Showing 126001 words to 129000 words out of 168002 words

Chapter 43 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

651

ba?ar Highlander mai tint glass, aka rufe suka tafi da shi.

Nana tana tsaye ta bayar da kuWi, za a bata kankana, dan daga ita har Sayyid, kawai ta ji gabanta ya yi wata irin mummunar faWuwa. Ta yi shiru, ta jiki gaba Waya jikinta ya yi sanyi. Kawai ta juya ta tafi. Mai kayan yana ta yi mata magana, amma ba ta tsaya ba, ta nufi gida har da Wan gudu saboda azabar sauri.
Tana zuwa ?ofar gidan ta ga ?ofar gidan a Salle, da hanzari ta shiga gidan, tana kiran sunan Sayyid. Amma wayam ba ya nan, ta shiga Waki baya nan. Ta duba banWaki nan ma ba ta gan shi ba.

Ta fita waje da sauri, tana kalle-kalle, ta tafi hanyar inda bishiyar kukar nan take, tana tunanin ko jikinsa ne ya motsa, ya tafi can, sai dai can ma baya nan.
Ta sake komawa gidan cikin tashin hankali, da wani yaro da yake zuwar mata aike ta haWu a ?ofar gidanta ta ce "Ashiru, ko ka ga Sayyid ya fito daga gidan nan? Wannan mutumin na gidana farin nan?"

"Wasu mutane ne suka shiga gidan suka tafi da shi, a mota suka zo"

Sak Nana ta tsaya, tana ?ure Ashiru da ido, tamkar ma ba ta gane yaren da yaron yake yi.

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
Cikin rawar murya Nana ta ce "Wace irin mota kuma Ashiru? Ka tabattar kuma Sayyid ne?"

"Wallahi na tabattar, ina nan ina wasa suka zo, a motoci wannan farin na gidanki suka Waukko."
Tamkar mahaukaciya ta bi sahun motar, ita ce har titi ko za ta ga motar da Ashiru ya ce, amma babu wata alama na za ta ga motar da aka daukar mata Sayyid aka saka a ciki.
Gaba Waya ta kasa kuka, sai tsuma da jikinta yake yi tamkar mazari. Tuni rana ta faWi, an fara kiran sallar magariba, ba ta san tafiyar da ta yi da nisa ba, sai da ta tashi dawowa.
Gidan Uwani ta nufa, ta tarar da ita ta yi alwala, za ta yi sallar magariba.
Uwani ta ce "Ke Nana, uban me ya fito da ke da magaribar nan, ga juna biyu kina da shi, duk da na san ba ki da Wan aike amma koma mene ne, ai kya bari a idar da salla ko?" Nana ba ta yi magana ba, ta nemi guri ta zauna a ?asa.
"Ke lafiya kuwa?" Uwani ta yi maganar tana tattara hankalinta a kan Nana. Amma Nana ta kasa magana, sai murza zoben hannunta da take yi, tana ajiyar zuciya.
"Ke ki yi mini magana, kar ki tayar mini da hankali mana".
"Sayyid ne ya Sata"

"Kamar yaya sai ka ce wani zakara?"

"Da gaske nake"

"To ai ban gane ya Satan ba ne? Mutumin da yake jinyar ne ya iya tashi ya fita har ya Sata?"

"Ai kwana biyu jikin da Wan sau?i, dan har ya ce mu zo nu gaishe ki" Ta yi maganar ba tare da tana iya tantance me ma take faWa ba.

"A'a Nana, wata?ila dai wani wajen ya je zai dawo. Tashi ki yi sallar magariba, zuwa anjima a raka ki gidan ko ya dawo"

Nana jin Uwani kawai take yi, ta tashi ta yi sallar magariba, aka yi isha'i. Uwani ta saka Nana a gaba zuwa gidanta, sai dai kamar yadda Nana ta bar gidan wayam babu Sayyid babu dalilinsa.
Nana dai ba ta gaya wa Uwani abin da Ashiru ya gaya mata ba, na ya ga an zo da mota an tafi da shi ba.
Sai wajen goma na dare, hankalin Uwani ya tashi. Ta sanar da samarin gidan halin da ake ciki. Nan suka bazama a cikin Buda yawon neman Sayyid, duk da galibi ma ba su san shi ba, kwatancensa Uwani ta yi musu, suka tafi yawon neman sa, har gurin jami'an tsaro aka kai rahoto.
Sai dai har bayan sha biyun dare, babu wanda ya ji ko Wuriyarsa.
Uwani ta saka aka rufe gidan, ta ce Nana ta zauna a nan, ko zuwa dare zai dawo.

Nana a ranta ta ce "Wane dare kuma bayan wannan"

Daren ya zame wa Nana dare mafi tsawo a rayuwarta. Damuwa da tunani ya cika mata zuciya. Ba ta tunanin Sayyid zai iya tafiya ya bar ta. Idan kuma da gaske zuwa aka yi aka tafi da shi, to suwaye su ka tafi da shi? Ina suka kai shi, me ya yi musu? Ko dai wani laifin suke aikatawa ba ta sani ba? Amma shi da yake kwance babu lafiya, kullum tana tare da shi a gida, yaushe har yake aikata wani rashin gaskiya da ba ta sani ba.
A haka har aka yi assalatu, a kan kunnenta.

****

Dare malafar rana, kowa ya bika ya shirya maka.

Dan?areriyar mota ce, ?irar highlander ba?a, take ta kwarara gudu a saman kwalta, tamkar hanyar domin direban kawai aka yi ta.
Gefe da gefen hanyat baki Waya babu komai, banda yashin sahara, sai busassun bishiyu jefi jefi. Kasancewar dare ne, wata ya kai kwana goma sha huWu, ya haska ko ina, ga taurari sun yi wa sararin samaniyar ado.
Titin ta tsakiyar sahara ya ratsa, wadda yashin saharar ya bayar da sassanyan yanayi.

Kallon sa ya yi, daga bisani ya ce "Kilom?tre nawa ce ta rage mana ne?"

Direban ya waiwayo ya kalli mai maganar wandaa fuskarsa a rufe take cikin rawani ya ce "Bai fi 95 kilom?tre ba"

"Dans? quelques minutes ?? (Nan da wani lokaci?)".

"Bai fi awa Waya ya rage mana ba"

"Dole fa mu ?arasa dai-dai lokacin da aka umarce mu, ni ina tsoron ma kar ya farka. Ka ?ara sauri"

Ya yi maganar yana haska fuskar Sayyid, da yake kwance a jikinsa ya haWa gumi, cikin wani yanayi kamar bacci kamar suma, sai dai? yadda yake gumi ya nuna a wahale yake baccin, babu in da yake motsi a jikinsa, sai ?irjinsa da yake Wagawa yana sauka lokaci zuwa lokaci, numfashinsa yana fita da ?yar.

Ya kai hannunsa, ya Wora a kan ?irjin Sayyid, idan zuciyar sa ta buga sau Waya, sai ta jima kafin ta sake bugawa. Sai dai duk bugawar da za ta yi, da ?arfi take bugawa tamkar za ta tsaga ?irjinsa ta fito dummm!.
Ayshacool
Cikin damuwa ya ce "Lowalli, sai ka ?ara gudu fa, kar ya mace mana, bugun zuciyarsa raguwa fa yake yi. Kuma ka san idan ya mace mana mun shiga uku mun lalace"

Lauwalli ya jinjina kai yana ?ara gudun motar. Ya ce "In sha Allah a raye za mu kai shi, ba za a samu matsala ba. Dan dai ka ?i yarda ne, da na ce mu tsaya a Asibiti".

"Kai dalla ka daina maganar tsayawa a wani Asibitin nan. Ka yi ka hanzarta mu cika umarnin nan, mukaWai ake dako"

"To shikenan, mun kusa in sha Allah" ya yi maganar yana ?ara gudun motar.

****
Antin Yusra ce ta kalle ta, ta ce "Yusra duk wannan kwalliyar fa? Ta karSar ba?on ce?"

"Eh mana Mami, yana hanya ma ai" ta yi maganar tana tafiya Wakinta, ta fesa turare.
Wayarta ce ta fara ringing, ta Waga wayar tana murmushi ya ce "Gani a layin"

"Duba lambar gidan, za su buWe maka"

Ya ce "Ok"

Bayan mintuna goma sha biyar, ta fito ta ce "Mummy na tafi"

"To a gaida ba?on, ya tabattar mana da alkhairi"

Kawai ta fice tana murmushi. Tana zuwa ta gan shi a tsaye a cikin falon, yana kallon ?aton frame na hoton mai gidan, da yake retired soja.
Ganin abin take tamkar a mafarki, wai Sagir Win ta ne a gabanta.
Jin ?amshin turarenta ne ya sanya ya waiwaya.
Da gudu ta ?arasa inda yake ta faWa jikinsa.
Babu tunanin komai, Sagir ya ?an?ame ta a jikinsa, bar siririn mayafin da ta yafa a kanta, yana zamewa gyararren gashin kanta, da yake ta ?amshin mayuka ya bayyana.
Ya din ga shafa bayanta yana murmushi, kawai ya ji tana sheshshe?ar kuka. A Wan rikice ya ce "Lafiya, kuka kuma Yusra?"
Ya zauna tare da ita a jikinsa, ya ce "Ina ta murna zan zo na gan ki, amma in zo ki din ga kuka, ko ba kya son ganina ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"To mene ne"
"Ka daina so na, tun da ka sake ni ba ka ?ara nema na ba" Ya Wago fuskarta su na kallon juna yace "Da na daina son ki, ba zan zo nan ba Yusra, kin san yadda rabuwarmu ta kasance, ban daina sonki ba, ban kuma daina tunanin ki ba"

"Almost three years, ba ka sake nema na ba"

Sagir ya marairaice murya ya ce "To yanzu ba gani na zo har nan saboda ke ba? Haba wifey" ta zumSura baki cikin Wabi'arta ta shagwaSa. Duk da ya zuciyarsa na tunatar da shi, tare da gargaWin sa a kan Yusra ba muharramarsa ba ce, amma ya kasa ya?ar kansa, ya ?yale ta a jikinsa yana jin yadda ya yi kewarta.

"Talk mana, na zo kuma kin haWe rai?" Tashi ta yi daga jikinsa, ta zauna a kusa da shi ta ce "Ya hanya?"

"Alhamdillah, ki na lafiya ya jikin naki?"

"Da sau?i"

"Kin warware?"

Ta girgiza kai ta ce "Bayan ?in yadda ku ka yi da gaske ba ni da lafiya. Sai ga shi na haWu da wata Nana, ita ma tana irin ciwon da nake ji, ai ita ta san ba ?arya nake yi ba."

Ya ce "To yanzu dai duk ba wannan ba, i miss you Yusra, irin sosai da sosai Win nan fa"

"Bayan ka yi aurenka, ba wani missing Wina da ka yi" ta yi maganar tana tsiyaya masa lemo a cup ta mi?a masa.
Ya karSa ya kai bakinsa yana tsare ta da ido. Ta kalli screen Win wayarsa da ya kawo haske, hoton Haidar ya bayyana a kan screen Win. Ta Wauki wayar tana kallon yaron ta ce "Waye wannan?"

"?anki ne Haidar, recently ma ta kuma haihuwa Wan ya rasu" ta yi masa wani kallo, da bai tantance na mene ne ba ta ce "Da tuni nima wata?ila na haihu"

Ya yi murmushi ya yi shiru, yana cin abincin da ta zuba masa. Cikin hikima ya karkatar da zancen suka ci gaba da hira.
Wayarsa ce ta fara ringing, ta ajiye masa ganin hoton heart a kan sunan. Ya Waga wayar tare da yin sallama "Hello love"

"Ka sauka lafiya?"

"Alhamdillah am good dear"

Shukura ta ce "To sai ka dawo, Allah ya tsare mana kai, take care"

Ya yi murmushi ya ce "In sha Allah dear" wani abu ne ya tokare wa Yusra a ?irji, ta zuba masa ido.

Ya ajiye wayar, bai kalle ta ba ya ce "Yusy, kin san na yi missing Win girkinki over?"

Jin ta yi shiru ya sanya ya Waga kai ya kalle ta, ya ga tana hararsa. Ya yi murmushi ya Webo Abincin ya kai bakinta.
Ta murguWa masa baki ta tsuke fuska.

"Smile, haba sweetheart" ta buWe bakin ya saka mata Abincin. Haka ya ribace ta, suka ci gaba da hira.

A nan ya yi sallar la'asar, sannan ta fito raka shi.
A jikin motarsa suka tsaya, tana yi masa wani irin kallo mai ?ayatarwa.
Ayshacool
"Tom sai yaushe zan dawo?"

"An jima kaWan"

Ya yi murmushi ya sake kallon ta ya ce "Yusra"

Ta ce "Na'am"

"Yaushe za ki dawo gidana, ji nake kamar na Wauke ki, na tafi da ke Kano, ina kewar ki sosai da sosai. Yaushe za ki dawo gidana?"

Ta girgiza masa kai ta ce "Ba zan dawo ba"

Cikin mamaki ya ce "Saboda me?"

"Ka auri wata, kuma Hajiyarka ba za ta bari na dawo ba, su Mami ma ba za su bar ni ba, kuma ma haryanzu ban gama warkewa ba"

"Haryanzu ki na so na?" Ta kalle shi ta sunkuyar da kanta ?asa.

"Idan ba kya so na, me yasa ki ka nemi lambata, ki ka kira ni? Kuma har ki ka ba ni dama na zo?" Ta sunkuyar da kanta ta ci gaba da murza yatsun hannunta.
"Yusra Sagir Win ki ne fa, Wago ido kalle ni" Kawai ya ga hawaye na bin fuskarta.

"Sagir Wina, da ya rabu da ni, saboda ba ni da lafiya ba" Ta yi maganar tana sheshshe?a. Ganin babu kowa a gurin da suke, ya sanya ya janyo ta jikinsa, ya Wago kanta yana kallon idonta ya ce "Yusra, ki na so na haryanzu?" Ta yi shiru hawaye na ci gaba da bin idanunta.
"Ki na so na har yanzu, shi yasa ki ka neme ni. Dan haka batun ina da aure, Hajiyata ba za ta bari ba, 'yan uwana ba sa son ki, haryanzu ba ki da lafiya, duk ba ta taso ba. Za ki dawo gidana a karo na biyu in sha Allah. Haryanzu ina son ki Yusra"

"Amma...

"Babu amma tsakaninmu, believe me zan dawo da ke gidana in sha Allah" Jikinta ya yi sanyi. Ya cika ta a hankali, ya shiga motarsa. Ta tsaya ?yam tana kallonsa, shi kansa da kyar ya tafi, tamkar ya Wauki Yusra ya tafi da ita.

Har ya kama hanyar Kano, zuciyarsa cike da tunanin ta ina zai fara. Dan shi har ga Allah yana son matarsa, ba a son ransa ya rabu da Yusra ba. Yanzu kuma da ya ganta, gaba Waya ya ?ara rikicewa ba abin da yake sai tuno soyayyar da suka yi, daga saurayi da budurwa zuwa auren su.

Ko da ya je gida, Shukura ta karSe shi tana yi masa sannu da zuwa.
Amsa mata ya yi yana kallon ta, kafin ya ?araso ta kira shi ya fi sau biyu, yana zuwa hatta ruwan da zai yi wanka ta tanadar masa.
Ya cire kayansa ya shiga wanka, kamar ta san ba zai iya salla ba, sai ya tsarkake jikinsa, saboda rungumar da ya yi wa Yusra.
Tana cikin tattare kayansa, hancinta ya ji ?amshin turaren da ba na sa ba a jikin kayansa. Turarensa Waya ne da ta san shi da shi. Jikinta ne ya yi sanyi, domin ta daWe da karantar alamomin rashin gaskiya a tattare da shi. Wani abu ne ya soki zuciyarta amma ta yi ta maza ta haWiye tare da ajiye kayan.

****

Aka shiga kwana na biyar, ba tare da jin ko Wuriyar Sayyid ba.
Nana duk ta fita hayyacinta, ba ta iya cin abinci, ba ta bacci. Ga Uwani tun tana rarrashinta, ta koma yi mata faWa tana ganin ta ?i tawakalli ta ci gaba da addu'a.
Ga shi ta hana ta komawa gidan nasu, a nan gurinta take zaune tare da ita.

Yanzun ma Uwanin ce ta mi?o mata kofi da fura a ciki ta ce "Ungo ki samu ki sha furara nan Nana, ko Wan cikinki ya samu wani abu shi ma. Rayuwa ba za ta yiwu a haka ba kina zaune babu Abinci, ga juna biyu ba. Idan wani gurin mutumin nan ya tafi, idan da rabo zai dawo ai"
Nana ta karSi kofin, tana ajiyar zuciya. "Maza ki shanye, kan na fito daga banWaki" Nana ta jinjina kai tana kallon kofin.
Uwani na shiga banWaki, Nana ta Wauki mukullin da aka kulle gidansu, ta tafi.
Gani take kamar tana shiga za ta tarar da shi a inda ta bar shi. ?ofar dama a lanjare take aka rufe ta.
Ta shiga Wakinsu, amma ta tarar wayam babu kowa a ciki.
Ta kalli kan katifar su, ta ga abin hiraminsa na rawani a kai. Ta dur?usa a kan gwiwoyinta, ta dam?i hiramin nan, da yake ta ?amshin turaren sa. Tamkar ta dam?i Sayyid Win. Cikin kuka ta ce "Haba Sayyid, daga cewa na je na dawo, sai ka tafi ka bar ni? Haba Sayyid yau kwananka biyar ba ka tare da ni. Da mutuwa ka yi na san wannan hukuncin Allah ne, dole na tawakalli, amma me yasa zaka tafi ban san halin da ka ke ciki ba. Haba Sayyid Haba Sayyid Nana ce fa" ta din ga soki burutsu tamkar zararriya. Wani irin kuka take yi mai haWe da gunji da ?unar zuciya.
Ba ta san lokacin da Uwani ta shigo ba, tare da abokiyar zamanta Sabuwa ba, sai ji ta yi ta taSa ta ta ce "Nana shi ne sai da ki ka fito ki ka zo ko? Ba na ce kar ki fito ba?"
Ayshacool
"Uwani. Sayyid ya tafi ya bar ni, na zata mafarki nake yi, me yasa zai tafi ya bar ni?"

"Ke ki ji mini 'ya da rashin ta ido, yo ina zan san dalilin da ya sanya ya tafin ni? Ke ba za ki iya dakewa ki kama kanki ba, idan guduwa ya yi fa?"

Sabuwa ta ce "A'a Yaya, su fa yaran birni su na nunawa junansu kulawa, ya za a yi mutum mara lafiya a neme shi a rasa, ki ce hankalinta ba zai tashi ba? Kina kallon yadda take tiri-tiri da shi take nula da abin ta ke kin san ba ?aramin so take yi masa ba, ai da tausayi"

Uwani ta ce "Kuma haka ne, amma tun da shi ya tafi nima jikata nake yi wa kar wani abu ya same ta, ga ciki. Ke Nana kuma ba garinsu ya tafi ba bai gaya miki ba? Ba kin ce Wan Nijar ba ne?"

"Ba shi da lafiya fa, ba zai iya wannan tafiyar ba"

"A'a kar ki ce haka, idan ki ka bibiya ma, can Win ya tafi, amma yanzu ki yi ha?uri ki tashi mu tafi gida"

"Uwani, dan Allah ki yi mini alfarma ki bar ni na kwana a nan"

"To ya za ki kwana a gida ke kaWai haka ake yi?"

"Ni dai dan Allah ki bar ni a nan, wallahi da safe zan dawo na yi miki al?awari"

"A'a sai dai na turo yarinya Waya ta tayaki kwana" Nana ta amince da hakan, aka turo mata yarinya.
Tuni yarinyar ta yi bacci, Nana kuma kwana ta yi aikin kuka.
Lokaci Lokaci, sai ta yi tasbihi tare da ajiyar zuciya.
Washegari da sassafe Uwani ta zo ta kawo mata abin karyawa.
Yadda idanun Nana suka kumbura, ya sanya ta fahimci Nana ba ta yi bacci ba.

"Wai ni Nana, babu wani wanda za ki kira, ki tambaye shi ko yaje? Ko kuma wani guri da za ki je a duba?"
Jiki a sanyaye Nana ta girgiza mata kai. "To shikenan sha kunun nan da ?osai, kar su huce"
Nana ta karSi kunun tana kurSa a hankali, ji take tamkar tana shan magani, saboda wani irin Waci da take ji kunun yake yi mata a bakinta. Amma saboda ba ta son faWan Uwani, haka ta din ga shan kunun nan da ?yar.
Ta Wan saci kallon Uwani ta ce "Uwani, ina ga gobe in Allah ya kaimu zan shirya na koma Kano"

"Gurin wa?" Uwani ta jefe ta ta tambayar.
Nana ta Wan yi shiru, Uwani ta ce "Gurin wannan masoron Ubannaki da bai san ciwon kansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login