Showing 93001 words to 96000 words out of 168002 words

Chapter 32 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

666

ta. Muryarta na rawa ta ce "Sayyid"

Ya kalle ta. "KuWinmu, kuWin da ka bani na saka a cikin wardrobe na...naa..ajiye a nan ban gani ba, ko ka Wauka?"

Ya yi shiru yana kallon ta, a zuciye ta nufi hanyar fita daga Wakin, ya ri?e ta. Jikinta yana tsuma take ?o?arin fizgewa amma ya ri?e ta yana girgiza kai ya ce "Kar ki yi magana, ki yi shiru ko waye mu bar wa Allah. Tun da na shigo, na ga alamar an buWe Wakin. Kuma laifinmu ne, da ba mu saka mukulli ba, muka rufe Wakin kawai."

"Sayyid ba a yi mana adalci ba. KuWin Abincinmu da maganinka, sun kwashe gaba Waya wace irin masifa ce wannan? Daga wannan sai wannan ya ake so na yi ne?" Ya ri?e ta gam yana shafa bayan ta, a hankali ya ce "Ki yi ha?uri, ki daina Waga murya, akwai Allah"

Kuka take yi iya ?arfinta, tana sheshshe?a, ya rungume ta gam a jikinsa, shi kansa ya ji zafi da raWaWin satar da aka yi musu. Ba iya kuWi ba, har da wasu daga kayan amfaninsu na Wakin an Wauka, ya san kuma hakan sabon ?alubale ne, saboda ba su da wata hanyar samun kuWi a yanzu.
Ji ya yi jikin Nana ya saki, kuma jikin yana Waukar sanyi. Karkarwa ta fara yi, tamkar ana jona mata shocking.
Cikin matsananciyar damuwa, ya zauna da ita a jikinsa, ya Wauki wayarta da ta saki a gurin, yana haska fuskarta. Ya ga hawaye na fita ta gefen idonta. Hannayenta da ?afafuwanta su na lan?washewa, goshinta kuma yana tsatstsafo da gumi.
Jin ta ta yi, jingine da wani abu da ba ta san ko mene ne ba. Ta shafa abin ta ji ?urzunu-?uruzunu, tamkar dutse. Gurin ba?i ?irin duhu ya gauraye gurin, ko tafin hannunta ba ta iya gani. A hankali haske ya fara shigowa gurin, har gurin ya yi haske ba ki Waya. Ta Waga kanta ta ga ba ta iya gano ?arshen Wakin.
Jin tari ta yi a bayan ta, ta waiwaya da sauri, ta ga ?aisar a zaune lulluSe da wani abu mai haske sosai.

"?aisar. Ba ka da lafiya?" Ta yi maganar tana nufar inda yake.

Ya yi shiru bai yi magana ba. Ta sake cewa "Dama kuma ku na rashin lafiya, kamar ka canza gaba Waya" ya yi murmushi ya ce "Mu na rashin lafiya mana, guba na ci" Ta waro ido ta ce "Guba kuma? Me yasa?"

"Tsohon nan na jikin mijinki, ya bani."

"Kuma ka sha? Wai meye ala?ar ka da shi? Kuma dan Allah me yasa yake bibiyar mijina?"

"Ba wannan ba, me yasa ki ka kira ni?" Cikin mamaki ta kalle shi ta ce "Kamar yaya? Ni ban kira ka ba ai"

"Fushi da Sacin rai, duk wanda ki ka yi tamkar kin kira ni ne. Kuma ni yanzu ba ni da wani tasiri sosai, saboda jinya nake yi. Babu wanda ya san ina nan. Giyaz ya saka ni a gaba, ya mamaye Library Wi na, yanzu rashin ganina zai sanya ya ci gaba da cutar da ku. Ba zan iya wani abu ba sosai yanzu, sai dai zan iya tasiri a kan bil'adama.
Duk ba wannan ba, duba can."
Ta Waga kai ta kalli inda ya nuna mata, Library Win ?aisar ta gani. Ta ga gangar jikin Sayyid a kwance. Tsohon nan ya WaWWaure shi da wata irin igiyar ?arfe. ?asan gadon da yake kai kuma, wata irin wuta ce take ci a ?asa. Nana ta zabura a rikice, ta ce "Wannan ai Sayyid ne"
"?warai shi ne, ba wani ba. Kuma Giyaz shi ya sanya masa matsalar da ku ke ciki na auratayya. Sai dai abu Waya zan iya gaya miki. Matsalar zuciya da hawan jini da yake fama, wannan ciwo ne yake damun sa. Amma Giyaz na assasa wani abin. Kuma... Amma dai shikenan"

Nana ta buWe baki za ta yi magana, ya ce "Kar ki tambaye ni komai, kin san sharaWin. Kalli" ya yi maganar yana sake nuna mata gurin.

Alhaji Fatuhu ta gani, ta yi ?uri da ido ta ce "Kamar na san wannan"

"Ba kama ba ce ba kin san shi, ciwo ne da zafin sihirin da aka yi masa ya mayar da shi haka. Sai kuma albishir da nake yi miki, da ?anwar ki ta zama cikakkiyar 'yar ?ungiyar asiri. ?ayar kuma wannan bararojin da ta taSa baki magani, ta aura mata Wanta, wanda yake ba?in aljani ne. Kuma ta tarkato kan iyalanta duk su na jikinta. Kuma kowanne akwai abin da yake mora a jikinta. Ke in ta?aice miki ma, a kowane lokaci za ta iya rasa hankalinta ko ma rayuwarta gaba Waya.
Ayshacool
Shikenan bissalam"

"?aisar" sai kuma ta yi ido huWu da Sayyid.

"Kin tashi?" Ta yin?ura ta tashi zaune, tana kallon Wakin.

Sayyid ya ce "?aisar Win ba shi da lafiya ne?" Ya yi maganar yana tsare ta ido.

"Wane ?aisar Win?"

"Tambayata ki ke yi?" Shiru ta yi, ita ba ta iya tuna koma ma a cikin abin da ya faru ba. Idonta ne ya sauka a kan kayan da suke gaban wardrobe a ?asa, sai kuma abin da ya faru ya faWo mata. Afujajan ta tashi ta sake nufar wardrobe Win, tana zazzage kayan tana kuka.

"KuWin nan fa babu su, an kwashe ki daina wannan dube-duben" ya zauna ta yi shiru ta sanya kayan a gaba tana kallo.

Ya yi mata shiru ya ?i kula ta, ya kwanta a kan katifa, yadda take a hasalen nan, idan ya matsa faWa za su yi. Cikin ?an?anin lokaci nannauyan bacci ya yi awon gaba da shi.

Barira na kwance a Wakinta, ta yi WaiWai tana bacci, ta ji kamar ana karta mata farce a ?afafuwanta. Har ta maze ta ci gaba da bacci, amma ta ji an cigaba. A fusace ta ce "Gali meye haka, za ka din ga karta mini faratanka, ina cikin bacci ne?" Shiru bai amsa ba. Ta laluba ta ji yo ?eyarsa a can ?arshen gado, yana bacci. Ta koma ta kwanta, amma ta ji an cigaba, ta tashi zaune tana zabga ashariya.
Ta kunna fitila, ta ga babu kowa. Ta yi tsaki ta sauka daga kan gadon, ta fito tsakar gida domin ta yi fitsari. Bayan ta fito daga banWakin, kanta ko Wan kwali babu, kawai ta yi karo da Nana a tsakiyar tsakar gidan tana yi mata wani irin mugun kallo.

Ta haska Nana ta ce "Nana lafiya kuwa?"

Sai dai Nana ba ta yi magana ba, ta sake haska ta, za ta yi magana. Ta ga ta rikiWe ta zama wata irin ?atuwar mage, ba?a ?irin, girman ta ya yi na tunkiya ?osashiya da ita, ta yo kanta tana buWe ha???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ora.
Da gudu Barira ta shiga Wakinta, tana ihu tana kiran sunan Gali.

"Ke mahaukaciya, mene ne haka za ki din ga ihu kina kiran sunana a tsohon daren nan?"

Ba ta ce masa uffan ba, ta du?un?une, tana mayar da numfashi. Ta tsorata sosai da sosai, da ?yar ta samu ta yi bacci. Sai dai a cikin baccin ma, mafarkin magen nan kawai ta din ga yi tana bin ta, tana karta mata farata tana cizon ta.

Sayyid kuwa yana jiyo kururuwar Barira, hakan bai dame shi ba, sai ganin Nana da ya yi a zaune, ta haWa kai da gwiwa.
Ya yin?ura ya tashi zaune, bai ce mata komai ba, ya kwantar da ita a kan katifar, ya rufe su da bargo ya rungume ta yana shafa bayanta. Yana jin ta tana kuka, har ta yi ta gaji bacci ya Wauke ta.
Dauriya kawai yake yi, amma ji yake tamkar ya taya ta kukan.

Washegari, Barira ta tashi da matsanancin zazzaSi da ciwon kai, ta din ga yi wa mijin kuka, tana cewa ya mayar da ita gidansu, mayu sun kama ta a nan gidan, ba za ta yadda a kashe ta a banza ba. Babu yadda ya iya ya tattara ta ya kai ta gidansu.

Kwanki biyu da sace kuWin nan, Nana ta rasa abin da yake yi mata daWi. Dubu talatin ce ta ragu a hannunta, shi ma cikin irin kuWin da ta zuba a jakarta ne suka fita da su. KuWin Nijar Win kuma ba ta san ma ina za ta a canza su ba. Bayan haka tayi tunanin idan Habu ya dawo fa, me za ta ce masa? Ta din ga tunanin yadda za ta yi da dubu talatin Win nan, ba tare da ta rushe gaba Waya ba. Ga shi magungunan da yake sha kawai, na wata Waya dubu goma sha biyu take sayen su.
Sai dai kamar yadda yake nanata mata, ta yi ha?uri, ya sanya ta fauwwala wa Allah lamarin.

Kwana biyar da kwashe kuWin nan, Sayyid ya hana Nana gaya wa kowa. Sai dai cikin dare ba ta iya bacci, saboda lissafi da tunani. Ta kira Ummi ta tambaye ta batun barkono, ta ce ana ta saya, ta sayar da ya kai rabin buhun. Kayan Abinci da Mama ta haWo mata da su, take ta cancana musu.
Da daddare ba ta iya bacci, saboda damuwa da tunani, sai dai abin yana damun sa fiye da yadda yake damun ta. Su ka wayi gari, ya tashi jikinsa babu daWi, yana ta numfarfashi.

Abin Duniya ya ?ara damunta, ya kuma ?i cin komai. Muryar Barira ta jiyo a tsakar gida, da ta dawo, tana maganganu tana ba wa su Sajida labari.

"Mayu sun kama ni a gidan nan, kuma da ?arfina na dawo, wallahi sai sun ci uban su, kurwata ta fi ?arfin mutum".

Sajida ta ce "Ban gane mayu ba, suwaye mayun kuma?"

Barira ta ce "Oho, ki zuba ido ki gani, Allah zai tona musu asiri"
Ayshacool
Ya gama ci, ta dafa ruwa ta kama hannunsa zuwa banWaki, tamkar jaririn goye ta yi masa wanka. Shi kansa a lokacin ya din ga jin wata lafiyayyiyar iska na shigar sa. Ta saka ya yi alwala, ya fito ya zauna ya fara jero sallolin da ake bin sa.
Ta ce "Sayyid kar ka ce sai yi a yanzu duka, sallolin da yawa.ka bari ka din ga ramawa a hankali.
Ya jinjina mata kawai kawai, tun yana yi a tsaye ya kasa tsaiwar ya koma yi a zaune. Ta yi shiru tana kallonsa, ta wasu guraren suna da kamanceceniyar halayya ita da shi.
Duk yanayin da yake ciki, muddin ba hankalinsa ne ya gushe gaba Waya ba, ba ya wasa da salla ko kaWan. Hakan ya sanya take jin ko a ainihin rayuwarsa haka ya siffantu da kiyaye salla a kan lokaci.
Har ?arfe uku da rabi, dan kansa ya ce "Ba zan iya ?arasawa ba, numfashina"

Ta ce "To ko za ka yi a kwance?"

Ya girgiza kai ya ce "Na fi so na yi a zaune, ko a tsaye"

Ta Wage masa labule, ganin yadda yake ta gumi. Ta shimfiWa masa sallaya a bakin ?ofa, ta jera masa fululluka, ya kwanta.ta zauna a gefen sa tana yi masa fifita. Ta Wora hannunta a goshinsa tana karanta masa abin da Allah ya sa ta tuna a zuciyarta.

Hannunsa ta ji yana saka wa a rigar ta, duk da idonsa a lumshe yake. Murmushi ta yi ta ci gaba da abin da take yi. Jin yana yi mata cakulkuli, ya sanya ta kwanta a jikinsa tana dariya. Shi ma dariyar ya yi. Ya ce "Ki kwanta a kusa da ni" ya yi maganar yana nuna mata kusa da shi. Kafin ta yi magana ta ga an dalle su da fitila.
Cikin hanzari ya juya kansa, ya Soye fuskarsa a cinyar Nana, gashin sa ya kwanta a kan filon. Nana ta saka hannu ta kare fuskarta.
Muryar Barira ta ji ta ce "Yi ha?uri dan Allah, jin motsi ya yi wa na fara jin tsoro, shi ne na fito na duba, ku yi ha?uri.
Ta kashe fitilar ta koma Waki. "Sayyid ka yi ha?uri, na san ba ka ji daWi ba, ka yi ha?uri"

Ya yi mata shiru, kuma bai Wago daga kan cinyarta ba. Ta shafa gashin ta ce "Shugabana, ka yi magana mana, ko na ji daWi, kwana huWu ka na bacci, ba ka yi mini magana dan Allah kar laifin wani ya shafe ni"
Sai kuma ya juyo a hankali, ta ce "Yauwwa Rayuwata"

"Kin daina aman?" Ta ji ya tambaye ta babu tsammani.

"Eh na daina"

"Allah ya sa ki haihu wannan karon "

"Amin, kuma Allah ya baka lafiya na haWa jariraina biyu, babba da ?arami"

Ya yi murmushi ya ce "In sha Allah, kafin ki haihu, idan na ji sau?i zan nemi aiki, na kula da ku da kaina"

"To Allah ya amince. Amma Sayyid ina kuWin nan da na gani rannan, a cikin wardrobe Win ka? Da na haWa mana kaya ban gan su ba. Da sai mu Wauka a yi maka magani, kuma mu canza gida"

"Ai Habu ya karSa, ranar da ya zo na ?arshe, ya karSi kuWin Nigeria da yawa, ya bar mini wasu, ya ce na Nijar ne. Kuma da kin duba kayan nawa sosai, su na ciki"

"A'a ni ba na caje maka kaya, idan Allah ya kaimu gobe, sai a lissafa mu gani idan za su isa."

Ya ce "To. Kwanta ki yi bacci" ya yi maganar ya ?ara matsa mata. Ta kwanta tana murmushi.

"Sayyid, idan har ba a ga su Habu ba, ina ga da ni da kai zamu je Nijar, mu nemi danginka da kanmu"

Ya yi shiru bai yi magana ba, ta Wan taSa shi ta ji har ya yi bacci.

*
Jamila a dole ta saki ranta, jikinta ta Wan samu ?wari, ya daina yi mata wannan mugun ciwon da yake yi mata. RaWaWin ma duk babu. Sai dai tana jin ?asan zuciyarta kamar za ta yi bindiga, saboda damuwa da tashin hankali. Sosai abin da ya faru ya tsaye mata, ta shiga banWaki ta sha kuka. Wai ita Aljani ya kwanta da ita, ta gaba da baya aka ci zarafin ta ta wannan mummunar hanyar.

Tana kwance a cikin bargo, Hajiya Sa'a ta fita shashashancinta. Wayarta ta fara ringing. Ta janyo ta Waga. Muryar Abba ta ji ya ce "?anwata, wunin yau ban jiki ba, lafiya kuwa?" Wani irin abu mai zafi ya taso mata, ya haddasa mata karaya. Muryarta na rawa ta ce "Yaya Abba ba ni da lafiya"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Me ya same ki?"

Rasa abin da za ta ce masa ta yi, kawai ta saka kuka. Aikuwa ya rikice ya din ga rarrashin ta.

Da ?yar ya lallaSa ta ta ce masa cikinta ne yake ciwo.

"To ina Mummyn take? Ba ta kai ki Asibiti ba?"
Ayshacool
"Ta kai ni, an ba ni magunguna ma, dan Allah kar ka yi mata zancen, ta yi mini iya ?o?arin ta,kar ka yi mata zancen dan Allah"

"No ai ba zan yi mata ba, ba ta san ma ina da lambar ki, mu na magana ba. Ki kwanta ki samu hutu kin ji ?anwatax

"To shikenan na gode sosai" suka yi sallama ta ajiye wayar, ta kwanta hawaye na ci gaba da bin idanunta.

*

Yana zaune a cikin mota, yana ?o?arin kunnawa, wayarsa ta fara vibrating. Ya kalli screen Win wayar, ya ga ba?uwar lamba. Ya Wauki wayar ya Waga ya saka a kunnensa.
"Hello" muryarta ta doki dodon kunnensa. ?an waro ido ya yi, ya gyara zaman sa ya ce "Wa ke magana?"

A raunane ta ce "Beb abin har ya kai ka manta muryata ma? Shikenan na gode" ta kashe wayar.

Da sauri ya bi kiran wayar, amma ta ?i shiga, ya yi ya yi, amma ta ?i shiga, sai ha?ura ya yi ya ja motar.

Shukura mamakin abin da ya zaunar da shi a cikin mota take yi, bai tafi ba har yanzu, sai dai tana Waga labule, ta hango ya ja motar ya tafi.

Video call Win Hajiya Amina, Shukura ta gani, ta Waga cikin fara'a tana faWin "Hajiya Mummy, ya ibada?"

"Ibada Alhamdillah, Shukura dan Allah me yasa ba kya ji ne? Ina zaman zamana, ina ibada kin jawo mini Sacin rai da damuwa"

Cikin rashin fahimta, ta ce "Ni Win kuma? Me na yi?"

"Baban ki ya kira ni, bai taho ba tukuna yana Abuja. Yana yi mini faWan wai ke ba ki san ?addara ba ne? Doctor Sharif ya kira shi cikin damuwa, yana gaya masa a gaban mutane ki na cewa yana kashe mutane, haka ake yi a kan ki a ka fara rasa Wa? Me yasa ba za ki girma ba ne Shukura"

"Mummy ki na ji na, network Win ki mai ?arfi ne ko?"

Ta ce "Eh, ina jin ki, kuma ina kallon ki"

"Ina son idan kin je gaban ka'aba, ki yi mini addu'a, muddin a kan gaskiya ta nake, Ubangiji Allah ya shiga lamarina ya ?arfafa mini gwiwa. Idan kuma ba a kan daidai nake ba, Ubangiji Allah ya kawar da kaina daga kai. Ya bani juriya da dangana na daina jin abin da nake ji a zuciyata.
Sai dai kin dawo amma akwai matsala ne fa."

"Shukura matsala wace iri ce, za ta sanya musulmi kasa yin tawakkalli?"

"Ki bari dai ki dawo Win"

"To shikenan, amma gaskiya mahaifinki ya yi fushi bai ji daWin abin da ki ka yi ba sam"

Shukura ta lallaSa ta, ta ajiye wayar.

*

Nana tana jan ruwa a rijiya, tana zubawa a cikin bokitanta, za ta kai banWaki.
Barira ta ce "Nana ki yi ha?uri dan Allah, jiya na haska ku, ba a son raina ba ne, kuskure ne" Nana ta ce "Babu komai"

Sajida ta ce "Uban me ki ka haska ki ka gani?"

Barira ta kwashe da dariya ta ce "Ni babu abin da na gani, duk da bai kyautu ba abin da na gani Win. Amma Nana mijinki balarabe ne ko bature?" Nana ta Waga ta kalle ta.
"Tun da ku ka zo dama bamu taSa ganinsa ba, gashi na gani kamar na mace dogo sosai"

Nana ta maze ba ta kula ta ba, ta kwashi kayan ruwanta, ta nufi Wakin su.

Sajida ta tuntsure da dariya ta ce "Maganinki da shegen shishshigi, ga shi ta gwale ki"

"Shegiya ba, ta fiye jin kan ta,kamar 'yar uban wani, kuma da 'yar uban wanin ce, da ba su kama hayar Waki Waya ba" Duk abin da suke faWa a kunnen Nana, amma ta yi kamar ba ta ji ba.

Bayan ta gama wanke banWaki ta fito, ta zo gabansa ta zauna. Ya Waukko sauran kuWin nan, ya ajiye a gaban ta.

Ta kalle shi ta ce "A ina ka Soye ne, ban gan su ba?"

Ya yi murmushi ya ce "Su na cikin kayana fa, ba ki duba bane ba. A cikin leda suke. Kuma da sun fi haka yawa, Habu ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login