Showing 132001 words to 135000 words out of 168002 words

Chapter 45 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

675

su ba, saboda idan maganar nan ta fasu akwai matsala"
Sultan ya numfasa cikin damuwa ya ce "Ni wannan bai dame ni ba, na bar ragamar komai a hannunka, ni lafiyar sa ce a gabana yanzu. Likita ku yi duk abin da ya dace kawai. Lafiyarsa ce damuwata a halin yanzu"

Likitan ya ce "In sha Allah" Dattijon ya saka hannunsa a cikin na mara lafiyan,yana kallonsa cikin matsananciyar damuwa. Kam?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 ar mafarki ya ga yana motsawa a hankali, sai ya ?ara tattara hankalinsa a kansa yana kiran sunansa.
Wata irin mi?a ya yi, yana ?o?arin buWe idanunsa, amma ya ji tamkar an cika masa idanun nasa da barkono.
"Imam..
Hannunsa ya Wora a ka yayi wata irin kururuwa, jin yadda naman jikinsa yake yi masa wata irin azaba, tamkar ana cizgar naman jikin nasa. Ga wani irin zafi da raWaWi da yake ji kamar yana cikin wuta.

"Zafi! Wayyo wuta Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wuta zafi jikina"

Kansa suka yi gaba Waya cikin tashin hankali, su na ?o?arin rirri?e shi, amma ya watsar da su ya diro daga kan gadon, yana girgiza kansa da yake yi masa wata irin azaba tamkar zai tarwatse. Tunaninsa ne ya hargitse gaba Waya, ?wa?walwarsa na ta kokawar ?wato wani abu daga cikin memories Win sa, amma abu ya kacame, gaba Waya tunaninsa ya hargitse, ya kasa tantance komai. Fizge-fizge ya din ga yi yana kururuwa jikinsa na rawa. Dattijon nan cikin jarumta da ?arfin hali, ya bi shi da sauri ya dam?e shi iya ?arfinsa.
Kokawa suka din ga yi, a rikice likita da Waya mutumin suka yo kansu, likitan ya haWa wata allura ya yi masa. Jikinsa ya saki a hankali bacci ya Wauke shi. Kan gadon suka mayar da shi suka kwantar. ?aya mutumin ya kalli likitan ya ce "Ka na ji na?" Likitan ya jinjina kai cikin nutsuwa.
"Ka san dai waye wannan, kuma ka san matsayinsa da girmansa ko?" Ya yi maganar yana nuna masa mara lafiyan.

Ya jinjina kai ya ce "Na sani"

"To muddin mu ka ji maganar abin nan da ya yi, ya fita waje, to ba wani ba ne ba kai ne, dole ka yi shiru da bakinka, kare sirrinsa wajibi ne a kan duk wani wanda yake yankin nan, idan kuma aka samu akasi ka furta wani abu, da rayuwarka za ka biya"

Likitan yana tsuma ya ce "In sha Allah ba zan faWa ba"



Da safe mijin Maijidda ya shura takalmansa ya fice, bayan sun gama jayayya da ita, tana ta ro?onsa tana yi masa magiya. Gaba Waya Nana ta ji dana sanin zuwa Bauchi da ta yi.
Babban abin da ya bata mamaki, ?atuwar kaza Maman ta saka aka yanka, ta gyare ta tsaf, ta yi wa Nana farfesunta, aka sayo mata ?aton buredi ta haWa mata shayi.

"Mama daga zuwana na Wora miki Wawainiya, ba ma na iya cin Abincin ni"

"?awainiyar ?aniyarki, da can na yi miki ne Nana? Dan Allah ki daure ki mayar da hankali ki ci ki ?oshi, idan kuma ki na son cin wani abin, ki gaya mini sai na dafa miki"

"A'a ba na son cin komai, amma ki zo mu ci tare da su Walida"

Maijidda ta ce "A'a, babu wanda zai ci, da rana ma ci Abincin tare, wannan dai na ki ne" Haka ta takura Nana, ta karya.

Nana ta fito da nufin, ta kama musu ayyukan gida, amma Mama ta hana, ta dafa mata ruwa ta yi wanka. Ta fito ta tarar Mama tana wanke kayan da ta cire.

"Haba Mama dan Allah ki bari na wanke da kaina, ya za ki din ga yi mini wanki?"

"Tafi Waki ki je ki zauna ki huta, ga lemon fata can da rake, ki Wan sha saboda WanWanon bakinki. Akwai riWi ma mai gishiri da mai suga, idan da wanda ki ke so" kawai Nana ta tsaya tana kallon ta, tana murmushi.

Maijidda ta ce "Ya dai?"

Ta girgiza kai ta ce "Ba komai Mama, na gode sosai"

Nana ta shirya ta canza kaya, Khadija da take 'yar autar Mama, Nana ta kama ta tana tsefe mata kai. Ta Wauki wayar Nana tana kallon hotuna. Sai ta buWe wani video da Nana ta yi wa Sayyid,? ta yi masa kitso sai hararta yake yi tana cewa "Ka ga yadda ka yi kyau 'yan matana, yi murmushi mana" ya Wago kansa ya hargitse idanunsa. Nana tana dariya. Sai da tsigar jikin Nana ta tashi, gani take kamar ta shiga cikin wayar ta ga Sayyid Win ta.

"Anty Waye wannan?"

"Mijina ne" ta ba ta amsa tana murmushi.

"Ya na gan shi da kitso, kuma fari?"

Nana ta yi dariya ta ce "Ni kuma ba?a ko?"

"Eh, kuma ba kyau maza su yi kitso fa"

"Wai in ji wa? Ba ki ga gashin nasa ne da yawa ba?"

Khadijah ta ce "Eh, to yana ina yanzu?"

"Ya je unguwa, zai dawo ya Wauke ni mu tafi"

"To ki nuna mini shi idan ya zo" Nana ta ce "To in sha Allah"

Mama ta ce "Ke Khadijah, tashi ki bar ta ta huta, Nana kwanta ki huta, ki rabu da surutun yarinyar nan"

Khadijah ta tashi tana zumSura baki, Nana ta Wan kashingiWa kawai wani abu mai kama da bacci ya yi awon gaba da ita, kasa tantance ma me take yi ta yi, bacci ne ko kuma ido biyu.

"Ma Vie" ta ji muryarsa a kunnenta. A razane ta waiwaya cikin damuwa. A tsakiyar sahara ta hange shi ta ce "Sayyid"
Ganinsa ta yi a tsaye a kanta, kayan jikinsa duk a yayyage, ya yi ba?i kamar ya ?one, gashin kansa a hargitse jikinsa sai fitar da haya?i yake, ya ce "Ma Vie sun mayar da ni inda za su kashe ni, dan Allah ki zo kar su kashe miki ni." Yayi maganar yana hawaye.

Ta tashi cikin tashin hankali ta ce "Suwaye? Kuma a ina suke?"

"Dan Allah ki zo, ni ban san su ba, amma na san mutuwa zan yi, dan Allah Husnah ki zo gurina, za su kashe ni. Idan kuma sun kashe ni, ki kular mini da Wa na"

"Sayyid, dan Allah kar ka tafi ka bar ni, dan Allah Sayyid ka dawo? Ka gaya mini kana ina, sai na zo na same ka na tafi da kai"
Guguwar Sahara ce, ta taso ta turnu?e gurin.
Nana ta din ga tari, muryar Mama ta ji a kanta tana faWin "Tari ki ke haka Nana?"
Kawai ta ga Nana ta tashi, ta yi waje. Ta ri?e ta ta ce "Ina za ki ke?"

Idanunta a rufe, fuskarta a murtuke ta ce "Ba ki ji Sayyid ne yake kirana ba?"

"Waye hakan?"

"Mijina mana" ta faWa a fusace.

"A'a babu wanda ya kira ki fa"

Nana ta fara ?o?arin fizge hannunta ta ce "Yanzun nan fa ya fita daga Wakin nan"
"Nana babu kowa fa a gurin nan, daga mu sai ke"

"Ni ki cika ni, na ji Muryar mijina gurinsa zan je yana kirana"

Tsawa ta daka wa Nana ta ce "Ina magana ki na Waga mini murya? Wuce ki zauna babu wani wanda yake kiran ki" Nana ta buWe idanunta, ta kalli Mamanta, sai dai ba ta yi magana ba, kawai ta ga Nana ta yi baya za ta faWi. Ta ri?e ta ta kwantar da ita. Jikin Nana ya hau karkarwa, idanunta na fitar da hawaye.
Cikin matsananciyar damuwa take kallon Nana, tana tunanin dama har zuwa yanzu, tana fama da larurar nan?.

Ta rungume Nana a jikinta, ta kama goshinta, ta fara karanta mata Suratul Jinn, tana tofa mata a fuskarta. A hankali jikin Nana ya saki ta fara bacci.
Ta yi shiru tana kallon fuskar Nana, tana tuna lokacin da take rungume da ita tana jaririya, cike da so da ?auna.? Tare da tuno irin soyayya da rawar ?afar da Isa ya din ga yi lokacin da aka haifi Nana, ba ta taSa tunanin zai yi wannan ri?on sakainar kashin da rayuwar Nana ba.

Adda Saude ce ta yi sallama, Mama ta amsa mata.

Ta Wan yi turus ta ce "Ya dai Nanan ba ta da lafiya ne, na ganta a kwance a jikinki haka?"

"Wallahi kuwa, shigo daga ciki" ta zauna ta ajiye kayan da ta zo da su. Ta ce "Tun jiya na so zuwa, tun da muka yi waya da ita da ta ce mini tana garin nan, babansu ne baya nan bai dawo da wuri ba ga yara gidan babu kowa. Ikon Allah ciki ne ma da ita haka?"

"Ga shi nan dai, har ya yi girma ma"

"Ikon Allah, na yi mamaki da na ji zuwa ta yi babu sanarwa, tare da mijin suka zo?"

Maijidda ta numfasa ta ce "A'a, matsala ma aka samu, ba a san inda mijin nata yake ba"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, garin yaya ina ya tafi?"

"Wallahi ban sani ba, na dai ce ta zauna a nan, kafin nu ga abin da Allah zai yi. Ashe rashin lafiya ya sha, yarinyar nan ba ta taSa gaya mini ba. Ga babanta bai karSe ta ba, ?arshe ma sai Buda ta koma ta yi jinyarsa, kuma dai ma ya tafi ba a san inda yake ba"

Cikin jimami Saude ta ce "Kai subhanallah, abin nan bai yi daWi ba, yanzu meya same ta haka?"

"Iska ne ya buge ta, na ba ta abinci ta karya, ta fara bacci kawai ta tashi wai mijin ne yake kiranta. Ashe haryanzu tana fama da wannan matsalar. Wallahi Adda na yi dana sanin biye wa Iliyasu na watsar da yaran nan." Ta yi maganar hawaye na cika mata ido.

"Ki yi ha?uri, amma yanzu ya ku ka yi da shi?"

"Hmm mu na nan muna ta bugawa, wai sai ta bar gidan nan, ni kuma Nana ba za ta bar gidan nan ba, sai dai mu tafi tare"

A Wan tsorace Adda ta ce "A'a Maijidda, idan da matsala, a kaita gidan Fati tun da tana da yalwar guri, ko gurin Yakumbo,kar ku samu matsala"

Ta girgiza kai ta ce "Ni na ke son kula da Nana da kaina. A cikin su ban san wanda zai ji ?an wani ba, dukkaninsu su na bu?atata".

Nana ta farka tana Wan yin mi?a, ta cewa Maijidda fitsari za ta yi, ta raka Nana banWaki ta je ta yi fitsari, ta saka ta ta yi alwala ta koma ta kwanta.

Har zuwa yamma Adda na gidan, sai daf da magariba ta tafi, Nana kuma ta wartsake sai ciwon jiki da mararta da ke Wan murWawa.
"Nana, ranar Litinin in sha Allah za mu je Asibiti, a fara yi miki awo, kuma zan duba gurin masu magungunan islamic Win nan, mu je a duba ki" Nana dai ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Da sallar Isha'i, Baban su Walida ya dawo, tun da ya hangi Nana a Waki, ya turnu?e fuska ya kalli Mai Jidda ya ce "Me na ce miki a game da yarinyar nan?"

"Baban Walida, ba a yi wa Wa mugunta, dan Allah ka yi ha?uri ka bar Nana a gidan nan, ka ga 'yan uwanta ma duk ba su santa ba, ba su saba ba. Kuma ba a san me gobe za ta haifar ba. Wata?ila ita ce mai tallafar rayuwar ?annen nata nan gaba."

"Ni ba nusari ne kamar ubanta ba, ni zan tallafi rayuwar 'ya'yana. Ba na bu?atar ko sisinta a kan yarana. Ta koma gidan mijinta ko gidan ubanta, idan ba haka ba sai dai ki zaSa, ko ta bar mini gida, ko kuma auren ki."

Kafin ya rufe bakinsa ta tari numfashinsa ta ce "Na zaSi 'ya ta, zan tafi tare da Nana, ko a daji ne na rayu da ita na kula da ita. Tun da ba dan wahala da bautarka da ta 'ya'yanka kawai Allah ya yi ni ba. Ba ka da kara Iliyasu. Nan har 'ya na ri?e maka na aurar da ita ban yi mata mugunta ba. Har 'ya'yan 'yan uwanka ka kawo mini na ri?e, ban taSa muzguna musu ba, na ri?e maka, nawa 'ya'yan ne na banza kenan? ?iri-?iri Wan da na dur?usa na haifa ya tsane ni, saboda yana ganin na kawo su Duniya amma ban damu da su ba. Su 'ya'yan da na ri?e maka haifar su na yi? Ko kuma dolena ne su, ni 'yar guda Waya ka gaza yi mini kara a kanta? To ka sani duka yau duka gobe shi ke sanya ba?in ba'auzine yin tawaye. Zan zube maka yaranka na Wauki 'ya ta na tafi da ita, na kula da ita. Ka kwaWa gidan ka cinye da kai da 'ya'yan naka"

Cikin matsanancin mamaki ya ce "Maijidda, ni ki ke gaya wa wannan maganganun?" Cikin ?unar rai ta ce "Na faWa Win, shekara nawa na rayu da ba?in cikin rashin ganin 'ya'yana, kullum na motsa zargina ka ke da tsohon mijina. ?addarar haihuwar yaran nan biyu ta sanya ban aure ka da fari ba na fara auren sa, amma a kan dalilinku marasa tushe balle makama kun azabtar da ni da nesan ta ni da yarana. Wallahi wannan karon na zaSi 'ya ta"

Kamar zubar wuta, haka Nana take jiyo cece kucen su. Dana sanin zuwa gidan ya cika mata zuciya. Tabbas ba za ta so mahaifiyarta ta kashe aurenta, da wannan gayyar 'ya'yan saboda ita kaWai ba, idan ta bari hakan ya faru ba ta yi musu adalci ba baki Waya. Zurfin tunanin da ta tafi, bai bari ta gama jin yadda rigimar ta su ta kaya ba. A cikin daren bayan gari ya yi tsit, ta tashi ta haWa kan kayanta cif.
Ta laluba jakunkunan yaran na makarantar boko, ta samu biro da takarda ta yi rubutu, ta ninke ta ajiye a kan katifar ta.
Da Asuba, Mama ta zo ta tashe ta, ta yi alawala ta yi sallar Asuba. Ganin yaran na Waya Wakin su na salla, Mama ma tana bedroom Winta, tana salla, ya sanya ta lallaSa ta Wauki jakarta ta fice daga gidan.
Ta din ga zumbuWa sauri, tamkar za ta tashi sama, ga faggon kaya. Tafiyar ?afa ta ci sosai da sosai, har sai da gari ya yi haske, masu abin hawa suka fara fitowa, ta tari wani ta ce ya kai ta tasha. Yana kai ta tasha, ta yi sa'a an yi lodi saura gurin mutum biyu, tare da wata mata suka shiga tasha suka nufi babbar tashar Bauchi.
Daga babbar tashar Bauchi, ta hau wata motar, duk da zuciyarta na raya mata kamar matakin da ta Wauka ya yi tsauri, wata zuciyar kuma na raya mata shi ne mataki mafi cancanta da za ta Wauka, mussaman idan ta tuna yanayin yadda ta yi mafarkin Sayyid.
Wayarta ta ciro, ta shiga lambar Ummi, ta rubuta mata sa?o, sai da ta tabattar ya tafi, sannan ta kashe wayar, ta cire layinta daga cikin wayar.

Gari ya Wan fara haske, Baban su Walida ya fice, a matu?ar zuciye, ya yanke shawarar tafiya ya kai ?arar ta, tun da dama ya san ya saba samun goyon baya, ba ga taSa kai ?ararsa ba, amma shi ya kai ta ta, ya fi sau shurin masa?i.
Su Khadija har sun fara ?iriniya a tsakar gida, a zuciye kasancewar da takaicin ubansu ta kwana ta daka musu tsawa, ta ce su koma Waki, kar su tashi Nana. A zaton ta Nana tana cikin Waki tana bacci.

Jamila ce zaune a gidan Ummi, tana jajanta abubuwan da suka faru da Nana, ba tare da ta san ma hakan ya faru ba.
"Wallahi Ummi da an sanar da ni zancen matar nan, da suka ce Nana mayya ce, wallahi da sai na saka an rufe ta, sai na ja shari'a da su har gaban Al?ali, sun san girman sharrin maita kuwa?"

"Hmm ke dai a yi sha'ani, ga shi Nana ta bar gidan, amma an ce Haryanzu tana kwance babu lafiya matar, ni na fi tunanin ko Aljanun Nanan ne suka yi mata wani abin, tun da ta ce Nana take gani. Jamila wayar Nana fa ba ta shiga, ni kaina sai na shafe sati biyu ban yi magana da ita ba, saboda garin babu network. Haka nan za mu tafi kawai."

Ummi ta shirya, da Jamila Abba ta so ya kai su, sai ta yi wani tunani ta fasa, dan ba ta san a yanayin da za su je su tarar da su Nana ba.
Sai dai Ummi ta sha mamaki da suka isa garin, suka tarar da gidan Nana a gar?ame.
"Ikon Allah, ita kuwa Nana ina tafi haka? Ko sun je Asibiti ne?"

Jamila ta ce "Asibiti yau Asabar?"

"To maybe emergency suka je, kin san matsalar Zuciya yake fama. Mu ?arasa gidan Uwani".

Suka zagaya gurin Uwani, ta yi murna sosai da sosai da ganinsu, sai dai ta hau Jamila da faWan ba sa zuwa sai yanzu, da yake Nana ce a garin.
Ummi ta yi ta bata ha?uri, ta ce sun zo duba Nana ne, sun tarar da gidan a rufe.

"Ohh abin tsiya, ba ma kwa bibiyar halin da take ciki, to Nana tun shekranjiya ta bar Buda, mijinta aka nema aka rasa ko sama ko ?asa sama da sati biyu, ta ce mini gurin Babarta za ta tafi a Bauchi, babu yadda ban yi da ita mu yi zamanmu da ita a nan, amma fafur ta ce in ?yale ta, tafiya za ta yi".

Jamila ta ce "Dan?ari"

Ummi kuwa "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" kawai take maimaitawa.

"Amma me yasa Nana ba ta dawo gida ba, sai ta tafi Bauchi, bayan ta san halin Baba"

"Baban wofi, uban me zai tsinana mata, ko ta je gurin nasa"

Suka gama jimamin da za su yi, suka tashi suka tafi.

Jamila ta ce "Anya Ummi mu gaya wa Baba kuwa?"

Ummi ta ce "Tun da shi ya haife mu, ba dole a gaya masa ba. Wallahi duk cikinmu babu wanda ya sha azabar ds Nana take sha a rayuwarta, da kin ga yadda take shan wahala da mutumin nan, sai kin tausaya mata, gaskiya idan guduwa ya yi ya bar ta, bai yi wa kansa adalci ba."

Suka ci gaba da jajanta lamarin.

Da suka shigo gari, Jamila ta tafi gida, Ummi ma ta tafi nata gidan.

Mama na ganin Jamila ta dawo, ta fara yi mata tambayoyi, amma Jamila ta yi burus, ba ta gaya wa Mama komai ba.


Tare da Kawun Mai jidda Iliyasu ya dawo, yana ta faman bambamin ta lalace, abin da ta ga dama shi take aikatawa.
Sai kuma Adda Saude da suka taho tare, dama sai da ta yi tunanin a samu matsala saboda zuwan Nana.

Suka tarar da Maijidda idanunta jawur, fuskarta babu annuri.
Suka zazzauna a falonta, kawunta ya dube

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login