Showing 153001 words to 156000 words out of 168002 words

Chapter 52 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

658

za mu je ne?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a Mummy na sha magani ai"

"Yakamata ki warke, mun kusa zuwa taron ?ungiya fa na shekara, lokaci ya kusa"

Kawai Jamila ta gyaWa kai.

"Ga shi kuma haryanzu babu wani labari da ki ka samo, a kan 'yar uwakki, dan haka sai ki shirya sadaukar da jini"

Jamila dai ta yi shiru, tana jin kamar ta kashe tsinnaniyar matar ta huta.

*

Nana na zaune tana shayar da Muhsin, Nene tana gefe tana lissafa kuWin da aka kawo mata daga gurin sayar da Abincinta.

Nana ta numfasa ta ce "Nene wai me yasa kwana biyu ba kya fita gurin Abinci ne?"

Nene ta kalle ta ta ce "Na fita ki samu damar guduwa ko?"

Nana ta yi turus tana kallon Nene.

Nene ta yi murmushi ta ce "Yarinyar nan ki na wasa da ni, tuni na gane duk wani take-taken ki ai, jira nake yi na ga iya gudun ruwanki. Ke yanzu idan ki ka fita gidan uban wa za ki je? Ki na da tabbacin za ki iya sake haWuwa da mutanen da za su kula da ke ne? Ko an gaya miki kowa ne zai iya yin taimako?

Kin tattara kayanki gaba Waya, kina Wauke Wanki daga Wakina, jira ki ke yi ki samu dama ki gudu, to ki tafi duk inda za ki tafi, amma ba za ki tafi da jaririn nan kina gararanba a gari ba, tun da duk ?o?arin da nake yi a kan ki ba kya gani. Kina zaune a nan na saka ana ta yi mini cigiyar masu gadi da suke zuwa Nigeria, ko akwai wanda ya san mai suna Habu ko Sayyid ki ka ce sunansa ko wa? Anma ba kya gani, to ki fita ki tafi duk inda ki ka ga dama, tun da ba ki da kan gado, kuma ba ki san darajar igiyoyi ukun da ke kan ki ba"

Nana ta sha jinin jikinta, da faWan da Nene take yi mata. Ta ce "Dan Allah Nene ki yi ha?uri, na ga na Wora miki Wawainiya ne ga shi haryanzu ina zaune babu wani labari a kan sa".

"Ni na ce kin Waura mini Wawainiya ne uwar iya? Ki yi duk abin da ki ka ga dama"

Nana ta ce "Dan Allah ki yi ha?uri ba zan sake ba" Nene ta yi mata shiru, daidai lokacin kuma Muhsin ya gantsarawa Nana cizo, da 'yan ha?oran da suka fara le?owa.

A fusace ta dake shi a kan pampers Win jikinsa, ta cire shi daga jikin Nonon, ta zaunar da shi tana ?ara tsuke fuska tare da hararsa.

Sexy eyes Win sa irin na mahaifinsa ya zuba mata, yana kallonta ko ?iftawa ba ya yi, gaba Waya ya rikiWe fuskarsa ta koma ta Sayyid sak, farar fatarsa ta yi jawur.

Nene ta ce "Yaka yaron kirki, ka ?yale ta da halin ta, shi ne za ki huce a kansa, ai ni na yi miki ba shi ba"

Ya rarrafa ya koma jikin Nene ya kwanta yana ci gaba da kallon Nana. Sai kuma jikinta ya yi sanyi ta ji zuciyarta ta yi mata nauyi da abin da ta aikata, ba tare da duba ?an?antar Wan yaron nata ba.

Ta shige Wakinta ta mayar da kayanta da ta haWe guri Waya inda suke. Wayarta ta Waukko da babu layi a cikinta, ta duba jakarta ta Waukko memorynta ta mayar kan wayar, ta fara duba hotunan Sayyid da ke ciki. Har da hotunan? Haidar Wan gurin Shukura a cikin wayar, da hotunanta na aure da aka yi mata da wayar.

Gaba Waya ta ji tana kewar ?asa Nigeria, amma hakan bai sanya ta ji za ta iya komawa a yanzu ba.

Tunaninta ya katse bayan da ta ji muryar wata ?awar Nene a tsakar gida, wadda ita ta yi hanyar kai Nana gurin koyon girke-girke. Amma Nana ta ?i fitowa.

Hira suke yi da Nene, take ba ta labarin ma'aikata ake nema, wanda suka iya girki sosai a wani restaurant, na wata Hajiya a can cikin birnin MaraWi.

Nene ta ce "Ba na yi wa Nana irin wannan harkar ne, saboda mutanen banza, ba dan haka ba ai da na ce ta je, tun da ta iya girki sosai"
Matar ta ce "To ai a Sangaren girki kawai za ta zauna, su na bu?atar kuku amma mai tsafta wadda ta iya girki, kuma tana biya sosai kin san buzayen nan kamar ba su san ciwon kuWi ba, buzuwa ce mai gurin"
Nene ta ce "Ai kin ga tana da yaro, shayarwa take yi, ai da na ce a kaita, amma idan za su Wauke ta da yaron shikenan".

"Anya kuwa, gaskiya ba na tunanin haka, ba ma za su yadda ba. Idan ta tafi a ?alla za ta iya yin wata, ba ta zo gida ba, za a ba ta komai a can. bari na tashi na tafi dama tsayawa na yi mu gaisa sai anjima"

Suka yi sallama matar ta tafi.

Nana ta fito da sauri ta ce "Nene, ina son zuwa gurin abincin buzayen nan"

Nene ta ce "Kin yarda mijin naki buzu ne kenan? Daga an ce gurin buzuwa kin rikice za ki je, bayan da kin ce mini ba ki san ?abilarsa ba, Allah dai ya shirye ki."

Nana ta yi shiru, tana mamakin yadda aka yi Nene take iya gano ta idan ta yi mata ?arya.

Nana tun dukan da ta yi wa Muhsin, juyin duniya har la'asar bai ?ara waiwayarta da sunan ta shayar da shi ba.

Sai da ta ji sun cika, sun fara damunta, sannan ta Wauke shi ta ba shi, amma fafur ya ?i karSa, ta kaWa ta raya ya ?i sha.

Nene tana kallon su, ta ?i magana, ta dama masa kunu ta haWa da nono ta zaunar da shi ta ba shi ya sha, ya ci gaba da wasan sa.

Nana ta ga sun mayar da ita saniyar ware ma. Har garin Allah ya waye, bai saurari Nana ba.

Ta sake Waukarsa, saboda yadda nonon ya cika, yake yi mata ciwo, amma fafur yaron nan ya ?i sha.

"Dan Allah yaron kirki ka yi ha?uri ka sha, ba zan sake dukan ka ba, dan Allah ka sha ba ka isa yaye ba" Nana ta yi maganar cikin damuwa.

Nene ta kwashe da dariya, ta ce "Kin ga ki ?yale yaron nan, ina ga fa ya yi zuciya ya yaye kansa, sai dai yi ha?uri"

Kamar Nana za ta yi kuka ta ce "Nene wata takwas sai ya yaye kansa? Ya yi wuri ai"

"To ba ke ki ka janyo koma mene ne ba?, tun da kin ce da babansa yake kama komai da komai, wata?ila har halayensa ya Waukko, kuma wata?ila wannan abin da ya yi akwai abin da yake nunawa bamu gane ba. Tun da yana shan kununsa, yana rarrafensa, ki rabu da shi kawai. A haWa sabaya da sauran saiwoyi, ki yi ta sha saboda kar su lalace".

Kamar Nana za ta yi kuka ta ce "Nene wata takwas fa"

"To ai ga ki nan ga shi. Sai ki ba shi ya sha ai"

Da Nana ta Wauke shi da nufin, ta shayar da shi, sai ya hau zunduma ihu,yana turjewa sai dai ta ?yale shi.

Nana ta din ga jinjina yadda aka yi, Wan wata takwas ya san ya yi zuciya da abu.

Sai da aka kwana huWu, Nana ta ga da gaske ya yaye kansa, iyaka ya zo jikinta ya yi wasan sa ya tafi.

Nene ta ce "Nana ki daina damuwa fa, girmansa tubarkallah da ?iriniyarsa kamar ta Wan shekara guda ce, ki rabu da shi kawai, daga yanzu idan za ki yi magana ki din ga yi masa da girmamawa, ki daina yi masa tsawa, manya ba sa son wargi. Kuma ki din ga duba darajar sunan da ki ka sanya masa" ta yi maganar tana yi wa Muhsin rawa.

"To Nene sai na bari ya lalace ba zan ce masa bari ba?"

"A'a ban ce kar ki ce masa bari ba, amma a wannan yanayin shi sarki ne, abin da yake so haka za ki yi ha?uri ki yi masa. Da kin tsaya a zare masa ido kawai da haWe rai, amma saboda na yi miki faWa, ki ka haWa masa da duka, kuma ki ka ?wace ki ka dungurar da shi, dole ya bar miki abin ki ai".

Nana kalle shi yana ta wasa da kofi, yana bugawa a ?asa, shi ma ya Wago ya kalle ta. Sayyid ta tuna lokacin da ya ritsa ta yana yi mata kashedin a kan daina yi masa tsawa ko Waga masa murya.

Wani guntun murmushi ya suSuce mata.

Nene ta ce "Ni kuwa Nana ga shawara"

Ta ce "To Nene"

"Kamar yadda ki ke faWa motsi ya fi laSewa, na ce ko dai za a jarraba ki je gurin aikin nan, na harkar dafe-dafen ko Allah zai sanya a dace. Duk da ba na jin a jikina, masu kuWi a cikin buzaye masu katafaren gurin abinci, za su iya tafiya aikin gadi, amma bamu san ina rana za ta faWi ba"

Nana ta Wan yi jimm sannan ta ce "Ban san ya zan yi ba ne, tun da kin ga ga Muhsin. Ko za su din ga bari na je na dawo kullum?".

Nene ta ce "Ki na ji fa ta ce sai ki yi wata ba ki zo gida ba, kuma akwai tazara a tsakaninmu sosai, kuma ba zai yiwu ki tafi da Muhsin ba, ba za su yarda ba. Amma ga shawara idan kin ga kin yarda da ni, ki bar mini Muhsin a nan, ki je ko ai

kin na wata uku ki yi, ko Allah zai sanya a dace, sai ki ci gaba da cigiyarsa a gurin."


Ayshercool

08081012143
Nana ta yi turus, tana kallon Nene.

Nene ta ce "Ba zan yi miki dole ba, dan kuwa wannan magana ce da kowacce uwa sai ta jinjina girmanta da nauyinta.
Sai dai ni ba zan takura miki ba kuma ban ce sai kin yadda da ni ba, ko mene ne za mu yi shi ne a gaban hukuma, mu je mu yi yarjejeniya mu saka hannu sannan ki tafi. Ban san dalilin da Allah ya sanya ya haWa ni da ke ba, duk rashin son mutane na, ki ka shiga raina ba nake tausayinki ke da yaronki. Har ga Allah ina fatan ki haWu da mijinki ko danginsa, ki samu ki koma gida ki nutsu ki kula da yaronki. Kamar yadda na gaya miki ne, ba zan yi miki dole ba, ki je ki yi shawara idan kin amince shikenan, idan ba ki amince ba babu wani abu, ni dai fatana Ubangiji Allah ya bayyana abin da ki ka fito nema".
Nana ta yi shiru, ?wa?walwarta gaba Waya ta Wauki caji da tunani daban-daban.


Jamila kuwa tun da ta je gida, Mama take tambayarta ko lafiya ta ganta wani iri, amma ta ce mata babu komai.
Ta shiga Waki ta nemi guri ta kwanta, sallolinta kawai ta yi na magariba da isha'i ta sake kwanciya. Gaba Waya abin Duniya ya gama damunta, dana sani da takaici duk ya cunkushe mata zuciya.
Wayarta ce ta fara ringing, ta duba ta ga ba?uwar lamba ce, jikinta ya ba ta Abba ne, ta Waga kiran ta saka a kunnenta.
Muryarsa ?asa-?asa ya kira sunanta ya ce "Ya jikin naki?"

"Da sau?i" ta amsa a hankali hawaye na ci gaba da gangarowa kan kumatunta.

"Dan Allah Jamila ina ?ara ba ki ha?uri, kuma ki dubi girman Allah ki rufa mini Asiri, ke ma kin san hakan ba halina ba ne ba. Wallahi na rasa inda zan sanya zuciyata na rasa abin da yake yi mini daWi. Yanzu haka zazzaSi ne a jikina. Dan Allah ki yafe mini Jamila, na san koma mene ne duk laifina ne. Amma in sha Allah kamar yadda na yi miki al?awari zan aure ki Jamila, wallahi ina son ki, duk abin nan laifin Mummy ne amma ki yi ha?uri ki yafe mini"
Jamila ta ci gaba da kuka, ta kasa ce masa komai, ya ?ara ruWewa ya ce "Dan Allah ki yi mini magana, dan Allah ki yafe mini idan ba ki yafe mini ba na san har na koma ga Allah, ba zan samu nutsuwa ba" Ya yi maganar yana kuka mai cike da nadama tamkar ?aramin yaro.
Duk yadda Jamila ta so jin haushinsa sai ta kasa, tabbas ita shaida ce wannan ba halin Abba ba ne, dan da halinsa ne da ba zai din ga wannan kukan ba, zai ga ya ci bulus ne kawai.

"Yaya Abba na yafe maka, mu haWu mu nemi yafiyar Allah, sannan ka daina kukan nan dan Allah, ka sha magani ka kwanta. Kuma Asiri idan na tona kaina na tonawa ba kai ba, Ubangiji Allah ya yafe mana"

Ya tashi zaune a kan gadonsa, cikin damuwa ya ce "Da gaske kin yafe mini Jamila?"

"Eh Yaya Abba, sai da safe, kaina yana ciwo sosai"

"To na zo na kai ki Asibiti ne?"

Jamila ta ce "A'a, na sha magani ina jin bacci ma, sai da safe" ta katse kiran tana ?ara du?un?unewa a cikin bargo.

Wata irin ajiyar zuciya ya din ga yi, ya nemi guri shi ma ya kwanta, zuciyarsa fal tunani daban-daban.

*

Nana hankalinta ya rabu kashi-kashi, a jikinta ba ta jin Nene za ta cutar da ita, duba da yadda take Wawainiya da ita da Wanta, tamkar ita ta haife ta. Sai dai ta yaya za ta iya ta tafi ta bar Wan ta, da matar da babu dangin iya babu na Baba a tsakanin su.
Sai dai tabbas akwai bu?atar ta gusa, ta yi wani yin?uri, domin ci gaba da ?o?arin haWuwa da mijin nata, amma ba ta ji ta gamsu da wannan shawarar ba.
Sai dai tun da suka yi maganar nan, da ta kwanta take mafarki ga ta a gurin girke-girken, tana cikin gurin girkin, ta waje sai ga din ga jiyo muryar Sayyid yana magana. Idan ta fita sai ta neme shi ta rasa, sai dai ta ci gaba da jin muryar ta sa, nesa da ita kaWan, sai dai ba ta san daga wane Sangaren muryar tasa take ba. Sai ta yi irin wannan mafarkin sai ta farka.
Ta rasa abin da yake yi mata daWi, kawai sai ta ci gaba da addu'a a kan lamarin, ta juya ta ci gaba da bacci, sai dai babu tsammani sai ga ta a Wakin karatun ?aisar, an yi mata gyara sosai, an ?ara yawan litattafan da suke ciki.
Ya saka mudubinsa a gaba, yana ta zuba masa wani ruwa yana wanke shi.
Bai ce wa Nana komai ba, har ta gaji da tsayuwa, ta Wan yi gyaran murya. Ya Waga kai ya kalle ta. Ta ce "Sannu da aiki"
"Yauwwa" ya amsa yana tashi tsaye.

Ta ce "Kwana biyu ina ka shiga ne?"
Ya Waga kai ya kalle ta ya mayar ya sunkuyar yana Waukar wani littafi.

"Amm dama ina ta son na ganka, na tambaye ka, sannan na ro?e ka alfarma. Dan da kai da Giyaz da duk wani mai son Waukar fansa a kan zuriyarmu, ya Wauka a kaina, dan Allah ku ?yale mini yarona. Na ga rannan ka ba shi wani abu da ban san ko mene ne ba, dan Allah kar ku yi masa komai"
Bai ko motsa ba, balle ta sanya ran zai yi mata magana.

"?aisar ka yi magana ma dan Allah"
"Na ce miki ne? Ko har kin manta abin da ki ka faWa a kaina, saboda abin da na yi wa mahaifina a kan na kare ki?"

Sai kuma Nana ta yi shiru, ta sha jinin jikinta.

Ya wurgo mata littafin nan da ta fara karantawa, ya ce "Ga wannan ki ci gaba da karantawa, wata?ila zai yi miki amfani a gaba" Ta kalli littafin ta kalle shi, ta ce "Me yasa ka amince na karanta wannan littafin, wancan kuma ka hana ni karantawa? Ni ba zan iya ci gaba da karantawa ba, babu komai a ciki sai tashin hankali da zubar da jini na tsagwaron rashin tausayi da adalci, ni bai burge ni ba, ba zan karanta ba"

"Ko? Amma idan an yi magana sai ki nuna kamar babu wata halitta da ta kai Wan Adam tsarki da tsoron Allah. Allah ya karrama Wan Adam a kan dukkanin halittunsa. Amma ba duk Wan Adam ne mai tsarkin zuciya ba. Wannan zubar da jinin da kashe-kashen da yake rubuce a cikin littafin nan, da gaske an yi su, domin cimma bu?atar Duniya, kuma haryanzu ana kan yi ma. Abu ne da ya faru wani ?arni a baya, kuma abin yake ta bibiyar zuriyar har wannan zamanin. Na ce ki karanta kin ?i, kin ce ba kya so shikenan ba zan yi miki dole ba, amma bari ki ga wani abu.
Ya Wauki littafin ya buWe cikin wani feji, Sangare Waya na bangon littafin zane ne, Sangare Waya kuma bayanin yadda taswirar zanen take ne. Ya haska littafin a jikin mudubin.
A nan take hoton ya bayyana a jikin mudubin, wannan Wakin da take ganinta a ciki ita da Sayyid shi ne ya bayyana a jikin mudubin, ba iya haka ba har ?amshin da gurin yake yi ta fara ji a hancinta.
A rikice ta ce "Nan gurin? Dama ina son sanin ina ne, yaya aka yi muke zuwa gurin nan ni da Sayyid, kuma idan abu ya faru a gurin kamar gaske."
?aisar ya rufe littafin ya ce "Ai kuma kin yi wa kan ki, ba zan bayar ba. Ya jefa littafin sama ya Sace Sat ita kuma ta tashi daga baccin.



Kwana biyu Jamila ba ta je gidan Hajiya Sa'a ba, saboda jikinta da ya matsa, idan Abba ya kira wayarta a kashe,? ga shi ba ta zuwa gidansu, shi ba abin ya tambayi Mummy ba.
Yana kwance a Wakinsa, ya tura mata sa?o. "Hankalina a tashe yake ?anwata, dan Allah ki yi mini ko flashing ne, hankalina na matu?ar tashe dan Allah ki Waga wayata"
Ya tura mata sa?on, tare da ajiye wayar.
Hajjya Sa'a ce ta shiga Wakin nasa, ta iske shi a kan kujera. Yana ganinta ya tashi zaune. Daga tsaye ta ce "Abba ba zaka fita bane? Baka fito ka karya ba, kuma baka fita kasuwa ba meyafaru ne?"

Ya girgiza mata kai ya ce "Babu komai fa"

"A'a akwai wani abu, na kasa gane kan ka 'yan kwanakin nan, hatta shirin bikinka nikaWai nake abina, me yake damunka? Duk saboda Jamila ne?"

Ya girgiza kai ya ce "Ba kin ce ba kya son ala?armu ba, ni kawai ba ni da lafiya ne" ta yi shiru tana nazartarsa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login