Showing 3001 words to 6000 words out of 168002 words

Chapter 2 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

643

kwance. Shiru ya yi yana ?o?arin tariyo abin da ya faru.
Fes komai ya dawo kansa, amma daga iya lokacin da ya biyo Nana, suka yi ido huWu da wannan Buzun, ya kasa tuna komai.

Ya tashi zaune yana ?o?arin saukkowa daga kan gadon, sai ga Hajiya Amina ta shigo Wakin, hannunta Wauke da kofin tea.

"Sannu Alhaji ka tashi?"

"Yaushe ki ka dawo?"

"Tun la'asar, nan muka tarar da kai a sume, Haidar na ta kuka na ce Nanan ba ta zo ba ne? Amma doctor Sharif ya zo ya ce ba sai an kai ka asibiti ba, ya yi maka abin da zai yi maka, ya ce jininka ne ya Wan hau"

Ya yi shiru yana tunanin to meya same shi haka? Amma ya kasa tuna komai.

****

Nana kuwa tana shiga gidansu, gaba Waya suka mayar da hankalinsu kanta, saboda a yadda ta shigo gidan, idonta a rufe, ?afafuwanta babu ko takalmi.

Suwaiba ta ce "Jaraba"

Kukan tsuntsaye ne ya gauraye ilahirin dajin, sai kuma ?aton tafki mai Wauke da ruwa shuWi, sai rugugi yake yi, yana tambal-tambal.

Tana tsaye tana kallon ruwan, ?aisar ya bayyana a kan ruwan, yana shawagi yana kaWa ruwan.

"Wallahi ba ka da wani amfani a rayuwata, kana kallon za a ci mini mutunci, amma ba ka yi komai ba, ba ka da aiki sai ?o?arin haukata ni." Ta yi maganar a hasale.

Bai yi magana ba, sai ?ara girgiza ruwan da yake yi, ruwan ya watso har sai da ya ji?a ta, sannan ya ce "Allah ne zai tsare ki ba ni ba"

Cikin kuka ta ce "Ai dama ban ce kai zaka tsare ni ba, idan ma gatse ka ke yi mini ba zan taSa neman taimakon ka ba, amma na meye za ka din ga razana ni a gaban mutane, sai na fita hayyacina na aikata abin da zai saka a ce ba hayyacina nake ba?"

"Abin da ki ka gani haka yake ko a zahiri, ba yi na yi dan na tsorata ki ba kawai" ya yi maganar yana fitowa daga cikin ruwan, da wani ba?in mayafi a jikinsa, yana jan ?asa tare da Wigar da ruwa.

"Biyo ni" ya yi maganr yana yin gaba. Bin bayansa ta yi, suka ?arasa gaban wani dutse, ba ta san ya aka yi ba, ta gan su a cikin libraryn sa.

Ya ce "Wannan mutumin da ki ka gani yana kuka da hawayen jini, yana daf da faWawa mawuyacin hali, a saboda abin da abokinsa zai yi masa. Abu Waya yake damunsa da yasa za a iya galaba a kansa, ba shi da ri?o da ibada sosai, sai ba?ar a?ida da ra'ayin ri?au. Kuma ni ba na zama a guri mai ?azanta, ko gurin da ake ta'amalli da jini, mussaman na bil'dama, ta yaya zan zo inda ki ke, alhalin inda ki ke zuwa ana ta'amalli da jinin bil'adama?
Jininku ya fi jinin kowace halitta ?arni mara daWi, amma ya fi kowanne za?i da daWi idan aka sha. Shi yasa masu aiki da jininsin aljnun da suke ta'amalli da jini, da an ba su jinin bil'adama, suke aiki cikin gaggawa, domin babu jinin da ya kai na su za?i da daWi in ji masu sha".

Mudubin da yake gurin ya nuna mata, ya ce "Kalli" cikin tsoro da razani, ta kalli mudubin.

Alhaji Zailani ta gani tsirara, ana kwarara masa jini a jikinsa, yana buWe baki tare da ziro harshensa waje, jikinsa yana karkarwa.

Wata irin razana ta yi ta buWe idonta, karaf ya sauka a cikin na Baba.

"Uban me ya dawo da ke gida yanzu? Ko suma kin yi musu wani abun sun kore ki?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"To me ya dawo da ke gida yanzu?"

"Kaina ne yake ciwo"

"Ki sha magani ki koma, idan ma korar ki suka yi, ki san abin yi, dan wallahi ban san ina zan nemo kuWin nan na biya ba"

Ya gama faWansa, ya bar ?ofar Wakin, tana nan zaune ta ji sallamar Inna a tsakar gida.

Ta amsa daga Waki, tare da bata damar ta shiga.

"Nana ya na ganki a haka? Ba ki da lafiya ne?"

"A'a me ki ka gani?"

"Idonki ya yi jawur sosai fa"

Nana ta yi murmushi ta ce "Lafiya ?alau bacci na yi "

Inna ta ce "Bacci kuma? Ina gurin aikin?"

"Daga can nake" ta bata amsa

"Wallahi da can gidan aikin zan je, kawai na fara zuwa nan".

Nana ta karanto damuwa a fuskar Inna, ta ce "Meyafaru?"

"Muhsin fa ya rasu yau ne uku"

Wata irin zabura Nana ta yi, ta ja da baya tana bin ?wayar idon Inna da kallo, domin ta gazagata abin da yake fitowa daga bakin Innan.
"Ba Muhsin Fatuhu ba amma ko?" Nana ta yi maganar cikin tashin hankali, da ya gaza Soyuwa a kan fuskarta.
Ayshacool
Cikin damuwa Inna ta ce "Shi mana, idan ba kya komai ki tashi mu je ki yi musu gaisuwa, an gano gidansu mun je ma daga makaranta".

Tamkar an tsinkewa Nana laka, haka jikinta ya mutu la?was, fatan ta a ce bacci take yi kawai mafarki ne. Can kuma sai mafarkin da ta yi da Muhsin Win ya dawo mata fes.
Zabura ta yi tai waje, Inna ta bi bayanta, tana kiran sunan ta.
Baba da yake tsakar gida ya ce "Lafiya ina za ki haka?"

Inna ta ce "?aya daga cikin Walibanta ne ya rasu za mu je gaisuwa" gaban Baba ya faWi cikin tsoro, ya fara fargabar kar dai ta tabbata iskokan Nana ke kashe wanda take mu'amala da su?.

"To Allah ya ji?an sa"

Inna ce ta amsa ta bi bayan Nana.

Inna ta tare musu abin hawa, suka hau suka tafi. Sam Nana ba ta gane abubuwan da Inna take faWa, fatanta kawai ya zamana mafarki ne ba gaskiya ba. Saboda akwai kyakkyawar sha?uwa a tsakaninta da Muhsin, saboda lokacin da aka kawo shi ma, bai kai a Wauke shi ba, saboda ?an?antarsa, har goya shi Nana take yi, Allah ya sa mata ?aunar yaron a zuciyarta.

Sosai ake zaman makoki a gidan Alhaji Fatuhu, Wan sa bai taSa mutuwa ba, sai a kan Muhsin, shi ne ?arami amma ya shiga ransa.
Rumfuna aka kafa a cikin gidan, inda yake karbar gaisuwa, cikin gidan kuma mata ne suke karSa gaisuwa. Gida ne katafaren gaske, ga girma ya sha kayan alatu.

Alhaji Fatuhu yana tsaye yana gaisawa da wasu, ya ga wucewar Nana da Inna.
Jikinsa ne ya yi sanyi, ganin yanayin tashin hankalin da yake kwance a kan fuskar Nana.

Inna har falon ta raka Nana, don yi wa babar Muhsin gaisuwa.

A gigice Nana ta shiga falon, kamar mai neman wani abu, ta tsaya tana rarraba ido ba tare da ta cewa kowa komai ba.

Inna ta taSa ta ta ce "Ga mahaifiyarsa ki yi mata gaisuwa"

Nana ta kalli matashiyar matar da ba ta wuce shekara ashirin da huWu ba, idanunta jawur.

Nana ta ?arasa gabanta ta risuna ta ce "Baiwar Allah wai dan Allah Muhsin ya rasu?"

Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama a falon, suka amsa Nana ta waiwaya tana kallonsa ya ce "Nana kin samu labarin mutuwar Wan ki ko?" Sai mahaifiyar Muhsin ta zabura ta ce "Ke ce Nanan dama? Muhsin har ya rasu kafin ya daina magana sunan ki yake kira, yana cewa a kai shi gurinki" sai a lokacin Nana ta ji kuka ya ?wace mata, Inna take ba su labarin Nana ta je makaranta ganin Muhsin lokacin ba shi da lafiya ba ya zuwa makaranta.

Cikin kuka maman ta ce "Na gode sosai da sosai, ?aunar da ki ka nuna masa ce ta sanya, duk wanda ya san shi, zai san sunan ki a bakinsa"

A wannan karon ta yarda da zancen mutane, ta fara lura da duk wanda ya shiga ranta take son shi, sai ya rasa rayuwar sa.

"Wai ke ba za ki daina kukan nan ba, kamar a kan ki aka fara rashin Wa? Wannan ai rashin tawakalli ne?"

Nana ta waiwaya ta kalli mai maganar suka yi ido huWu. Matar ta ce "Ahh wannan ba Nana ba ce, yayar Jamila"

Alhaji Fatuhu ya ce "Kin santa ne? Antyn su Muhsin ce a Young talented academy"

Hajiya sa'a ta ce "Na santa, ba ki gane ni ba ne?" Nana ta girgiza mata kai alamar a'a.

"Ba da ke mu ka haWu kwanaki a gidan maman khairat ba?" Nana ta sake Waga ido ta kalle ta, a take ta so ta nemi nutsuwarta ta rasa.
Wani abu mai muhimmancin gaske take son tunawa, amma abu ya gagara sai ma wani irin sarawa da kanta ya yi.

Hajiya Sa'a ta nemi ta rasa nutsuwar ta, ganin fuskar Nana tana canzawa kamar ba ta mutum ba, tana wani irin ja tamkar an shafa mata jar kala. Neman guri ta yi ta zauna da sauri, jin jiri zai Webe ta.

A hankali Nana ta Wauke kanta, daga kallon hajiya Sa'a, ta yi musu gaisuwa, ta tashi jiki a sanyaye ta ce tafiya za ta yi.

Mahaifiyar Muhsin ta ce "Bari mu je ki yi wa kakarsa gaisuwa dan ita ma ta sanki a bakinsa.
Haka Nana ta din ga yi musu gaisuwa, tana jin tamkar su ma suna zargin ita ta kashe musu Wa, mussaman da aka ce yana ta kiran sunanta.

Ta rako Nana har harabar gidan, tana ci gaba da yi mata godiya. Alhaji Fatuhu ya ?araso ya ce "To Nana Allah ya ?ara mana ha?urin rashin Muhsin"

Ta jinjina kai amma ta kasa magana. Ya kalli maman Muhsin ya ce "Yanzu Alhaji Zailani ya kira ni, yake bani ha?uri bai shigo ba yau, ba shi da lafiya ne wai"
Ayshacool
"Ai Wazu Hajiya Amina ta zo da safe tare da mai aikinta sun kuma yi mana gaisuwa ai ba komai sun yi ?o?ari mun gode sosai"

Gaban Nana ya yi mummunar faWuwa, ba dai Alhaji Zailanin dai da ta sani ba, tuno abin da ta gani a falonsa Wazu ta yi. Sai dai ta rasa me ma za ta ce, wata?ila ma ?aisar ne kawai yake wasa da hankalinta.

Haka suka kama hanyar komawa gida.

Nana na komawa gida la'asar, kasancewar ba ta salla, sai ta shiga ta yi wanka ta kintsa jikinta.
Wani abu mai Waci ya tsaye mata a wuyanta, har ya fara ?o?arin hana ta numfashi.
Ba ta ko iya gani saboda azabar jiri da ciwon kai, ta kwanta ta yi shiru ta rufe idanunta, ta din ga tuna mutanen duk da suka rasa rayukansu da yanzu ita ma take kyautata zaton saboda ita ne.
Ta fashe da kuka, tana "Wannan wace irin rayuwa ce, gaba Waya na kasa tantance ni mece ce ma gaba Waya. Allah ya tsinewa tsohuwar da ta gada mini wannan masifar wallahi ba zan yafe ba".

*
Malam Gambo mai allon ?asa ne zaune a kan buzunsa, ya nutsu yana sauraren Alhaji Zailani.

"Ni dai abin nan ya firgita ni malam, ni ban taSa abu makamancin haka ba, yanayin kamar Wimuwa ko gushewar hankali"

Malam Gambo ya numfasa ya ce "Me yasa ka yi gaggawa? Wutar ciki ce da kai Alhajin Allah, ai a sannu za ka bi ta, ba kowacce yarinya za ka yi wa irin wannan tayin kai tsaye ba, mussaman idan ba ta saba ba, duk lalacewar zamani akwai na Allah"

"Wallahi kuwa yarinyar ta bani mamaki, akwai taurin kai na tsiya"

"Yanzu ba wannan ba, matsalar da nake gaya maka akwai, ita na du?ufa bincike a kai, kwanaki ba akwai wani wuridi da na yi maka ba, na kira wani aljani ya yi mana aiki ba ya ?i?"

Da sauri Alhaji Zailani ya ce "Eh an yi haka"

"To wannan aljanin shi ne a kanta, goWiyarsa ce"

Alhaji Zailani ya waro ido ya ce "Haba, ni fa na ce, wallahi da ta buge ni ta wuce, kamar wani ingarman doki ne ya hankaWe ni"

"To ya zame maka dole ka kula ka yi taka tsantsan, ka bi a sannu burinka ya cika idan ka ci gaba da far mata zai iya ajalinka!"

"Ajalina fa ka ce?"

"?warai da gaske, hatsabibin matashin saurayin aljani ne, ba ya neman rigima da kowa amma idan aka taSa shi faWa da shi ba ya ?arewa har abada"

Alhaji Zailani ya jinjina kai cike da gamsuwa, dan kuwa a rayuwarsa babu babban abin da yake tsoro sama da mutuwa, ko zancenta ba ya so gani yake, yana da cikakkiyar lafiya da ba za ta tunkaro shi a daidai wannan lokacin ba.

Sai da Nana ta shafe kwanaki uku, babu lafiya ga wani irin zazzafan zazzaSi da take fama. A kwana na huWu ta lallaSa ta koma gidan Alhaji Zailani.
Hajiya Amina na ganinta cikin damuwa ta ce "Nana kwana biyu lafiya kuwa?"

"Wallahi Hajiya ba ni da lafiya ne"

"Allah sarki, ga shi ke ba waya balle a ji halin da ki ke ciki, Haidar duk ya damu yana ta tambayar ki."

Tana rufe bakinta sai ga Haidar ya fito da gudu, ya Wane jikin Nana. Sai ta tuno da Muhsin, take wata fargaba ta shige ta, kar shi ma abin da ya samu Muhsin ya same shi, saboda sun sha?u sosai. Jiki a sanyaye ta rungume Haidar.

"Nana anya kin warware kuwa, bari na kira Doctor Sharif ya zo ya duba ki, duk kin yi zuru-zuru".
Ita dai Nana ba ta ce komai ba, har mamakin kirkin Hajiya Amina take yi.

Har gida doctor Sharif ya zo, ya duba Nana, ya bata magunguna da allurai, ya saka mata ruwa a gidan. Ganin Nana a kwance duk sai Haidar ya damu, ya koma kusa da ita ya kwanta shima.
Nana cike da ?aunar yaron take kallonsa, tana tuna Haidar, ta din ga addu'a Allah ya kare shi ya kiyaye shi, kar abin da ya samu Muhsin shi ma ya same shi.

Kafin yamma Nana ta Wan ji ?warin jikinta, har ta din ga Waga Haidar tana yi masa wasa, saboda yadda duk ya damu, da ganinta a kwance.
Hajiya Amina ta fito falon ta mi?owa Nana waya, Nana ta saka hannu ta karSa tana kallonta.

Ta ce "Tun da shi sirikin nawa, bai kawo miki waya ba, ni ga shi na baki, ki lallaSa da ita, bai kamata a ce budurwa kamar ki ba ta da waya ba. Ga dubu uku, idan kin fita ki tsaya ki sai layi a yi miki rijista ki saka a ciki, in sha Allah nan da kwana uku za a biya duk ma'aikatan gidan nan albashin su. Ko wani abun ne ya faru kya din ga bugo waya ki sanar"
Ayshacool
Nana ta juya wayar, da gani ba wani amfani aka yi da ita ba, sai ?yalli take yi, har da charger.

"Yanzu Hajiya wannan tawa ce?"

"Eh mana Nana, ko ba ta yi miki ba?"

Nana ta girgiza kai ta yi murmushi ta ce "Wallahi ban taSa zaton zan ri?e waya mai kyau da tsada har haka ba. Allah ya faranta miki, ya kula miki da zuriyar ki, ya dauwwamar muku da farin ciki na gode sosai da sosai"

Hajiya Amina ta yi murmushi ta ce "Nima na gode sosai, ina jin daWin yadda ki ke kula da Haidar da zuciya Waya, na ga kina da yawan ibada da azumi, dan Allah ki yi mini Addu'a idan ina da rabo Allah ya bani haihuwa" Turus Nana ta yi tana kallonta, a wannan shekarun nata me za ta yi da wata haihuwa?.

Ta yi murmushi ta ce "Kin yi mamaki ko? Ai ban taSa haihuwa ba, ki ro?a mini, idan kuma ba ni da rabo, Allah ya ?ara mini dangana"

Nana a ?asan zuciyarta murna ta taya Hajiya Amina, na rashin haWa zuriya da wannan majanunin mijin nata mara addini. Amma a zahiri ta ce "Ki yi ha?uri Hajiya, kin san komai rabo ne, kuma Allah ya fi mu sanin abin da ya dace da mu. Ko kin bar duniya in dai Wan Adam zai rama halacci ire-irena da yaran da ki ka ri?e, za su yi miki addu'a. Kar ki manta ba ke kaWai ba ce uwar mumunai Allah ya ?ara mata yarda, ba ta samu haihuwa ba amma uwa ce ga dukkanin muminai, a rashin samun haihuwar nan, ke ba ki san me Allah ya tanadar miki ba, wanda bai bawa waWanda suka haihu ba" kai tsaye kalaman Nana suka din ga shiga zuciyar Hajiya Amina, da sai da hawaye ya cika mata ido. Ta ji daWin kalaman Nana, na ?warin gwiwa, ta yi mamakin yadda Nana ta iya tsara maganganu cikin hikima.

"Na gode sosai Nana, kin ?ara sawa na ji nutsuwa, Allah ya ba ki zuriya ta gari. Ka da Allah ya jarrabe ki da ?addarar rashin haihuwa. Duk ta tawakallinka, akwai gaSar da mutane mussaman 'yan uwanka mata sun saka ka ji tamkar ba ka da amfani."

"Amin na gode sosai Hajiya. Amma ta ki jarrabawar ki ka sani, da wata jarrabawar gara rashin haihuwa sau dubun dubu" haka su ka din ga hira da Hajiya Amina, har lokacin tafiyar ta ya yi.

Tana shirin tafiya, Shukura ta dawo, Haidar yana kallonta, amma bai damu ya je gurinta ba, ya rirri?e Nana yana cewa zai bi ta ta tafi da shi ba. Da ?yar ta lallaSa shi, ta fita.

Habu na ganinta ya taso zai buWe mata gate, ya ce "Malama har kin taso?"

Nana ta ce "Eh malam Habu, shekaranjiya na zo zan fita, duk ba kwa nan"

"Eh wallahi mai gidan nan ne ya aike mu"

Ta ce "Allah sarki, yauwwa dan Allah ina wannan Wan uwan naku?"

Habu ya ce "Wanne daga ciki?"

"Wannan Win nan"

"Ya sunan shi?"

Nana ta girgiza kai ta ce "Ban san sunansa ba, Waya Wan uwan naku dai Sule ya ce mini ba shi da cikakkiyar lafiya, kurman nan" Habu ya kwashe da dariya ya ce "Kayya ba kurma ba ne ba yana magana"

Ta ce"To ai shi kullum baya magana, fuska a rufe kamar amarya. Shi ya buWe mini ?ofar ranar na fita"

"Allah sarki, yana gane komai, kawai da larura ce a ?wa?walwarsa, ba kuma wai hauka yake yi tuburan ba, wasu lokutan ma sai ya shafe sati bai ce uffan ba, yana kwance ma ba lafiya"

Cikin tausayawa Nana ta ce "Allah ya sauwwa?e, na tafi sai da safe"

"To sauka lafiya, Allah ya tsare" ta amsa da Amin ta tafi.

?oye wayarta ta yi, saboda ta san tsaf Baba zai ?wace wayar nan, mussaman yanzu da yake neman kuWi ido rufe.

Bayan Nana ta koma gida, Jamila take tambayarta ashe sun haWu da Hajiya Sa'a a gidan rasuwa, amma ta ce ba ta santa ba.

Nana ta ce "Ina cikin jimami da alhinin mutuwar yaron ne, shiyasa na kasa gane ta"

Jamila ta ce "Allah sarki, ashe yaron ma s??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????unanki ya yi ta kira kafin ya rasu"

Nana ta kalli Jamila daga sama zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login