Showing 102001 words to 105000 words out of 168002 words

Chapter 35 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

659

baje a kwance"

"Kuma sai ka ce 'yata mayya ce? To wallahi ?arya ne, kaf danginmu babu mayu, ku dai nemo wani abun, ba maita ba wallahi" 'Yan sanda suka shiga maganar, aka tafi da Barira Asibiti.

Sai da aka bar 'yan sanda biyu, gudun abin da ka iya faruwa, saboda matan da abun ya faru a gaban su, su na ta ?ara balbalawa wutar fetur. Tare da mayar da abin da aka yi da wanda ma ba a yi ba. Gaba Waya zancen ya zagaya unguwa.
Har sha Wayan dare case bai ?are ba, Nana ta farfaWo ta ga Ummi a Wakin su, ga duhun dare ya fara yi.

"Ummi lafiya kuwa?"

"Ina fa lafiya Nana, meya haWa ki da mutanen gidan nan, ga shi ana cewa ke mayya ce".

"Mayya kuma?"

"Eh mana, yanzu case na hannun 'yan sanda, Baba yana can tare da su, ana jiran likitoci su faWi sakamakon binciken su."

Nana ta gaya wa Ummi iya abun da ta iya tunawa. Sai dai ta sha mamaki, ta ji wai Baba ya zo kan matsalar ta.
Ta kalli Sayyid da yake kwance lamo, abin Duniya duk ya dame shi.
Sajida ta haWa kayanta, ta gudu ta ce ba za ta iya kwana da Nana a gidan ba.

Sai zuwa da safe, Likitoci suka tabattar da anemic shock ne ta samu, bayan binciken ?wa?waf da suka yi, suka gano ta yi Sari sati biyu baya, ta kuma zubar da jini sosai ba ta je Asibiti ba. Ta zo ta yi zazzafan zazzaSi na typhoid amma suka ala?anta hakan da mayu, nan ma ba a je Asibiti ba. Hakan ne ya haddasa faWuwar ta. Bayan fito da sakamakon, mijinta da 'yan uwanta suka ce ba su yarda ba, sakamakon ?arya ne kawai aka gaya musu.
Ga Barira ta farfaWo, tun a cikin daren ma, har ta ci Abinci, amma suka ci gaba da surutu a kan Nana mayya ce.

Ummi tare da su Nana ta kwana, saboda tsananin tsoro. Dan da gidanta akwai guri can za su tafi ma. Sai dai tashin hankalin abin da ya faru, ya sanya jikin Sayyid rikicewa gaba Waya, ya zamana kamar ma ba ya gane wanda yake kansa.

Hankalin Nana ya yi mummunan tashi, ga shi babu isasshen kuWin tafiya Asibiti. Ta kuma san tashin hankali, da damuwar abin da ya faru ne, ya sanya jikin nasa ?ara rikicewa.

Nana ta rasa abin da yake yi mata daWi, ga matan gidan kowacce ta koma gidansu, sun ?i dawowa gidan wai tsoro suke ji.
Ummi ce ta yi sallama, Nana ta amsa ta yi mata izini ta shiga Wakin. Hannunta ri?e kular Abinci. Ta kalli inda Sayyid ke bacci a wahale, numfashinsa na fita sama-sama. Cikin damuwa Ummi ta ce "Yanzu Nana haka jikin nasa ya koma?"

"Wallahi Ummi, gaba Waya hankalina a tashe yake"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ana wata ga wata"

Cikin damuwa da rashin fahimta ta ce "Me ya faru?"
Ayshacool
Cike da karaya, da matsanancin tausayin ?anwarta ta ce "Mai gidan nan ne, ya je ya same ni, ya bani dubu goma sha biyu, wai ga sauran kuWin ku nan, ku tashi. Ba ya son tashin hankali, kuma ga sauran 'yan hayar sun ce ko ku tashi, ko ya mayar musu da kuWinsu su tashi. Nayi-Nayi ya ?ara wani abu, tun da ko wata ba ku yi ba, amma ya ?i wai wannan Win ma da ?yar ya samo su ya kawo."

Nana ta jingina da jikin bango tana maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"

"Nana mene ne abin yi yanzu?"

Nana ta girgiza kai, jiki a sanyaye ta ce "Ban sani ba Ummi"

"To ko wani gidan za a nemo? Sai na koma na neme shi, na ro?i alfarmarsa?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a Ummi, an riga an yi mini mummunan tambari a unguwar nan, abu ne mai wahala ma mu sake samun wani gidan a unguwar nan"

"Bari na kira Baba na ji me zai ce"

Nana ta ce "A'a Ummi, kin san halin Baba, kar ranki ya Saci"

"To Nana ya zamu yi, dole a kira shi mu ji me zai ce" Ummi ta kira lambar Baba, yana Waga wayar muryarsa a sama ya ce "Ya kuma aka yi, ba an kashe case Win a gurin 'yan sanda ba?"

Ummi sai da ranta ya sosu, amma ta maze ta ce "Baba ba wannan ba ne. An kori su Nana daga gidan da suke ne, mai gidan da suke ya ce sai sun tashi"

"To sai kuma aka yi yaya? Ni zan nemo musu wani gidan? Ko kuma mijinta ne yakamata ya nemo musu wani?"

"Baba ka fa zo gidan nan, ka ga halin da mijin nata yake ciki na rashin lafiya, saboda haka aka kore shi daga gurin aikin gadi. Dan Allah Baba ka yi wani abu a kan yarinyar nan. Nana yarinya ce ?arama pressure ta yi mata yawa."

"To Ummi ya ki ke so na yi? Ni dai nan gidan babu gurin da zan ajiye ta, ita da mijin nata, idan kuma ke ki na da guri ki taimaka ki ba su. Idan ba haka ba ta nemo 'yan uwansa su Wauke shi, su rakata inda danginsa suke. Kin san dai nan gidan idan ta dawo, abin da za ta ci ma aiki ne. Nima yanzu sai abun da aka samo aka bani"

Hawaye ya cika idon Ummi, cike da takaicin yadda Baba bai fiye damuwa da damuwarsu ba. Ta ce "Baba da ina da inda zan ajiye Nana da mijinta, wallahi ba zan kira ka ba"

Nana ta ce "Ummi, dan Allah ki katse kiran nan, nima ba zan koma can gidan ba."

Tarin Sayyid ta ji, ta mayar da hankalinta kan sa, ta nufe shi tana faWin "Sannu Sayyid"

"Ki ba ni ruwa" ta amsa da to. Ta Waukko ruwan leda, ta buWe masa ya tashi zaune ta fara bashi.

"Sannu Sayyid" Ummi ta faWa cikin tausayawa, kallo Waya ta yi masa ta gane yana jin jiki. Da da ne, kome za a yi,ba zai bar gashin nan a buWe ba. Amma yanzu ba ta gashin yake yi ba, ga fuskarsa duk ta kumbura. A zuciya irin ta Nana, ta san ko a titi ta tsince shi a wannan yanayin, ba za ta iya tafiya ta rabu da shi ba, balle mijinta.

?arar da wayarta ta yi ne, ya sanya ta dawo hayyacinta. Ta Waga wayar tare da yin sallama.

"Ke Hansai, ina ta kiran wayar ki, amma ki ka ?i Wagawa?"

Ummi ta ce "Eyya, ba haka ba ne Uwani,ba na kusa ne, ya gida ya mutanen garin?"

"Lafiya ?alau, ya na ji muryar ki ?asa-?asa, laulayi ko rashin lafiya"

Ummi ta yi ya?e ta ce "Ba gara a ce laulayi nake ina kwance ba, da abin da yake faruwa"

"Subhanallah, meyafaru?" Kasancewar Uwani kaka ce a gurin su Nana, ?anwar kakarsu ce, da kakarsu wadda Nana ta ci sunanta da Uwani, uwa Waya uba Waya suke. Sai dai ita tana can Garko da iyalinta. Ummi ba ta Soye mata komai ba, ta gaya mata. Uwani ta rafka salati. Ta ce "Sai an yi magana ku nuna ku mutanen birni, kun fi mutanen karkara wayewa. Ina wayewar take. Aikuwa sai na kira Isa na ci ubansa mara mutunci. Tuntuni nake ganin take-takensa kamar har da ?iyayyar uwar su, take shafar su a gurinsa. Ai Imrana yana zuwar mini nan. Ya hana kowa ri?e su kuma shi yana yi musu ri?on sakainar kashi. Yanzu ina duk sauran 'yan uwanki Ummi, ina 'ya'yan Atine, ina su Gaddafi da ba za ku iya taruwa ku rufa wa 'yar uwakku asiri ba?"






AREWABOOKS
"Wallahi Uwani mun yi iya yinmu ne.."
Ayshacool
"Rufe mini baki, ina wani iya yinku, kuma duk wanda ya ce mana mayu Allah ya isa bamu yafe ba. Mu bamu gaji maita ba, balle a saka yarinya a gaba a tsangwame ta.
Na san babu lallai ta iya zaman ?auye, amma mu nan akwai Wakuna, har ma da gida da babu kowa, idan za su iya zama ta yi jinyarsa. Babu mai damun ta, kuma babu mai cewa ta tashi.
Amma tabbas kun ji kunya, idan har ku ka bari Asma'u ta wula?anta, a ce an rasa inda za ta zauna, ta yi jinyar mijinta, yawan ku kun zama taron tsintsiya babu shara." Ummi ta yi shiru, Uwani akwai kirki da karamci, amma idan ta botsare tana faWa, to duk gaskiyar ka, sai dai ka yi ha?uri. Ta gama faWan ta, Ummi ta kashe wayar.

Ta kalli Nana, ta ga yadda ta tattara hankalinta a kan mijinta, tana ba shi Abincin da ta kawo musu, sai lallaSa shi take, da alamu abincin ma ba ya so.

"Nana, kin ji abin da Uwani ta ce?"

Nana ta girgiza kai ta ce "A'a.

"Cewa ta yi idan za ki iya zama, ku tafi can Buda ki kula da shi, akwai inda za ku zauna. Kin ga nan tun Baba ya san maganar maitar nan, kamar Mama ta ji ne. Ita kuma kin san gishiri za ta ?arawa abin ta yi ta bayar da labari. Amma ban sani ba ko ki na da wata shawarar?"

"Ummi wace shawara? wanda yake ruwa ko takobi aka mi?a masa, ai karSa zai yi. Sai dai shi nake tausayawa, amma ba ni da wata mafita da ta wuce wannan Win. Ni in dai zan samu inda zamu zaune na kula da shi, ba komai zan zauna ko a cikin dutse ne ba ?auye ba"

"Kin tabattar Nana? Da wayonki fa sau Waya Baba ya taSa bari, muka je muka kwana biyu"

Nana ta ce "Ba komai, zan zauna"

Sayyid ya sanya hannunsa biyu, ya dam?e na Nana.
Nana ta kalle shi ta ce "Sayyid, mene ne?"

Idanunsa sun kaWa sun yi jawur, wata jijiya a saman goshinsa ta Waga ta kumbura, fuskarsa ta yi jawur. LaSSansa sauka din ga karkarwa yana son ya yi magana, Nana ta girgiza kai ta ce "Ba sai ka yi magana ba Sayyid. In sha Allah duk rintsi ina tare da kai, har Allah Ubangiji ya baka lafiya" Ummi ta kasa jurewa ta fashe da kuka.

Nana ta ce "Ummi idan ki ka yi kuka,ni ya zan yi? Kun saka ni a tsakiya, nama fi ku juriya, har da kai ma" ta yi maganar tana murmushi bayan saka idanunta cikin na Sayyid, duk da idon nata a cike da hawaye.

"Ummi ki gaya wa Uwani na amince"

Ummi ta share hawayenta ta ce "To shikenan, ya za a yi tafiyar to?"

"Ina ga a sayar da kayan Wakin nan, katifar ta ishemu, sai a sai ledar Waki, sai kayan sawarmu"

"Nana, kina amarya amma a ce Wakin ki babu kayan Waki, haka za ki je ki zauna? Kin san mutanen ?auye ba sa raina abin surutu dai"

"Ummi ai ba ado da kwalliya zan je ba. KuWin kayan ma ri?e saboda Wawainiyar abinci da kuma magani"

Ummi ta Wan yi shiru ta ce "Kuma haka ne, yanzu zuwa gobe in Allah ya kaimu, zan samo dillalai su saya"

Cikin sauri Nana ta ce "A'a Ummi, ba na son ci gaba da zama a unguwar nan, ban san me za su yi mana ba. Idan da hali a nemo su yau kawai. Su saya gobe in Allah ya kaimu mu tafi"

"To shikenan, bari na fita na gani"

*

Yana zaune a cikin office Win sa, ya Wora ?afafuwansa a kan tebur, yana juyi, ya din ga kiran lambar cike da fatan a Wauka. Har ya yanke tsammani, kawai ya ji ta Wauka, sai dai ta yi shiru.

Da sauri ya sauke ?afafuwansa ya ce "Hello" ta yi shiru ba ta amsa ba.

"Hello ki na ji na?"

"Eh" ta amsa a raunane.

"To ba za ki yi mini magana ba?"

"Ba cewa ka yi ba ka gane ni ba, ranar da na kira ka?" Ya Wan yi guntun murmushi ya ce "Ki yi ha?uri, sai daga baya na Wauki muryar ne. Ya ki ke ina fatan kina lafiya?"

"Ai baka damu da ina lafiya ba, tun da ka sake ni baka ?ara nema na ba, saboda ka yi aure matarka ta haihu, dama ni haushina ka ke ji, ba na haihuwa"
"A'a Yusra, kar mu fara haka da ke. Kin san ko bayan mun rabu, na yi ta neman lambarki, amma ba ta shiga har na ha?ura. Ya jikin ki?"

"Da sau?i, amma ni ba mahaukaciya ba ce"

Sagir ya ce "Ai dama ban ce ba"

"Lokacin da muna tare ai ka ce" ya yi murmushi ya ce "Wannan ba ya wuce ba? Amma Mami ba ta san kin kira ni ba ko?"

"Eh, ina gidan Mummy Zahra, da wata na haWu sunanta Nana, ita ma ta san irin rashin lafiyata. Ita ma tana yi"

Ya ce "Haba dai?"
Ayshacool
"Wallahi. Ita ta din ga ba ni shawara, ita ce ma ta ce na kira ka fa, na ma zata ba zaka Wauka ba, ka Wauka amma ka nuna ba ka gane ni ba" dariya ya yi ya sakankance sosai, yana sauraren Yusra. A yanayin surutun da take yi, ya fuskanci jikinta da saura, ba ta warke ba, amma ya tattara hankalinsa yana sauraren ta. Hirar ta din ga tuna masa da yadda suka zuba soyayya a baya kafin aure. Yana kallon kiran Shukura amma ya ?i Wagawa ya ba wa Yusra lokacin sa.

"Ki na ji na"

"Eh"

"Yanzu ina gurin aiki, kuma lokacin salla ya yi, zan sake kiran ki, in sha Allah"

"Tom sai anjima"

"To 'yar farata, bye-bye"

Kamar tana gabansa ta saki murmushi, cike da sanyin jiki, saboda ta yi kewar jin sunan.

Shi ma murmushin ya yi, yana tuna wasu abubuwa da suka wuce.

Ya kira Shukura, sai da ta kusa katsewa sannan ta Waga. "Madam ya aka yi ne?"

"Ina ta kiran ka, kana waya, har da rejecting kirana"

"Sarkin ?orafi, kin san da wa nake wayar ne?"

"Ai ba sai ka gaya mini ba, na san 'yan matanka ne"

"Ni ba da 'yan mata nake waya ba. Ya aka yi?"

Shukura ta ce "Ba komai"

"Madam Shukura, bakomai Win ki, na nufin akwai komai. Yanzu dai a yi mini afuwa da ni da 'yan matan nawa."

"Ni shikenan kawai" ta kashe wayar. Ya girgiza kansa tare da Wan lumshe idonsa.

****

A ranar dillalai, suka saye wardrobe da mudubin Nana, da sauran kayan da take ganin za su zame musu shirgi.
Ta tattare musu kayan su cikin bagcco, duk wani kayan amfaninsu ta tattare. Da safe ?arfe goma, ita da Ummi suka je suka samo taxi. Har fargaba take yi kar mijin Ummi ya yi ?orafi a kan yawon da take yi saboda ita. Duk da ba mazauni ba ne. Suka yi cinikin a nawa zai kai su Garko cikin ?auyen Buda.
Aka Waure katifa a saman taxi, aka loda kayan su a ciki.
Ummi ta shiga gaban motar, ita da babbar 'yar ta Islam.
Nana kuma suka shiga bayan motar, tare da Sayyid.
Ya kwanta a jikin Nana ya yi shiru, ita kuma ta ri?e hannunsa tana matsa masa a hankali cike da kulawa.

Awa Waya da rabi, suka isa har cikin garin Buda. Sai dai shigar su garin ke da wuya, Nana ta fara jin sanyi yana ratsa ta.
Addu'a ta din ga yi, a kan Ubangiji Allah ya rufa mata asiri, ya kawo musu Wauki, ya shiga tsakaninsu da su ?aisar.

"Ma vie" ta ji ya yi magana.

"Na'am Sayyid" Sai kuma ya yi shiru, bai sake cewa komai ba. Yara suka firfito suka tatstsaya bayan ganin mota ta tsaya a ?ofar gidan Uwani.

Uwani da kanta ta fito tana tafa hannu, tana "Maraba da mutan birni. Ina yayar tawa take?" Nana ta buWe motar ta fito tana murmushi.

Ummi ta sallami mai motar, Uwani ta ce "Ina mai gidan?"

Nana ta buWe taxi Win, ya fito a hankali, kansa rufe da mayafi.

Uwani bakinta fal magana, amma ta haWiye ta yi musu maraba, zuwa cikin gidan. Babban gida ne mai Wauke da Sangarori. Ta kai su sashen ta, aka yi shimfiWa Sayyid ya zauna ya jingina da bango.
Abin da dai ba ya ?auna, ya sake tararwa a garin, kallo. Ba ya son a zura masa ido, amma ya lura da yadda ake ta kallon sa.

Uwani ta karrama su da ruwan pure water, da abinci shinkafa da wake.

Ummi ta ce "Kafin cin abinci, Uwani a ina za su zauna, a gyara musu?"

Sai da Uwani ta sake yi wa Ummi ta tas, tamkar ita ce Baban, sannan ta kalli Nana ta ce "Yayata, kin ga cikin gidan nan, akwai Wakuna, idan ma ba zaku zauna a nan ba, nan baya tafiyar babu nisa, akwai gida da Wakuna biyu da tsakar gida. Babu kowa a gidan idan za ku zauna".

Nana ta ce "Gara su zauna a inda babu kowa"

Ummi ta ce "Maimakon ku zauna a cikin mutane, yadda ko wani abin ne, a taimaka muku"

Nana ta ce "Akwai dalili gara mu zauna inda babu kowan" Nana kuwa ta yi hakan ne, domin samun rufin asiri na larurar da suke fama daga ita har Sayyid. Ga uwa uba takura da Sayyid ba ya so.

Uwani ta saka yara, su ka je su ka share gidan tas, aka wanke.

Nana ta ce "Sayyid, bari mu je da Ummi, a gyara gidan, sai mu zo mu tafi da kai" Ya saka hannu ya ri?e nata, tare da girgiza mata kai alamar a'a.

"Mu tafi tare za ka iya tafiya?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

"To ta so" Ya yin?ura a hankali ya tashi tsaye.

Uwani ta ce "Nana, ku bar shi a nan mana, tun da ba shi da lafiya, ke ku je, ku gyara gidan"
Ayshacool
Nana ta ce "Ai ba zai zauna ba, ya ce bin mu zai yi"

"Ikon Allah, ni da bita zai-zai, to Allah ya taimaka" Nana ta yi murmushi kawai, tare da jin nauyin abin da Sayyid Win ya yi.

Sauran yaran gidan Uwani, suka bi su Nana, su taya su shirya kaya. Wanda galibi Nana ba ta ma san su ba, saboda ba zuwa garin suke yi ba, domin ita rabonta da garin ma, har ta manta.
Gidan ?asa ne tsura, da zunzurutun turSaya. ?aki Waya ne gyararrre, sai aka yi masa siminti, da plasta, aka shafa farar ?asa, da ?ofar langa-langa. Sai wani Wakin kuma, si kuma ko rufi babu, sai banWaki.
Duk lalacewar gidan su Nana ya fi nan nesa ba kusa ba, Ummi jarumta kawai take yi, zuciyarta a cunkushe babu daWi, biyo bayan tuna cewar a nan Nana za ta rayu. Sai dai ta ga tsantsar tawakkalli a fuskar Nana. Su ka gyara Wakin aka shimfiWa leda, sai katifar su. Sai kuma tarin kayan su, na girki sai na sakawa a cikin bagco.
Uwani ta aiko musu da Abinci.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login