Showing 123001 words to 126000 words out of 168002 words

Chapter 42 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

676

ita ma ta yi aure ta hayayyafa.
A cikin 'ya'yanta aka samu wadda ta gaje ta, duk da ba irin tauraronta Waya da Lanti ba. A lokacin Musulunci ya shigo cikin mutane, duk da bai yi ?arfi a garin Buda ba.
Asma'u ta bayar da magani ita ma, ta yi aiki tare da ?aisar, sai dai ba ta da ?arfin zuciya da juriya irin ta Lanti. Gaba Waya ita ma ba wani daWin aiki ya ji da ita ba. Ko yaya ya buWe mata ido ta ga abu, sai ta kwanta ta hau jinya. Daga baya ma ta watsar ta tattara komatsan borin ta ajiya, ta ce ta tuba ta daina.
Ganin ba a samun masu irin tauraron Lanti, ya sanya ?aisar fara sarewa, da ha?ura da batun bayar da magani ta hanyar bil'adama. Sai dai yana iya yin sa gurin bawa zuriyar su Lanti kariya, daga cutarwar zuriyarsu.
Duk abin da yake faruwa, Giyaz yana ankare da ?aisar, kuma yana murnar yadda Wan sa ba zai ci gaba da zama bawa ga bil'adama ba.

Aka din ga samun ci gaba a garin Buda, wasu suka din ga barin garin su na tafiya fatauci, wasu kuma tashin hankalin Aljanun da ya addabi garin ne ya sanya suka bar garin, ciki har da wasu daga cikin zuriyar Lanti.
A can Bauchi aka haifi Maijidda, har ta girma, an saka mata rana saura watanni uku aurenta, su ka zo Buda, a nan suka haWu da Isa, ya ?allafa rai a kanta.
Yayar kakarta ta ce sai an warware wancan baikon da aka yi da na can garin Bauchi, an yi da Isa, saboda ?ara dan?on zumunci, kuma hakan zai sanya su din ga kawo musu ziyara a kai a kai, da ?ara samun zaman lafiya a tsakanin zuriyar maharba da ta wanzamai.
Ayshacool
Aka mayar wa da wancan na Bauchi kuWinsa, ita kuma ta auri Isa.
Gidansa na Kano, inda yake harkokin kasuwancinsa, nan ya tafi da ita. Ya ajiye ta a gidansa da suke tare da matarsa babar Gaddafi.
Ya Wora wa Maijidda son duniya, kamar a kanta ya taSa aure. Ba uwargidansa ba, hatta 'yan uwansa sai da suka fara jin haushin Maijidda saboda ba ya Soye son da yake yi mata, ga ta yarinya ?arama amma su na ganin kamar ta mallake shi, dan shekarunta goma sha shida a lokacin.
Kasancewar daga zuriyar Sarkin Aska Maijidda take, ta auri Wan zuriyar Sarkin Baka, sai Aljanun da suka yi wa sarkin Aska hidima, suka shiga cikin lamarin auren, su ka fara haddasa musu matsala. Haka kurum sai ta ji ta tsani Isa, ba ta ?aunar ganinsa ga yawan rashin lafiya. Kishiya da facaloli suka sako ta a gaba, ga jarabar dangin miji.
Ana haka ya samu matsala da uwargidansa, da ta haifa masa Gaddafi da Ummi, ya sake ta. Nan ma aka ce Maijidda ce sila.
Ya auri Rabi, suka zama ita da Maijidda. Yayarsa Atine ta ?ara haWe kai da Rabi, su na cizguna mata.
Maijidda ke ri?on su Gaddafi, tana iya kokarinta amma kullum cewa ake yi tana azabtar da su. Kasancewar Gaddafi ya fi Ummi wayo, ya tsani Maijidda cewa yake saboda ita aka saki babar su, kamar yadda Yaya Atine take faWa. Ita kuma Ummi tana matu?ar ?aunar Maijidda.
Nan ma Rabi ta saka Maijidda a gaba, da kishi da ?age kala-kala.
Bayan haihuwar Imran sai da ya shekara uku da rabi, ta haifi Nana. A lokacin Isa ji yake kamar ba a taSa yi masa haihuwa ba sai a kan Nana. Ya saka mata suna Asma'u, sunan kakarsa da ta ri?e shi take bala'in son sa. Hatta hakika biyu ya yi wa Nana, Ummi ma da ya saka mata sunan mahaifiyarsa bai yi mata abin da yake yi wa Nana ba.
Isa kofur ne na 'yan sanda, abokan aikinsa suka yi masa ?age, aka kore shi daga aiki har da prison. Ya koma harkar fawa, ya fara samun rufin asiri, harka ta buWe masa yana samun rufin asiri sosai , sai dai kasancewar sa mutum ne da ba shi da sirri, duk samun sa sai ya bayar da labari, abokansa suka jefe shi sana'ar ta fita daga ransa ya daina zuwa ko ina, sai zaman gida.
Tun da Allah ya sanya aka haifi Nana ?aisar ya ganta ya rikice, tamkar Lanti ta yi kaki ta ajiye saboda kamanin su. Ga irin tauraronta Waya da Lanti. Gaba Waya ?aisar ya tattara hankalinsa a kan Nana Asma'u yana ganin, ya samu uwar gijiya a zuriyar Lanti. Giyaz na fuskantar abin da ke shirin faruwa, ya fara ?o?arin raba ?aisar da Nana. Dan kullum yana tattare da ita. Wasu lokutan ya zungure ta tayi ta kuka. Manyan bokaye da ?ungiyon Asiri na zawarcin son yin aiki da ?aisar, saboda tarin baiwa da kuma ilimi da binciken ?wa?waf da yake yi. Wanda za su aiki da shi ne, ya din ga taimaka musu, su kuma su din ga yi masa hidima, amma fafur ya ?i. Saboda ba ya son duk wata ala?a da jini.
?aisar ya yi tafiya zuwa wata ?asa, ganawa da wani tsohon Aljani, a kan wani rubutu da yake yi, ya dawo ya tarar an saki Babar Nana, ita kuma Nana ta daina magana, ta daina tafiya ga Baba ya ?wace ta, ya hana Maijidda ita. Ya fuskanci aikin mahaifinsa ne Giyaz. Ya je ya same shi yake tambayar sa me yasa ya yi wa Nana haka.
Giyaz ya ce "Ka sani ba zan taSa sake yadda, ka zama bawan bil'adama ba, da ka sake zama bawan bil'adama gara na kashe ta ko na kashe ka, kowa ma ya huta."
?aisar ya san Giyaz ba ya magana biyu, idan ya faWi magana sai ya aikata.
Dan haka ?aisar ya fara ?o?arin kare Nana, ya yi amfani da jakar da ya saka Lanti ta haWa, ta yi amfani da ita gurin kashe Sarkin Aska. Ya ?ara yi mata aiki, da saiwoyi da wasu hatimai, ya yi wa Giyaz tarko da ita.
Cikin matsananciyar sa'a, Giyaz ya faWa tarkon ?aisar, saboda ya san muddin ya bar Giyaz, zai iya nakasta Nana nakasa ta har abada, ko ma ya kashe ta, kamar yadda ya furta.
Ya Wauki Giyaz, ya kai shi can nesa ya sadaukarwa wani boka shi, bisa musayar da za su yi, zai ba shi wani abu mai muhimmanci. Wanda ya yi hakan domin nesan ta shi da Nana da zuriyar Lanti.
Ayshacool
Duk da abin da ya yi ya dawo ya dame shi, yana matu?ar ?aunar mahaifinsa, duk da saSanin da suka samu, amma babu yadda iya, hakan ne kawai zai sanya ya nisanta shi da Nana.
Sauran 'yan uwan ?aisar da tuntuni suke jin haushinsa, suka yo caaa a kan ?aisar, har suka nemi hallaka shi, saboda abin da ya yi wa mahaifinsu, amma sun san ko sun hallaka shi, idan Giyaz ya kuSuta suma sai ya kashe su.
?an uwan Giyaz Duna, ya yi ta ?o?ari gurin ganin ya kuSutar da Giyaz, amma abu ya gagara.
Nan suka din ga kai wa Nana hari, da yin?urin hallaka ta.
Maijidda kuwa bayan mutuwar aurenta, tana gama idda, Iliyasu tsohon saurayinta ya sake dawowa ya aure ta. Ko da Baban Nana ya samu labari, sai ya ce tana sane, ta ?i zama da shi, saboda ta koma ta auri Iliyasu, dama son zama da shi take yi ba.
Nana ta ga garari tun da ?uruciya, babu cikakkiyar kulawa, kuma tun ba ta fi shekara uku ba take ganin ?aisar, da ma sauran 'yan uwansa da suke ta kokarin azabtar da ita.
Maijidda ta so karSar ko Nana ce, saboda rashin cikakkiyar lafiya, amma Isa ya hana fafur, ita ma can mijinta ko yaya ta motsa tana son ganin 'ya'yanta, sai ya hau bala'i wai za ta gurin tsohon mijinta.
Tun Nana na ?arama, take nuna alamun rashin lafiya, amma babu wanda ya kula. Ta kan wuni tana bacci tun safe, har dare babu wanda zai damu. Wasu lokutan ta daina magana ma ko tafiya gaba Waya. Idan kuma ta warware ta din ga fitinar da ta fi ?arfin shekarunta nesa ba kusa ba.
Ta kan ga ?aisar a zahiri, ko kuma a cikin bacci. Babu wanda ya damu da ta ci Abinci ko ba ta ci ba, mussaman da Baba ya daina sana'ar komai, sai dai Imran ya nema ya bata. Idan ta fita ?aisar ya kan zo a suffar mutum, ya ba ta abinci. Allah ya sanya masa matsananciyar ?aunarta. Ya fara bayyana a jikinta ne, tun wani duka da Mama ta yi mata, bayan faWa ya haWa ta da Jamila.
Sai da ta kwana biyu a san?ame, tun daga nan suka gane halin da take ciki. Da ranta ya Saci sai hankalinta ya gushe. ?aisar ya sha Wauke Nana, a neme ta a rasa kwana Waya ko biyu ya je ya ajiye ta gurin sa.
Baba ya yi ?o?arin nema wa Nana magani, amma abu ya gagara. Labari ya iske Maijidda halin da Nana ne ciki, bayan da su Adda Saude suka zo ganin su Nana. Rabi ta haWa tuggu a gurin Baba, ya ce kar su sake zuwar masa gida, kuma ba zai bayar da Nana ba. Wahala ta saka Imrana fara sace-sace saboda su ci Abinci, Rabi ta saka Baba ya kore shi daga gidan. Haka Nana ta tashi a cikin wahala, ga wanda bil'adama suke yi mata, ga wadda ?aisar yake yi mata da sunan kulawa.

Ji ta yi tamkar an sanya hannu an sha?e ta, a dole ta saki littafin ta ja da baya tana tari.

Ta Waga kai ta kalli ?aisar, bai ce mata komai ba, ya Wauki littafinsa ya juya ya tafi. Yana barin gurin Haula ta zagayo ta dafa Nana. Ta Waga kai ta kalle ta ta ce "?awata, kwana biyu. Hadiminki ya ?i saurarata balle na sanya ran zai karSi bu?ata ta, ki yi wani abu a kai dan Allah"

Nana ta ce "Haula, gaba Waya jinsinku ba abin yadda ba ne, ki rabu da ni da wannan maganar ta ku"

"Shikenan, na rabu da ke, amma kin yi ganganci abin da ki ka yi wa dattijo, Allah kaWai ya san me zai yi miki idan ya gama jinya. Kuma har ?aisar ki ka janyowa shi ma ba zai bar shi ba"

"Duk hukuncin da ya yi wa ?aisar yayi daidai, Wa na gari ba zai taSa yi wa babansa abin da ya yi wa nasa mahaifin ba"

Haula ta ce "Kash! Nana kar ki zama butulu mana. Sai dai ina fatan kin fuskanci jakar gurin Sarkin baka da ya baki, wace jakar ce"

Nana ba ta ba wa Haula amsa ba, Sayyid ya tashe ta.

"Ma vie" yayi maganar yana matsawa jikinta sosai. Jiki a sanyaye ta amsa masa. Ya ce "Lafiya dai?"

"Mmm"

"Ko ?aisar Win ne?"

"A'a"

"To me yasa ki ka tsorata? Mene ne ya baki tsoro?"

"Bakomai"

"es-tu s?r? (Kin tabatta?)"

Ta ce "Eh. Haryanzu hannunka lafiya ?alau ko?"

"Eh, amma akwai abin da ya tsorata ki, gaya mini mene ne?"

Ji ta yi tamkar ta gaya masa, dan a wannan karon ba ta manta abin da Giyaz ya gaya mata ba, a kan idan ya warke zai sake waiwayar su.

"Ma viee"

"Sayyid" ta amsa a hankali.

Ya yi maganar yana taSa wuyanta "Sanyi ki ke ji Rayuwata"

"Eh, amma ba sosai ba"
Ayshacool
"In baki Wumi ne?" Yayi maganar muryarsa ?asa-?asa

Dariya ta yi ta ce "A'a na yafe, ?ona ni za ka yi"

Shi ma dariyar ya yi ya ce "To ni ki bani sanyin ina so" Ya yi maganar da sigar shawaSa.

"Wai kai ba ka jin bacci ne? Kawai ka farka cikin dare?"

"Soyayya ce ta tashe ni" Sai da jikin Nana ya Wan yi sanyi, ta ce "Soyayya kuma Sayyid?"

"Eh, je t'aime ma femme"

"To ai ban san me ka ce ba"

Ya yi kissing Win goshinta ya ce "Ina sonki matata" wani abu ne ya tsirgawa Nana, tun daga tsakiyar kanta, har tafin ?afarta.
Shafa hannunsa ta yi, kamar mai tantamar abin da ya ce, ta ce "Sayyid"

"A'a, kar ki yi tantama, ko ki yi kokwanto, shi yasa na baki sunan Rayuwata. Ko a wannan Duniyar, ko ma a wace Duniyar, kawai ina son matata, saboda ita Win Rayuwata ce. Babu abin da zai canza hakan."

"Sayyid ina tsoron idan ka tuna waye kai, ka ji ba ka so na, zan cutu da yawa, zamana da kai na sha?u da kai sosai zuciyata ba za ta iya Wauka ba" Ta yi maganar cikin rauni da tsoro.

Ya Waga kan Nana, ya sanya hannunsa a wuyanta, ta lumshe idanunta hawaye na bin gefen fuskarta.

"?a'idar ba za ta canza ba har abada, babu ruhin da zai samu nutsuwa a gangar jikin Wayanmu muddin ba ma tare, ki saka haka a ranki. Sayyid yana son Rayuwarsa. Ko babu raina fatalwata za ta ci gaba da sonki" Nana ta yi ajiyar zuciya tare da dariya, ta shafa gashin kansa.

"Allah ya sa haka. Ina son mijina sosai nima" murmushi ya yi yana kissing Win ta.

Har garin Allah ya waye, maganganun Sayyid ne ke kai komo a cikin ?wa?walwa, zuciya da kuma gangar jikin Nana. Wani irin shau?i da farinciki ne yake kama ta, da tuna kalamansa.

"Amarya" ya yi maganar yana kallon ?wayar idonta.

"Amarya da wannan Win?" Ta yi maganar tana nuna cikinta da ya fito sosai.

Yayi murmushi yana shafa cikin ya ce "Duk da haka amarya ce ai, ko kin manta?" Ya yi maganar yana kashe mata ido.
Ta yi murmushi tana ci gaba da ninkin kayan da ta wanke.

"Sayyid, bari na je kasuwa na nemo kayan magungunan ka, na dafa maka, ka ci gaba da sha, kuWin hannuna sun Wan taru, zuwa ranar Monday in Allah ya kaimu, duk yadda za a yi, mu tafi Kano Asibiti. Na ji haryanzu zuciyarka ba ta bugawa sosai, na san ?arfin hali kawai ka ke yi"

"Gaskiya kin fiye saka ido, ya aka yi ki ka gane hakan, mai magani?"

Ta jinjina kai ta ce "Au haka ma za ka ce ko? Hmm ai shikenan, za ka ga mai magani, yau sai na wanke ka da magani na kulle ka a Waki"

"Eh saboda cin zali ba, kuma ke ki gudu, alhalin kamata ya yi ki yi mana tare"

Ganin yadda yake rungumota ta ce "Sayyid na gama shiryawa, fita fa zan yi"

Ya ce "Na sani"

"Ka sani kuma ka ke son na Sata lokaci? Dan Allah Sayyid jiya throughout the night mu na tare, yanzu kuma...

"Shhhh... Ba ki ji jikina ya fara zafi ba"

"Wallahi lafiyarka ?alau, normal babu zafi a jikinka, wai wannan surutun duk daga ina?"

Haka ya hana Nana fita, har bayan Azahar, kawai ta zuba wa Sarautar Allah ido. Kuma a fuskar sa take ganin tsantsar ?arfin hali, amma ba shi da lafiya.
Sai bayan la'asar ta marairaice ta ce "Dan Allah ka bar ni na je na haWo kayan nan Sayyid, ko haryanzu ba ka gama jin Sanyin ba?"
Ya Waga mata gira. "To ga mafici, yi ta fifita, har na dawo" Dariya ya yi yana Wan jan hancinsa. Ya kamo hannunta ya Wora a wuyansa ya ce "Kin ji da zafi ko?"

"Ba wani zafi. Waccan ranar ma wayo ka yi mini, wai na baka sanyin jikina"

Dariya yake son yi sosai, amma sai ya yi kaWan ya cije, ya ce "Ai ni ?aisar wasu lokutan taimakona yake yi"

A sanyaye ta ce "Shi me yasa ba ka kishi da shi?"

"In ji wa? Kawai abu Waya ne da babu yadda muka iya. Ala?arsu ta Wa da mahaifi tana tasiri a rayuwarmu ni da ke"
Cikin mamaki Nana ta ce "Ta yaya? Kuma ya aka yi ka san ?aisar Wan Giyaz ne?"
"Yadda ki ke ganin ?aisar ku yi magana, haka nake ganin Giyaz, kuma na fuskanci waye shi a tattare da ni. Yanzu ki je ki dawo"
"Kai amma na yi mamaki fa, kuma ba ka taSa gaya mini ba. Bari na je na dawo, ina da tarin tambayoyin da zan yi maka"

"Tom sai kin dawo"

Ta saka hijjabinta, har za ta fita ya kirawo ta. Ya ce "Ba ki yi mini ba"

Ta yi masa kiss a goshinsa, da bakinsa.
Ayshacool
"Allah ya yi miki albarka. Ki kula mini da kanki, kar wani ya kula mini ke, ki kular mini da babyna ki tafi a hankali ki je ki dawo"

Ta kalli cikin ta ce "To Shugaba, in sha Allah"
"To a dawo lafiya, I love you"

Cikin murmushi ta ce "Inyee Wan gayu, ka yi furansanci, ka yi turanci, ka yi hausa ga kuma yarenku. Zan koyo yaren da baka iya ba, na din ga tashin kanka da kalaman soyayya"

Ya ce "Je ki dawo ki yi mini wa?a"

"Sai dai na je na dawo, na yi maka tsifa, na yi maka sabon kitso" ya tsuke fuska yana hararata. Ta fita tana waigensa tana murmushi.

Tana fita y????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
a jingina da jikin bango, yana dafe saitin zuciyarsa, yana haki sama-sama. Ya fito tsakar gida da kyar, ya zauna yana sake danne saitin zuciyarsa da yake jin wani irin abu kamar shocking daga zuciyarsa yana zagayawa bayansa har cikin kansa.
Tsayuwar motoci ya ji a waje, sai dai hankalinsa ba ya kan hakan. Ya ji an daki ?ofar gidan da ?arfi. Ya Waga kai ya ga wasu murWaWWun ?arti sun shigo cikin ba?a?en kaya.

Duk da mawuyacin halin da yake ciki, haka ya yin?ura ya tashi da ?yar, ganin an shigo da Habu hannunsa da sar?a.

Ya din ga bin mutanen da kallo, Habu cikin matsananciyar damuwa ya zube a kan gwiwoyinsa ya ce "Ka yi mini Afuwa Imam, ba laifina ba ne ka yi ha?uri, na gaza baka kariyar da ta dace" Sayyid ya din ga bin sa da kallo, da alama ma ba ya gane me Habu yake nufi.
?artin nan biyu daga cikin su, suka yo kansa, suka ri?e shi.

A rikice ya ce "A'a, ku rabu da ni. Me na yi muku?"

?o?ari suke su tasa shi su tafi da shi cikin salama, amma ya turje. Suka juya yare zuwa faransanci, su na rarrashin sa, ya wuce su tafi.

"Ba zan je ko ina ba? Ina zan tafi na bar matata" Habu ya din ga girgiza masa kai da alamar ya daina faWar maganar da yake yi.

"Ku rabu da ni, ina zaku kai ni na tafi na bar Nana" maganar da yake yi cikin Waga murya, ga ?o?arin turjewa da yake yi, ya sanya zuciyarsa yin rauni, ya yi baya zai faWi. Suka tare shi suka saSa shi suka yi waje da shi.
Aka saka Habu a cikin wata motar daban, Sayyid kuma aka saka shi a cikin wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login