Showing 117001 words to 120000 words out of 168002 words

Chapter 40 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

667

kukansa ta ji, duk da yadda ta san ya daWe yana dauriya, da son Soye gazawarsa, sai dai ta ga hakan a idanunsa.

"Sayyid idan ka na kuka, ni kuma ya zan yi kenan? Dan Allah ka daina" ta yi maganar muryarta na rawa. Ta din ga shafa bayansa a hankali, har ya yi shiru, bacci ya Wauke shi.
Ayshacool
Sai dai tun daga wannan, haka aka sake shafe kwanaki biyu, bai sha ko ruwa ba. Dama rashin maganarsa ya daina damunta.
Ga shi yau abin ya tashi sosai, haukan yake yi da gaske. Ta rufe shi a gidan, ta je ta samo gasara a gidan Uwani, ta dawo ta dama masa kunu. Ta nufi Wakin cike da fargaba tare da fatan ya samu ya sha ko kaWan ne.

Sai dai ta ji wata irin guguwa ta taso mai ?arfi.

Jin yadda guguwar ta taso da ?arfinta, take fatali da duk abin da ta ci karo da shi a tsakar gida, ya sanya ta tashi da azama, ta fara ?o?arin rufe ?ofar katakon da take Wakin. Sai dai tana danna ?ofar guguwar ma na danno ?ofar.

A take ta fara karanto "A'uzubillah, Allahumma inni as'aluka khairiha wa a'uzubika min sharriha. Allahumma inni as'aluka khairiha wa khairi ma fihi, wa khairi ma ursulat bihi, wa a'uzubika min sharriha wa sharri ma fiha, wa sharri ma urisilat biha" take ta ji nauyin da ?ofar ta yi ya ragu, ta samu ta rufe ta, ta juya da sauri ta nufin gurin da yake.

Da fari yana zaune a guri Waya ne, amma yanzu Jifa yake da kayan Wakin da hannu Waya, da sauri ta fara? bi tana tattarewa, cike da damuwa.
Cikin siriryar muryarta ta ce "Sayyid za ka ji wa kan ka ciwo, ka saurara ka saurari muryar matarka, ni ce a gare ka, ni ce fa, Husnan ka ce fa" Ta ?arasa maganar a raunane, duk yadda take ?o?arin tare shi ta kasa, domin ta gama firgita da lamarinsa. Tun safe take fama da shi, ya ?i cin komai, kuma ta kasa sarrafa shi duk rarrashin da ta yi a banza.
Cikin matsananciyar damuwa, hawaye na bin kuncinta ta ce "Ubangiji ka dubi mijin Nana, ka cire masa zafi da raWaWin da yake ji, ka saita masa tunani da ?wa?walwarsa, ya yi rayuwa mai cike da nutsuwa da farin ciki irin na sauran mutane" sai kuma ya tsaya cak, ya juyo yana kallonta.
Ta ?arasa gurinsa, ba tare da fargaba ba ta? ri?o hannunsa cikin nata jikinsa zafi sosai. Ta kalli cikin idanunsa sai taga yana birkice mata yana rikiWewa kamar ba Sayyid Win ta ba, idanunsa har wani haya?i yake fitarwa, gaba Waya kaminsa sun sauya.
Ta lallaSa ta zaunar da shi, Ta yun?ura zata tashi, domin ta Waukko kununsa ta sake jarraba ba shi, ta ji ya cafko ta yana wani irin sambatu bakinsa na kumfa da dalalar da yawu, da alama magana yake son ya yi mata. Rashin ?arfin jiki ya sanya ta faWa jikinsa. Ya ?an?ame ta sosai, saboda zafin da yake ji, ita kuma jikinta sanyi ?alau. Ita ma jikinta ya Wauki rawa, ta lafe a jikinsa ta kwantar da kanta a ?irjinsa tsawon mintuna, jin ya Wan nutsu jikinsa ya rage zafin ya sanya ta zare jikinta a hankali.

Ta Waukko kofin kunun da cokali, sai wani Wan ?aramin tsumma, ta zauna a gabansa ta Webo kunun a cokali ta kai bakinsa, sai dai ya tsaya yana bin ta da ido, kamar ya ga ba?uwar halitta, ta buWe nata bakin, ya kalleta shi ma ya buWe nasa.
Ta fara zuba kunun a bakinta ta haWiye, sannan ta zuba masa a bakinsa shi ma. Ya haWiye sai dai wani na biyo gefen bakinsa, bai haWiye duka ba. Tana bashi tana goge masa wanda yake? zubowa. Sai da ta tabattar ya ?oshi, sannan ta goge masa bakinsa. Ta Wauki kofin ta nufi ?ofa ta buWe a hankali ta ga an daina iskar, ta fita da kofin ta ajiye, ta tattara abin da guguwar ta watsa sannan ta dawo Wakin.

Jiki a sanyaye, ta zauna a gabansa tana ?are wa kyakyawar fuskarsa kallo. Da ?yar yake jan numfashi yana saukewa.? Ta sanya hannayenta biyu, ta gyara masa gashinsa, da ya rufe masa gefen idonsa, ta saka idonta a cikin nasa, cikin rauni da karaya, idanunta na zubar da hawaye ta motsa bakinta, ta fara magana

"Sayyid, dan Allah ka yi magana ko na ji daWi, wannan karon ka daWe ba ka ce mini komai ba. Da na sanya ran ka fara samun? lafiya, amma kullum lamarin nan gaba yake yi. Ka gaya mini wane ne kai? Daga ina ka ke? Ina zan samu danginka da 'yan uwanka, wata?ila kai naka dangin ba za su guje mu ba, za su karSe mu, tare da sar?ar da ta haWa ?addarorinmu wuri guda, duk da ban kasance Waya daga cikinku ba, ni fatana a nema maka magani ka samu lafiya, ba na son ganin ka cikin wannan mummunan yanayin, idan na ci gaba da ganain ka a haka, zuciyata za ta iya bugawa. Dan Allah ka yi magana" Ta yi maganar wasu hawayen na zirarowa daga cikin idanunta.
Ya haWiye wani irin yawu, da yake yi masa zafi a ?irjinsa, yayi ?o?arin Wago hannunsa na dama, sai ya tuna ya riga ya shanye, ba ya iya komai da shi. Ya buWe baki da nufin ya kira sunanta, saboda tasiri da kuma ciwon da kukanta yake yi masa a zuciyarsa, amma ya gaza bakin ya karkace yawu ya fara zubowa daga bakin nasa, maimakon kiran sunanta da ya yi yin?urin yi.
Tana kuka, ta sanya tsumman da tayi amfani da shi wurin ba shi abinci, ta goge masa bakinsa. Ba shi da zaSin da ya wuce, ba wa hawayen da yake ma?ale a cikin idanunsa damar zubowa, ko shi ma ya samu sassauci abin da yake ji.
A hankali ya hura mata iskar bakinsa a fuskarta, a take ta silale ta faWi a jikinsa.
Ya sanya hannunsa mai lafiya, ya rungume ta, ya ci gaba da kuka. Jikinta gaba Waya ya saki.

?aisar ta gani a gurin haWe-haWen magungunan sa, yana ta haWa wani abu a cikin kwalba. Zuciyarta ce take ta azalzalarta, da ?o?arin ingizata, sai dai ba ta yi magana ba.

Babu tsammanni, ta ji ya fara magana "ZaSi Waya ya rage miki, a halin yanzu, ko dai ki yadda da abin da na zo miki da shi, ki rungumi ?addararki, ko ki na kallo Buzun nan zai mutu, domin ba zai taSa tuna waye shi ba har abada, muddin Giyaz yana tare da shi. Dan ba na tunanin akwai wanda zai iya raba shi da shi. Idan har bai iya tuna waye shi ba, shikenan kin ga ba ki da wata makoma. Abu Waya zai sanya a wannan karon na bar miki abin da yake cikinki, duk da ba ni da tabbacin zai zama mai cikakkiyar lafiya ko akasin haka, Giyaz da mu?arrabansa sun riga sun fara taSa shi a cikin ki. Kin san meyasa ban ?arasa lalata wannan cikin ba?" Bai jira ta ba shi amsa ba ya ce "Saboda zan so na ga yadda za ki yi, a lokacin da Wan zai amsa sunan shege, kuma ba za ki iya hanawa ba, domin ba ki da hujjar kare kanki. Idan Buzun nan ya rayu bai san waye shi ba, ga kuma nakasa. Idan kuma ya mutu suwaye dangin baban Wan ki? Daga ina yake? Suwaye ahalinsa? Kin san ku a jinsinku na bil'adam da uba ake ado ba riga ba. Babu wanda zai damu da wacece ta haifi mutum, amma za a damu da waye ubansa meye nasabarsa? Tun da ki ka zo garin nan, zuriyarmu suke alwashin yadda fansar su za ta kasance a kan ki. Kafin zuwa wannan ?adamin babu abin da ban gaya miki ba, na gargaWi. Dan haka dabara ta rage ga mai shiga rijiya"

Cikin kuka Nana ta hau girgiza kai ta ce "Ba zan yi bori ba ?aisar, ba zan yi shirka da Allah ba. Babu tsanani ko wahalar da za ta sanya na rabu da imanina. Amma na rasa gaba na rasa baya, ba dan ina neman taimakon ka ba, ko ka kawo mini Wauki ba. Na san Ubangiji Allah shi zai taimake ni.
Amma dan zatin Allah idan ka na da hannu a ciwon Sayyid, ka yi mini rai ka rabu da shi, shi ne kaWai duniyata. Ina matu?ar tausayin sa, ban damu da jinya da nake yi ba, wahalar da yake sha ta isa haka. Idan kuma laifikan zuriyarmu ne suke shafar sa, dan Allah ku yi ha?uri ki ?yale shi haka"

Cikin sautin muryarsa mai ban tsoro, da ya kan yi amfani da ita, idan ya so razana ta, ko yi mata magana mai muhimmanci? ya ce "Na sha gaya miki na maimaita miki, daga lokacin da ki ka fara bani umarni, kin yadda kin amince da bu?ata ta ne. Ba ni da hannu a ciwon mijinki, kuma bai ya cikin zuriyar ku, sai dai ?addara mai ?arfin gaske, ta haWa ku tarayya guri guda. Amma muddin ki na son ya warke daga wannan rashin lafiya, ba ma iya haka ba, ya tuna waye shi, sai kin karSi ?addararki.".

Nana ta sake marairaicewa ta ce "Ba zan iya shirka ba, ba zan iya zama 'yar bori ba. Zan jure jarrabawata komai zafinta amma ba zan yadda rasa imanina ba"

?aisar ya ce "A cikin biyu dole abu Waya ya faru, tunda kakaninki su suka ?yan?yashi wannan matsalar. Na yi iya ?o?arina gurin dakatar da ita a wancan lokacin, amma ta sake tasowa a wannan karon. Dole a cikinku Waya zai warke ya rayu Waya ya mutu a haka, dan babu alamar Giyaz zai sassauta wannan mummunan ?udirin nasa a kan zuriyar ku. Gefe ga aikin da ya karSa yake yi a akan mijinki, ko dai ki ci gaba da rayuwa da shi, laifukan ku na shafar sa, ko kuma ki yarda ki karSe ni a matsayin hadiminki ki yi abin da nake so, ni kuma na san yadda zan yi da Giyaz, na baki maganin da mijinki zai warke"
"Ta yaya? Me yasa sai ni? Me yasa ni zan biya zunubin da lokacin da aka aikata shi ba na nan, zunubin da zamanin da aka aikata shi, ya yi nisa da nawa zamanin? Me ya sa kakannina suka zaSi zama 'yan bori? Suka gada mini wahala da masifa take ta bibiyar rayuwata. Na zama mujiya a cikin mutane, duk inda na tsuguna sai wata masifa ta afku, da za a jefa mini zargi, kasantuwata ni ba mutum ba ni ba wani jinsi daban ba? Me yasa zan girbe ba?ar shukar da ban san a lokacin da aka dasa ta ba? Ina son mijina duk da daga ni har shi, ba mu san waye shi ba.
Duk da Nijar ba Waki Waya bane ba, ba kuma ?aramar al?arya ba ce ba, ?asa guda ce, na gwammace zagaye ta neman ahalinsa na dam?a shi a gare su, da na ci gaba da zama da shi, mummunar ?addarata tana shafarsa, ko kuma na zama 'yar bori na ci gaba da gadar da wahala da masifa ga zuriyarmu, gara ko ma mene ne ya ?are a kaina." Ta ?arasa maganar cikin ?araji, tana kuka mai bayyanar da tsantsar ba?in cikin da yake binne a cikin zuciyarta.

*

A hankali yake driving cikin nutsuwa, yana sauraren Jamila, da ke bin wa?ar da ke tashi a cikin motar ?asa-?asa, sai kuma ta yi shiru.

"Ya ki ka yi shiru kuma?" Ta ce "Au wai ka na ji na?"
Abba ya ce "Eh mana, har kin fi masu wa?ar ma iyawa" Dariya ta yi ta ce "Ka ji ziga, muryar ta su da aka tace, aka goge tawa kuma a haka, ka ke cewa na fi su iyawa"

"Au ba ki yarda ba? To shikenan ni dai na san kin fi iyawa" ya yi maganar yana parking Win motar a harabar gurin shan ice-cream Win. Abba bai taSa soyayya ba, duk wannan abubuwan da yake yi wa Jamila, bai taSa furta mata cewar yana sonta ba. Sai dai ita sarai ta gane sonta yake yi, so kuma ba na wasa ba. Sai dai tana mamakin yadda duk wannan abin da yake yi mata, ba ya iya nuna wa a gaban Hajiya Sa'a, hakan ya sanya ta fara tunanin ko dai yana da wata manufa a kanta ne.
Sai dai ta lura halaye da Wabi'unsa, sun sha banban da na Hajiya Sa'a, shi Abba akwai tsantseni, da gudun saSa wa Allah. Dan duk da son da yake yi mata, sai da ya yi mata faWa a kan shigar banza da ta kan yi wasu lokutan.

Ice cream su ka sha, yana ba ta labarin yadda ya yi karatu, da irin ?alubalen da ya fuskanta na rayuwa. Su ka gama ya Wauke ta ya mayar da ita gida.

Bayan ta shiga gida, Mama ta ce "Yauwwa ke nake jira dama, gas ya ?are na kira wayar ki kuma ba ki Waga ba"

"Ina hanya ne, ga ATM Wina, a bawa Nasiru ya je ya Wuro. Har za ta shiga Waki sai ta fasa ta ce "Ni kuwa jama'a ina Nana ne? Wayarta ba ta shiga, shekaranjiya waccan ma na biya gidan da mijinta yake gadi, na ga kamar babu kowa a gidan"

Mama ta taSe baki ta ce "Au ke ba ki san abin da yake faruwa ba dama?"

Ta tsaya tana kallon Mama ta ce "Mene ne yake faruwar?"

"Ai tuni aka kore su daga wannan gida. Ke ba zama ki ke yi ba ne shi yasa, suka koma unguwar su Ummi, to kin santa duk inda ta zauna bala'i ne yake bibiyar gurin, hatsaniya ta haWa ta da matan gidan da suke, suka ce mayya ce aka tashe su. Ai nan Babanku ya je aka yi ta fafatawa, da ta kwaso jiki ta taho nan, wai za ta dawo mijinta babu lafiya, na ce bani da gurin jinya a gidan nan. Allah ya raba ni da masifa, ba za ta dawo mini ba, to ?arshe dai wai yanzu tana ?auye, can gurin Uwani a can take jinyar mijin nata"

Jamila ta yi sak, ta ce "Mama Nana tana ?auye fa ki ka ce?"

"Eh mana, to idan ba ?auyen ba ina za ta je? Tana can"

"To waye yake ba ta Abinci?"

Mama ta ce "Oho ina na sani?"

"Amma ya aka yi tsawon wannan lokacin ban sani ba? Yanzu ba kamar da ba ne, ban ji daWin abin da ki ka yi ba Mama, bai kamata a kore ta ba a ce ta koma ?auye da zama ba. Da ina nan ko na sani, da na kama musu wani gidan, gaskiya sai ta baro ?auye"

"To ke ina ruwanki? Mene ne naki a ciki uwar Iya? Kina kallon irin ba?ar azabar da na sha, a kan zamana da ita a gidan nan. Na meye za ki kuma jajubo mana ita. Gara ki bani kuWin da za ki k????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
ama mata hayar na bawa WanLadi, Wan autanmu ya tafi kasuwa da zaman banzae da yake yi, na yi masa aure tun da Allah ya sanya kuttun arziki ya fashe mana, ba ki kai kuWi inda babu amfani ba"
Jamila ta dubi Mama ta ce "Wannan Wan uwanki ne, sai ki nemi kuWinki ki yi masa, nima 'yar uwata nake tunani. Haba Mama, ko wani Nana ta kashe miki ?iyayyar ta isa haka ai. Ai yakamata a tausaya mata, miji babu lafiya ga zaman ?auye, ita Uwanin za ta Wauki nauyin Abincinsu ne? Tun da muka tashi a wahala muke a gidan nan, amma ita nata ya fi na kowa ma" Jamila ta ?arasa maganar cikin damuwa, ta shige Waki, ta bar Mama da buWaWWen baki.

*
Kallonsa Nana take yi, suna zaune sun yi juguum daga ita har shi. Bayan ta gama yi masa kitson zanen hannu guda takwas, ta yanke masa faratansa na hannu da na ?afa.
Kamar wadda aka mintsina ta tashi tsaye, ta kalle shi ta ce "Sayyid, bari na je na dawo" ya bi bayanta da kallo har ta fice.

Sai dai a ?alla ta kai awanni biyu kafin ta dawo, ko da ta dawo ta tarar da shi ya haWe fuska, ta yi shiru ba ta kula shi ba, ta koma tsakar gida.
Ta laluba kayanta, ta Waukko wata takarda mai Wauke da ayoyin ru?iyya da na karya sihiri, sannan ta hura wuta a cikin murhu.
Ta dawo tsakar gida ta zauna, ta fara da Bismillah da karanta Suratul fatiha, sai Suratul fala?i da nasi. Ta karanta ayoyi biyar Win farko na Suratul Ba?ara, ta fara karanta Suratul mulk, a hankali sai ta fara gani dishi-dishi, ta fara daina ganewa. Ta busa ayoyin a cikin ruwan, Sai ta ajiye takardar. Ta Wauki wata leda da ta zo da ita, ta fito da man habbatussauda da jan Almiski.
Saboda wauta sai ta buWe miskin, ta kai hancinta, da sauri ta dungurar da shi a gurin, ta ja da baya, dan tuni ta ji jikinta ya fara tsuma.
Sai da ta Wan samu nutsuwa, sannan ta zazzaga tazargaWe a cikin bokitin, ta kawo ganyen magarya guda bakwai, ta saka a leda ta Wan bubbuga musu muciya, ta haWa a cikin ruwan. Ta yi shiru tana tunani a ranta ta ce "Allah ya sa ba mai magani na zama ba, ?aisar bai mayar da ni 'yar bori mai bayar da magani ba, larurar Sayyid ta saka na fara koyi da magungunan sarkin baka."
"Amma ai ayoyin Alkur'ani ki ka karanta, shi ma kuma Sarkin Bakar yana amfani da Alkur'ani" wata zuciyar ta tunatar da ita. Haka dai ta ci gaba da wasi-wasi.
Can yamma, bayan ta tabbatar da ganyen magarya da tazargaden sun tsumu, ta Wumama ruwa ta tsiyayi ruwan tofin ta tace ta haWa da ruwan Wumin, ta kawo man habbatussauda ta tsiyaya a ciki, ta kawo jan miskin nan da ta saka kwalbar a ruwan Wumi, ya narke ta tsiyaya a ciki, ta Webo garwashi a kasko ta shiga Wakin. Yana ganin Nana ya tashi zaune yana kallon ta, ya ga ta samu ?yalle ta Waure hancinta da bakinta.
Ta nufo shi ya ga ta hau tuSe masa kaya, ya din ga bin ta da ido, ta bar shi daga shi sai gajeren wando. Hannunsa da yake ma?ale take kallo cikin damuwa, ta shafa hannun.
Sai kuma ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login