Showing 87001 words to 90000 words out of 168002 words

Chapter 30 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

648

ruwan ki da lafiya ko ma babu, abin da ki ke neman maraba da shi?"
Ayshacool
Sayyid take kallo, zuciyarta na raya mata, ta matsa kusa da shi, ta jarraba yi masa karatu, amma tsoro ya kama ta, saboda gudun kar ya cutar da ita, ga ?aramin ciki a jikinta, da take ta lallaSawa tana fatan Allah ya bar mata.

****

A hankali Jamila ta buWe idonta, ta ganta a Wakin da suka sauka da Hajiya Sa'a. Ta yin?ura za ta yaye bargon da take lulluSe da shi, amma ta ji jikinta na yi mata wani irin ciwo mai tsanani. Ga wani irin raWaWi da azaba da ta ji a ?asanta zuwa gurin bayan gidanta, tamkar an sanya abu mai kaifi an haWe guraren biyu.

Ta yaye bargon ta ganta a tsirara, jikinta duk an yi mata zane da jini, ta Waga ?afarta Waya tana ?o?arin tashi zaune, amma ta ji ba za ta iya ba, saboda azabar raWaWi da zafin da take ji.

"Wayyo Allah Mama, na shiga uku mene ne ya same ni haka? Nana, Suwaiba dan Allah ku taimake ni na shiga uku"

Hajiya Sa'a ce ta shigo da sauri, tana faWin "Daughter kin tashi?"

"Mene ne ya same ni, me ya faru da ni?"

"Yi shiru, ki kwantar da hankalinki, zan yi miki bayani. Amma ki daina wannan kukan.
Taso mu je, ki yi wanka ki gasa jikin ki, ki karya tukuna.
Cikin kuka ta ce "Ba na so, ki yi mini bayanin mene ne ya same ni? Ina ne nan? Me yasa nake jin wannan zafin, kuma me ye wannan rubutun a jikina?"

Hajiya Sa'a ta ce "Ke ba na son hauka. A lokacin da Safiyya ta haWa ni da ke. Nake kashe miki kuWaWe a banza zan yi miki ne, ba tare da na amfani komai a tattare da ke ba?? Kin gaza kawo mini jinin 'yar uwakki, kin ?i shiga cikin harkar mata yadda nake so, kuma ga burinki na son abin Duniya, dan haka tallafawa burinki kawai na yi cicciSa ki"

Hawaye na kwarara daga idonta cikin sanyin murya ta ce "Yanzu me ya same ni?"

"Taronmu na ?ungiya ki ka zo, kuma na nema miki sassauci ta hanyar ki bayar da budurcinki, ga sarki da kuma dodon ?ungiya maimakon a ce ki kawo jini tashin farko.
Aljanin da ke da alhakin bamu kuWaWe,da jagorantar ?ungiyar, shi ne ya shiga jikin sarkin ?ungiya ya kwanta da ke, a matsayin barka da zuwa na ?ungiya kuma da sadaukarwar ki ta shekara!!!

(Alhamdillah, da haka muka kawo ?arshen book 1, sai mun haWe a kashi na biyu).

Ayshercool 08081012143
Ayshacool
Ya gama ci, ta dafa ruwa ta kama hannunsa zuwa banWaki, tamkar jaririn goye ta yi masa wanka. Shi kansa a lokacin ya din ga jin wata lafiyayyiyar iska na shigar sa. Ta saka ya yi alwala, ya fito ya zauna ya fara jero sallolin da ake bin sa.
Ta ce "Sayyid kar ka ce sai yi a yanzu duka, sallolin da yawa.ka bari ka din ga ramawa a hankali.
Ya jinjina mata kawai kawai, tun yana yi a tsaye ya kasa tsaiwar ya koma yi a zaune. Ta yi shiru tana kallonsa, ta wasu guraren suna da kamanceceniyar halayya ita da shi.
Duk yanayin da yake ciki, muddin ba hankalinsa ne ya gushe gaba Waya ba, ba ya wasa da salla ko kaWan. Hakan ya sanya take jin ko a ainihin rayuwarsa haka ya siffantu da kiyaye salla a kan lokaci.
Har ?arfe uku da rabi, dan kansa ya ce "Ba zan iya ?arasawa ba, numfashina"

Ta ce "To ko za ka yi a kwance?"

Ya girgiza kai ya ce "Na fi so na yi a zaune, ko a tsaye"

Ta Wage masa labule, ganin yadda yake ta gumi. Ta shimfiWa masa sallaya a bakin ?ofa, ta jera masa fululluka, ya kwanta.ta zauna a gefen sa tana yi masa fifita. Ta Wora hannunta a goshinsa tana karanta masa abin da Allah ya sa ta tuna a zuciyarta.

Hannunsa ta ji yana saka wa a rigar ta, duk da idonsa a lumshe yake. Murmushi ta yi ta ci gaba da abin da take yi. Jin yana yi mata cakulkuli, ya sanya ta kwanta a jikinsa tana dariya. Shi ma dariyar ya yi. Ya ce "Ki kwanta a kusa da ni" ya yi maganar yana nuna mata kusa da shi. Kafin ta yi magana ta ga an dalle su da fitila.
Cikin hanzari ya juya kansa, ya Soye fuskarsa a cinyar???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? Nana, gashin sa ya kwanta a kan filon. Nana ta saka hannu ta kare fuskarta.
Muryar Barira ta ji ta ce "Yi ha?uri dan Allah, jin motsi ya yi wa na fara jin tsoro, shi ne na fito na duba, ku yi ha?uri.
Ta kashe fitilar ta koma Waki. "Sayyid ka yi ha?uri, na san ba ka ji daWi ba, ka yi ha?uri"

Ya yi mata shiru, kuma bai Wago daga kan cinyarta ba. Ta shafa gashin ta ce "Shugabana, ka yi magana mana, ko na ji daWi, kwana huWu ka na bacci, ba ka yi mini magana dan Allah kar laifin wani ya shafe ni"
Sai kuma ya juyo a hankali, ta ce "Yauwwa Rayuwata"

"Kin daina aman?" Ta ji ya tambaye ta babu tsammani.

"Eh na daina"

"Allah ya sa ki haihu wannan karon "

"Amin, kuma Allah ya baka lafiya na haWa jariraina biyu, babba da ?arami"

Ya yi murmushi ya ce "In sha Allah, kafin ki haihu, idan na ji sau?i zan nemi aiki, na kula da ku da kaina"

"To Allah ya amince. Amma Sayyid ina kuWin nan da na gani rannan, a cikin wardrobe Win ka? Da na haWa mana kaya ban gan su ba. Da sai mu Wauka a yi maka magani, kuma mu canza gida"

"Ai Habu ya karSa, ranar da ya zo na ?arshe, ya karSi kuWin Nigeria da yawa, ya bar mini wasu, ya ce na Nijar ne. Kuma da kin duba kayan nawa sosai, su na ciki"

"A'a ni ba na caje maka kaya, idan Allah ya kaimu gobe, sai a lissafa mu gani idan za su isa."

Ya ce "To. Kwanta ki yi bacci" ya yi maganar ya ?ara matsa mata. Ta kwanta tana murmushi.

"Sayyid, idan har ba a ga su Habu ba, ina ga da ni da kai zamu je Nijar, mu nemi danginka da kanmu"

Ya yi shiru bai yi magana ba, ta Wan taSa shi ta ji har ya yi bacci.

*
Jamila a dole ta saki ranta, jikinta ta Wan samu ?wari, ya daina yi mata wannan mugun ciwon da yake yi mata. RaWaWin ma duk babu. Sai dai tana jin ?asan zuciyarta kamar za ta yi bindiga, saboda damuwa da tashin hankali. Sosai abin da ya faru ya tsaye mata, ta shiga banWaki ta sha kuka. Wai ita Aljani ya kwanta da ita, ta gaba da baya aka ci zarafin ta ta wannan mummunar hanyar.

Tana kwance a cikin bargo, Hajiya Sa'a ta fita shashashancinta. Wayarta ta fara ringing. Ta janyo ta Waga. Muryar Abba ta ji ya ce "?anwata, wunin yau ban jiki ba, lafiya kuwa?" Wani irin abu mai zafi ya taso mata, ya haddasa mata karaya. Muryarta na rawa ta ce "Yaya Abba ba ni da lafiya"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Me ya same ki?"

Rasa abin da za ta ce masa ta yi, kawai ta saka kuka. Aikuwa ya rikice ya din ga rarrashin ta.

Da ?yar ya lallaSa ta ta ce masa cikinta ne yake ciwo.

"To ina Mummyn take? Ba ta kai ki Asibiti ba?"


Ayshacool
"Ta kai ni, an ba ni magunguna ma, dan Allah kar ka yi mata zancen, ta yi mini iya ?o?arin ta,kar ka yi mata zancen dan Allah"

"No ai ba zan yi mata ba, ba ta san ma ina da lambar ki, mu na magana ba. Ki kwanta ki samu hutu kin ji ?anwatax

"To shikenan na gode sosai" suka yi sallama ta ajiye wayar, ta kwanta hawaye na ci gaba da bin idanunta.

*

Yana zaune a cikin mota, yana ?o?arin kunnawa, wayarsa ta fara vibrating. Ya kalli screen Win wayar, ya ga ba?uwar lamba. Ya Wauki wayar ya Waga ya saka a kunnensa.
"Hello" muryarta ta doki dodon kunnensa. ?an waro ido ya yi, ya gyara zaman sa ya ce "Wa ke magana?"

A raunane ta ce "Beb abin har ya kai ka manta muryata ma? Shikenan na gode" ta kashe wayar.

Da sauri ya bi kiran wayar, amma ta ?i shiga, ya yi ya yi, amma ta ?i shiga, sai ha?ura ya yi ya ja motar.

Shukura mamakin abin da ya zaunar da shi a cikin mota take yi, bai tafi ba har yanzu, sai dai tana Waga labule, ta hango ya ja motar ya tafi.

Video call Win Hajiya Amina, Shukura ta gani, ta Waga cikin fara'a tana faWin "Hajiya Mummy, ya ibada?"

"Ibada Alhamdillah, Shukura dan Allah me yasa ba kya ji ne? Ina zaman zamana, ina ibada kin jawo mini Sacin rai da damuwa"

Cikin rashin fahimta, ta ce "Ni Win kuma? Me na yi?"

"Baban ki ya kira ni, bai taho ba tukuna yana Abuja. Yana yi mini faWan wai ke ba ki san ?addara ba ne? Doctor Sharif ya kira shi cikin damuwa, yana gaya masa a gaban mutane ki na cewa yana kashe mutane, haka ake yi a kan ki a ka fara rasa Wa? Me yasa ba za ki girma ba ne Shukura"

"Mummy ki na ji na, network Win ki mai ?arfi ne ko?"

Ta ce "Eh, ina jin ki, kuma ina kallon ki"

"Ina son idan kin je gaban ka'aba, ki yi mini addu'a, muddin a kan gaskiya ta nake, Ubangiji Allah ya shiga lamarina ya ?arfafa mini gwiwa. Idan kuma ba a kan daidai nake ba, Ubangiji Allah ya kawar da kaina daga kai. Ya bani juriya da dangana na daina jin abin da nake ji a zuciyata.
Sai dai kin dawo amma akwai matsala ne fa."

"Shukura matsala wace iri ce, za ta sanya musulmi kasa yin tawakkalli?"

"Ki bari dai ki dawo Win"

"To shikenan, amma gaskiya mahaifinki ya yi fushi bai ji daWin abin da ki ka yi ba sam"

Shukura ta lallaSa ta, ta ajiye wayar.

*

Nana tana jan ruwa a rijiya, tana zubawa a cikin bokitanta, za ta kai banWaki.
Barira ta ce "Nana ki yi ha?uri dan Allah, jiya na haska ku, ba a son raina ba ne, kuskure ne" Nana ta ce "Babu komai"

Sajida ta ce "Uban me ki ka haska ki ka gani?"

Barira ta kwashe da dariya ta ce "Ni babu abin da na gani, duk da bai kyautu ba abin da na gani Win. Amma Nana mijinki balarabe ne ko bature?" Nana ta Waga ta kalle ta.
"Tun da ku ka zo dama bamu taSa ganinsa ba, gashi na gani kamar na mace dogo sosai"

Nana ta maze ba ta kula ta ba, ta kwashi kayan ruwanta, ta nufi Wakin su.

Sajida ta tuntsure da dariya ta ce "Maganinki da shegen shishshigi, ga shi ta gwale ki"

"Shegiya ba, ta fiye jin kan ta,kamar 'yar uban wani, kuma da 'yar uban wanin ce, da ba su kama hayar Waki Waya ba" Duk abin da suke faWa a kunnen Nana, amma ta yi kamar ba ta ji ba.

Bayan ta gama wanke banWaki ta fito, ta zo gabansa ta zauna. Ya Waukko sauran kuWin nan, ya ajiye a gaban ta.

Ta kalle shi ta ce "A ina ka Soye ne, ban gan su ba?"

Ya yi murmushi ya ce "Su na cikin kayana fa, ba ki duba bane ba. A cikin leda suke. Kuma da sun fi haka yawa, Habu ne ya karSa".

Nana ta duba kuWin, sai tarin kuWin nijar, na Nigeria ba su dubu Wari da goma ba.

Ta ce "Sayyid, idan ka Wan ?ara hutawa, ko zuwa gobe in Allah ya kaimu ne, za mu koma Asibiti a sake duba ka. Da za su kai da na haWa da sauran na guri na, a fara yi maka allurar nan ko guda Waya ce"

"A'a, kin manta yanzu mu zamu din ga sayen Abinci. Idan su ka ?are ba mu da hanyar samun kuWi. Kuma da akwai isassun kuWi, gara mu bar gidan nan, da a yi mini magani"

"Ni kaina Sayyid ba na son gidan nan. Mama za ta aiko mini buhun barkono, idan aka kawo, na ga ana ciniki, sai mu ci gaba da sayarwa".

Ya jinjina kai ya ce "To, in anjima ki raka ni masallaci" Ta kalle shi ta ce "Da gaske masallaci za ka je?"
Ayshacool
"Eh, ina son zuwa masallaci. Idan ki ka raka ni, sai ki dawo"

Ta yi murmushi ta ce "To shikenan, Alhamdillah sau?i yana samuwa. In sha Allah zan kai ka. Bari na ajiye kuWin nan, idan na raka ka ma, dan Allah zan je gidan Ummi" ya jinjina kai. Har za ta tashi ya ri?o ta, ya cire hijjabin da yake jikinta.

?onuwar da take wuyanta ya gani, ya ?ura wa gurin ido sosai sannna ya ce "Mene ne wannan?"

Ta Wan basar ta ce "Ba komai fa, Wan ?onewa ne kawai na yi"

"Ba Wa ba ne ba, me ya kai ruwan zafi wuyan ki? Waye ya zuba miki?"

"Ba wanda ya zuba mini, sha nake yi ya zube" kawai ya rabu da ita, ba dan ya gamsu da amsar da ta ba shi ba.

Ta tattare kuWin nan, na Nijar ta zuba su a cikin jakar gidan Sarkin Baka. Na Nigeria kuma ta haWe su, ta saka a cikin kayan ta. Ana kiran salla, ya yi alwala, Nana ta ba shi mayafin rawaninsa, ya yafa a kan sa.
Nana ce ta fito tsakar gida. Barira ta gani, tana girki sanye da wata 'yar riga, milik ce amma ta yi ba?i saboda dauWa, ko brezia babu a jikinta. Ga gashin hammata ya fito zaro-zaro idan ta Waga hannunta. Zanin jikinta ma ba?i ?irin, tamkar an yi matsar man ?uli da shi, sai annakiya take yi.

Nana ta ce "Barira, dan Allah ko za ki gyara, zamu wuce"

Barira ta ce "Bismillah ki wuce mana"

"A'a ai ni da mijina ne"

"Ku wuce ba wani abu ai" Nana ta yi shiru tana jinjina tumasanci da rashin sanin ciwon kai, na mutanen gidan. Babu yadda ta iya, haka ta kammo hannun Sayyid, ya fito ta rufe Wakin. Ya ja mayafin ya rufe fuskarsa da rawanin, saboda yanzu ba ya iya naWa shi, saboda numfashinsa.
Tun da ya fito Barira take kallon sa, ta na son ganin ainihin fuskarsa, amma ya sunkuyar da kai, kuma ya rufe fuskar sa suka fice.

Su na tafe Yana hutawa, saboda haki, a hankali har suka isa masallacin. Ta ce "Za ka jira ni na je gidan Ummin na dawo?"

"Zan koma gida da kaina"

"Har ka gane hanya?"

Ya ce "Eh ki gaishe ta"

Nana ta ce "Ai ba daWewa zan yi ba ma"

Ya shiga Masallaci Nana kuma ta tafi gidan Ummi.

Su Nana na fita, Barira ta buga banWakin tsakar gida ta ce "Ke Sajida kashin dan?o ki ke yi ne? Ki na manne a banWaki yau mijin 'yar rainin hankalin nan dai ya fito. Ashe dole ta Soye shi, fari ne tas wannan gashin da na gani, da gaske nasa ne."

Sajida ta fito da buta a hannunta ta ce "Kai haba, ban gama ba ne shi yasa ban fito ba, zogala na ci da ?uli ya ruWa mini ciki"

"Aikuwa kin rasa, ba ki gan shi ba. Sai na ga kamar mata na rako, da na tuna Gali, ga ba?i ga ?eya"

Sajida ta ce "Ba gara Gali ba da nawa mijin? Ke Gali na da tsawo, ni nawa ga gajarta ga muni"

"Gaskiya Sajida mijinki akwai muni kam, dogon baki kamar dangin burrai"

Sajida ta tsuke fuska ta ce "Ba na son iskanci kuma. Gara shi dai a kan Galin, da ki ka ce ba ya iya tsinana miki komai a shimfiWa. Kalarsa kalar... Kafin ta ?arasa Barira ta ?unduma mata Ashariya, take faWa ya kaure, suka ci wa junan su mutunci tsaf, suka tona wa kan su Asiri. Suka gaji dan kan su, suka ha?ura.

****
Nana ta bawa Ummi labarin barkono da za a kawo mata.
Ta ce "Amma Ummi sai dai a kawo miki nan, can Wakinmu babu gurin da zan ajiye a can"

"Bakomai a kawo, kuma nan da nan za ki ga an saye shi ba, ai unguwar nan fuskar jama'a ce, idan ka kasa kaya za ka samu alkhairi"

Su na tsaka da hira, babu zato babu tsammani sai ga Saleh ya afko cikin gidan. Wata irin mummunar faWuwar gaba ta ziyarci Nana, bayan da ta gan shi babu tsammani. Duk ya ?ara lalacewa.

Turus ya yi yana kallon Nana, cikin mamaki ya ce "Nana, dama kina nan?"

"Eh" ta amsa a ta?aice.

"Nana da yanzu nine mijinki, amma ki ka guje ni"

Ummi ta haWe rai ta ce "Saleh Nana fa matar aure ce, dan haka babu ruwan ka da ita dan Allah"

Saleh ya ce "Dan matar aure ce, kuma shikenan ba za mu yi zumunci ba? Nana kina lafiya? Na ji an ce wani baroroji aka aura miki ko?"

Nana ta haWe rai ta tashi ta ce "Ummi zan tafi, zuba mini Abincin idan kin gama"

Ummi ta ce "Bari na wanke babban flask, kuma idan Islam ta zo ki ba ta kwano na, dan ba zan bar miki ba"
Ayshacool
Nana ta ce "Gaskiya sai kin bar mini, ki zo Wakina, ki Wauki duk abin da ya yi miki. Kuma a ?aramin kwano za ki zuba mini. Sayyid na yi masa girki, ni zan ci wannan"

Ummi ta ce "Hajiya Nana, an sake haWiyar wake kenan, to Allah ya inganta"

"Dawa na haWiya ba wake ba"

Tsulum Saleh ya sake cewa "A nan unguwar gidanki yake kenan? Na ji Ummi ta ce Islam na zuwa gidan naki. Da aka ce mijin naki gadi yake yi"

A ?ufule Ummi ta ce "Dan zatin Allah Saleh ka fita, ba da kai muke magana ba, babu ruwan ka da mu. Wai har ka manta har ubanmu ka saka a rufe saboda kuWinka, dan rashin kunya kuma, ka zo zaka addabe mu?"

Sum-sum Saleh ya fice daga gidan. Ummi ta zubawa Nana tuwon shinkafa da miyar yau?i, har da man shanu, Nana sai haWiye yawu take yi cikin farin ciki, kamar ta dur?usa ta ci a gurin.
Ummi ta shiga Waki, ta Waukko wa Nana dambun kifi ta ce "Ungo, jiya na yi shi aka kai mini shago, na Webar miki"

Nana ta karSa tana murmushi ganin sa fal a roba, ta ce "Allah ya yi miki abin da ki ke yi mini na alkhairi na gode sosai" suka yi sallama Nana ta fita.

Tana cikin bin wani lungu, ta ji Muryar Saleh na kiran ta.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login