Showing 108001 words to 111000 words out of 168002 words

Chapter 37 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

653

na zagaya da ke, har inda danginta suke a nan"

Cikin mamaki ta kalli Uwani ta ce "Danginta kuma?"

"?warai da gaske, tushen Maijidda garin Buda ne. Kakanninta 'yan nan garin ne, can wajen unguwar Wanzamai, ?arewa ma a nan garin suka haWu da babanku. Ai kakarta aka raina a Bauchi, aka haifi babarta da ita a can.
Har an saka mata rana, suka zo garin nan, ke ma Babanki ya zo gida, suka haWu a dandali. Aka yi ta Wauki ba daWi suka ?ulla soyayya. Ga shi can garinsu an saka mata rana da wani, ina ga shi ne mijinta na yanzu da take aure. Asali tun kan ta auri babanku da shi aka fara saka mata rana. Kakarta ta ce sai an warware wancan baikon ta auri babanku, ko ba komai sa din ga zuwa gida a kai kai. Haka aka mayarwa da wancan kuWinsa ta auri babanku.
Ya Babanku ya? so ta sosai da sosai, kuma aka ?ulla auren nasu da tunanin hakan ya ?ara kawo zaman lafiya a tsakanin zuriyarmu da zuriyar wanzamai kin san a tarihin garin nan ba zaman lafiya ake ba.
Kuma dai cikin ikon Allah sun fara zamansu lafiya gwanin sha'awa, amma Allah ya ?addara rabuwar su."

Nana ta yi shiru tana tunanin, kamar ta san wani abu mai kama da wannan labarin da Uwani take ba ta, amma sam ta kasa tunawa. Gaba Waya hirar ta Uwani ta gundure ta, saboda ta san shi kansa Sayyid a takure yake, ba ya son mutane ko kaWan, balle uwa uba dogon surutu. Ita kuwa Uwani tamkar an ?ona ta a ka ko gajiya ba ta yi. Babu wanda ya taSa ba ta wannan labarin, sai yanzu babu wanda ya taSa gaya mata cewar mahaifiyarsu tushenta a garin Buda yake, sai dai kamar ta san labarin da Uwanin ta bata.

"Ga wata 'yar rama na zo muku da ita, sai ku ci kafin Abincin dare ya sauka. Wai shi mijin naki kurma ne?"

"A'a ai kin ga ba shi da lafiya ne"

"Eh gaskiya ne, Allah ya ba shi lafiya, amma a ina ki ka samo Buzu haka? Ni wai anya ma labarin da Rabi ta din ga bayar wa ranar bikinki nan gaskiya ne? Abin dai da mamaki. Allah ya ba shi lafiya bari na tafi, dan Allah idan ki ka samu lokaci kya zo a je a gaggaisa.

"To in sha Allah zan zo"

"Yauwwa, zan din ga turo miki yara, idan da aike kya din ga ba su, duk 'yan uwanki ne, 'ya'yan 'yan uwa ne. Kuma ki kwantar da hankalinki duk abin da ku ke bu?ata ku sanar mini, da yardar Allah ba zai gagara ba"

Nana ta ce "In sha Allah, mun gode sosai da sosai"

"Ba komai, ki yi ha?uri ki ri?e mijinki ki kula da shi, sai ki ga kaf ayyukan ki, Allah bai karSa ba, silar wannan jinyar ta sa ki shiga aljanna, a yi ta ha?uri yayata"

Nana ta tashi ta raka ta, ta ce "In sha Allah"
Ayshacool
Ta yi ?asa da murya ta cewa Nana "Dan ubanki, ki din ga Soye mijinki, kar ki bari 'yan mata su din ga zuwa su na kallon sa." Uwani ita iya rage muryarta kenan, amma Sayyid na jin ta. Nana ta Waga kai suka yi ido huWu, ya yi murmushi yana sunkuyar da kai.

*

Alhaji Fatuhu, farin cikinsa ya kasa Suya, duk da halin rashin lafiya da yake ciki, idan aka zo duba shi, sai ya yashe ha?oransa da sukaWai suka rage farare a jikinsa.
Alhaji Zailani ya ?ura wa jaririn ido, ya kalli Alhaji Fatuhu da yake ta yashe baki.

Hajiya Sa'a ta ce "Kai Fatuhu. Sai ka ce ba a taSa yi maka haihuwa ba, ji yadda ka ke washe baki, kana fama da kan ka"

Hajiya Suwaiba ta kwaSe baki ta ce "Abin da na gani kenan"

Alhaji Zailani ya ce "A'a ku bar shi ya yi, Wan mutum fa, kyauta ce Allah ya ba shi, da duk Duniya babu mai ba shi. Ni ba gani ba 'ya'yan duk babu sai biyu ne suka tsaya." Ya yi maganar yana zuba wa jaririn ido, yana tuna na Shukura. Tun da yake harkar ?ungiya, bai taSa bayar da jinin da ya tsaya masa ya kasa mantawa ba, sai na Shukura. Mussaman idan yana tuna irin ba?ar wahalar da ta sha.
Ya kalli Fadila, da take Wakin a zaune, ga jego tana yi, amma ta tare a Asibiti da Wanyen jaririn da ko suna ba a yi ba.

Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Wane sunan za ka saka masa?"

"Muhsin Wina zan mayar" ya yi maganar muryarsa Wauke da rauni.

Hajiya Sa'a ta ce "Wai an din ga saka Muhsin Win kenan?"

"Sunan mahaifin Fadila ne, shi za a mayar mu ci gaba da kiransa Muhsin, ni na yi mata al?awari shi yasa. Na so Muhsin Wina da ya rasu sosai da sosai. Na ji zafin rashin sa, sai dai ina tausayawa wannan Muhsin Win. Ya zo lokacin da mahaifinsa ba shi da komai, ba zan iya Waukar nauyinsa na kula da shi ba. Wata?ila ma kafin ya yi wayon sani na na rasu. Ga shi ko hakika ba zan iya yi masa ba" ya yi maganar hawaye na zubowa daga idanunsa.

"Haba Fatuhu, ya haka? Dan dai Hakikar da za ayi wa jaririn nan, ka san ba za ta gagara ba, amma ya za ka zauna kana kuka kamar ?aramin yaro, a gaban iyalinka da 'yan uwanka hakan bai kyautu ba ai".

Alhaji Fatuhu ya Wago idanunsa da suka yi jawur ya ce "Zailani. Ka san me nake ji kuwa? Gidaje da motocin hawa nake da, ina kyautar ma?udan kuWaWe ba tare da na ji komai ba, da abu ya dame ni, zan sai ticket na tafi umara. Ina da shaguna dukiya Allah ya yarje mini, bayan gwagwarmaya da na sha ta rayuwa. Astagfirillah ba ?arar Allah nake kawowa ba, ko rashin imani da ?addara ba, ina jinjina girman lamarin Ubangiji, kuma ina jin babu daWi Wa na na cikina, ba zan iya saya masa ko wando ba"

Fadila ta ce "Dan Allah Daddy ka yi ha?uri. Mu na murna sau?i yana samuwa, ga shi ka na ta magana sosai da sosai, kukan nan karya mana zuciya yake yi. Kuma da ka yi mana a baya, yanzu kuma da Allah ya kawo jarrabawa shikenan sai a yi ha?uri"

Su na nan zaune, sai ga ?anin Baban Fadila, ya zo duba Alhaji Fatuhu ya kuma jaririn Fadila, wanda shi ne waliyyin Fadila. Sai dai shi ma ya tsorata da ganin Alhaji Fatuhu.

"Alhaji haka jiki ya zama? Subhanallah Allah ya baka lafiya"

"Amin kawu, amma jiki ya yi kyau Alhamdillah, tun da ina ta magana"

"Haka ne, amma menene takamaiman abin da aka ce ya same ka ne?"

Fadila ta ce "Haryanzu ba a gano takamaiman mene ne ba, yau a ce ?odarsa ta kumbura, gobe a ce ko cancer ce, an yi gwaji ba ita ba ce. An yi gwajin zuciya shi ma lafiya ?alau"

Cikin damuwa ya ce "Amma Fatuhu ana haWa maka da na addini kuwa? Ka san muna da ido ne ba na ganin gari ba. Mussaman ku da ku ke shahararrun mutane da Allah ya ba wa wadata. Yakamata a yi na sihiri da shaiWanu"

Alhaji Zailani ya ce "A'a ga likitoci su na kula da shi, ya za a yi a ce kuma a kawo wani abu daban? Magungunan gargajiyar nan kashe mutane suke yi ai, tun da ba auna su ake yi ba".

Alhaji Fatuhu ma ya ce "A'a ba wannan ba ne, wa ya damu da ni da zai yi mini sihiri. Larura ce kawai kuma likitoci na kula da ni"
Ayshacool
"Kai, kalle ni da kyau. Duk bokon ka, nima Wan boko ne, kuma na san ilimin addini, amma sihiri da shaiWanu gaskiya ne. Tun da aka yi Annabi Sallallahu alaihi Wasallam sihiri, duk duniya ban ga wanda ba za a yi wa ba.
Ciwo ya ?i ci ya ?i cinye wa ai akwai alamar tambaya, ga lalacewar dukiya lokaci guda. A dai tsananta addu'a. Ya gama bambaminsa ya fita. Alhaji Zailani ya din ga ziga Alhaji Fatuhu, tare da kushe magungunan gargajiya. Ba tare da jin nauyin Fadila da take gurin ba.

Ya gama soki burutsunsa, ya tashi ya yi musu sallama, tare da cewa zai aiko da abin hakika.

Har ya kusa ?arasa wajen motarsa, ya waiwaya ya ga Hajiya Sa'a ta nufo shi, ya tsaya ta ?arasa.

Ya ce "Ya dai?" Ya yi maganar yana kallonta.

"Zailani"

"Na'am"

"An sauke Wan uwana daga shugabancin 'yan kasuwa an Wora ka, ka saka an dawo da shi Asibitin nan, ?ar?ashin kulawarka, an ce a yi masa maganin gargajiya ka ha?i?ance kana kushewa.
Kar ka kuskura na tarar da sanya hannunka, a cikin wannan abubuwan da suke faruwa da Wan uwana"

Ya gyara tsayuwarsa ya yi murmushi ya ce "Babu sanya hannuna a ciki. Ina ?o?arin zama aboki mai halacci ne kawai.
Sannan ki daina mazewa kamar ke Win mai ?aunarsa ce, bayan sadaukar da 'ya'yansa maza da ki ke yi"

"Duk da haka, munin abin da na yi bai kai wanda ka ke aikatawa ba, ka fi ni sanin kai da me da me ka sadaukar, dan haka ka kiyaye ni". Ta juya ta koma. Bin bayanta ya yi da kallo, ya ji wani abu ya tsirga masa, tabbas idan Hajiya Sa'a ta ci gaba da wannan gigin, zai Wauki matakin da ya dace a kanta."

*

Cikin bacci, take jin hayaniya? a bayan Wakin, tamkar ana cin kasuwa. Ga wata irin sukuwa da take ji a roofing Wakin, tamkar ta dawakai.
Tun da ta farka sai juyi take yi, bacci ya gagari idanunta, ayatul kursiyyu ce ta zo bakinta ta din ga maimaitawa, har ta samu nutsuwa daga razanin da take ciki.
Ta ruge idanunta, sai dai a maimakon ta yi bacci, sai wata irin kewar Sayyid take addabar ta. Ta rasa dallin da ya sanya, ba ya kula ta yanzu. Duk da ba shi da lafiya tana yi masa wannan uzurin, amma duk da haka da ya kan yi attempting sai ya ?yale ta, yanzu kuma gaba Waya ya daina yin?urin aikata komai ma.
Wanda da idan ya sako ta gaba, har takura take yi.

Ta tashi zaune ta gyara maganin sauro, ta taka a hankali ta Waga labulen Wakin, saboda zafi. Ta dawo ta Wauki fitilar wayarta ta kunna. Ta haska shi ta ga idanunsa a lumshe, yana bacci. Ta zuba masa ido, ta fara tunanin ko ita ce mai matsala gaya mata ne bai yi ba, ko ma sharrin ?aisar ne?.
Ta yi ajiyar zuciya, ta kashe fitilar, ta kwanta a gefen sa tana wasa da gashin ?irjinsa. Zuwa na fuskarsa.
Ta sake matsawa a hankali, tana sumbatar leSansa, tamkar mara gaskiya. Gaba Waya a tunaninta bacci yake yi, sai da ta ji ya sanya hannayen sa, ya zagaye ta, tare da ba ta damar sumbatar bakin nasa.
Nana za ta iya cewa, tun da Allah ya sa ta buWi ido a duniya, ba ta taSa jin kunya irin ta yau ba, cikin sauri ta fara ?o?arin rabuwa da jikinsa ta matsa, amma ya mirgina ya rungume ta gam a jikinsa yana numfashi a hankali.

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
https://chat.whatsapp.com/ItWyjFX6W6447Co1XrARAH?mode=ac_t



Yana jin yadda jikinta yake tsuma, tamkar wadda aka kama tana aikata wani abin ashsha! Ko kuma wadda ake kaWawa mazari.
Magana yake son yi mata, amma abu ya gagara, duk ?o?arin da ya yi amma abu ya ci tura.
Ya ?ara ?an?ame ta tamkar wani zai ?wace ta, ya din ga murza hannunta har ta fara jin zafin ri?on da ya yi mata. Yanayin ya ?ara ninka mata halin da take ciki, ta rintse idanunta.
A hankali ta ji yana hura mata iska a cikin kunnenta, tamkar yana zuba mata wani sindari, haka ta ji wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.

?amshin nan ta ji yana ratsa hancinta, ta buWe idonta a hankali, kamar yadda ta yi tsammani, a wannan Wakin ta gan su. Ta hau waige-waige. Ta wata ?ofa ta ga ya fito, ?ugunsa Waure da wani abu kamar zani, ya zauna a kusa da ita yana kashe mata ido.

"Sayyid ka warke?"

"Eh mana"

"Ka daina jin duk abin da ka ke ji?" Ya jinjina kai yana murmushi. "To ka yi mini magana mana"

"Ma vieee" ya faWa yana Wan jan maganar yana kwanciya a gefen ta. "Har na ji daWi da ka samu lafiya, Allah ya Worar maka da sau?in nan Sayyid"

"Amin rayuwata, matso ki kwanta mu yi bacci"

Ta no?e kafaWa ta ce "A'a"ya saki murmushi yana kama hannunta. Duhu ne ya gauraye Wakin. Dariya ta fara jin Sayyid Win yana yi mata cakulkuli. Ta kasance da shi cikin wani yanayi mai tsayawa a zukata.

Ba ta iya tantance a wani hali take, ta daina ganinta a Wakin, sai a libraryn ?aisar.
Ta tsaya tana kallon gurin, tana tunanin yaushe rabon da ta zo gurin nan.

?aisar ta hanga, a tsaye yana gyara litattafan sa.

"?aisar ka warke kenan?"

Yayi shiru yana goge wani littafi, ya gama ya ajiye littafin sannan ya ce "Eh, na warke. Waye ya ce ki je ?auyen nan?"

"Ban gane waye ya ce na je ba? Zan kwana a titi ne? Ga mara lafiya ina da shi"

"Gaskiya ne, bai kamata ki kwana a titi ba. Wannan dalilin ya sanya tun a farkon auren nan, na din ga haska miki matsalolin da za ki iya fuskanta, amma gani ki ke yi kamar ?arya nake yi, to yanzu sai ki san yadda za ki yi, ki rayu da ke da wannan lanjararren mijin naki, da duk larurar duniya ta ?are a kansa".

A ?ule Nana ta ce "Larura Allah ne ya Wora masa, kuma kun taka muhimmiyar rawa a larurarsa. Kuma ka daina ganin laifina. Zan tsallake shi ne a wannan yanayin da yake ciki, na bar shi? Mu bil adama mu na da bambanci da ku, mu na da tausayi da kuma nuna kulawa ga waWanda muke ?auna"

"A'a kar ki tsallake ki bar shi, amma ki yi Wamara fiye da ta baya, garin Buda ki ka zo za ki zauna, ban sani ba ko kin fahimci abin da nake faWa ko ba ki fahimta ba. Idan ma ba ki fahimta ba, za ki gane daga baya. Bil adama ku na tausayi da nuna kulawa ga wanda ku ke ?auna, ku ke iya Waukar jinin makusantanku ku bayar, a yi muku tsafi ko? Da kyau matsala kuma ki sani, ba ki ga komai ba" Daga haka ya Sace Sat. Ta buWe idonta a hankali.

Tana buWe idonta, ta ji ana kaWa kacakaura, da garaya a tsakar gidan su. Ana ta hayaniya tamkar ana cin kasuwa a tsakar gidan.
Sanyi ta fara ji yana ratsa ta, bugun zuciyarta ya ?aru, fiye da da, waiwaya ta yi tana son ganin ta inda za ta ga ?aisar, ko makamancin hakan amma ba ta ga kowa ba.

Wata irin guWa ta ji an rangaWa da wata irin murya, mai sauti, sai kuma aka ce "Yeeee barka da zuwa wakilin rafi, ku matsa ku bayar da hanya ga ango mairamu ya iso" ta ji wata murya na faWa, ana ci gaba da shewa da kaWe-kaWen garaya.
"Ku kawo Nono da suga, a kirawo 'yar Mairo ga mijinta ya iso. Ga farin goro ?warya dubu biyu ta rafi ta ce a bawa mamman wakilin rafi, gaisuwar iyaye" sai kuma aka saka shewa. Ba yau Nana ta fara ire-iren wannan jiye-jiyen ba, amma ta tsorata da wannan sosai da sosai. Ta rirri?e Sayyid, ga sanyin da take ji ya fara damunta.
Cas cas cas, ta fara jin sautin kaWawar wani abu mai kama da abin ado na mata.
Ta kalli tsakar gidan ta hango wata irin zan?aleliyar mata, mai tsawon gaske ?afafuwanta duk sar?o?i, ta yi shigar Fulani, sai dai ita ma ba a iya ganin sawayenta tamkar a kan iska take tafiya. Ta Wan ?ara buWe idonta, ta ga rana ce tarwai a tsakar gidan, ga dandazon mutane ana ta hada-hada.
Ayshacool
Sai dai shigar mutanen irin na zamanin da ne can baya sosai, kamar dai taron wani abu ake yi.
Wata mata ta hango sanye da kayan sa?i farare tas, ?ugunta sanye da wuri, kanta babu Wan kwali duk ta yi wa tulin gashinta adon wurin, hannunta ri?e da sandar dargaza, tana kaWa ta tana juyi.

Wannan bafulatanar ce ta tsaya a bakin ?ofar Wakin Nana ta ce "Ba?uwarmu, bikin girka ake yi, ko za ki taso ki ga yadda muke gudanar da al'adun bikin girka?" ta yi maganar tana zuro zan?alelen hannunta cikin Wakin Nana".

"La'ilahaillalah, Sayyid, Sayyid wayyo Baba" ta tashi a gigice, rirri?e ta ya yi, ya janyo wayarta, ya haska ta. Fuskar sa cike da mamaki yake kallon ta, yanayin fuskarsa ke bayyanar da alamar tambaya.

"Sayyid wata mata ce, wata mata ce take ziro hannunta, tsoro nake ji, wasu mutane ne a tsakar gidan nan" ya haska Wakin ta ga babu komai, haka tsakar gidan ma dare nesai hasken farin wata, babu komai. Sai a lokacin ta fahimci mafarki take yi. Ya ji jikinta ya yi sanyi ?alau, amma bai ga ?aisar a gurin ba, bai kuma ga wata alama da take nuna yana gurin ba.
Gaba Waya ta nemi ko addu'a Waya, ta rasa a cikin kanta. Ta kaWa ta raya amma babu abin da ya zo da kanta. Tana so ta karSi wayarta ta kunna karatun Al?ur'ani, amma ko ?wa??waran motsi ba ta son yi, saboda tsoron da take ji.
Da ?yar wani baccin ya ?ara sace ta.

Babu babban abin da ya ba shi mamaki, irin yadda da safe take komawa normal, babu ma alamar akwai wani abu da yake ba ta tsoro cikin daren.
Haka ta ci gaba da sabgoginta. Sai dai gaba Waya a kunyace take, ko idonsa ba ta iya kallo, saboda abin da ta aikata ya kama ta cikin dare. Shi ga tausayin kan su, ga kuma dariya ta ba shi.

*
Baba yana zaune yana shan koko da ?osai a tsakar gida, sai ga kiran wayar Uwani.

Ya kalli wayar tasa ya ce "Tofa! Wannan jarababbar tsohuwar ko me za ta ce mini, take kira na da safiyar nan oho.

Ya Waga kiran ya saka a kunnensa. Sai dai ba ya jin ta sosai saboda rashin network. Ba ta ha?ura ba ta din ga kira har sai da ransa ya fara Saci.

"Uwani ko a ha?ura da wayar ne, kin ga babu network ne"

"A'a ina jin ka yanzu. Amm dama kiran ka na yi, na tambaye ka ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login