Showing 156001 words to 159000 words out of 168002 words

Chapter 53 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

665

kawai ta yi ?wafa ta fice daga Wakin.
Ya koma ya jingina, ya lumshe idanunsa, sai kiran Jamila. Ya Wauka ya katse kiran ya kira ta cikin azarSaSi ya ce "?anwata lafiya kuwa? Ba kya Waga wayata ko haryanzu kina fushin ne?"

Cikin numfarfashi ta ce "A'a Yaya Abba, ba ni da lafiya ne haryanzu"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ya aka yi ba ki gaya mini ba? Kina gida ne?"

"Eh" ta amsa muryarta ?asa-?asa.

"To shirya gani nan, bari na zo mu je Asibiti"

"To Yaya Abba, na gode" ta ajiye wayar da ?yar. Hankalinsa ya yi mummunan tashi, a zatonsa aika-aikar da ya yi ce, ta sanya mata rashin lafiya har haka.
Da sauri ya zura kaya, ya Wauki mukullin motarsa ya yi waje ya tafi gidansu Jamila.
Yanayin yadda Jamila ta fito, tamkar ya je ya Waukko ta, fuskarta duk ta kumbura, da alama tana jin jiki sosai da sosai.
Ya buWe mata gaban motar ta shiga. Cikin tausayawa ya ce "Sannu ?anwata, haka jikin naki ya yi ba ki gaya mini ba?"
"Ba na son tayar maka da hankali ne, kai ma ba ka da lafiya, amma Mama fa ta kai ni Asibiti" Gabansa ya faWi ya ce "Allah ya sa ba ta gane komai ba"

Ta girgiza kai ta ce "Babu abin da ta gane, zazzaSi ne fa kawai"

A tsorace ya ce "Jamila ko ciki ne?"

Ta kalle shi, sai da ta ji kamar ta yi dariya, duk da halin da take ciki. "Tun kan hakan ta faru ai nake rashin lafiya, ba wannan ba ne ba, ba wani ciki".

Ya sake cewa "Amma duk da haka kamar ya assasa miki ciwon, amma bari mu je Asibitin" haka ya ja motarsa su ka bar layin.

Safiyya ce ta tarar da Hajiya Sa'a ta cika ta yi fam, tana zaune a falonta.
Da kyar Hajiya Sa'a ta iya amsa mata sallamarta. Ta zauna a kusa da Hajiya Sa'a ta ce "Mummynmu maganin kukanmu, lafiya kuwa na ga ranki a Sace?"

"Ba dole ki ganni a haka ba? Da gaske fa Abba son Jamila yake yi, nema yake ya bujire mini, kin ga yadda duk ya damu saboda na raba su. Ga bikinsa na ?aratowa da Yasmin.

Maman Khairat ta tuntsure da dariya ta ce "To meye a ciki, idan tana son sa ki bar su mana"

Hajiya Sa'a ta kalle ta ta ce "Amma ba ki da hankali,? yarinyar da shugaban ?ungiya suka kwanta da ita, sai Abba ya auri ragowa? Ba ma wannan ba, kar ki manta idan ?ungiya ta bu?aci ta bayar da jininsa fa, shikenan ta bayar da jinin tilon Wan nawa?"

Maman Khairat ta ce "Na fahimce ki Mummy, da wasa nake yi miki, amma maganar gaskiya yanzu haka kan na taho ma, na ga motar Abba a unguwarmu, kuma na san ba ku da kowa a unguwar, dan haka gurin Jamila ya je"

Cikin matsanancin Sacin rai ta ce "Gurin Jamila kuma? Yarinyar nan ta zame mini masifa da bala'i ko? Maganinta zan yi, wallahi sai ta rabu da Abba, ko ita ta haifar mini shi"

Maman Khairat ta ce "Ki yi dai a hankali, kin san halin yaran zamanin nan" Hajiya Sa'a ta ci gaba da huci, tamkar macijiya saboda takaici.

Maman Khairat ta ce "Ina dai ?ara gaya miki, ki bi komai a sannu, kin san halin yaran zamanin nan, sai su baki mamaki. Shi kansa Abban duk yadda yake yi miki biyayya, idan ba ki yi wasa ba, a wannan karon tsaf zai bujire miki".

"Ai ga alamu nan ina gani, amma ni zan sanya wa Abba doka, na hana shi abu, amma ya zagaye ya je ya aikata? Shikenan, na san matakin da zan Wauka. Da ni suke zancen.

Alhaji Fatuhu ne zaune a harabar gidan sa, a kan kujera, ya kan Wan iya dogara sanda ya tashi tsaye yanzu. Idan aka taimaka masa har harabar gidan yake iya fitowa, duk da idan jikin ya tashi kuma, sai ba ya iya hakan ko kaWan.
Yana zaune a harabar gidan, yana kallon ?aramin Wan sa na gurin Fadila, yana? ta wasa da Ball, yana jin yadda ?aunar Wan ke ratsa masa zuciya. Gefe guda yana tausayin yaron nasa, dan bai taSa iya saya masa abin naira biyar ba da kuWinsa. Hatta abincin da suke ci, 'yan uwa da abokan arziki ne suke kawo musu, ga shi wanda ya sai gidansa ya ba du aronsa suke zaune a ciki, ya fara ?ishin-?ishin Win yana bu?atar gidan.

Fadila ce ta ?araso tana murmushi ta ce "Daddy kallon Ball ka ke yi?"

Ya yi murmushi ya ce "Eh mana, yana ta in tashi mu yi tare, ina ma zan iya da ko sau Waya mun yi tare, no na saka shi farinciki"

Ta zauna a Waya daga cikin fararen kujerun, ta ce "A hakan ma, ka na sanya shi farin ciki ai"

"Fadila"

Ta tattara masa nutsuwarta ta ce "Na'am Daddy"

"Kin san wani abu?"

Ta ce "A'a sai ka faWa"

"Ina yarinyar nan Nana?"

"Wace Nanan?"

Ya Wan yi shiru sannan ya ce "Malamar Muhsin, da yake faWa"

Ta ce "Ohh Allah sarki, na tuna ta"

"Mafarkinta nake yi"

Ta Wan yi saroro ta ce "Mafarki kuma?"

"Eh Fadila, har aikawa na yi gidansu, a yi mini alfarmar a faWa mini inda gidanta yake, wani abu nake gani da ya fara damuna"

Ta danne kishinta ta ce "To ka yi mini bayani mana"

"Kin dai san ni ba ma'abocin, biye-biye ba ne ba, da yarda da harkokin shirme da zai sanya na ji wani zai iya cutar da ni ba, amma a jere sau kusan biyar ina mafarki da ita".
Cikin ?osawa ta ce "Daddy ka yi mini bayani, ka na ta kwana-kwana da ni"

"Ganinta nake yi a mafarki, tana ce mini an yi mini sihiri, karo kusan biyar fa"

Fadila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kuma ka yarda?"

"Ba ma son na yarda na gazgata hakan, amma na ji kamar na fara amincewa, saboda yadda nake ganinta abin ya yi yawa, ya wuce a ce shirmen mafarki ne kawai."

Fadila ta numfasa ta ce "Ai ni tuntuni na zargi hakan, amma sanin halinka na rashin son irin wannan abubuwan, ya sanya ba na yi maka maganar. Ko wannan sau?in da ka ke samu, na san tasirin addu'a ne. Dan kuwa Umma kuWi take bayarwa ana sauke karatun Alqur'ani."

Cikin mamaki ya ce "Amma ke kina ganin, akwai wanda zai damu da ni, har ya iya yi mini sihiri? Ina azkar Wina da addu'oina, gani nake sun wadace ni, babu wanda zai damu da ni ya yi mini wani sihiri."

Ta gyara zamanta sosai ta ce "A duk Duniya waye ya koyar da mu azkar Win? Na san za ka ce manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, amma an yi wa fiyayyen halitta sihiri, kuma ya kama shi.
Daddy ka yi ha?uri da abin da zan faWa maka. Kana ibadarka ta farilla daidai gwargwado, amma ba ka damu da nafilfili ba, da tsananta addu'a. Kana ganin Allah ya baka duk abin da ka ke bu?ata, ba ka fiye tsananta addu'a da neman kariyar Allah ba.
Sannan azkar da ka ke yi, kuma a yi shiri ya kama ka, ba ya nufin Allah baya kare ka, amma wata?ila jarrabawa ce daga gare shi,? kamar yadda ya ce zai jarrabe mu, ba a fasa jarraba mai imani, kuma jarrabawa alama ce ta soyayyar Ubangiji. Allah ya jarrabe ka da cuta, ka nemi magani shi ma a cikin jarrabawa ne, amma Daddy ka naWe ka dage, kai sai na Asibiti kawai, bayan akwai magungunan musulunci da suke na halal babu kauce hanya, idan an jarraba ba a san inda za a dace ba, amma ka ?i ka ce kai sai na bature, na baturen kuma ba a gano komai ba, kame-kame kawai ake yi."

Ya yi shiru yana nazarin kalaman Fadila, ya numfasa ya ce "To yanzu mene ne abin yi? Kin ga yanzu bani da kuWi, kuma irin wannan abubuwan sai da kuWi".

"Kar ka damu, zan yi wa Kawu magana, shi ma ranar da ya zo duba ka, ai ya ce a yi na islamic, Alhaji Zailani ya ce ba za a yi ba. Da haka za tuntuSe shi, in sha Allah ba zai gagara ba"

Alhaji Fatuhu ya ce "Allah ya sa, dama duk ina tsoron, kar a aikata abin da zai kauce wa hanya ne, amma na amince yanzu a yi Win"

Ta yi murmushi ta ce "To shikenan, yaya ita yarinyar an gano ta Win?"
Ya girgiza kai ya ce "Ina fa, an ce wai ba ma ta ?asar nan, amma ina ta mamakin dalilin da ya sanya nake mafarinta, kuma idan na farka sai na ji kamar a zahiri, shi ya sanya ma na fara yarda"

Fadila ta ce "To Allah ya sanya a dace" ya amsa da "Amin"

*

?angaren Nana kuwa, gaba Waya kanta ya kulle a kan lamarin nan, kawai sai ta dasa addu'a, a kan idan da alkhairi a tafiyarta, Ubangiji Allah ya sanya mata son tafiyar, ya tsare mata Muhsin, idan kuma babu, Allah ya cire mata abin daga zuciyarta.

Kamar yadda ta saba ji haka ma wannan karon, ta ji muryarsa, da gudu ta ajiye abin da take yi, ta nufi taga ta le?a sai ta hango giftwarsa da doguwar riga ba?a a jikinsa.
Da gudu ta fita daga gurin, ta nufe shi tana ?wala masa kira, amma ya Sace mata.
Cike da takaici ta yi juyi, tare da jan guntun tsaki, kawai ta ji hancinta ya fara shinshino mata, ?amshin wannan Wakin na cikin dutse, da take ganinsi tare da Sayyid.
Ta buWe idonta a hankali, ta ji ana shafar cikinta a hankali, tare da yi mata numfashi a wuyanta.
"Sayyid" ta furta a Wan tsorace.
"Asmyna, ina kewarki da yawa, gangar jikina na ta kewarki. Idan ina jin zafi babu mai bani sanyin da ki ke bani, babu wanda yake iya fahimtar kurman ba?in rayuwata, ki ?araso gare ni Please" ya yi maganar yana shafa wuyanta, tare da yin maganar ?asa-?asa.
Ta saka hannu ta shafa gashinsa ta ce "Ina ta gaya wa Allah Sayyid, ya san lokacin da ya dace ya haWa mu, amma jikina yana ba ni, ina daf da kai in sha Allah"
"Ki ?araso da wuri Asmyna, ina cikin matsananciyar bu?atarki"
"Ina ta ?o?ari Sayyid, kuma ina gaya wa Allah, na san zai haWa mu a nan kusa, kuma ina ro?onsa ya kare mini kai a duk ind????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
a ka ke, na san kuma yana ji ya kuma amsa in sha Allah"
"Nana, wai ba kya salla ne, gari ya fara haske fa" ta ji muryar Nene. Ta tashi tana mustustuke idonta, hancinta na ci gaba da jiyo mata sauran ?amshin turaren nan.
Da ta yi salla ta idar, ta je ta samu Nene a Wakinta, suka gaisa.

Ta ce "Nene na amince"

"Da me?"

"Zan tafi gurin yin girkin nan"

Nene ta ce "Ina fatan ba wani ne ya matsa miki ba? Ko kuma kunyata ki ka ji ba ki ka ce za ki je?"

Nana ta girgiza kai ta ce "A'a, wa ma na sani na saba da shi, da zai ziga ni na Wauka? Babu wanda ya ziga ni"

Nene ta ce "To shikenan, zan kira ta a waya na ji, idan ba a samu wata ba, sai ki je. Sai mu je gurin jami'an tsaro mu yi yarjejeniya mu yi rubutu, mu je a yi a gaban su Auwwalu ma da Hajara"

Nana ta girgiza kai ta ce "A'a Nene, na yarda da ke, abin duk bai kai haka ba ai"

Nene ta ce "A'a, haka kurum wani irin ki ka yarda da ni, Wan mutum fa zan ri?e miki, a'a, mu je mu yi a rubuce, yadda jami'an tsaro ma za su din ga sanya ido, kar wani abu ya faru ma. Sai dai abin da Allah ya aiko na ?addara wannan ba yadda muka iya, kuma na san za ki yi mini uzuri a wannan. Amma idan aka yi haka kema sai kin fi sakewa, hankalinki ya kwanta.

Nana ta jinjina kai ta ce "Ni dai, bakin da zan yi miki godiya ba ni da shi, amma ina fatan Allah ya yi miki tukuici da abu mafi dacewa da abin da ki ka yi mini na alkhairi, a duniya da kuma Lahira"

"Amin Nana, ai Wa na kowa ne, Allah ya tabattar mana da alkhairinsa, ya kuma bayyana miki mijinki da ahalinsa cikin aminci".

"Amin uwata ta kaina" ta yi maganar tana murmushi.

Sai dai tun da Nana ta amince za ta bar wa Nene Muhsin, ta fara jin kewar Wan nata, ta din ga jin kamar ta ce ta fasa. Saboda kallonsa kawai na sanya mata matsanancin farinciki da nishaWi, idan ta tuna mallakinta ne shi Win. Tana jin ko ba ta ga Sayyid ba tana da ?aramin Sayyid, duk da tana fatan ta gan shi Win, ko ba komai al'umma sa kalli Wan nata da kima da daraja.

Ko da Nene ta kira matar, Matar ta tabbatar wa Nene, akwai sauran space Win da Nana, za ta yi musu aiki, sai dai a saka ranar da za su tafi ta kai ta.

Haka nan fargabar Nana ta ?aru, ta rasa murna take ko tsoro, duk da abu mafi rinjaye kewar Wan jaririn Wanta ne, da yanzu take ?ara sha?uwa da shi,?aunarsa take ?ara shiga ranta. Tana jin tamkar ta fasa tafiyar nan, amma ?asan zuciyarta tana jin tafiyar ta ta alkhairi ne.

*

?angaren Abba kuwa, sai da aka yi wa Jamila ?arin ruwa, typhoid ne ya yi mata mummunan kamu.
Sai kuma damuwa da take ciki, jininta ya Wan hau. Abba ya biya duk bills Win, ya janyo kujerar Wakin, ya zauna a gaban gadonta, ruwan da aka saka yana shiga jikinta.

"Ko a kira Mama a waya a sanar mata ne?" Ya yi maganar cikin kulawa.

Ta ce "A'a, na gaya mata Asibiti zan je, ana gamawa sai ka mayar da ni gida"

Ya ce "To shikenan, mai zan sayo miki ki samu ki ci?"

"Ba na son cin komai, kawai kar ka matsa daga kusa da ni, ka zauna a nan" ta yi maganar tana ri?e hannunsa a cikin nata.
Ji ya yi zuciyarsa ta narke, da matsanancin tausayin kan su, ya ce "Ina tare da ke matata, har abada in sha Allah" ta yi murmushi tana ?ara ri?e hannunsa. A hankali kuma ta saki hannun nasa, da tuna rashin dacewar hakan, sai dai wani irin abu mai wuyar fassara take ji, game da Abban.
Yana kallon kiran Hajiya Sa'a, amma ya ?i Wagawa, kawai ya din ga jin zafinta.
Har azahar sannan ruwan da ake saka mata ya ?are, ya Wauke ta a motarsa, ya yi mata sayayya sannan ya mayar da ita gida.

Sai da ya tabattar ta shiga gida, sannan ya kira Mummy.

"Sai yanzu ka ga damar Waga wayar tawa?"

"A'a caji take yi ne, ki yi ha?uri?"

"Kana ina ne?"

Ya ce "Na Wan je wani uzuri ne, na zo ne?"

"A'a shikenan" ta ?yale shi, bayan tuna shawarar da Safiyya ta bata, wato maman Khairat.

*

Kamar yadda Nene ta bu?ata, sai da suka je gurin jami'an tsaro, suka yi yarjejeniya, aka rubuta da yaren hausa, French da kuma turanci, duk suka sanya hannu, a gaban su Auwwalu da jami'an tsaro.

Daga nan suka dawo gNene ta ba wa Nana wata 'yar madaidaiciyar Jaka, da za ta haWa kayanta da za ta bu?ata a ciki.
Ta kalli Nana ta ce "Nana dan Allah ki kula da kan ki, duk da na san ke kamammiyar yarinya ce, ba mutuniyar banza ba, amma tunatar da mumini abu ne mai kyau, ki ri?e mutuncinki, ki kiyaye hakkin aurenki. Idan ki ka ga wani abu na ba dai-dai ba, ko wanda ya saSawa addininki, a ha?ura da sabgar nan. Kuma cikin hikima za ki din ga bincikawar,ba sai kowa ya fuskanci ainihin abin da ya nai ki gurin bax

Nana ta jinjina kai ta ce "In sha Allah Nene zan kula da kaina, ba zan ba ki kunya ba, ki taya ni da addu'a, Ubangiji Allah ya sanya zuwana ya zame mana alkhairi baki Waya"

"In sha Allah, addu'a ina nan zan ci gaba da yi miki ita da yardar Allah."

Nana ta haWa kayanta, amma ji take kamar ta fasa tafiyar, amma ta ?arfafi zuciyarta, ta hana hakan yin tasiri a ranta.
Ranar Asabar, da safe matar ta zo domin tafiya tare da Nana.

Nene ta ce mata "Dan Allah gata nan amana, Hansatu, kar ki kai ta idan za a cutar da ita, kin ga yaro ne da ita ?arami, dan Allah idan akwai matsala a gurin nan, gara ki saka a sallamo ta ta dawo gida."

Hansatu ta ce "Haba Nene, ya ki ke haka kamar ba ki yarda da ni ba ne?"

"A'a ba rashin yarda ba ne ba, 'yar amana ce shi yasa nake jadda da miki, ga kuma ?aramin yaro da take da shi"

"Ba ki da matsala fa, ki kwantar da hankalinki"

Nana ta kalli Muhsin, da yake jikin Nene, yana wasansa, idanun Nana fal hawaye ta ce "My little Sayyid, zo ka yi sallama da Umminka" ya taso daga jikin Nene ya nufo Nana.

Hatta dogayen gaSoSin jikinsa, irin na Sayyid ne sak.

Ta rungume shi a jikinta, hawaye na zuba daga idanunta "Allah ka kula mini da Wa na, Allah kar ka saka wani abin cutarwa ya same shi, Ubangiji Allah ka sanya na je na dawo na tarar da shi lafiya" ta furta a hankali ?asa-?asa.

Ta Wago ta kalle shi ta ga yana yi mata murmushi, ta sumbaci goshinsa, ta mi?e ta Wauki jakar kayan nata, Nene ta rako su har bakin ?ofa, suka hau abin hawan da Hansatu ta zo da shi, suka tafi.

08081012143
Nana ta din ga waige, tana hango su Nene tare da Muhsin, har suka Sacewa ganinta gaba Waya.

Hansatu su na tafe su na ta? hira da direban motar, aka biya gidanta, aka Wauki wasu matasan matan sannan suka Wauki hanyar tafiya.

Tana jin yadda suke ta hirarrakinsu a cikin motar, amma ta kasa tofa komai, da ta rufe ido, Wan jaririnta take hangowa, gefe guda kuma zuciyarta cike da fatan Allah ya sa tafiyar nan, ta yi mata rana.

A ?alla sun yi tafiyar awanni biyu da rabi a mota, sannan suka isa wani gida.
Hansatu ta yi musu bayanin, a nan za su sauka su huta, washegari ta kai kowacce inda ta Waukko ta za ta kai ta. Nana ta din ga addu'a da fatan Allah ya sanya ba mugun hannu ta faWo ba, duk da kafin ta taho Nene ta bata layi ta saka a wayarta, ta ce mata duk abin da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login