki, wata?ila malaria ce, unguwar akwai sauro sosai. Kin ga wani magani da likita ya bani Waya na sha, na ji daWin sa sosai da sosai, nake yawo da shi a mota. Ki ba shi ga paracetamol ma, zai ji daWin sa. Je ki kawai zan buWe ?ofar Allah ya sauwwa?e"

Nana ta saka hannu biyu ta karSa ta ce? "Na gode sosai da sosai"

"Ahh ba damuwa" Nana ta ji dadin mutuntawar da ya yi mata, duk da za su yi sa'anni da shi, amma ya yi mata karamci saSanin 'yar uwassa da ta wula?anta mata miji"

Ya sauka ya buWe gate Win ya fita, ya dawo ya rufe.

Nana na shiga Wakin, ta tarar da shi a tsakiyar Wakin a tsaye, yana muzurai.

"Ya na ganka a tsaye kuma? Ka kwnata ka huta, ga magani ma ya bayar ya ce a baka, sai ka samu ka sha"

Ya koma kan katifar, ya kwanta, ba tare da ya tanka mata ba.

*
Shukura ba ta san adadin lokacin da ta shafe ba ta hayyacinta ba.

A hankali ta buWe idonta, amma sai dai dishi-dishi take gani, tana jin maganganu, amma sama-sama, ba ta gane me ake cewa. Sai sannu a hankali idanunta suka washe ta gane komai.

Mummy ta taso tana faWin "Sannu Shukura ya jikin"

A wahale ta ce "Mummy"

"Na'am Shukura"

"Ina abin da na haifa?"

"Ki kwantar da hankalinki, an kai shi nursery ne, an saka shi kwalba"

Kawai Shukura ta fashe da kuka tana faWin "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ya sa ba mafarkina ne zai tabatta ba, dan Allah Mummy ni a karSo mini Wa na, a ciro shi daga kwalbar ba na so a dawo mini da jaririna ba na son wata kwalba"

Cikin damuwa Mummy ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Shukura yanka ki aka yi fa, ko awa uku ba a yi ba, sai kin yi wa kan ki illa? Mene ne dan an kai shi nursery?"

"Ni dai ba na so, ki ce su dawo mini da Wa na, wallahi zan tashi na je na karSo Wa na, idan ba za ki karSo mini Wa na ba"

"Shukura ina za ki tashi ki je, jikinki da ciwo meye haka ne?"

Iya ?arfinta take ?o?arin tashi da gaske, sai ta tashi sai dai ?afafuwanta suka ?i motsawa. Hargowar Shukura da kukanta, ya janyo hankalin ma'aikatan gurin. Suka haWu a kanta ana ba ta ha?uri, amma fafur ta ?i yin shiru. A dole aka yi mata allurai ta koma bacci.

Sosai yake tsala gudu a kan titin, yana fatan ya isa gari ya waye.
Ayshacool
Yana yi yana kallon inda ya kwantar da jaririn a gefensa, jikinsa kaca-kaca da ?azantar haihuwa da sauran jini, ga mahaifarsa a gefe ita ma kaca-kaca da jini a jiki.

Yaron baya iya kuka, sai kaWan-kaWan, bakinsa sai rawa yake yi, saboda azabar sanyin da yake ji.

Alhaji Zailani yana yi yana kallon yaron, sai dai ?irjinsa ya yi masa nauyi, ya rasa dalilin hakan. Yana matu?ar ?aunar Shukura, haka kurum ya din ga jin kamar bai kyauta mata ba. Amma da ya tuna girman bu?atar sa, na mamaye duniyar sa da samun duk abin da ya sanya a gaba, sai ya ?ara azama da ?ara gudun giyar motar.

Daji ne sosai da sosai, ya yi parking ya Waukko jaririn, ya fita ya nausa cikin duhun du?ununun dajin.
Yana tafe ya hango wuta tana ci, ya ?arasa gurin da wutar take ci. Malam Gambo ne sanye da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login