Showing 60001 words to 63000 words out of 168002 words

Chapter 21 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

650

jajayen kaya, ya nufo shi yana faWin "Ka kusa makara fa"

"A yi mini afuwa, amma ina fatan wannan aikin zai zama daidai da sadaukarwata ta shekara".

"?warai kuwa, ba za a sake neman jini daga gare ka ba a wannan shekarar"

Ya mi?a wa Malam Gambo jaririn, ya saka hannu ya karSi yaron, ya Waga jaririn kansa a ?asa, ?afafuwansa a sama, ya danna tafin ?afar jaririn, a take ya tsanyara ihu, ihun jaririn ya cika dajin.

Malam Gambo ya haska fitila, ya Waukko wani abu a cikin wata jaka, ya saka shi a wuta, ya yi ja ya juya bayan yaron, ya zana wani hatimi a jiki, ya sanya sunan Fatuhu Magaji a cikin hatimin. Yaron ya din ga tsala ihu tamkar ana zare masa rai.

Suka haWu da shi da Malam Gambo, suka tona rami, suka binne jaririn da ransa.

Duk da ba yau Alhaji Zailani ya saba irin wannan abubuwan ba, amma na wannan karon shi kansa ya girgiza zuciyarsa.

Malam Gambo ya Wauki mahaifar, ya ce "Wannan na 'yan aike ne, su za su cinye ta, kai za ka iya tafiya, bayan kwana talatin za mu zo a cire ?warangwal Win, za a yi wani aikin da shi. Ka huta ka yi yadda ka ke so Alhajin Allah, in dai Duniya ce ka same ta yadda ka ke so".

Suka yi sallama Alhaji Zailani, ya hau motarsa ya nufi gida.

A wani irin mugun razane Nana ta tashi daga nannauyan baccin da take yi, ta tashi zaune. Tsaf abin da ta gani ya dawo mata kai fes ba ta manta komai ba.

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ka duba lamarin nan, Allah ya sa shirmen mafarki ne"

Tashi ya yi zaune shi ma ya ce "Me ya faru?"

Ta yi ?o?arin Soye damuwarta ta ce "Babu komai, maganar ta dawo?"

"Eh" ya faWa a ta?aice.

"Sannu ya jikin?"

"Alhamdilillah"

"Ko na Waukko maka maganin da aka bani, ya ce yana da kyau ka jarraba sha"

Ya ce "Ba na sha" ya yi maganar yana kwanciya.

Ta dafa shi ta ce "Sayyid, duniya ba za ta yiwu mu rayu mu biyu ba kawai, dole wasu lokutan mu na bu?atar taimakon mutane, dan mu rayu cikin aminci mu ma. Na san ha??o?inka na aure da suke kai na, dan baka da cikakkiyar lafiya ba ya nufin zan ci amanar auren ka.
Na san ni Ahalinka ce, kuma wani shinge da babu wanda zai ratsa shi." Ya yi mata shiru.

Ta kwanta a gefensa, tana shafa gashin sa, ta ce "Sayyid ka yi mini magana mana"

"Ba ki san me nake ji ba ne"

"Na sani mana, ka manta ruhinmu Waya ne?" Ya yi shiru ya lumshe idanunsa yana jin daWin, yadda take wasa da gashin sa.

"Sayyid"

"Ma vie"

"Dan Allah da gaske Alhaji Zailani ya ce maka ka sake ni?"

Kamar ba zai yi magana ba ya ce "Eh, ya ce zai ba ni kuWi. Zuciyata kamar zan mutu a ranar"

Ta ce "Me ka ce masa?"

"Ba zan iya tunawa ba, kawai dai na ji numfashina zai Wauke ne, na manta meyafaru"

Ta Wan yi murmushi ta ce "Rayuwa kenan, daga ni har kai dai gamu nan kawai, Allah ya shiga al'amarinmu. Sayyid ina jin tsoron kar ka tuna waye kai, ni kuma ka manta da ni"

Ta ji shiru, bai yi magana ba. "Sayyid " ta kira sunansa, amma tuni ya yi bacci. Saurin baccinsa har mamaki yake bata.

Zuciyarta kuma ta ci gaba da hasko mata mummunan mafarkin da ta yi, da Alhaji Zailani, dan haka take ta fatan, gari ya waye, ta kira Hajiya Amina ta ji yaya ake ciki.

Sai dai ta kasa komawa bacci, ta din ga tunane-tunane daban-daban a cikin ranta.

Ba ta san adadin lokacin da ta shafe a haka ba, ta ji ya ce "Ba ki yi bacci ba haryanzu? Mafarki ba gaske ba ne ba fa"
Ayshacool
Nana ta ce "Ba mafarki na yi ba, na kasa baccin ne"

"?arya babu kyau, kin tsorata a mafarki. Kuma kin gaji ma yau sosai, kina ta kula da ni, na gode sosai bari na yi miki tausa"

"A'a ci gaba da baccinka, daga tausar nan har a yi asuba ba zan yi bacci ba, bar ni kafin a kira salla na rage na yi baccin"

Dariya ta ji yana yi ya ce "To a bari sai bayan sallar asuba"

"A'a ba ni da lafiya" ya ?ara matsawa kusa da ita, ta ji shiru har ya sake komawa bacci.

?aisar ta gani yana Waure Sayyid a jikin wata itaciya. A razane ta nufe shi ta ce "?aisar mene ne haka? Me ya yi maka?"

"Kar ki kuskura ki zo gurin nan, ai na gaya miki tun da ya kwance ?ullin nan, sai ya WanWana shi ma"

Nana ta ce "Wai tayaya ya kwance Waurin da ka yi? Shi da ba aljani ba, kuma bai san abin da yake Soye ba, ka sauke shi dan Allah"

"Ke ki ke ganin shi mutum kamar kowa, na gaya miki kar ki kuskura ki zo gurin nan, zan yi miki illa"

Ba ta tsaya ba ta ci gaba da tunkarar sa.

HankaWe ta ya yi gefe, ya cigaba da Waure Sayyid a jikin itacen nan.

Ta yin?ura ta tashi da ?yar, ta sake nufar sa, sai dai kafin ta ?arasa, tsohon nan ya bayyana ya make ?aisar gefe.

Da sauri Nana ta ?arasa, ta hau kwnace Sayyid da yake a galabaice, ya fita daga hayyacinsa. FaWa ne ya kaure tsakanin ?aisar da tsohon.

Sayyid ya yi shiru, ya zubawa Nana ido, yana jin duk yadda take, furta abin da take gani a cikin mafarkinta a zahiri.

Ya cigaba da kallon fuskarta, ds yadda gumi ya tsatstsafo mata a goshinta, ta rirri?e shi gama tana kuka.

Ya saka yatsunsa biyu a ?yerta ya danna, a take ta yi shiru, jikinta ya saki.

Da Safe yana ta bacci, ta tashi ta yi aikace-aikacen ta.

Bayan tashin sa ya karya, ya yi wanka ya fita waje, sai dai tun da ya tashi bai yi magana ba.

Ta gama aikinta ta fito, ta nufe shi ta zauna a kusa da shi tana yi masa hira, yana jin ta amma ba ya magana.

Kubra ce ta nufo inda suke zaune, tana tahowa ya sunkuyar da kai.

Nana ta tashi ta ?arasa inda take, ta ce "Sannu ina zuwa haka?"

"Fita zan yi"

"Ki je ina?"

"Fita kawai zan yi" ta bawa Nana amsa.

Nana ta mi?a mata hannu da nufin su gaisa.

Ita ma ta mi?a mata suka gaisa, sai dai a wannan karon Nana ba ta ji sanyi ba. Nana ta kalle ta daga sama zuwa ?asa, riga da wando ne na bacci a jikinta, kanta ko Wan kwali babu.

Nana ta ja ta Wakinsu, ta shimfiWa mata sallaya ta ce "Zauna" babu musu ta zuna.

Nana ta zuba mata abinci ta ce "Na ji an ce ba kya cin abinci, bismillah mu ci" babu musu ta kama cokali ta na cin abincin.
Cikin tausaywa Nana take kallonta, tana matu?ar jin tausayin mai fama da irin wannan larurar, wanda duk ba shi yake Wauke da larurar ba, ba zai gane wahalarta ba. Mussaman idan na kusa da shi, ba su fahimci kan ciwon ba.

Ta cinye tas, Nana ta Wauke kwanon ta kalli Nana ta ce "Na daWe ban ci Abinci da yawa ba"

Cikin kulawa Nana ta ce "Me yasa?"

"Ba na so kwata-kwata. Ba ma na iya bacci."

"To me ki ke ji a jikin ki?"

Ta Wan yi shiru ta ce "Kawai dai ji nake mutuwa zan yi, sai na yi ta kuka"

Nana ta tashi ta Waukko mata pillow, ta ajiye mata ta ce "Kwanta da yardar Allah za ki yi bacci" ta kwanta ta yi shiru, Nana ta kunna mata karatun Alkur'ani. Ta nutsu tana saurara, har bacci ya Wauke ta. Farin ciki ya kama Nana, ganin ta yi bacci. Ta ce "Ya Allah, kai ka ke jarraba bayinka da larura, wasu ka haska musu maganinta, wasu kuma ka Soye. Ya majiSancin lamarinmu, Allah ka yaye mana wannan larurar".

*

Misalin ?arfe goma da rabi da safe, Baba yana ya bala'in an ba shi koko Wan kaWan babu sugar, alhalin an san ba isar sa zai yi ba.

Mama ta ce "Da ka samu wannan Win ma, Jamila ce ta bayar da kuWin gasarar, yarinyar da ka ke nufi da sharri kai da Wan ka, sai ka bari idan ka nemo, ka fara kawowa sai ka nuna isa da iko"

Sallamar da aka yi ya amsa, yana jiran ya ga suwaye, sai dai ya saroro baki buWe yana kallon masu sallamar. Su ka shigo ni?i-ni?i da kaya a hannun su.

Mama ta fito daga kitchen, ta ga suwaye, ta ce "Too ikon Allah, yau kuma da abin da muka tashi kenan?"

"Lafiya yaya aka yi?" Ya tambaye su kamar ya ga annoba.

"Malam Isa ai kwa bamu guri mu tsuguna tukuna"
Ayshacool
"Ba wani a baku guri ku tsuguna, ba na son fitina, meya kawo ku?"

?aya daga cikin su ta ce "A'a duk ba abin zafi ba ne ba ai, labarin auren Nana mu ka ji, shi ne muka zo mu tabattar"

Baba ya ce "Eh, haka ne na aurar da Nana, tun da 'yata ce, kuma ina da hurumin aiwatar da hakan"

Saude ta ce "Haka ne, amma mahaifiyarta da mu ma, mu na da hakki a kan ta, ai yakamata a sanar da mu"

"Ba zan sanar ba, na ce ba zan sanar ba Win? Me sanar mukun zai amfanar?"

Mama ta ce "Rakiya auren ne fa aka yi shi babu shiri, saboda magana ta nemi ta Waukko mana aka yi shi, ba wani taron kirki aka yi ba"

"Amma duk da haka, ai ya kyautu mu sani"

Baba ya taso kamar zai dake su ya ce "Kin ga ku bi hanyar da ku ka shigo mini gida ku fita".

"Dan Allah Malam Isa ka yi ha?uri, abin duk bai kai haka ba, ka bari a kaimu ko gidan nata ne, mu ga Wakinta, mu gaisa da ita, mu ba ta sa?on mahaifiyarta"

"Na yi muku iyaka da 'ya ta, ba zaku taSa ganinta ba, ba ta bu?atar ku, ku bar mini gida, kafin na yi muku Wibar albarka"

Ganin babu mutunci a lamarin Malam Isan, ya sanya suka kwashi kayan da suka zo da su, su ka fice.

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
Hargowa da bala'in da Baba ya yi wa su Adda Rakiya, ya yi masifar Sata musu rai, a zaton su duk abubuwan da suka faru a baya sun riga sun wuce, dan aure ya mutu ba ya nufin a wanzar da gaba a tsakanin yara da mahaifiyar su, ko a yanke duk wata da za su yi ala?a da ita.

Ga gajiyar tafiya da su ka sha a mota, amma Baba ya yi musu wannan mummunar tarbar.

Can gidan su Nana kuwa, ana ta neman Yusra, ba a ganta ba, hankalin Hajiya Halima ya yi mugun tashi, suka fito neman ta harabar gidan tare da Siyama.

Gurin Sayyid su ka nufo, Hajiyar take tambayarsa "Dan Allah yarinya ba ta zo ka buWe mata ?ofa ta fita ba? Wata 'yar fara haka?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.

"Na shiga uku, ni kuwa ina yarinyar nan ta shiga haka? Kirawo mini Nuradeeni a waya, ko sun fita tare?"

Siyama ta ce "Su fita tare su je ina, su da ba shiri suke yi ba, ina zai kai ta? Wata?ila tana cikin gidan nan wani gurin ta samu ta shige kawai"

"To tana cikin gidan nan, mu ganta mana"

"Ki yi ha?uri mu koma, mu ci gaba da duddubawa"

Nana kuwa ba ta san me ake yi ba, tana zaune a gefen Yusra, tana bin karatun Alkur'ani da ta kunna a wayarta. Ta ji daWin yadda take raira karatun yau, ba tare da ta ji kanta ya fara ciwo ba, ko ta fara jin sanyi ba. Yusra kuwa baccinta take yi da gaske.
A ?alla ta kai awanni biyu tana bacci, har Nana ta idar da karatun Al?ur'anin, ta Wora girki. Ta kammala babu jimawa ta farka daga baccin. Nana ta saka ta yi alwala, ta ba ta hijjabi ta yi alwala ta yi salla. Ta sake zuba mata abinci ta ci, sannan ta ce "Mu je na raka ki cikin gidan, zan zubawa mijina abinci shi ma na ba shi"

Ta kalli Nana ta ce "Ki na da miji?"

Nana ta jinjina kai ta ce "Eh, ina da shi, shi ne a waje yake yi muku gadi"

Yusra ta ce "Mhmm ni da na fara rashin lafiya, shekara biyu kenan, mijina ya sake ni, ya ma yi aure ba zai zauna da ni ba. Ba wanda ya san me nake ji, amma ke na ga kamar kin san me yake damuna, ke ba za ki ce ?arya nake yi ba. Mami ta ce "Ina sane na kashe aurena, na ji haushi sosai da sosai"

Nana ta ri?e hannunta ta ce "Ki yi ha?uri, na ki ?alubalen kenan, tabbas na san ciwon nan, na san babu daWi, kuma babbar jarrabawa ce a ce na kusa da mu sun kasa fahimtar mu, su din ga ganin muna sane muke yin abin da muke. Dan haka dolenmu ne, mu dage mu yi ta adduo'i da azkar domin Allah ya bamu lafiya"

Ta jinjinawa Nana kai ta ce "Na gode sosai da sosai"

Nana ta tashi suka fito daga Wakin, dama Sayyid a matse yake ya shiga Wakin, zaman Yusra a Wakin ya hana shi shiga.

"Wannan ne mijin naki?"

"Eh shi ne"

Ta ce "Sannu dattijo"

Ya Wago ya kalle ta, ya Waga mata hannu. Ta yi murmushi kawai.

Nana ta ce "Dattijo kuma?"

"Eh, ke matashi ki ke gani, ni kuma Dattijo nake gani, duk da kema ki na ganin haryanzu dai ki na wasi-wasi ne"

Nana ta ce "Haula"

Ta amsa da "Na'am uwar gijiyar ?aisar"

"Amma me yasa za ki yi mini haka? Matar ta farfaWo ta samu ta ci abinci, ta yi bacci kuma kawai sai ki zo za ki sake burkita ta"

Yusra ta yi murmushi ta ce "Tuba nake, wallahi ba da wata manufar na zo ba, gaisuwa na zo kwasa kuma na yi sai anjima"

Nana ta Wan ?ura wa Sayyid ido, amma ya ?i kallonta, ya tafi Wakin su. Ta jinjina kai a hankali ta ce "Biri ya yi kama da mutum"

Har cikin falon Nana, suka shiga tare da Kubra. Hajiya Halima na ganinsu ta mi?e ta ce "Laa a ina ki ka ganta? Tun Wazu muke bulayin neman ta a cikin gidan nan"

Nana ta ce "Subhnallah, wallahi ban sani ba, gani na yi za ta fita na hana ta, mu na tare da ita a Wakina, kuma na yi ragon azancin ban zo na sanar miki ba".

"Mami ta bani abinci, kuma na yi bacci ma"

"Ikon Allah, yau kin yi baccin kenan?"

Yusra ta ce "Eh, na yi bacci sosai mai daWi, na ga ma Sagir a baccin"

A fusace Hajiya Halima ta ce "Ba za ki daina maganar Sagir Win nan ba ko? Mutumin da ya riga ya sake ki, ba zai zama da ke ba, mene ne na zancen sa "

Siyama kuwa da ranta ya Saci ta ce "Amma baiwar Allah wannan shiga hakki ne, tun Wazu mu ke neman ta fa, kuma saboda wula?anci da rashin mutunci mijinki ya ce bai ganta ba, wannan ai gidadanci ne da rashin hankali"
Ayshacool
"Laifina ne, ba nasa ba ki daina zaginsa dan Allah, ba na jin daWin hakan"

Hajiya Halima ta ce "Siyama ya isa haka dan Allah, amm Nana sunan ko? Mun gode sosai da sosai"

Nana ta juya za ta tafi, Yusra ta ce "?awata sai anjima"

Nana ta yi mata murmushi ta ce "Kar ki manta abubuwan da na gaya miki fa"

Ta amsa mata da "To"

*

An Waga Shukura daga kwanciyar da take yi, an yi mata wanka, aka kawo mata abin???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ci, amma ta ?i ci, tana zaune tamkar gawa.

"Shukura yanzu haka rayuwa za ta kasance mutum babu tawakalli kenan? Da Allah ya baki lafiyar ba za ki gode masa ba kenan?"

"Mummy"

"Naam"

"Kin ga gawar abin da na haifa?"

Hajiya Amina ta ce "Eh mana, awansa shida a nursery ya rasu, sai da na gan shi sannan Sagir ya tafi da shi ya binne."

Hawaye ya gangaro kan kumatunta, ta ce "Amma me yasa ba a bari na gan shi ba?"

"Shukura ba kya cikin hayyacinki, za a yi ta zama da gawa ne ba a binne ba? Ai ba zai yiwu ba"

Ta ce "Haka ne, amma ina baban Haidar Win yake?"

"Bai daWe da tafiya ba ki ka tashi, kuma da na san za ki farka da wuri an jira, kin gan shi. Amma na san ya Waukar miki shi a hoto ai. Na tura family group ma, amma dai na ?ara gaya musu, ban da zuwa dubiya ba kya jin daWi"

Ta ce "To Mummy na gode sosai, tun da dai kin ce mini kin ga gawar babyn shikenan, Allah ya sanya mai ceto ne. Ke ma Allah ya baki ladan Wawainiyar da ki ke ta yi da mu"

Cikin jin daWi Hajiya Amina ta ce "Amin ya Allah, ko ke fa Auta, dan Allah ki ci abincin ko na ji daWi"

"To Mummy amma saboda ki ji daWi zan ci kaWan, ba na son cin komai"

"Ba komai, hakan ma na gode sosai da sosai Autar Mummy"

Haka Shukra ta din ga ya?i da zuciyarta, da ?o?arin kawar da tunanin mafarkan da take yi.

*
Har Gaddafi ya gota matan, da suke zaune a kan barandar ?arshen layin, sai kuma ya dawo da baya ya ce "Sannun ku"

Su ka amsa masa da "Yauwwa sannu"

Ya ce "Kamar 'yan uwan babar su Imrana"

Adda Rakiya ta ce "Laa Gaddafi kai ne?"

Sai ya gyara tsayuwarsa, su ka gaisa. Ya ce "Ya na gan ku a nan?"

Adda Rakiya ta so ta kare, amma Fati ta gaya masa abin da ya faru.

Ya girgiza kai ya ce "Ku yi ha?uri, abu ne da ya faru ya riga ya wuce, amma an ?i bari ya wuce, ake ta nanatawa, bari na nemo muku Nasiru, ya raka ku."

Bayan tafiyar sa Rakiya ta ce "Fati, wannan ba Gaddafi ba ne ba, mai cewa zai daki Mai Jidda, yau shi ne da gaishe mu"

Fati ta ce "Wallahi nima abin ya bani mamaki sosai da sosai"

Su na cikin tattaunawa, Gaddafi ya kawo musu ruwan sanyi da lemo, ya nemo Nasiru, ya tarar musu abin hawa, ya biya kuWin suka tafi.

*
"Sayyid"

Ya Waga ido ya kalle ta.

Ta ce "Ko dattijon ne?"

"Wane dattijon?"

"No ba komai"

"Ki daina kallona, kamar ki na tuhuma ta"

Ta ce "Tuhumar ta ka nake yi ai"

Ya tsaya da cin abincin ya ce "Da me?"

"Ci abincinka, zan gaya maka"

Ya ci gaba da ci, ta sake kiran sunansa.

Ya Wago ido ya kalle ta.

Za ta yi magana,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login