Showing 138001 words to 141000 words out of 168002 words

Chapter 47 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

656

a rufa shi, a ci gaba da addu'a, amma dole a nemo zoben nan, idan ba haka ba zai fita daga sahun Imams"
Sultan ya sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya yana kallon yadda yake bacci a kan gadon.


Sai da Nana ta shafe kwanaki huWu a gidan Hajara, ba a samu inda za ta zauna ba. Nana ma abin daya dame ta, sai Wawaniya suke faman yi da ita, ga shi tana tsoron kar su ?osa da ita, dan babu mai jurewa yau da kullum sai Ubangijin da ya halicci bawa.
Ranar kwana na huWu da yamma mai gidan ya dawo, Hajara ta kira Nana.

Bayan sun sake gaisawa ya ce "Malama Nana, wallahi ba a samu gida ba, sai dai ina tafe a hanya wata shawara ta faWo mini. Akwai wata 'yar uwar Babana a can wata unguwa, itakaWai take zaune a gidanta, kuma akwai Wakuna a gida, kuma ba mazauniya ba ce, tana fita sana'iinta. Sai dai fa mace mafaWaciya, tana da yawan faWa, ba wuya ta hasala. Ban sani ba ko za ki iya zama da ita?"

Cikin farin ciki Nana ta ce "Zan iya zama da ita, in dai ta amince"

"A'a dai ki yi tunani, mafaWaciya ce sosai, idan kin amince zan tafi na je na same ta a daren nan, na yi mata bayani"

Nana ta ce "Wallahi kar ka damu, zan iya zama da ita"

Ya ce "To Allah ya sa, zan ne yi mata magana, idan ya so ko kuWin hayar ne ita sai a bata" Nana ta yi ta masa godiya tana murna.
Har Nana ta yi bacci bai dawo ba, sai washegari da safe, bayan ta karya,? Hajara ta cewa Nana ta shirya, za su tafi can gidan matar.
Nana ta yi wanka ta shirya, suka fita suka hau abin hawa.
Hajara ta ce "Nana kamar kar ki tafi, kwana biyun nan har na saba da ke"

Nana ta yi murmushi ta ce "Nima haka, sai dai har Abada ba zan taSa daina yi muku godiya da fatan Alkhairi, ba dan ba ?aramin jihadi ku ka yi ba, ne ceton rayuwata"

"Ba komai, mu ma bamu san ta inda Allah zai taimake mu ba".

Sun yi tafiya mai Wan nisa, kafin su je unguwar da matar take.
Mijin Hajara ya sallami mai abin hawan, ya Wauki kayan Nana su ka shiga layin gidan.

A tsakar gida suka tarar da matar, ta cake Wauri tana ta lissafin kuWi. Ta amsa musu sallamar tana yi musu maraba.
Suka shiga Waya daga cikin Wakunanta. Ta kawo musu ruwa da lemo ta ajiye.
Cikin girmamawa Nana ta gaida matar.

Ta kalli mijin Hajara ta ce "Wannan ce yarinyar?"

Ya ce "Eh Nene"

"To a haka dai ta yi zubin nutsuwa, dan dai ka matsa ne, amma ni ba na son yayime-yayime na je na Waukko wadda za ta hana ni sukuni, shi yasa duk girman gidan nake zamana nikaWai abina.
Sannan zan fara zama da ita na wata Waya, idan ba ta da ma????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? tsala mu ci gaba da zama, idan akwai matsala na mayar mata da kuWinta ta tashi ta bani guri. Kuma wallahi dan ma dai kai ne, da ba zan yadda ba".

Nana cikin girmamawa ta ce "In sha Allah ba za ki same ni da matsala ba, in Allah ya yarda".

Nene ta ce "To Allah ya sa, bari na buWe Waya daga cikin Wakunan ta zaSa"

Mijin Hajara ya ce "?akunan a rufe, ai na san sun sha ?ura yanzu, ki yi ha?uri tun da akwai gyararru ki kwashe kayanki daga Waya ki ba ta. Kin ga Wakin da ba komai, sai an nemi labule, da sauran abubuwa". Haka ya takure Nene, ta bawa Waki Waya, mai Wauke da labulaye da carfet.
Nana ta din ga godiya, ta ce? "Saura kuWin hayar, nawa ne zan biya?"

"Ai na biya ta, ba wani abu in sha Allah, ki zauna kawai"

Nana ta ce "Ai da kuWi a gurina"

Hajara ta ce "Kar ki damu, ba wani abu ya biya, idan akwai wata matsala ko ba za ki iya zama ba, ki ce Nene ta kira mu a waya, in sha Allah babu wani abu"

Nana sai da ta yi hawayen murna, ta raka su har waje sannan ta dawo.
Ta tarar da Nene ta fito da wake fal za ta tsince. Nana ta lallaSa ta zauna a kan tabarmar ta ce "Kawo na tsince miki"

Nene ta ce "A'a ke da ki ke ba?uwa, yi zaman ki ki huta, kan Auwwalu ya dawo ya ce ina azabtar da ke, tun da ya ce ni masifaffiya ce". Ita Nana har ta gama zaman gidan ma, ba ta san sunansa ba.
Ta yi murmushi ta ce "A'a ba komai, dan Allah ki bani na taya ki, ai na ga waken da yawa, kuma daga zaune zan taya ki"
Ta dawo da robar waken tsakiyar su, ta kalli Nana ta ce "Nana ko?"

Nana ta jinjina kai ta ce "Eh"

"Ciki ne da ke haka ne?" Nana ta sunkuyar da kai tana tsince wake.

"Ke kuwa me ya yi miki zafi, ki ka baro ?asar ku da wannan tsohon ciki ki ka taho inda ba ki da kowa? Amma fa ki yi ha?uri da tambayoyina, kin san yanzu duniya babu gaskiya sosai"

Nana ta ce "Haka ne. Mijina Wan ?asar nan ne, nice 'yar Nigeria. Na zo neman danginsa ne a nan"

"Allah sarki, to a ina dangin nasa suke? Kuma shi yana ina" Nana ba ta son yayata halin da take ciki, ta fi son sai ta nutsu, ta ga kamun ludayin mutanen ?asar tukuna, kafin ta saki jiki, amma ga Nene ta saka ta a gaba da tambayoyi. Kafin ta ba ta amsa, Allah ya taimake ta, aka kira Nene a waya, hakan ya sanya ba su ci gaba da zancen ba.


Cikin tsananin tausayawa, yake bin matashin da kallo, saboda yadda duk ya fita daga hayyacinsa.
Cikin damuwa ya kira sunansa a hankali ya ce "Mahmudu" ya Wago idanunsa a galabaice, ya kalli wanda ya kira sunan nasa.
"Ka yi musu bayanin duk abin da ya faru, ka faWa musu iya gaskiyarka, ko Allah ya sanya su rabu da kai, wannan wahalar da ka ke yi ta isa haka?"
Murya a cunkushe ya ce "Me zan gaya musu? Me zan ce da ka ke tunanin idan na faWa za su yarda da ni?"

"Iya abin da ka sani Win zaka faWa"

"A tunaninka tsawon wannan lokacin, ba iya abin da na sani Win ba nake gaya musu? Sai dai akwai abin da ko za a kashe ni, ba zan furta ba"
"A'a Mahmudu, idan har za ka ci gaba da shiru da Soye wasu abubuwan, ba fa za a ?yale ka ba, za su ci gaba da azabtar da kai ne kawai a banza. Ni dai zan faWi abin da na sani"

Mahmudu ya ce "Ka kwana da sanin, ka na furta wani abu, to tabbas kai ma za ka tsinci kanka, a halin da nake ciki yanzu. Ka yi shiru mu bar komai a yadda yake. Rufe sirrin Imam wajibi ne, akwai abin da idan na furta, zai iya janyo asarar rayuka ba Waya ba ba biyu ba, in dai wahala ce na san Wayan biyu ne, ko na mutu ko ta wuce. Abu Waya nake so da kai, shi ne; dan Allah Ashiru, ka binciko a wani hali yake ciki? Tun da muka baro Nigeria, ba a haWa mu a mota Waya ba ma, ban san ina aka yi da shi ba"
Ashiru ya ce "Kai wannan fa babban aiki ne, tun Satansa fa, ba a bari labarin ma ya fita ba, balle a sanya ran jin halin da ake ciki yanzu, amma dai zai Wan ?yan?yasa a Soye, na ga ko za a samu wani bayani. Sannan ina ?ara neman afuwarka a kan abin da ya faru"

"Babu komai kar ka damu, an saki sauran ko? Su Sulei"

"Eh an sake su, ai tun da suka fuskanci, ba su ma san a kan me ake binciken ba, an sake su amma fa an killace su"

"Shikenan tashi ka je, kar a fahimci wani abu" Haka Ashiru ya tashi ya tafi yana waiwayen sa.

*

Sannu a hankali take tafiya, yana zaune a cikin mota yana hangen ta, ta tsallako titi, ta nufo motarsa tana murmushi.
Ta buWe motar ta shiga ta ce "Yaya Abba me ka ke jira a titin ne haka?"

Ya lumshe idanunsa, jin yadda ?amshin turaren jikinta, ya gauraye motar baki Waya. Ya ce "Wa zan jira ban da ?anwata, kwana biyu ban gan ki ba, da gida zan bi ki ma, to sai na ji tsoron kar na je ko ki na da ba?o, ban sanar da ke zan zo ba. Kawai na tsaya a nan na ce bari na jira fitowar ki"

Ta yi murmushi ta ce "Ko akwai ba?o, ba dolena na sallame shi na saurari yayana ba, kuma wani ba?i zan yi da safe haka?. To me ma zan samu ne?" Ta yi maganar tana laluba motar.

Ya yi dariya ya ce "Laluba ki Wauki duk abin da ki ke so" ta yi dariya ta ce "Dan ka san ba ka ajiye komai ba ko? Mu je kar Mummy ta yi ta jira na"

Ya ce "Ok" ya fara tu?a motar a hankali. Yana tu?i yana satar kallon Jamila, wani irin kyau take ?arawa a idanunsa kullum. Kullum ?ara shiga ransa take yi, ga shi ya kasa fitowa ya sanar mata da ainihin abin da yake cikin zuciyarsa. Duk wasu alamu da zai nuna mata sonta yake yi, ya yi amma ya kasa gaya mata baki da baki. Su na daf da shiga layin gidan ya tsaya ya ce "?anwata"

"Na'am Yaya Abba"

"Ina son za mu yi wata magana da ke, amma maybe sai na dawo tukuna"

Ta yi murmushi tare da gyara zaman mayafinta, ta ce "To shikenan babu laifi, a dawo lafiya"

"Allah ya sa, ki kula mini da kan ki Please, zan kira ki idan na je kasuwa"

Ta ce "To, ka sayo mini aya mai sukari a kasuwa"

Yayi dariya ya ce "Aya kawai?"

"Eh ita kawai"

"To an gama ranki ya daWe" ta fita daga motar tana Waga masa hannu"

Da ta shiga cikin gida,ba ta tarar da Hajiya Sa'a a falo na, dan haka ta bi ta bedroom.
Ta tarar tana wanka, ta nemi guri ta zauna tana danna wayarta. Can Hajiya Sa'a ta fito daga ita sai towel. Jamila ta kalle ta ta kawar da kai.

"Jamila har na fitar da ran za ki zo ai"

"Ba na jin daWi ne, shi yasa da kamar ma ba zan zo ba fa"

"Eyya sannu, bari na shirya ki raka ni mu je na duba Fatuhu"

Jamila ta ce "Tom"
Hajiya Sa'a ta zauna a kusa da Jamila, ta Wan ri?o hannunta ta ce "Daughter wai ke haryanzu ba za ki waye ki faso gari ba? Ina ta saita ki a hanya kin ?i yarda ki shiga layi"

Jamila ta Wan Sata fuska tana zame hannunta ta ce "Gaskiya ni Mummy ba na so, ni me zan tsinta a jikin mace 'yar uwata, ni abin ma bai yi mini tsari ba sam wallahi"

Ta yi murmushi ta sake matsawa kusa da Jamila ta ce "Ai da gwaji jirgin sama ma ya tashi Jamila, da za ni jarraba da kin gane abin da nake nufi. Shi ne za ki yi babu ruwanki da damuwa da aure, ko tashin hankalin yin planing saboda Waukar ciki. Kuma...

"Ni dai gaskiya Mummy ba na so, ni ban ga abin da mace 'yar uwata, ni abin ma bai yi mini tsari ba sam wallahi"
Ta yi murmushi ta sake matsawa kusa da Jamila ta ce "Ai da gwaji jirgin sama ma ya tashi Jamila, da za ni jarraba da kin gane abin da nake nufi. Shi ne za ki yi babu ruwanki da damuwa da aure, ko tashin hankalin yin planing saboda Waukar ciki. Kuma...

"Ni dai gaskiya Mummy ba na so, ni ban ga abin da mace za ta tsinana mini ba, ni bai ma yi mini tsari ba gaba Waya gaskiya. Ba gara na bi maza ba"

Hajiya Sa'a ta kwashe da dariya, ta ce "Yaro man kaza, ai shikenan Daughter, bari na shirya mu fita". A gaban Jamila ta gama shirinta, ba tare da jin nauyin abin da ta tunkari Jamilan da shi ba, ta gama suka fita.

Umman Fadila ce take kallonta a tsanake, bayan ta gama yi mata komai za ta tafi. "Fadila"

"Na'am Umma"

"Na san yanzu da da ba Waya ba ne ba, amma ko yaya Wan abin da ki ke da shi idan ya samu, ko abinci ko kuWi, ki din ga bayar da sadaka, da nufin Ubangiji Allah ya kawo muku Wauki,ya sassauta muku wannan yanayin da ku ka tsinci kan ku a ciki"
Fadila ta jinjina kai ta ce "In sha Allah"
"Tun kwanank da kawunki, ya zo ya duba mijinki, ya kira ni yake mitar, kun tare ku na maganin Asibiti, kun ?i mayar da hankali ku yi na gargajiya. Na ce masa mijin naki ne Wan a?ida, kuma ke na haifa ba shi ba, balle na yi masa dole. Amma nima hankalina ya fara karkata ga a yi na hausan, mijinki mutumin kirki ne, ba zan manta halaccinsa a gare mu ba, dan haka na bayar da kuWi a yi saukar Alqur'ani, da fatan Ubangiji Allah ya yaye masa koma mene ne, tun da shi Alqur'ani waraka ne. Ki yawaita karanta masa, ko ki kunna ya saurara, ko ki din ga busa wa a abincinsa ko abin shan sa.
Ba mu san a inda za a dace ba, wannan abu ya ?i ci ya ?i cinyewa, na Asibitin ba wani haske da ake gani, idan hagu ta ?i ai sai a koma dama ko?"

Fadila ta ce "Haka ne Umma, in sha Allah, zan yi duk abin da ki ka ce, kuma addu'a mu na yin ta sosai, ina yi masa. Sai dai kin san lamarin Ubangiji ba a yi masa dole, duk addu'arka sai lokacin yankewar abu ya yi tukuna".
Umma ta ce "Haka ne, amma hakan ba ya nufin a sare, a ce an ha?ura gaba Waya ba za a yi ba" Sosai Fadila take jin daWin rarrashi da nasihar da Umma take yi mata a duk lokacin da ta zo gidan.
Ko da su Hajiya Sa'a suka je gidan Alhaji Fatuhu, Alhaji Zailani yana gidan. Yana sashen Alhaji Fatuhu tare.

Alhaji Zailani ya din ga kallon Jamila, yana ganin kamar ya santa, amma ya manta a inda ya san fuskarta.
Suka gaisa Hajiya Sa'a ta kalli Fatuhu ta ce "Yaya ya jikin naka?"

Ya jinjina kai ya ce "Alhamdillah"

"Ka na samun sau?i, ko dai haryanzu babu afuwa?"

Ya yi murmushi ya ce "Da sau?i" Daga haka suka koma hira da ita da Alhaji Zailani, tamkar ba dubiya su ka zo ba, bar sai da abin ya ba wa Jamila mamaki. Sun jima sannan su ka shiga suka gaisa da matansa suka tafi.

Su na tafe a hanya Jamila ta ce "Mummy, mara lafiyar nan shi ne wanda Wan sa ya mutu kwanaki ko? Yaran da Nana take koyarwa a makaranta"

"Eh shi ne"

"Allah sarki, to shi wannan Alhaji Zailanin, ko shi ne a can quaters Win bayan makarantar nan na ?ofar famfo?"

Hajiya Sa'a ta kalle ta ta ce "Ya aka yi ki ka san shi?"

"A'a na tambaya ne dai kawai, kenan shi ma Nana ta yi aiki a gidansa, yana da 'ya Shukura ko?" Hajiya Sa'a ta jinjina kai tana kallon Jamila.

"To ai da Nanan gidanmu zai aura, ba a yi ba, aka yi aurenta da wannan Buzun, lokaci Waya kawai ya fito ya ce wai zai aure ta"

Shiru Hajiya Sa'a ta yi tana kallon Jamila, ta san abu ne mawuyaci a ce haka kurum Alhaji Zailani ya ce zai auri yarinyar da ta fito daga gida kamar na su Nana, da ?yar idan ba ya san sirrin da ke tattare da Nanan ba. A take gabanta ya faWi, dan kuwa ko me za a yi ba za ta taSa barin Alhaji Zailani ya riga ta amfani da jinin Nana ba"

Jamila ta ce "Mummy ya na ji kin yi shiru ne?"

Ta girgiza kai ta ce "Babu komai Jamila, dole mu nemo Nana ne duk inda ta shiga"

Jamila ta ce "Saboda me?"

"Saboda ?ungiya, za ta iya neman ki kawo jinin mafi kusanci da ke, a kowane lokaci!

Ayshercool
08081012143
Jamila a ranta ta ce "Ni kuwa zan ga abin da ya ture wa Buzu naWi, zan ga abin da zai faru idan na bijirewa bu?atar ?ungiyar"
Jamila ta numfasa ta ce "Mummy, dan Allah tambayar ki zan yi"

"Ina jin ki"

"Wai dan Allah, ya aka yi ki ka shiga ?ungiyar nan?"

Hajiya Sa'a ta kalli Jamila, sannan ta mayar da hankalinta kan tu?in da take yi tana murmushi. Ta ce "Dogon labari ne Jamila, amma me yasa ki ka tambaye ni?"

"Ina son na ji tarihin gwagwarmayar ki ne, ko nima zan daure na yi koyi da jarumtar ki, haryanzu wasu lokutan zuciyata tana rawa ne a kan lamarin"

"Ai na ga alama kam. Jamila na sha gaya miki, muddin ki na son cimma abin da ki ke buri a rayuwa, babu ruwanki da kowa kan ki kawai za ki din ga dubawa.
Na tashi a gidanmu bamu da komai, babata da babar Fatuhu, su ne ?anana a matan gidan, kamar dai yanayin rayuwar gidanku, a haife ka, ba a damu da Wawainiyarka ba.
Manyan yayyenmu babu ruwansu da mu, saboda iyayen su mata sun cusa musu a?idar ?in iyayenmu. Babanmu ya mutu shi ma saboda bai bar komai ba, babu wanda ya damu da mu.
Yayyenmu iyayensu kadai suke taimako da ?annen su, mu kuma namu iyayen ke ta fafutuka da wahala.
Fatuhu ya yi ta faWi tashi da rayuwarsa, da ta mahaifiyarsa, sai dai yana tunawa da ni.
Zailani tsohon saurayina ne, da rashin abin yi ya hana mu yin aure da shi.
Ya shiga makaranta, bisa tallafin karatu, a can ya samo mana wannan ?ungiyar.
Shi kuma lokacin Fatuhu ya fara zuwa kasuwa, ni kuma na riga na yi aure.
Zailani ya gaza jan Fatuhu ?ungiya, saboda mutum ne mai tsantseni da ra'ayin ri?au. Ni kuma har a lokacin mijin da nake aure, ba shi da komai ba na samun irin rayuwar da nake so. Sannu a hankali na ci gaba da hulWa da Zailani ya kai ni ?ungiya, ya zamana ba na rasa kuWin kashewa dai.
Fatuhu kuma ya ja Zailani kasuwa, suke kasuwanci tare, sai dai duk da tasirn ?ungiya, Zailani ya kasa tara abin da Fatuhu yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login