Showing 30001 words to 33000 words out of 168002 words

Chapter 11 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

634

ya ce "Hajiya Anty Nana amarya" da?uwa ta yi masa ta ce "Gidanku"

Ya yi dariya ya ce "Na yi missing Win ki sosai"

Take ta manta da damuwar da take ciki, ta ware suka hau hira. Ta juye musu sauran abincin da ba ta ci ba, ta ce za ta Wora musu wani.

Ummi ta ce "Ke a ?oshe muke, ga shi wannan miya ce na Wan yi miki, tun bayan kawo ki da kwana biyu, na so yi miki, bana jin daWi ne. Ga Wan cin-cin da dubulan na yi miki. Ga kuma turarukan wuta da wata ma?wanciyar ku, ta bayar a kawo miki ga humra ma. Sai kuma kaya da na Wan ?ara sayo miki"

Nana ta ce "Allah sarki, na gode sosai da sosai Anty Ummi, Allah ya saka da mafificin alkhairi. Jamcy ya garin ne?"

Jamila ta ce "Uhumm mamaki nake yi, kamar ba ke ce ki ka gama uban kuka ba, an aura miki buzu, amma kalli yadda ki ka ware yanzu"

Nana ta yi murmushi ta ce "To ba dole na ware ba, lafiyayyen Waki, ga wardrobe, ga katifata ga banWakina nikaWai ba takura ga wuta 2hrs ba yankewa"

Suwaiba ta ce "Katifa ko abin da ake yi a kan katifar?"

Nana ta ce "Duka Wan sunna ai ba zai ?i sunna ba Jamila, tun da dan haka ake auren"

Ummi ta ce "Dan uban ku da yara a gurin ku ke yi mana batsa"

Nana ta yi murmushi ta ce "Ya Baba, ina mama su ba za su zo ba?"

Ummi ta ce "Za su zo ne, Baba babu lafiya ?afarsa ce take ciwo"

Nana ta ce "Ciwon ?afa kuma?"

"Wallahi kuwa, ba za ki kira mijin naki mu gaisa ba"

Nana ta Wan kwaSe baki ta ce "Ba kula? ku zai yi ba, Nasiru ya makaranta" ta karkatar da zancen ga Nasiru. "Makaranta lafiya ?alau Alhamdilillah"

A ?ofar Wakin ya yi gyaran murya ya tsaya, Nana ta yin?ura ta tashi, ta Waga labulen. Babu hijjabi a jikinta, sai doguwar rigar atamfa.

Ya mi?o mata leda, ta saka hannu biyu ta karSa, bai ce mata komai ba, ya juya ya koma bakin gate.

Fura da Nono ne kaya guda, abin sai da ya bawa Nana mamaki, ba ta san a ina ya samo su ba. Ta ajiye musu suka dama, suka sha.
Ayshacool
Jamila ta mi?a wa Nana Wan ?aramin flask ta ce "Nana ga mutuniyar ki na yi miki wainar fulawa" Nana ta haWiyi yawu cikin murna ta din ga yi wa Jamila godiya. Ta ce "Wannan sai dare zan dafa shayi na ci da ita"

Suwaiba ta ce "Ashe fa buzu ki ke aure, ba za a gaya miki shayi ba yanzu"

Nana ta ce "Kamar kin sani, ni yanzu shayi ai sai dai na koya wasu, kwana muke mu wuni shan shayi babu ?a??autawa" suka yi dariya.
Har magariba su na gidan, sai da suka yi sallar magariba,? Nana ta fito har bakin gate ta rako su, sai dai baya nan.

Ummi ta ce "Kin ga har zamu tafi, bamu haWu mun gaisa ba"

Nana ta ce "Ina ga yana masallaci"

Suka yi sallama, suka tafi Nana ta koma Waki. Har cikin ranta ta ji daWin zuwan su.

Ta yi wanke-wanke ta gyara Wakin fes. Ta Waukko flask Win wainar fulawar, ta saka a gaba ta fara ci. Ba ta ci da yawa ba, Haula ta yi sallama.

Nana ta amsa cikin sakin fuska, duk da ta yi mamakin ganinta a daidai wannan lokacin.

"Anty Haula ba ki yi fushi ba? Haryanzu ban fara fita ba, shi yasa ban shigo miki ba"

Haula ta ce "Allah sarki, kar ki damu wallahi, ashe ba?i ki ka yi?"

Ba tare da Nana ta yi tunanin komai ba, ta ce "Eh, 'yan gidanmu ne su ka zo, bismillah matso mu ci abinci" Aikuwa Haula ta gyara zama ta zura hannu a kwano, ta fara cin abincin. Kafin Nana ta yi loma Waya ta yi huWu da rabi, kafin wani lokaci Nana sai filin kwanon ta gani, Haula na ta suWar baki saboda yajin wainar.

Sai da ran Nana ya sosu, dan kuwa ta so cin wainar nan ta ?oshi.

Labulen Wakin kawai ya Waga ya shigo, Haula ta tashi zumbur. Ta kalli Nana ta ce "Na gode sosai sai anjima" sai da Haula ta fice sannan ya shigo Wakin.

Ya zauna a gurin da ya saba zama, Nana ta Waukko ta sa furar da ta ajiye masa, da cin-cin da dubulan a plate, ta nufe shi.

"Sannu da zuwa" ya jinjina mata kai.

" 'yan gidanmu ne fa suka zo" ta yi maganar fuskarta na bayyanar da annashuwa. Ya gyaWa mata kai.

"Na gode sosai da sosai, da karamcin da ka yi mini, ga taka furar ga kuma wannan" ta yi magana tana tura masa plate Win dubulan.

Ya saka hannu biyu ya karSi kofin furar, Nana ta zauna a gefensa, a tsanake yake sha, ya Wauki cin-cin ya saka a bakinsa, maimakon ya tauna yadda yakamata, amma ya din ga tauna shi a hankali kamar mai tsoron tauna dutse.

"Da daWi?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

Nana ta Wan yi ?asa da murya ta ce "Dan Allah ka din ga yi mini magana mana. Haryanzu ban san sunanka ba" ya kalle ta yana ci gaba da tauna cin-cin Win sa.

"Ka gaya mini sunan ka" ya ajiye kofin hannunsa yana hamma, ya jingina da jikin bango yana lumshe idanunsa.

Ta gaji ta ?yale shi, ta fara shirin kwanciya, ta shiga banWaki domin kama ruwa ta yi alwalar kwanciya bacci.

A sukwane ya mi?e, duk da bacci ya fara Waukarsa, kwanon da Nana ta ci wainar nan ya Wauka, ya jujjuya kwanon ya ga babu komai a ciki.

Ya ajiye kwanon, ya koma gurin da yake kwanciya, ya zauna ya yi shiru.

Nana kuwa tana saka ?afarta a banWakin, ta ganta a cikin wani gida, mai dogon gini, mai Wauke da ?ofofi daban-daban. ?aya daga cikin kofofin ta bi, tana neman hanyar fita, amma da ta shiga sai ta ga ta koma ainihin gurin da take da farko.

Tana cikin laluben ?ofar, kawai ta ci karo da Baba, ?afarsa Waya an nannaWe ta da sar?a, an Waure ta tamau.
Da sauri Nana ta nufe shi, cikin tashin hankali ta ce "Baba lafiya kuwa? Me ya same ka haka?"

"Ni ma ban sani ba Nana, dan Allah ki kwance mini sar?ar nan, ina jin ?afata kamar za ta cire, ba na iya bacci"

Cikin damuwa ta ce "Ka kwantar da hankalinka, bari na gani idan zan iya kwance maka" Ta dur?usa ta fara ?o?arin kwance masa sar?ar, sai dai ta rasa ina ne ainihin gurin da aka ?ulle ?afar.

"Idan ki ka kuskura ki ka kwance masa, ba zai sake taka ?afarsa ba har abada" Nana ta Wago tana kallon ?aisar.

"Dan me za ka ce kar na kwance masa? Ba ka ga halin da yake ciki ba, ko iya taka ?afar baya yi ba?"

?aisar ya ce "Ban gaya miki sai na hukunta shi ba? Har yanzu ba ki yadda mu na cikin mummunan haWari daga ni har ke ba, a dalilin wannan auren. Dan haka dole shi ma ya WanWana kuWarsa"
Ayshac??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ool
Cikin Waga murya ta ce "?aisar baban nawa? Ka kwance masa ?afarsa" kawai tana waiwayewa ta daina ganin Baba.

"Idan duniya za ta taru, babu wanda ya isa ya kwance masa ?afar nan, idan bai yi wasa ba sai ta yi ajalinsa" yayi maganar cikin Waga murya.

Tamkar mai shirin haukacewa ta ce "Ba zai yiwu ba, wallahi sai ka kwance shi, wai kai wane irin halitta ne da babu Wigon imani, a zuciyar ka?"

?aisar ya ce "Ko ma dai mene ne, abu Waya za ki yi ki kwance masa ?afar nan, wanda kin san mene ne, ba sai na gaya miki ba. Mu ajiye wannan a gefe tukuna, ban san iya adadin lokacin da za a Wauka kafin ki san ciwon kanki ba, ki daina wasa da rayuwar ki ba. A wannan karon ma an baki abu kin ci, za kuwa ki WanWana kuWar ki, a nan na nuna miki an tsaface ?anwar ki, amma ta kawo abu ta baki ki ka ci"

Nana ta ce "Idan ma ka nuna mini, da na tashi nake manta komai, kuma ba zan taSa yarda da maganganun ka ba, yaudarata kawai ka ke so ka yi, domin na amince da mugun nufin ka, kuma har abada ba zan amince ba, ko da ba ma jituwa da su, na san ba za su cutar da ni ba"

Ya ce "Shikenan, zamu gani"

A hankali ta yi kokarin yin juyi a kan katifar, amma ta ji wani irin azababben fitsari, tamkar mararta za ta yi bindiga, ga wata irin ?ullewa da mararta ta yi har cikin bayanta da ?afafuwanta. Da ?yar da dabara, ta tashi ta tafi banWaki. A zaton ta da ta yi fitsarin shikenan, za ta ji marar ta saki, amma babu abin da ya canza.

Da bin bango ta fito ,ta dawo kan katifar ta kwanta. Bacci ne a kanta, amma wani irin azababben ciwon mara ya turnu?e ta.
Yana kwance yana jin nishinta sama-sama, tun farkawar ta da shigarta BanWaki, duk a kan idanunsa.
Mur?ususu ta din ga yi a kan katifar, tana numfarfashi. Rabonta da ciwon mara mai irin wannan azabar, tun farko-farkon fara period Win ta. Da idan ta fara sai an kai ta chemist an yi mata allurai.
Daga baya abin ya ragu sosai, amma na yau kam, ba ta taSa makamancin irin sa ba, ji take tamkar ba za ta wayi gari ba.

Ko na minti Waya ciwon baya lafawa, ga shi ya haWe mata da ciwon ciki, da na ?irji kamar za ta bar duniya. A du?e ta sake komawa banWaki ta saka pad.

A haka ta wayi gari, cikin mawuyacin hali, ta yi kukan ta gaji. Ta saukko daga kan katifar ta kwanta a ?asa amma babu afuwa. Ko sau Waya bai ce mata sannu ba, da gari ya yi haske ma bar mata Wakin ya yi, saboda yadda kukanta ya cika masa kunne.

Tamkar za ta haihu, haka ta fita daga hayyacinta, gaba Waya ta manta da batun ba itakaWai ce a Wakin ba, ta cire kayan jikinta, ta bar vest da underwear. Rashin tanka matan da ya yi ba ?aramin ?ona mata rai ya yi ba.

Can amai ya din ga taso mata, ga wata irin gudawa ta azaba da fitar ta kawai, yake ?ara gigita ta saboda sai cikin ya haWu ya ?ule da marar sannan take yin ta. Ga fitarta tamkar tana zawon wuta haka take ji, ta ga duniyar tana juya mata, ta din ga salati tana ambaton Allah. Tun tana iya zuwa banWakin a du?e, ta koma rarrafe.

Ta din ga wani irin amai, mai wari da ?arni. Idanunta suka yi zuru-zuru, kamar ta yi wata da watanni tana rashin lafiya.

Ta kwanta ta yi rub da ciki, ta lumshe idonta. Ta ji an Wagota. Sosai ya Wago ta ya haWa ta da ?irjinsa. Babu rawani a kansa, ya kwance gashin kansa,? ya sauka a kan kafaWarsa. Suna haWa ido, ta sake fashewa da kuka, saboda ta ji zafin rashin kula ta da ya yi balle ya yi mata sannu.

Ya kai dogwayen yatsunsa ya share hawayen da yake fitowa daga idonta. Ta saka hannu ta ture hannunsa, da yake share mata hawayen.

Ya kama bayan hannunta ya kai bakinsa ya sumbuta, ya Wago ya ?ura mata ido, yana matsa hannunta a hankali. Zuba masa ido Nana ta yi, sai ta ga kamar ba shi ba. Ya sake kai bakinsa goshinta ya sumbaci goshin nata.
Ta sake fashewa da kuka, ya haWa goshinsa da nata ya ce "Shhhhh"
Gabanta ya faWi, sai da ta razana jin ya Wora hannunsa a kan marar ta.

A hankali ta fara jin releif, daga wannan matsanancin ciwon da take ji.
Bai Wauke goshinsa daga nata ba, numfashin sa da yake shiga nata, jikinta ne ya saki ya mutu murus, ta kasa ko ?wa?w?waran motsi. A hankali ta fara jin bacci yana Waukar ta.
Ayshacool
Su Jamila kuwa bayan sun dawo daga gidan Nana, Baba ya tambaye su ya suka baro ta.

Suwaiba ta ce "Tana nan lafiya kalau, ta ce a gaishe ka"

"Ina amsawa, ya gidan nata akwai abinci kuwa?"

Nasiru ya yi farat ya ce "Baba Waki dai, a Waki Waya take da banWaki, amma akwai abinci a Wakin. Har mijinta ya kawo mana fura da Nono".

Baba ya ce "Ko ma dai a rami suke ba Waki Waya ba, ai ita ta jiyo, tun da Allah ya nufi ya rufa mata asiri, ya bata miji na gari na rufin asiri ta zaSi ta tonawa kanta asiri, yanzu ta ?are a tantalbatete"

Jamila dai kawai fatan ta, Allah ya sa ta yi nasara a kan Nana.
Babu kunya Mama ta saka Nasiru a gaba, tana yi masa tambayar ?awa?waf da son sanin halin da Nana take ciki na daWi ko akasin haka.

****
Bangaren Shukura, duk da ta kan yi mafarkai na ban tsoro barkatai, amma bai fiye damunta ba, wasu lokutan da ta farka ma shikenan, mussaman idan tana da ciki ta fi irin wannan mafarkan. Amma a wannan karon ta kasa mantawa da wannan mafarkin da ta yi, a cikin jikinta take jin tsoro da fargaba a kan mafarkin.

Duk da ba ta iya gaya wa Sagir abin da ta gani a mafarki ba, kawai ta ce masa mummunan mafarki ne, ya yi ta kwantar mata da hankali, da tabattar mata da mafarki ba gaskiya ba ne ba.

Sai dai jin abin take yi, tamkar ma ya riga ya faru ne, ko kuma yana daf da faruwa, haka kurum sai ta ji gabanta ya faWi ta razana.

****

Tare da su Habu ta hange shi zaune kan wani ?aton carfet fari tas, a cikin sahara , suna ta shan shayi su na hira cikin nishaWi, gaban su dabino kala-kala a cikin tasoshi, yana cikin su ba ya magana sai murmushi. ?yam ta tsaya tana ?are masa kallo. Karaf ya Wago kai suka yi ido huWu.

Ya yin?ura ya nufo ta yana murmushi. Ta kawar da kanta gefe ta haWe rai.

Bai ce mata uffan ba, ya rungume ta yana ci gaba da murmushi ya ce "Ya aka yi ne?"

"Ni rabu da ni, bayan ka ?i yi mini sannu" ta yi magana cikin shagwaSa.

"Tuna dai, na yi miki fa, to yanzu ya jikin naki, me ki ke ji?"

"Ba komai"

"Kin tabatta?" Ta Waga masa kai alamar eh.

Ya zagayo da hannunsa, ya Wora a kan mararta, ya sunkoyo daidai kunnenta ya ce "Hmm haka ne, na ji da sau?i, na yi uzuri a wannan karon, amma idan aka ?ara zan Wauki mataki"

Nana ta ce "Me aka yi da zaka Wauki mataki?"

"Komai ma"

Ta yi murmushi ta Waga kai ta kalle shi ta ce "Har yanzu ba ka gaya mini sunan ka ba"

Ya yi dariyar da ta ?ara masa kyau, ya ce "Sunana ki ke son sani?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

Cikin raWa ya ce mata "BUZU"

"Buzu" ta maimaita a hankali tana buWe idonta.

Shiru ta yi tana jin mafarkin da ta yi a ?wa?walwarta, sai kuma abun da ya faru da ya rungume ta Wazu, ya fara dawo mata. Ta nutsu sosai ta ga shi ma a mafarki abin ya faru. Ta ?arewa Wakin kallo, babu kowa a cikin sa sai ita kaWai.
Sai dai ta ji mararta ta daina ciwon, ta tashi ta Wora ruwa ta yi wanka, ta gyara jikin ta, ta rasa abin da yake yi mata daWi, ga shi ta kasa cin abincin. Dabinon da ya taSa bata ta Waukko ta hau ci.

Bayan sallar magariba, ya shigo Wakin da leda, kai tsaye ya tafi kusa da ita ya zauna.
Ko kallon gurin da yake ta ?i yi, saboda ta ji haushin yadda ya kasa kula ta duk wannan azabar wahalar da ta sha.

"Ki ci" ya yi maganar yana ajiye mata ledar.

MurguWa baki ta yi ta ce "Ba na ci" ya yi shiru yana kallon ta.
Ta kawar da kanta gefe tana ci gaba da ?un?uni. ?arshe ma ta tashi ta koma can gefe ta yi zamanta.

Ta Wago ta ce "Ka ci ni na ?oshi, ba zan iya girki ba, ba na son ?amshin abinci" kawai ya yi shiru bai ce komai ba.

Ta kunna kallo a wayarta, tana yi tana cin dabinonta.

"Salamu Alaikum" suka ji ana sallama a wajen Wakin.

"Wa'alaikum salam warahmatullah. Viens" ta ji ya amsa, ganin abin ta yi banbarakwai. Habu ne ya shigo da sallama fuskarsa Wauke da damuwa.

Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Hankalina duk a tashe, ya kira ni ya ce ba ki da lafiya, ba ki ci abinci ba tun safe" Nana ta waiwaya ta kalle shi, ya maze abin sa.

"Ta ina ya gaya maka?"

"Ta waya" Habu ya amsa mata.

Ta Wan kwaSe baki ta ce "Abin da ma bai ce mini sannu ba, kuma yana kallo na kusa mutuwa"
Ayshacool
Habu ya yi murmushi ya ce "Amma ya damu sosai ai, tun da ya kira ni kuma ya saka na tafi neman abin da za ki ci." Ya ajiye mata ledar ya ce "Ga abin da ya ce na sayo miki"

Ta ce "Ni idan bai ce mini sannu ba, ba zan ci ba"

Habu ya kalle shi yana murmushi, ya yi masa magana da french.

Ba tare da ya kalli Nana ba ya ce "Na faWa Wazu"

"Da yaushe?"

"Ki na bacci"

Mamaki ne ya cika ta, jin ya yi doguwar magana, dan haka ta yi yin?urin jan maganar.

"Dama mutum ya san abin da ake yi ne, idan yana bacci, ni na ?oshi"

"Sannu" ya faWa a ta?aice.

Habu ya ce "Lallai abin mamaki, abin ya burge ni, ga kayansa nan an wanke an goge, tun da jikin naki da sau?i, Alhamdilillah ni zan tafi"

Nana ta ce "Mun gode sosai, ka gaida gida"

"Allah ya sauwwa?e ya ?ara lafiya" bayan tafiyarsa Nana ta ci gaba da kallo, ba tare da ta taSa ledar da Habu ya kawo ba, balle wadda ya shigo da ita.
Babu tsammani ta ji an fizge wayar hannunta, sai da ta tsorata, a fusace yake kallonta.

"Ki ci abinci" ya faWa a hasale. Murmushi ne ya so kufce mata, amma a zahiri sai ta kwaSe fuska kamar za ta yi kuka.
Ya janyo ledar da ya fara shigowa da ita, ya buWe ta kankana ce a ciki. Sai dai ta sha mamaki da ya buWe ledar da Habu ya kawo ta ga gasashshiyar kaza. Ita dai ta san tsakiyar wata ne, a ina suke samo kuWin da suke wada?a haka?"

"Ci" ta kuma jin muryarsa.

Sai kuma ta yi tsuru-tsuru ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login