Showing 72001 words to 75000 words out of 168002 words

Chapter 25 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

632

Imrana ya ?arasa hankaWa ?ofar ya shiga, Nasiru ya bi bayansa.

Nasiru ya ce "Ga mijin Nanan nan" ya yi maganar yana nu na masa Buzu.

Imran ya ?are masa kallo, ya ce "Ikon Allah, kai ka auri Nana? Tana ina?" Sayyid ya yi shiru yana kallon Imrana.

"Malam magana nake yi, ko kurma ne? Ina take?"

Nasiru ya ce "Kamar fa ba ya magana, amma Nanan tana cikin Wakin nan"

"Dan Allah ji wula?anci, Wakin mai gadi, ba ta samun arzikin a ajiye ta a gida ba ma, sai Wakin daga shi waje, koma mene ne ya zo ya afka mata"

Nana tun tana banWaki take jiwo, kamar muryar Imran, amma ta kawar da tunanin, a ganinta mai zai kawo shi yanzu.

Ta fito daga banWakin ya shigo, Nana ta zabura ta ce "Imrana" sai kuma ta tsaya da tuna halin Buzu a kan kishin tsiya.
Ayshacool
"Ke ashe ba ki da hankali? Ki ka zauna aka aura miki mutum kawai ki ka biyo shi yawon gadi? Gidan babanki ba mamora gidan miji ma haka? To wallahi sai kin bar gidan nan, sako hijjabinki mu tafi"

"Imarana mu tafi mu je ina?"

"Ko ma ina ne. Amma wallahi ba za ki zauna a gurin nan ba. Haka zamu zauna babu ci gaba?"

"To ka zauna mana, ka sha ruwa ka ci abinci, sai mu yi magana. Mama ma ta yi mini aike su Adda Saude sun zo...

"Dalla rufe mini baki, ina ruwana da wata? Addar wofi da can ba su zo ba sai yanzu. Ki Waukko hijjabinki mu tafi daga nan har human rights, na san biyayya kawai ki ka yi wa Baba ki ka auri mutumin nan, tun da dama ke ba sanin ciwon kanki ki ka yi ba"

Nana ta yi shiru, tana kallon in da Sayyid yake tsaye, ya tsare ta da ido. Tsoro take ji kar Sayyid ya yi wani abun da zai tunzura Imran, dan ta san ko zai kashe shi ba zai yi shiru ba.

"Imran na gode da ziyara, da kuma soyayyar da ka ke nuna mini. Amma ka yi ha?uri ina son aurena"

Wani irin takaici ya kama Imran ya ce "Nana me za ki zauna ki yi a shago, Wakin nan meye marabarsa da shago? Na san zaman gidanm ne ba kya so, ba can za ki koma ba. Harkoki sun fara buWe mini, karatu zan mayar da ke, kyakyawar rayuwa nake so na ga kin yi"

Ta sake kallon Buzu, da ya zubo mata idanunsa, Imran ya waiwaya ya ga abin da take kallo.

Sayyid ya shigo cikin takunsa na kamala da nutsuwa.

Ya sauke takunkumin fuskar sa, ya sakar wa Imrana murmushi, ya ce "Kun yi kama sosai, da alama ku na da ala?a sosai" ya yi maganar yana mi?a wa Imran hannu su gaisa.

"Ba zan gaisa da kai ba, ?anwata za ka sakar mini, Nasiru ya gaya mini duk wani abin da ya sani. Ni ban ji na gamsu da wannan auren ba ko kaWan. Ya za a yi sama ta ka a aura miki mutumin da ba ?abilarmu ba, babu wani dogon bincike. Ni jikina yana bani wani abu, ni ban yarda da auren nan ba gaskiya."

"Nima na fuskanci akwai sharuWWan da ban cika ba, aka yi wannan auren. Amma ko me za a yi mini, ba zan iya rabuwa da ita ba, tana Wauke da ruhina a jikinta. Idan ka raba ni da ita, ni ya zan yi? Zan kula da ita, ka daina raina inda Allah ya ?addara zamana da ita, ba ka san gobe ba"

Imrana ji yake kamar ya mangare Buzun nan ya huta, haka kurum ya ji bai yi masa ba. Kuma ya san wannan kyawun ne ya ruWi Nana, har take cewa ita ba za ta rabu da shi ba.

Ya sake kallon Nana ya ce "Kin zaSi zama ko Nana?"

Idonta fal hawaye ta ce "Ka yi ha?uri Imran, Allah ne ya haWa ?addarorinmu, ba komai zan iya yi maka bayani ba, amma ina son aurena. Sayyid na bu?ata ta a rayuwarsa".

Imran ya haWiye wata irin ?wallar takaici. Ya zura hannu a jakarsa, ya ?irgo kuWi, ya tako gaban Nana, ya kamo hannunta ya saka mata ya ce "Ga wannan babu yawa, cikin abin da nake tarawa ne, domin na dawo gida na inganta rayuwar ki. Dama Saboda ke na dawo, daga nan ko gida ba zan kma ba, zan tafi inda na fito. Kai kuma tun da ta zaSi zama da kai, idan ka ci amana na bar ka da mai hudowar rana da faWuwar ta"

Ras Sayyid ya ji gabansa ya faWi, ya ji maganar Imran ta yi masa nauyi da yawa.

Ya kalli Nasiru ya ce "Mu tafi"

Nana da tuni hawaye ya wanke mata fuska ta ce "Imrana ba zaSarsa na yi a kan ka ba....

"Shhh ba sai kin yi mini bayani ba ai, tun da ki na farin ciki da auren ki Alhamdilillah" ya juya zai fita ta sake cewa "Ka bani lambar wayar ka, da zan din ga kiran ka a waya" bai waiwayo ba ya girgiza kai, ya ce "Babu bu?ata"

Daga bayansa, yanayin yadda ya kai hannu fuskarsa, Ya sanya Nana gane Imran kuka yake yi. Sakin kuWin hannunta ta yi a ?asa ta dur?ushe a gurin ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ita ma.

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
"Jiki Alhamdilillah " ta yi maganar tana mayar da hankalinta, kan Hajiya Amina.

"Mummy, wai dan Allah lokacin da aka yi mini tiyata, da a ka fito da ni, an baki babyn a hannunki kin gani"

Hajiya Amina ta ce "Sau nawa zan yi miki bayani Shukura, ke kaWai aka fito da ke, ba a bani jaririn ba. Doctor Sharif ya ce na Wan jira, jaririn ne ake fama, ko ba bu wadatacciyar iska ko me, oho maganganun su na likitoci. Na dawo Waki gurin ki, ya shigo ya ce mini, an kai babyn Nursery, da safe na je na gan shi"

Alhaji Zailani ya yi gyaran murya ya ce "Shukura, duk wani abu da za ki yi, abin da ya faru ya faru, ba za ki yi jayayya da ikon Allah ba. Kamata ya yi ki gode wa Allah, da ya baki lafiya. In dai da rai da lafiya, Allah zai baki wani mai amfani. Yanzu lafiyar ki muke bu?ata, wannan damuwar ba ta dace da ke ba. Kin rasa babynki, nima ba zan so rasa tawa babyn ba, Please ki yi tawakalli na san kin sha wahala a kan cikin nan, amma ki yi ha?uri"

Shiru Shukura ta yi, zuciyar ta fal wasi-wasi. Ta ?ara ?aimi gurin ya?ar mummunan tunanin da yake ta yi mata yawo a zuciya, ta hanyar kawar da batun mafarki da ta san ba gaskiya ba ne ba.
Duk mahaifiyarsu ta rasu, amma ba su tashi da zafin maraici ba, Alhaji Zailani ya yi aiki tu?uru a kan rayuwar su, Hajiya Amina ma kuma ba ta taSa yi musu mugunta ba, ta ri?e su da gaske tamkar 'ya'yanta. Saboda haka take ganin tamkar zuciyarta ba ta yi mata adalci ba. Amma fafur take jin ?iyayyar mahaifin nata a cikin zuciyarta, ta kuma kasa yarda da cewa Wan ta mutuwa ya yi ta ha?i?a, ba wani abin ne ya faru ba.

****

Kwana biyu Nana ta samu sau?in jikinta, jikinta ya Wan yi ?wari babu zazzaSin. Sai dai abinci ne ba ya ciwuwa ta daWin rai.

Ta saka Sayyida a gaba, a kan lallai sai ta yi wa gashinsa kitso, ta gaji da ganin kan a haka. Yana kwance a kan cinyarta, ta saka kibiya tana tsaga gashin nasa. Ta ce "Sayyid kishi nake da gashin nan naka, gaskiya aske shi zan yi, ya za ayi ina matarka a ce ka fi ni gashi?"

Ya yi dariya ya ci gaba da kallon da yake yi da wayarta. Ta yi guda biyu ta ce "To gyara, a yi na can Sangaren"

Ya girgiza kai ya ce "Ki ?yale ni"

Ta ce "A'a sai an ?arasa"

Fafur ya ?i gyarawa, ya ce shi fa kitson da zafi.

"Dan Allah ka yi ha?uri mu ?arasa, haba Shugaba ba ka ga yadda kitson nan ya yi kyau ba. Yauwwa nawan" ya Wago kansa ya harare ta. Ta sakar masa murmushi tana lumshe masa ido.
Ya gyara kwanciyar, ta ci gaba da kitsa gashin nasa, mai matu?ar santsi da laushi.

Babu tsammanni aka bankaWo labulen Wakin, sai da Nana ta razana, a hankali ya Waga kai ya kalli ?ofar.

Siyama suka gani a tsaye, Kunya ta kama Nana,yanayin da ta tarar da su. Shi kansa dogon wando kawai a jikinsa, ya Wora kansa a kan cinyar Nana, tana yi masa kitso.

"Amm dama Mami ce ta ce na zo na duba, ko Yusra ta zo ba mu ganta ba da ma. Amma shikenan" Ta saki labulen a hankali ta ja da baya, saboda yadda jikinta ya yi sanyi.

Kamar babu abin da ya faru, ya ci gaba da kallon wayarsa.

" Ya jikinki ya yi sanyi? Me ya faru?"

"Ba komai" ta furta a hankali.

Ya juyo sosai ya kalle ta, sai kuma ya fasa maganar da ya yi niyya, ya sake gyara kwanciyar sa.

Dannewa kawai Nana ta yi, amma sai da ta ji tamkar ta Wura wa Siyama ashar, saboda kawai su na masu gadi, ya ba ta damar ta shigo musu Waki, ba bu izini. Danne fushin ta ta yi, saboda kar ta saka shi a damuwa, amma tana ji a ranta wataran sai ta zagi Siyama.

Da yamma, Nana ta yi kwalliya cikin doguwar rigar material mai taushi, da hula. Ta fesa turare sannan ta Wora girkin dare, sannan ta kunna turaren wuta a Wakin.
Neman guri ya yi ya zauna a Wakin ya ?i fita, sai aikin kallonta kawai da yake yi.

"Shugaba, ba zaka fita shan shayin ba ne?"

Ya yi dariya ya ce "Kin yi kyau sosai da sosai, ba zan fita ba"

Ta sake cewa "Ka ga yadda ka yi kyau da kitson nan kuwa? Zo ka ga"

Ya yin?ura ya taso, ya zo ya tsaya a gaban ta, ta nuna masa mudubi ta ce "Kalli yadda ka yi kyau fa"

Ya shafa kansa ya ce "Na zama kamar mace"

Ta yi dariya ta ce "Ka yi mini kyau sosai a haka, dama nikaWai ya dace na ga ka yi kyau".

Ya sunkuyo ya yi mata kiss a goshinta.
Ayshacool
Cikin dariya ta ce "Ni idan ka na yi mini wannan abun, kunya ka ke bani"

Ya ce "Wanne?"

"Ko wanne" ya ?ara tsare ta da ido, da sai da ya sanya ta sunkuyar da kanta saboda kunya.

"To matsa na wuce"

"A'a kirana fa ki ka yi"

Ya yi maganar yana haWa bakinsa da nata.

Bayan ya cika ta, ta sunkuyar da kanta tana jin kunya. Ji ta yi jikinta ya fara sanyi, ?irjinta yana bugawa, ta kalle shi ta ga fara'ar fuskarsa ta kau, ya haWe rai. A tsorace ta Wan ja jikinta, tana tunanin me ta yi masa. Tana kallon mudubin ta ga duhu ya gauraye Wakin sai iya wannan tsohon ta iya gani a cikin mudubin a tsaye, sai dai a wannan karon ci yake yi da wuta.
Tattara nutsuwarta ta yi, ta fara Addu'a a cikin zuciyarta, ta waiwayo ta kalle shi.

Ta ga fuskar sa Wauke da murmushi.

Ya mi?o hannunsa zai taSa ta, ta ri?e hannunsa, ta yi yin?urin kallon idonsa amma ta kasa, ta ji tamkar zuciyarta za ta buWe.

"Waye kai?"

Ya amsa da "Mijinki mana"

Ta yi murmushi ta ce "Ba Sayyid ba ne? Ai na riga na ganka. Me yasa ka zaSi muzgunawa rayuwata ne? Da ina zargin ko ?aisar ne, amma na fara fahimtar kai daban shi daban. Mece ce manufarka a kaina? Me ka ke bu?ata?"



AYSHERCOOL
08081012143
Ayshacool
Wata irin dariya ya saki, ya ce "Har kin yi ?warin da ki ka daina razana da ganina kenan. Haka nake so fansa zan Wauka, yanzu ne lokacin da ya dace na Wauki fansata"

"Wani laifi na aikata maka da ka ke i?rarin Waukar fansa a kaina"

Ba tare da tsammani ba, ya sha?e ta, ya Waga ta ya yi jifa da ita, ta bugu da jikin wardrobe ta faWi.

?akin ya gauraye da matsanancin duhu, ta ri?e wuyanta tana numfarfashi cikin yanayi mai kama da Wimuwa da kuma suma.

Ta daWe a haka kan ta ji kamar daga sama muryar Sayyid.

"Rayuwata bacci kuma daf da magariba a ?asa? Ga abincinki ya fara ?onewa"
Nana ta Waga kai ta kalle shi suka haWa ido, amma ba ta ji komai ba. Ta tashi da ?yar ta ji mararta ta ?ulle, ga hannunta da ta bugu. Amma ta daure ta kashe gas din, ta shiga yin alwala.

Abubuwa da dama su ka zo zuciyarta, tabbas wannan sabon ?alubale ne a gare ta. Muddin zai cigaba da fita daga hayyacinsa yana yi mata haka, to tana tsoron wataran ya yi mata illa.

Haka kurum yake jin sa cikin farin ciki, sai dai lokaci Waya ya lura ita ba ta cikin walwala.

Su na cin abinci, ya Wan shafa cinyarta. Ta farga ta kalle shi.

Ya ce "Ba kya cin abinci mene ne?"

Ta yi murmushi ta ce "Lafiya ?alau, Abincin ne ba na so"

Cikin damuwa ya ce "Na sayo miki buredi za ki ci? Ko ?os"

"A'a zan ci wannan Win" da ?yar ta tilasta kanta, ta ci.

Yanayin yadda yake ta bin ta da ido, ya sanya ta san akwai abin da yake so, sai dai a Wan tsorace take. Haka ta ci gaba da addu'oi da neman Waukin Ubangiji.

Duk da haryanzu tana jin nauyin sa, amma ta shirya cikin kayan baccinta na gwanjo, da Ummi ta ba ta ta shafa turare. Sai dai zuciyarta gaba Waya a tsinke take.

Kwanciyarta babu jimawa, ya zo ya kwanta shi ma.

"Rayuwata duk kin rage walwala"

Ta Wan ja numfashi ta ce "'yan kwanakin nan, baki ya buWe, Ubangiji Allah ya Worar da lafiya"

"Amin ma vie. Ina jin daWin haka sosai"

"Saura kuma, Ubangiji Allah ya sanya ka tuna waye kai. Hankalina zai fi kwanciya"

Ya Wan yi shiru ya ce "Ina wannan ?o?arin, ji nake kamar abin ya fi ?arfina. Amma ko da nan gaba, idan ban tuna waye ni ba, ki nuna wa Wa na su Habu a matsayin dangina, tun da ku kaWai na sani" Ya yi maganar muryarsa na rawa.

"Shikenan mu bar wannan maganar." Ya yi shiru bai kuma magana ba.

"Sayyid fushi ka yi ne?"

"A'a ban yi fushi ba"

Ta din ga shafa kansa zuwa bayansa, sai dai daga ?o?arin rarrashin sa, ya fara ?o?arin zarcewa.

A hankali ta fara jin wannan ?amshin turaren, yana ratsa kafofin hancinta.

"Sayyid ba ka jin wani ?amshin turare?"

"Ina ji a jikinki"

"A'a ji nake kamar ba a Wakinmu muke ba"

Ya yi dariya, ya cika ta ya ce "Ba sai kin yi mini wayo ba, na ?yale ki" Ya Wan ja jikisa ya koma gefe, yana ajiyar zuciya. Ta Wora hannunta a kan nasa ta ce "Ba wayo zan yi maka ba, ai ka san ba na gudun ka."

"Kar ki damu, ki yi bacci" ya Wora kanta a ?irjinsa yana shafa bayanta.

*

Shukura ji take yi, tamkar za ta haukace, sai kokawa take da sashe daban-daban na ?wa?walwarta, domin samawa kanta nutsuwa.
Gari ya tsit amma ita sai kaiwa take yi tana komowa a cikin Waki, tamkar mai jiran sa?on wani abun.

Ta zauna ta haWa kai da gwiwa ta yi tagumi.
Ta sake tashi tsaye, ta tafi bakin taga ta tsaya tana kallon waje. Ta ?udurce a ranta, sai ta tuntuSi doctor Sharif ta ji mene ne ya kashe mata Wa? Haryanzu ta kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali.

Alhaji Fatuhu kuwa, ?arfin hali kawai yake yi, ji yake tamkar an daddane rayuwarsa da jikinaa gaba Waya. Babu abin da yake yi masa daWi, ya daina jin daWin komai, tamkar ya fasa ihu ko zai ji sanyi a ransa.
?arfin hali ya yi gurin sanya Fadila farin ciki, har ya samu ta yi bacci, tun da ta yi bacci ya raba ta da jikinsa a hankali, ya tashi zaune ya rafka tagumi ya din ga jin tamkar ana buga masa abu mai nauyi a kansa.

Ya shiga banWaki ya yi wanka, ya yi alwala ya zo ya tayar da salla, amma tunani da wasi-wasi ya mamaye shi, ya kasa nutsuwa a cikin salla. Ya din rafkanuwa. Ya din ga sallamewa yana sake tayarwa har ya gaji ya nemi guri ya zauna.
Ayshacool
Tunanin yadda kayansa za su iso, a sallami mutane ya ?ara mamaye kansa, ya rasa bakin zaren matsalar baki Waya, haka ya zauna har aka yi kiran sallar asuba.

****
Tari ne ya sar?e Nana, ta tashi ta ji kamar wadda ta ?ware tana numfashi sama-sama. Ta shafa ta ji Sayyid ba ya gurin, ta ji an kama hannunta an bata kofi, ta karSa ta shanye ruwan, ta ajiye kofin saboda yadda wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.

?aisar ta gani a tsaye yana kallonta, jikinsa duk a ?one, bai yi mata magana ba, ya dan?i wuyanta ya zuba mata wani abu mai kama da haya?i a cikin bakinta.

A take ta ji cikinta ya hautsuna, mararta ta ?ulle, ta kalle shi a razane ta ce "?aisar me ka yi mini?".

"Cikin jikinki ba shi da amfani, dole ya bar jikin ki"

"Saboda me, ina ruwanka da cikina?"

"Saboda ba zan ?arar da rayuwata a matsayin bawa ga zuriyar ku ba, ki na wahalar da ni."

Kafin ta yi magana, ta ji tamkar ana fizgar naman cikin mararta, ta yin?ura ta tashi a gigice.

"Subhnallah, Sayyid, Sayyid" ta kira sunansa a wahale.

Daga banWaki ya fito a tsorace, ya nufo ta. Ta mi?a masa hannu, ya ri?e ta.

"Kai ni banWaki" ta faWa tana rintse idanunta.

Ya kamata ta mi?e, jini ya fara biyo ?afafuwanta, ya kai ta banWaki. Su na shiga ta dur?usa a kan gwiwoyinta, ta saka hannu Waya ta rirri?e ?afarsa tana girgiza kanta cikin matsanancin ciwo. Da ta ja numfashi da ?arfi, sai ta ji jinin yana zuba da yawa.
Ya rasa yadda zai yi, ga baki ya rufe ya kasa magana.

Can ta yi wani irin nishi, ta ?ara rirri?e ?afarsa da ?arfi, sai ga gudan jini ya faWo. A hankali ta din ga samun releif, ta jinginar da kanta a jikin ?afarsa ta kasa motsi. Jin yadda ?arnin jinin ya ishe ta, ya sanya ta motsa a hankali, ta yin?ura ya kama ta, ta tashi tsaye.

"Ka canza kaya ka yi sallar, bari na wanke jikina"

Ya motsa baki, amma magana ta gagara, ya dage yana ?o?arin yi, amma gumi ya fara tsatstsafo masa.

"Ya lafa mini, ka yi salla kar ka makara, zan wanke jikina" da ?yar ya fita, ta rufe banWakin ta wanke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login