Showing 159001 words to 162000 words out of 168002 words

Chapter 54 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

663

ga ba ta yarda da shi ba, ta kira ta ta sanar mata.
A duk lokacin da Nana ta Waga wayar ta kalla, sai ta tuna Hajiya Amina, Haidar da kuma sauran jama'arta na Nigeria.

A gidan nan suka yi salla, aka ba su abinci suka ci, sai dai Nana ta yi mamaki ganin mata da yawa a gidan. Duk da ?abilu ne daban-daban matan, akwai Zabarmawa, akwai Bugaje, da hausawa da sauran ?abilun ma da ba ta sani ba a Nijar. Wai gidan kamar kamfani ne, wannan matan aiki ake nema musu, duk ciki Nana ce kawai 'Nigeria a cikinsu. Gaba Waya ta takure kanta ta kasa jikinta da su.
Gaba Waya daren ranar, Nana ta kasa bacci, ta din ga tunanin Muhsin, da tunanin ko zai yi kukan rashin ganinta.
Washegari Hansatu ta ce wa Nana ta shirya, ta Wauki kayanta su tafi. Haka kuwa aka yi ta sake Waukarta su ka fita.

Nana ta sha mamaki, ganin haWuwar da gurin cin abincin ya yi, kuma babban abin da ya ?ara bata mamaki, gurin cin abincin tamkar hotel.
Suka shiga cikin gurin, Hansatu ta kai Nana wani katafaren ofishi, da yak3 gurin mai kula da Waukar ma'aikatan, da yake namiji ne. Rawaninsa ne ya tabattar mata da buzu ne, ganinsa kawai sai Nana ta ji wani irin sanyi, tamkar ta ga Sayyid.

Nana ta gaishe shi, ya amsa sama-sama yana Wan basarwa.
Hansatu ta ce masa "Wannan ita ce ma'aikaciyar, na kawo ta a yi mata gwajin, a gani idan za ku Wauke ta" Ya Waga kai ya? sake kallon Nana ya ce "Sannu ko"

Nana cikin girmamawa ta ce "Yauwwa sannu da aiki"

Ya mi?o mata ?unshin wasu takardu ya ce "Ga wannan duba, ki ga yadda tsarin aikin namu yake, ki gani idan sun yi miki, kafin mu je inda za a yi miki gwajin, idan kin ci sai ki sanya hannu a takardun, ki fara aiki da mu"
Nana ta saka hannu ta karSi takardun, amma ta ga rubutun French, ta kalli Hansatu, ta kalle shi ta ce "Ai ban iya fransanci ba"

Ya kalli Nana ya ce "Ba ki yi makaranta ba?"

Ta ce "Na yi, amma ni ban iya French ba, turanci na iya sai Hausa"

Hansatu ta ce "A yi ha?uri YallaSai, 'yar Nigeria ce, daga Nigeria take"

Sai kuma ya kalli Nana ya faWaWa murmushinsa ya ce "Daga Nigeria ki ke? Ki ka baro babbar ?asa kamar Nigeria ki ka zo jamhuriyar Nijar ki yi aiki da mu?" Nana ta Wan risunar da kai tana murmushin dole, ganin yana murmushi shi ma.

Ya ce "Ahh to ai 'yan Nigeria ?awayenmu ne, ba ma ?awaye ba 'yan uwanmu ne. Dan haka zan ba ki aiki amma da sharaWin za ki koya mini turanci, idan kin yarda na baki aiki" Nana ta yi murmushi, saboda yanayin yadda ya yi maganar cikin zolaya. Ya yi 'yar dariya ya ce "Ai duk wanda ya zo Nijar, mussaman daga Nigeria ba?onmu ne, akwai bu?atar mu karrama shi sosai da sosai, ko dan ?ara zumuncinmu da mutanen Nigeria. Dan haka babu wani abu, wannan wani ci gaba ne ma zan iya cewa gurin Abincinmu ya samu, kin ga girke-girken da ba a yi a nan, na can ?asar kya din ga yi mana.
Mu na da gurin kwana na ma'aikatanmu, awa ashirin da huWu muke yi mu na aiki. Kamar yadda ki ka gani babban gurin cin abinci ne da manyan mutane ke zuwa cin abinci.
Masu sayar da abinci daban, masu girki daban, ke za ki kasance a Sangaren masu girki ne. Mu je mu zagaya ku ga gurin sosai da sosai.
Ya jagoranci su Nana, ya nuna musu gurin, tsarin ya yi wa Nana sosai, duk da abin da ba ta ji daWi ba, maganar zuwa hutun sati Waya ne kacal, duk ?arshen wata.
Su Hansatu za a din ga tura wa albashinta, su cire nasu kason su bawa Nana sauran.
Ita Nana duk hakan bai dame ta ba, babban fatanta bu?atarta ta biya kawai.

Suka kammala duk cike-ciken da za su yi, aka sallami Hansatu, Nana kuma aka kaita gurin kwanan ma'aikata.
?akin da aka kai Nana, su uku ne a ciki, da banWaki a ciki. Ta ajiye jakar kayanta, Hansatu ta kalle ta ta ce "To Nana, kamar dai yadda ya gaya miki, mu kamfani ne, kuma a ?ar?ashinmu ki ka zo nan, dan haka gurinmu albashinki zai din ga tafiya, mu zamu din ga sallamar ki"
Nana hakan ko a jikinta, dan ita ko ba za su ba ta komai ba, indai akwai gurin kwana da abinci, kuma kwalliya za ta biya kuWin sabulu, hakan ba damuwarta ba ne ba.

A fili ta ce "Babu damuwa, hakan ma na gode sosai da sosai, Allah ya saka da mafificin Alkhairi".

"Amin, a hakan ma gaskiya kina da sa'a sosai da sosai, sai da muka kawo musu mata uku, da ?yar suka Wauki Waya, wai duk ba su yi musu ba, wasu kuma sai an zo yi musu gwaji sai su faWi. Amma ke ya ce ba zai yi miki ma gwaji ba, kawai an Wauke ki aikin.
Abin da zan gaya miki kawai shi ne ki kula, ki kula da kanki sosai da sosai, banda ?azanta banda son jiki.
Sannan kar ki ga kin tsallake wannan matakin, ya Wauke ki aiki a haka cikin sau?i, ki zata mi?e ?afa za ki yi, mace ce mai gurin nan, kuskure kaWan za ki ta ci mutuncinki ta kore ki. Su kan su ma'aikatan kwantar da kai suke yi, su na yi mata biyayya, duk wata tijara da bala'inta kawai ki toshe kunnenki ki yi ha?uri." Nana ta yi shiru, sai da Hansatu ta gama gaba Waya sannan ta numfasa ta ce "To Ubangiji Allah ya iya mana"

Hansatu ta amsa da "Yauwwa Amin"

Hakanan Nana ta ji a jikinta, ba za ta Wauki wula?anci da cin zarafi ba, duk da kuwa abin da take son cimma. Ko Nene da ake kambama faWanta da masifarta, ba ta cin mutunci, kuma duk abin da za ta yi faWa a kai, to a kan gaskiya ne. Amm yanayin yadda Hansatu take yi mata bayanin mai gurin nan, a kaikaice dai ba ta san darajar mutane ba.

?akin da Nana take, ita da wasu Zabarmawa ne guda biyu. Ta yi alwala ta yi sallar Azahar.
Ta daWe a kan abin salla, tana gaya wa Allah, cikin magiya a kan ya sanya ta samu abin da ta fito nema, ya kuma raba ta da duk wani sharri da abin ?i.
Bayan ta idar, Waya daga cikin 'yan Wakin, ta ce mata ta zo su je ta zagaya da ita.
Can Sangaren da ake girke-girken ta kai Nana, suka zagaya daga nan ta kaita cikin gurin da ake sayar da abincin. Nana ta yi mamakin girman gurin, da yadda gurin Abincin yake da tarin kwastomomi. Sai dai da gani ka san na manya ne, dan duk waWanda suke zuwa gurin cin abinci akwai alamun abin hannu a tattare da su.

*

?angaren su? Shukura cikin jikinta ya tsufa sosai, sai dai a wannan karon ta dage fafur ta ?i yin awo a Asibitin su Doctor Sharif.
Gefe Sagir ya jewa mahaifiyarsa, da maganar son dawo da Yusra, amma ta ce ba ta lamunta ba, ba ta bu?atar ya sake rayuwa da Yusra, gara yaje ya auro wata can daban, amma ba Yusra ba.
Gaba Waya ya shiga damuwa, saboda mugun sabo da sha?uwar da ya kuma yi da Yusra.
Ita ma Hajiya Halima tun da ta samu labarin, Sagir ne tsohon mijin Yusra yake zuwa gurinta, ta din ga bala'i ta ce ko shi ne autan maza, Yusra ba za ta koma hannunsa ba, balle a sake ci mata mutunci a sako ta. Ga shi daga shi har ita su na son junansu. Dan haka ya yanke shawarar tafiya gurin ?anin mahaifinsa ya yi masa magana.
Shi kuma ya kira Hajiya Halima ya din ga yi mata faWan dan me za ta hana shi mayar da matarsa alhalin sulhu alkhairi ne, wancan karon da auren ya mutu ma, gutsuri tsomarsu ce ta kashe Auren.
Mussaman ta kira Sagir gida, ds ya je ya same ta, ta dirarar masa da bala'i.
"Wato ?arata ka je ka kai wa ?anin ubanka saboda mace ko Sagir?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a Hajiya ba ?ararki na kai ba"
"Rufen baki ko na make ka, ba ?arata ka kai ba ya kira ni yana faWa? Tun da abin da ka zaSa kenan, ka je ka yi duk abin da ka ga dama"
Kalaman na Hajiya, tamkar Wsure shi ne da jijiyoyin jikinsa, gaba Waya ya rasa abin da yake yi masa daWi ba ya son ya yi abin da daga baya zai zo yana dana sani, saboda rashin amincewar Hajiyarsa.


Daren yau sam Nana ba ta samu isasshen bacci ba, da yake sai washegari aka ce za ta fara aikin, ba ta yi aikin komai ba ranar.
Raba dare ta yi tana nafilfili addu'oi, saboda a jikinta tana jin wani abu game da gurin, wanda ta kasa tantance ko mene ne.
Washegari da safe, suka shirya ita da 'yan Wakinsu, suka tafi gurin aikin Abincin.
Kayan girki ne ga su nan a zube, kamar abin banza, yanayin yadda aka jibge kayan a gurin, Nana ta sha jinin jikinta, ta san aiki ne tu?uru za a yi shi gurin.
Aka ba su jadawalin abinccicikan da za a girka a ranar, Nana ta san wasu, wasu kuma ba ta san su ba.
Su na nan tsaye shugabar Sangaren na ?ara yi wa Nana bayani, da gurSatacciyar hausarta, sai ga mutumin jiya shigo.
Gaba Waya suka wani ruWe, masu gyara tsayuwa na yi, masu kama aiki suna yi, Nana dai ta ?ame a gurin da take. Ba yabo ba fallasa ya din ga amsa gaisuwar da ake yi masa, sai da ya zo kan Nana ya saki murmushi ya ce "Ba?uwarmu, ya ki ka ga gurin namu, ba dai wata matsala ko?"
Nana ta girgiza kai ta ce "Babu matsala"

Ya ce "Yauwwa, ki saki jiki ki yi aikinki da mu, kamar kina Nigeria, duk abin da ba ki gane ba, ga shugabar sashin nan, idan kuma ba haka ba ni ki zo ki same ni ki yi mini magana"
Ta jinjina kai ta ce "To in sha Allah, na gode sosai da sosai"

Ya kalli matar ya ce "Dan Allah kar a ce za a sakar mata aiki lokaci Waya, a koya mata abin da ta sani ba a hankali, kafin a sakar mata aiki"

Matar ta risuna ta ce "In sha Allah, amma za a yi mata gwajin ne ita ma?"

"Kin ji na ambaci hakan ne, a maganata?"

Ta girgiza kai ta ce "Tuba nake"

Ya ce "'Yar Nigeria, a yi aiki lafiya"

"Na gode sosai" Nana ta yi maganar cikin girmamawa. Ya wuce ya fita. Bayan ya fita suka juya yare, suka Wan yi maganganu, sai dai duk da Nana ba ta jin yaren nasu, ta san gulmarta suke yi. Suna aiki amma gaba Waya hankalin Nana ba a kan aikin yake ba, yana kan halin da Sabir yake ciki. Tana ta tunani yaya yake? Yana rigima ko kuwa bai damu ba ya kwantar hankalinsa, haka ta yi ta wasi-wasi a zuciyarta.

*
Hajiya Amina ce ta yi shirin tafiya Umara, ta tsaya a Egypt za ta kwana biyu, ta tsaya a Wan binciki lafiyarta. Sai dai ta din ga ji a ranta, yakamata a ?ara bincika mata matsalarta ta rashin haihuwa, mussaman da take tuna maganganun Nana. Sai dai gefe guda tana tuna yadda Alhaji Zailani yake gargaWinta a kan shi ya fauwwala wa Allah, bai damu lallai sai ta haihu ba, tun da an nemi magani ba a dace ba.
Sai dai a wannan karon, ta sake jin tana son jarraba da bibiyar lafiyarta, da ganin likita, ko za a dace, tun da ba ta daina al'ada ba ma.
Da harshen turanci suka tattauna da Likitan, ta yi masa bayani, ya rubuta mata gwaje-gwaje ya ce ta je ta yi, ciki har da hoto.
Kasancewar komai na su ba kamar na ?asarmu ba, cikin ?an?anin lokaci aka yi duk gwaje-gwajen, aka tura wa Likitan sakamakon.
Bayan ta koma gurin Likitan ya duba na'ura mai ?wa?walwarsa, ya kalli Hajiya Halima ya ce mata "Sakamakon hoton da aka yi mata, ya nuna babu mahaifa a jikinta gaba Waya" wata irin ?ara cikinta yayi, zuciyarta ta buga a jejjere da ?arfin gaske, sai ta hau kame-kame tana tunanin, ko kunnuwanta ba su ji daidai ba? Ko kuma turancin nata ne ya ?wace.

Cikin rawar murya ta ce "Ka tabattar da abin da ka gaya mini, ko kuma nice ban fahimta ba?"

Ya ce "Na tabattar, shi ne sakamakon gwajin da aka turo mini, amma idan ba ki yadda da sakamakon ba, kina iya zuwa wani Asibitin a sake duba ki!.

Yammm ta ji kanta yana yi, ta daina gane komai, hankalinta ya rarrabu kashi-kashi, tana son yi wa likitan tarin tambayoyi amma kanta ya kulle.
Shin da gaske ana iya samun mace babu mahaifa, ko kuma wani abin ne daban? Ya aka yi duk tsawon lokacin da ta Wauka tana bulayin neman haihuwa ba a taSa gaya mata ba ta da mahaifa ba sai yanzu?.
Gaba Waya Hajiya Amina, ta rasa kalmomin da za ta tattaro ta sake furta wani abu. Jikinta rawa kawai yake yi, wani irin gumi yana tsatstsafowa ta kowace kafa ta gashin jikinta.
Likitan ya ci gaba da yi mata bayani, amma ta kasa fahimta.
Ba ta san ma da ya aka yi ta bar Asibitin ba, ta koma masaukinta saboda tsabar Wimuwa. Ta kuma rasa wa za ta kira ta sanarwa wannan maganar.
Gaba Waya kanta ya juye, dan ba ta ma iya tuna yadda su ka ?ar?are da Likitan ba.
Tana so ta zubar da hawaye, ta ji sanyi a ranta, amma abu ya gagara idanunta suka bushe zuciyarta ta yi nauyi. Babbar tambayarta ita ce, dama ana iya samun macen da ba ta da mahaifa? Ko kuwa ta ta ce ta yi Satan dabo?. Tambayar da ta rasa wa za ta yi wa, balle a ba ta amsa.

*

Nana kuwa gurin nan aiki ake yi tamkar babu gobe, duk da ba ta da son jiki, amma aikin yana da yawa ga babu isasshen hutu, sai aikin Worawa da saukewa.
Ga shi ta kasa sakin jiki da ma'aikatan gurin, saboda yadda suke tsangwamarta, da nuna mata ?abilanci, saboda ita ba 'yar ?asar su ba ce ba. Sam ba sa gaban Nana, duk da tana Wan saka ido ta ga, ko akwai wata mai hankali da za ta ji ta yarda da ita, a kaikaice ta Wan fara ?wan?wasa cigiyar Sayyid. Sai dai gaba Waya ba su yi mata ba ma'aikatan gurin, gaba Waya ba ta ji ta aminta da ko mutum Waya daga cikin su ba.
Kullum da safe Al hussain, mutumin da ya Wauke ta aiki, sai ya zagaya su ya ga yadda suke gudanar da aikin safe da yamma.
Da ya zo ma'aikatan suke nutsuwa, kowa ce ta kame kanta, marasa kamun kai kuma su fara Wan karairaya. Shi kuma ya tsuke fuska yana basarwa. Sai dai da ya ga Nana sai ya saki fuska, ko ba ta kula shi ba, shi sai ya yi mata magana.

"'yar Nigeria ya al?awarinmu ne?"

Nana ta Wan saki fuska ta ce "Wanne?"

"Au har kin manta?"

Ta yi murmushi ta ce "Duk lokacin da ka shirya, sai mu fara"

Ya ce "Kin san akwai wani abokina, sonake kafin na haWu da shi, ko gaisuwa na iya da turanci, saboda ya iya turanci ni ban iya ba, ya juya yare ya yi ta magana ba na gane me yake cewa, to kin ga yakamata na ba shi mamaki nima"

Nana ta ce "Gaskiya ne, shi ma Buzu ne kamar ka?"

Al Hussain ya ce "Ya aka yi ki ka san ni Buzu ne?"

"Ga rawani nan ka na yi" ya yi dariya ya ce "Kash, to shikenan tun da kin gane, shi ma buzu ne, mun kwana biyu ma bamu haWu ba, ban je Agadez ba"

"Duk Buzaye a Agadez ku ke?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a, sai dai mun fi yawa a can, ko kina son zuwa ne? Mu na da wani gurin Abincin ma a can, babban wannan sai a mayar da ke can" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a tamabaya dai kawai na yi"

Ya jinjina kan ya ce "To yaya aikin?"

"Alhamdillah"

"To ma sha Allah, Allah ya taimaka"

Tun da suka fara hirar nan, Nana ta lura da irin kallon da ake yi mata, saboda ya tsaya sun yi hira. Sai dai ita ba kallon ne ya dame ta ba, a jikinta take jin sam ba ta kyauta ba, tsayawa da ta yi tana magana da Al Hussain har take yi masa murmushi ba, saboda ta san da Sayyid yana gurin, ko da makamancin wasa ba za ta taSa aikata hakan ba, saboda yadda yake tsananin kishinta.
A hankali ta ce "Ka yi ha?uri Sayyid, babu yadda na iya ne, duk a ?o?arina na son zuwa gare ka ne, ka yi mini afuwa" ta furta a hankali kamar mai raWa.

"Nana wai a ina ki ka san Al Hussain ne?"

Nana ta Waga kai ta kalli Shugabar gurin nasu, da take yi mata tamabaya cike da tuhuma. Kamar Nana ba za ta yi magana ba, sai kuma ta ce "Waye hakan?"

Matar ta ce "Kamar yaya?"

Nana ta ce "Wanda ki ke tambayata"

Gaba Waya suka kalli Nana, jin yadda take bawa Adama, shugabar Wakin girki. Ita kuwa Nana ko a jikinta da irin amsar da ta bawa Adaman.

Cike da takaici Adama ta ce"Mutumin da ya fita yanzu"

Nana ta ce "Au sunansa kenan dama? A nan Nijar na san shi, meyafaru?" Ta yi maganar tana tsare Adama da ido, tana jiran abin da za ta sake cewa.
Sai dai ta yi shiru ba ta kuma magana ba, su kuma suka hau mamakin irin amsar da Nana ta bata, kuma ba ta iya ce mata komai ba.
Gaba Waya Nana hankalinta ya koma kan sauran kwanaki nawa ta koma gida, duk da kullum sai ta yi waya da Nene. Amma ta ga kamar kwanakin ba sa matsawa sam.
Hajiya Amina revers ta yi, ta dawo gida Nigeria, saboda kiWima da tashin hankali da take ciki, ta rasa wanda za ta fara tunkara da maganar. Ta so samun mijin Alhaji Zailani a waya, ta fara yi masa bayani, amma ba ta same shi a waya ba. Ta koma gida a kiWime, amma ta tarar da sa?on ya yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login