Showing 111001 words to 114000 words out of 168002 words

Chapter 38 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

671

Nana kuwa?"

"Nana, tana gidan mijinta"

"Gidan mijinta wanne?"

"Mijinta dai na aure"

Uwani ta ce "Eh a ina gidan yake?"

"Amm can wajen gidan Ummi ne"

"Rufe mini baki, mutumin banza da na wofi. Ai kwana uku kenan ina neman layinka, amma bana samu saboda garin nan bamu da natiyok ake cewa ko me?"

"Uwani wai me ya faru ne?"

"Ai ba za ka san meyafaru ba, tun da ka bar yarinya tana ragaita ita kaWai ranta ga miji mai larura,an kore su daga gidan haya, ba su san ma inda za su je ba, kana zaune hankalinka kwance. Ai ko 'yar ri?o ce Nana ka duba lamarinta"

Ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, ta wanke shi ta tas, ta ?are masa zagi da cin mutunci, ta ce kuma za ta kira Yaya Atine ma, sai ta ci ubanta.

Ran Baba ya yi mummunan Saci, kenan Ummi da Nana haWa kai suka yi, suka kai ?ararsa gurin Uwani. Ya kira Ummi ita ma ya fara sauke mata kwandon tijara. Ranta ya Saci ta ce "Ni fa Baba ban kai ?arar ka gurin kowa ba, Uwani ce ta kira waya,? mu na tsaka da alhinin halin da Nana ne ciki, na gaya mata komai, kuma ni na faWa ba Nana ba. Shi ne ta ce Nana su koma ?auye can gurin ta".

Sai kuma Baba ya yi sak. "?auye kuma? Ta yi me a ?auye?"

"To Baba zaman nan Win ya ?i, kai kuma ka ?i taimakawa, babu yadda muka iya Nana tana Buda"

"Ke Ummi ki na ji na, duk yadda za ki yi, ki nemi kuWin mota, ki je Buda ki taho mini da 'ya ta. Lallai ya sakar mini 'ya ku taho tare, ya je Allah ya ba shi lafiya"

"Baba ya sake ta, 'yan uwansa ma ba a sa inda suke ba, wa za ta bar wa shi a can?" Yana cikin bambami kuWin wayar suka ?are.
Dama Mama na tsaye tana jiran ya gama wayar, yana gamawa ta dube shi ta ce "Wato Nana ta kaso aurenta ta dawo ko? To wallahi ta dawo gidan nan ba ta da gurin zama, wai har ka manta irin zaman azabar da muka yi da yarinyar nan a cikin gidan nan? Babu bacci kullum bala'i da tashin hankalin iskokai, ba zai yiwu ba wallahi"
Ayshacool
Sai dai kafin Baba ya ba ta amsa, suka ji Suwaiba ta ?ya?yace da wata irin dariya mara daWin ji tana faWin "Asma'u a ?auyen Buda, tushiya masomar dawa, kowa ya bar gida gida ya bar shi" ta yi maganar tana ci gaba da ?ya?yata dariya kamar ba mace ba.

"Ke Suwaiba meye haka, wannan wace irin dariya ce? Ban hana ki irin wannan dariyar ba kamar ba mace ba?"

Suwaiba ta ce "Ina ruwan ki da dariyata"

Baba kawai ya gyaWa kai, ya gyara hularsa ya fice ya bar gidan gaba Waya.

****
Rashin maganar nan ta Sayyid, ba ?aramin damun Nana take yi ba, abin ya yi yawa sosai.

A wannan karon ta yi sa'a, ya bar ta ta je gurin Uwani, daga nan kuma ta je ta yo musu sayayya. Ta tafi ta bar shi da wayarta, domin ta Webe masa kewa.

*

Alhaji Zailani ya saka sabon layin da ya sayo a cikin waya, ya kira lambar Nana. Sayyid yana kwance yana jin yadda wayar take ta vibrating, amma ya yi banza. Saboda ko ya Waga ba iya magana zai yi ba.
Jin mai kiran ba shi da niyyar daina kiran, ya sanya ya Wauki wayar zai kashe. Sai dai ya fasa kawai ya Waga kiran ya kara a kunnensa.

"A tunanki dan kin yi blocking Win lambata, zai sanya na kasa cimma burina a kan ki ne? Yanzu hankalina ya dawo gare ki, na saka an kori mijinki daga gurin aiki. Kuma zan nemo ki duk inda ki ka shiga sai na cika burika a kanki" wani irin jiri Sayyid ya ji ya fara Wibar sa.

"Ba za ki yi magana ba?" Alhaji Zailani ya yi maganar yana kallon wayarsa. Wani irin haske ya ga wayar tana yi, tana fafar fafar za ta Wauke. Mamaki ya kama shi, dan wayar ba ta taSa yin haka ba. Fitilun Wakin suka Wauke, duhu ya gauraye Wakin nasa. Sai ya rikice ya tashi tsaye yana waige-waige.
"Karo na biyu, ka sake shigowa hanyata, duk da gargaWin da na yi maka, cewar mallakina ce, ina sake yi maka gargaWi, kafin na tona maka asiri." Alhaji Zailani ya toshe kunnensa, saboda wani irin sauti da yake ji mara daWi, ga Wakin yana ta jujjuya masa.
Can ya ji shiru ya daina jin sautin, ya buWe idanunsa a hankali. Sai dai ya ga Shukura a tsaye a gabansa, jini yana bin ?afafuwanta, ga wu?a a hannunta, tsirara ta.

Ya mi?e cike da razani, ya fara ja da baya.

"Daddy ina jaririna? Ka bani jaririna Daddy" Ya ci gaba da ja da baya. Da gudu ta bi shi, da wu?ar tsirararta. Ya fita da gudu yana ihu.

"Alhaji lafiya kuwa? Anya hawan jinin nan bai fara taSa maka ?wa?walwa ba, ya ya zaka din ga ihu haka?" Hajiya Amina ta yi maganar cikin mamaki tana kallonsa. Ya kalli gurin ya gan shi a kan gado, a Wakinsa. Yana son yi wa Hajiya Amina tambayoyi, amma abu ya gagara saboda tsabar razani da tashin hankalin da yake ciki.




AREWABOOKS

*

Uwani ta din ga yawo da Nana a cikin ?auyen nan, tana nuna ta a dangi, tana gaya musu 'yar gurin Isa ce. Dan galibi ba su santa ba.
Nana gaba Waya hankalinta yana kan Sayyid da ta baro a gida, shikaWai tana gudun kar ta je yana bu?atar wani abin. Ganin gantalin ya yi yawa, ga duk inda suka je sai Uwani ta tsuguna ta surutu kamar babu gobe.
Tun Nana tana jurewa, har ta gaji ta ce "Uwani, na bar mara lafiya a gida, ko za mu je inda zan yi sayayyar, na koma kar na je yana bu?atar wani abin.

Uwani ta ce "Kuma fa haka ne, to mu je na raka ki. Na so ma sai ranar kasuwa za ki je sayayyar, an fi samun rahusa. Ai tun da Allah ya sa ki ka zo garin nan, za ki yi ta ganin 'yan uwa da dangi, za a yi ta zuwa duba mijin naki ma"

Ita dai Nana ta yi shiru, dan duk surutunta, Uwani sai da ta saka ta gaji, ga azabar tafiyar ?afa da suka sha.

Ta rakata inda ta yo musu 'yan sayayyar kayan abinci, gaba Waya tsoron taSa kuWin take yi. Gani take yi kamar ?arewa za su yi.

Uwani ta raka ta har gida, sannan ita ma ta zagaya, ta koma nata gidan.

Nana ta shiga Wakin da Sallama, tana faWin "Sayyid, ka ganni sai yanzu ko, ka yi ha?uri Uwani ce ta din ga ja na, ?afafuwana kamar su karye" Sak dai ta yi shiru ganin wata irin kwanciya da ya yi a kife a kan cikinsa, hannunsa a lan?washe, kuma ba kamar mai ruf da ciki ba.
Ga shi a tsakiyar Wakin, ba inda ta tafi ta bar shi ba.
Ayshacool
Ta zube kayan ta nufe shi jikint a sanyaye, gabanta na bugawa saboda fargaba da tsoron ko mutuwa ya yi.
Aikuwa tana juya shi ta Wan ja da baya a tsorace tana sauke numfashi.

Wayarta ta gani a ?ar?ashin inda ya kifa, idanunsa a kakkafe, babu ba?ar ?wayar idon, sai farar. Ga jikin zafi rauuu tamkar wuta.
Ajiyar zuciya ta yi cike da damuwa, ta matsa kusa da shi ta yi Bismillah ta fara rage masa kayan jikinsa. Ta Webo ruwa ta din ga shashshafa masa tana sake nanata Bismillah.
Ta je ta rufe ?ofar gidan, ta dawo ta cire rigar jikinta, ta kwanta a jikinsa, tana rintse idanunta saboda raWaWin da take ji a fatarta.
Wani irin nishi yake, tamkar zai yi gurnani, yana mi?a jikinsa yana ?ara sandarewa.
A hankali ta ji tamkar hankalinta yana gushewa, ita ba a farke be, kuma ita ba mai bacci ba. Ta Wan Waga idonta, ta ga ?aisar tsaye a jikin ?ofar Wakin yana kallon su. Ta yi shiru ba ta yi motsi ba, kuma ba ta yi magana ba, fatanta Sayyid ya samu sassauci daga azabar raWaWin da yake ji.
"Ko dai ki bi a hankali, ko wannan Wan tayin na cikinki ya yo waje saboda zafin jikinsa. Ko kuma Giyaz ya yi masa mummunar illa." Nana ta Waga kai ta kalli inda ?aisar yake, jikinta ya yi mata wani irin nauyi, ba ta ko iya motsa Wan yatsanta.

"Babu irin kashedin da ban yi miki ba tun da fari, ki ka yi burus da ni, gani ki ke kawai cutar da ke ne kaWai abin da nake yi.
Amma tun da jimirnki taurin kai, wahala sai ranar da Allah ya yanke miki, tukuna ma." A hankali ta lumshe idanunta har ta daina jin muryar ?aisar.

****

Cikin damuwa Maijidda take kallon Saude ta ce "Yaya Saude haryanzu lambar Nanan ba ta shiga ko? Gaba Waya na kasa nutsuwa duk ji nake hankalina a tashe".

Saude ta ce "Dan Allah ki daina damun kan ki, in sha Allah tana cikin ?oshin lafiya, kin san sharrin wayoyin nan, da rashin network, amma zan ci gaba da kiran ta, da na same ta zan sanar miki, kuma zan sake zuwa har gida na haWa ki da ita."

"To Allah ya sa dai lafiya, kin ga na yi, na yi, na kaWa na raya, Baban su Walida ya ?i ba ni wayata, tsawon wannan lokaci haka nake zaune babu waya. Kuma duk wasu dabaru da zan yi na samu dama na je Kano na samu na ga yaran nan, abu ya ci tura sai ka ce ba Muslimi ba, ba ya jin magiya ba ya jin rarrashi".

"A'a kul Maijidda, uban 'ya'yan naki ki ke cewa kamar ba musulmi ba, kar ki sake. Ki rabu da shi da halinsa. Duk da Nana tana cewa za ta zo ita da mijinta, idan ma ba su zo ba, ni zan sake komawa na gano miki ita in Allah ya yarda. Iliyasu kuma ki rabu da shi ku lallaSa kar ki fusata shi ya yi wani abin da ba a fata"

Maijidda ta yi ajiyar zuciya, ta jinjina kai kawai, amma gaba Waya ba ta cikin nutsuwarta.

****

Abu kamar wasa, aka shafe kwanaki biyar, Sayyid yana cikin wannan yanayin, sai dai Nana ta juya shi, ta goge masa jikinsa, ta yi masa ?anin wanka a Waki, ta shafa masa turare ta saka masa kaya.
Ga shi juya shi kawai aiki ne, saboda yadda ya yi mata nauyi, ga jikinta babu ?wari saboda azabar laulayi. Juriyarta ce kawai ta sanya ba a gane mawuyacin halin da take ciki, dan ba ta taSa yarda ta kwanta.
Ga shi jikinsa duk ya kumbura, mussaman ?afafuwansa.
Tana zaune ta yi shiru tana kallonsa, kawai tamkar an yaye mata wani abu daga kanta, sarkin baka ya faWo mata. Sai da ta Wan zabura ta tafi tunanin ko yana wani hali yanzu?.
"Ko dai can zan kai ka Sayyid?" Ta yi maganar tana kallonsa.

"To ni da ban ma san a ina yake ba, ta yaya zan kai ka?"

"Kul mene ne sahihancin magungunan da yake bayarwa? Mene ne halacci ko haramcin abin da yake yi, da za ki je neman magani gurinsa?" Wata zuciyar ta gargaWe ta.
Sai kuma ta yi shiru, tana tuna irin wahalhalun da ta sha, da faWi tashin gurin masu magani, ita dai tana da ya?inin har gurin bokaye da 'yan tsubbu an kai ta, domin a nema mata magani. Domin wasu ?arara ayyukansu da abubuwan da suke faWa, ne nuni da kaucewa hanyar gaskiya.
Ayshacool
"Allah na tuba, Allah ya sanya ba wannan ne dalilan da ya sanya nake ta shan wannan wahalar ba. Allah ka yafe mini, ba da son raina aka din ga kai ni wasu guraren ba.
Allah ka bamu lafiya da ni da mijina, Ubangiji Allah ka yaye masa wannan larurar, ka dawo masa da tunaninsa. Allah ban yanke tsammanni da daga falalarka da ni'imamominka ba"

Ta juyo a hankali ta dubi gurin da yake, ta ga idanunsa sun dawo daidai yana kallon ta. A rikice ta ce "Sayyid"

"Ma vie"

Cikin tsananin murna ta ce "Alhamdillah, ka tashi?" Ya jinjina kai yana lumshe idanunsa da suka yi masa nauyi. Ya ja jikinsa ya tashi zaune da kyar. Sai dai jikin nan duk a kumbure,ga kuma haki da ya farfaWo da shi. Haka yau ma ta taimaka masa ya yi wanka ya ci Abinci ya fara rama sallolinsa a zaune.

Kallonsa take yi cikin damuwa, yakamata a ce sun koma Asibiti. Amma kafin a nemo mota a saka shi, su yi sammako su koma Asibiti, aiki ne. Mussaman da babu wadattacen kuWi a hannun ta.
A take ta tuna da maganin da sarkin baka yake haWawa masu hawan jini, da wanda Sarin jikinsu ya shanye a sakamakon hawan jini da matsalar zuciya.

Ba ta jira ya idar ????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ba, ta zari hijjabi ta yi waje. Ta din ga tuhumar kanta da yadda aka yi tuntuni ba ta tuna ba, sai yanzu. Tun da su magunguna ne da yake haWa s da saiwoyi ba wani surkullen ya yi ba.

Ta dawo ta tarar ya dawo bakin ?ofa ya zauna yana kallon hanya.

Tafiya mai nisa ta yi sosai da ta fita, ta samo Sawon kwakwa da sassa?en zogale, sai kuma farin zoSo.
Ta hura wuta ta wanke su, duk ta zuba a tukunya ta zuba ruwa, ta kawo Wan kanumfari ta zuba a ciki.
Sai da ta kammala sannan ta koma gurinsa, ta ce "Ka yi ha?uri, magunguna na je samo maka, na fita ka na salla"

"To na gode"

"Allah ya baka lafiya shugabana, Allah ya sanya ya wuce kamar ba a yi ba"

"Amin. Ke ma Allah ya baki lada, ya saka mini ke a aljanna. Ya sanya ki ma?wabci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam a aljanna" waro ido ta yi? ta gigice gaba Waya hawaye ya fara zirarowa daga idanunta ta ce "Sayyid ba ni da aikin da zai kai ni wannan matsayin. Amma ban san matsayinka a gurin Allah ba. Ban sani ba ko Allah ya karSi addu'ar da ka yi mini. Amma a ce na ma?wabci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Innalillahi wa Innalillahi raji'un Sayyid na rasa me zan ce. Baiwa ce mai tarin zunubai kuma mai tarin rauni. Amma Allah kai mai yawan rahama ne da falala, Allah ka amsa wannan addu'a da ya yi mini shi ma ka ba shi abin da ya ro?a mini"

Ya yi murmushi ya ce "Amin rayuwata"

"Sayyid, anya an taSa yi mini addu'a da ta tsuma ni kamar wannan? Subhanallah, subhanallah. Na ji daWi wallahi"
Shima idanunsa ne ya cika da hawayen, ya ci gaba da bin ta da idanunsa. Kawai sai Nana ta ji ta manta kaso mafi yawa na damuwarta. Da ta tuna Addu'ar da ya yi mata sai murmushi ya kasa barin fuskarta.

Maganinta ya daWe yana dahuwa, ta sauke ta mayar da ruwan girki. Ta tsiyaya masa a kofi, ta je ta zauna a gaban sa.

"Sayyid ga magani na dafa maka, mu jarraba, bamu sani ba, ko Allah zai sanya a dace" ya kalli kofin ya kawar da kansa gefe, yana Sata rai.

Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka sha, babu Waci ko bauri fa"

"Ba na son magungunan nan, babu yadda na iya ne nake shan na Asibitin ma, ni wahalar da ni suke yi"

"To ai wannan ba na Asibiti ne ba, dan Allah ka daure ka taimaka, ba dan ni ba"

Da ?yar ya yarda ya karSa, ya WanWana ya ji babu Waci, sannan ya ci gaba da sha, sai ma ya ji Wumin maganin ya yi masa daWi.
Bayan ya shanye, ta dafa masa shayi kuma, ya Wora dan duk wahalar ciwon da yake ciki, ba ya iya ha?ura da shan shayi.

Nana ta dage da bawa Sayyid, wannan ruwan maganin, tana addu'ar Ubangiji Allah ya taimake su, ya sanya ya karSe shi.
Cikin ikon Allah, sai kumburin da ya yi, ya fara sacewa a hankali, har yana iya cin Abinci sosai. Nana kamar ta zuba ruwa a ?asa ta sha.
Nana ta din ga murna, ganin ana samun ci gaba a yanayin jikinsa. Har banWaki yana iya zuwa, ba tare da ta kama shi ba, yana tafiya a hankali a hankali da kansa yana iya yi wa kansa Wasu abubuwan.

Yana zaune tsakar gida, yana shan shayi ta ce "Ashe maganin Sarkin baka yana yi"
Ayshacool
Ya kalle ta, ta ce "Ka san Sarkin baka?" Ya Wan yi shiru yana kallon ta.

"Ranar da aka kai ni, kai ma an kai ka, zaku tafi lokacin, ni kuma a lokacin ni kuma a lokacin na ji na fita daga hayyacina. Kai mun fa daWe muna haWuwa da kai."

Ya yi murmushi ya ce "Ruhina ne ya addabe ki, sai da ki ka nemo ni, ki ka aure ni ki ka nutsu"

Ta Sata fuska ta ce "Ba wani nan, kai ne ka din ga bi na dai, har ka aure ni".

Ya Wan sake zu?a shayin hannunsa ya ce "A'a. Har gidan da nake ki ka bi ni fa"

"Ni ba bin ka na yi ba, kuma ai kai ka ce a biya maka sadakin aurena"

Ya maze ya ce "Ai gani na yi kin li?e mini, har cikin Wakinmu na gadi ki ka bi ni, na ce kai yarinyar nan idan ban aureta ba, akwai matsala haka za ta yi ta bina saboda ruhinta da yake jikina. Kina ganina kuma ki ka rikice"

"Ni ba ina sane na shiga Wakinku ba, Jummai ce ta ce na ajiye muku Abinci, kawai na ji ana kirana a cikin Wakin, ban ma na san na shiga ba. Kuma ni da na shiga wannan tsohon na gani. Kuma ai kai ma idan ka ganni kallona ka ke yi"

"A'a faWi gaskiya dai, ni ki ka le?o ki gani, ranar ba ki ganni ba, sh... Kawai ya ga tana hawaye. A diririce ya ajiye kofin hannunsa ya ce "Mene ne?" Ta yi masa shiru.

"Laifi na yi miki? Wasa fa nake yi" ta yi masa shiru, tana matse ?walla. Ba wai wasan da yake yi mata ne ya sanya ta kuka ba. Tuna yadda aka yi auren abin da Baba ya din ga faWa da wanda Mama ta din ga yamaWiWi da ita, abin ne kawai ya dawo mata.
Ji ta yi yana goge mata hawaye, fuskarsa Wauke da damuwa, ya ce "Ba zan sake ba" KwaSe baki ta yi cikin shagwaSa, wasu hawayen na ziraro mata.

"Na ce na daina fa, ki bari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login