Showing 48001 words to 51000 words out of 168002 words

Chapter 17 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

664

da na ce"

"Har abada. Har abada ba zamu yi maka biyaya ba, duk da kasancewar ka abu mafi soyuwa a zuriyarmu."

Nana ji ta yi an yarfa mata ruwa a fuska, ta buWe idonta da sauri. Ido huWu suka yi, ya sakar mata tattausan murmushi. Ya ajiye matajin da yake taje kansa da shi ya nufo ta, cikin hanzari ta shige cikin bargo da kanta.

Ya zauna a kusa da ita, ya saka hannu ya janye bargon, ta ?i buWe idonta, sai ma mi?a da ta yi, saboda duk jikinta ciwo yake yi, kuma sam baccin bai ishe ta ba. Ya zuba mata ido, murmushi ya gaza barin fuskarsa.

"Ina kwana" ya faWa yana kallon ta. Kasa kallon sa ta yi, ta sunkuyar da kanta tana basarwa.

"A tashi a karya" ya yi maganar murmushi ya kasa barin fuskarsa. Ta ja jikinta ta tashi zaune da ?yar.

"Bari na yi brush" ta tashi ta nufi toilet.

A banWaki ta tsaya ta yi shiru tana tunanin littafin da take karantawa na ?aisar, ta san yanzu kafin ta sake samun littafin sai an daWe. Kenan da gaske dai shi ne uban du?usa? Ya aka yi sunansa ya canza zuwa ?aisar?

Ta wanke fuskarta ta yi brush ta fito. Har ya karkaWe mata shimfiWa.

Ta zauna, ya Waukko kofi da murfi ya mi?o mata. Ta saka hannu ta karSa, ta buWe ta ga abu a kofin kamar madara, da Wan wani gari gari a kai.

Ta kalle shi ya ce "Sha" ta kai bakinta, ta ji babu ?arni, ta yi bismillah ta fara sha.

Babu za?i, sai dai akwai garWi da mai?o a baki, ga Wumi kuma babu ?arni mai damu. Sai da ya saka ta shanye tas, ta kalle shi ta ce "Wai mene ne wannan?"

Ya yi murmushi ya ce "Nonon ra?umi ne"

"Ra?umi kuma? A ina ka samu Nonon Ra?umi?"

Ya ce "Habu na saka ya kawo miki, jikinki zai yi ?wari, ga abinci ma sun haWo da shi, na ce ba ki da lafiya"

"Gaya musu ka yi?"

Ya ce "Me?"

"Abin da ya faru jiya?"

"A'a ban ce musu, kin kore ni waje ruwa ya ji?a ni saboda ki na tsoro na ba"

Ta ce "Ba wannan ba"

"To me?"

"Ba komai" tayi maganar cikin basarwa.
Ya yi dariya ya ce "Ban faWa ba, daga ni sai ke kawai wannan" ta yi shiru wata irin kunya tana mamaye ta.

Babu babban abin da yake ?ara sanya Nana farin ciki, sama da samun abinci sau uku a rana da take yi a wadace, babu geji kuma babu hantara.

?aton buredi ne lafiyayye, aka soya ?wai fal, shayin ma shi ya zuba mata. Tana ci yana ?are mata kallo.

"Ka daina kallona, ko na tashi"

"A'a"

Ta ce "A'a me?"

"Ba zan daina ba"

Ta juya gefen sa, yadda sai dai ya kalli side Win fuskarta, ta gama ci ta koma gefe.

Shi ya yi mata komai, da ta motsa sai ya ce ta zauna. Sai dai ya lura gaba Waya ta zama so silent yau, ba karaWi da surutu. Duk sai ya ji hakan babu daWi. Ita kuwa ta yi matu?ar mamaki, ganin yau bai fice ya bar ta ita kaWai ba.

Ya dawo kusa da ita ya zauna, har gashin sa yana taSa wuyanta, kasancewar bai tufke shi ba, sakin sa ya yi.

"Me ya faru?" Yayi maganar yana Wora hannunsa a nata.

Ta girgiza masa kai, alamar babu komai.

"Ko ana fushi ne?" Ta Waga kai alamar eh.

"Me yasa?" Ya tambaye ta, yana shafa jikinta.

A ranta ta ce "Ikon Allah, ji mutumin nan da samun guri"

"Ba ki ce mini ya jiki ba, kin kore ni ruwa ya ji?a ni, ba ni da lafiya"

Nana ta tura baki ta ce "Ba ga shi ka warke ba, kuma ai ba ina sane bane ba "
Ayshacool
Nana ta haWiye wani abu mai matu?ar Waci, ta ji zafin maganganun da aka gaya wa mijin nata. Duk da ta san ya yi laifi amma kalmomin sun yi tsauri. Ta kalli idonsa ta ga ya yi jawur, hannayen sa na rawa, launin fatarsa ya canza zuwa ja.

Ta zauna a kusa da shi a kan bencin, ta Wora hannunta a bayansa ta ce "Sayyid. Ka yi ha?uri na fika jin zafin abin da ta gaya maka, amma ka yi ha?uri ka ji?" Kawai ya jinjina mata kai.

Ta sake kallon idanunsa, yadda suke ?ara rinewa zuwa launin ja, hakan ya ?ara bayyanar da matsanancin Sacin ran da yake ciki.

"Taso mu koma ciki to, tun da ka buWe mata" ya girgiza mata kai alamar a'a.

Jiki a sanyaye Nana ta tashi ta ?yale shi, dan ya fara ba ta tsoro.

Duk da yanayin da take ciki, ta ji daWin hirar da suka Wan yi da shi.

Ta kama aikace-aikacen ta a cikin Wakin.

*

Jamila ce take gaya wa Mama batun unguwar da Hajiya Sa'a ta ce za ta raka ta.

Mama ta ce "To mene ne a ciki? Ai babu komai yadda take nuna miki ?auna, ni ko bangon duniya ta ce za ku je, ai ba zan hana ba"

"To Mama Baba fa? Ni ba na son masifar nan tasa"

"Dalla rabu da shi, uwar me yake bamu a gidan, Ubangiji Allah ya haWa ki da iyayen Waki masu ?aunar ki, mu na samun alkhairi ta hannunsu, za ki din ga kawo zancen sa, ki yi tafiyar ki, ni na san abin da zan gaya masa"

Jamila ta yi murmushi ta ce "To shikenan, ni dama ba na jin ki, na san za ki bar ni"

Can Asibiti kuwa, likitoci sun yi deciding, tiyata za a yi wa Shukura a cire jaririn cikinta, saboda a tseratar da rayuwarta da ta abin da yake cikinta.
Sai dai da Jininta ya sauka sai ya sake hawa, saboda gaba Waya a tsorace take, ta yanke tsammani da rayuwar duniya ba ki Waya. Duk da irin rarrashi da ?o?arin kwantar da hankalinkin da ake yi mata.

Bayan Nana ta Wora girki, ta kira Hajiya Amina su gaisa, a nan take gaya mata halin da ake ciki, cewar su na Asibiti an kwantar da Shukura. Hankalin Nana ya tashi sosai da sosai, tana son zuwa duba Baba da Jamila ma, ga kuma wannan maganar ta rashin lafiyar Shukura. Sai dai yadda ransa yake a Sace ta san ba ta da damar yi masa magana.

Tun da abin nan ya faru, bai sake shigowa Wakin ba, ta je ta same shi a kan ta gama girki ya yi mata shiru. 'yar walwalar da ya fara yi ta gushe baki Waya.
Gaba Waya abin ya dame ta sosai da sosai, ko abincin kirki ta kasa ci.

Sai bayan sallar isha'i ya shigo Wakin ya nemi guri ya zauna, ba tare da ya furta komai ba.

"Sayyid ba ka ci abinci ba fa tun na safe ba ka kuma cin komai ba, dan Allah ka yi ha?uri ka ci abinci".

Bai ko kalle ta ba, balle ta saka ran zai ci, ?arshe sai ha?ura ta yi ta zura masa ido.

Ta gama shirinta, ta nemi guri ta kwanta, amma yana zaune. Nana ta jinjinawa girman zuciyar sa. Ya jima a zaune sannan ya tashi ya canza kayan jikinsa.

Bacci har ya fara Waukar Nana, ta ji yana shigowa cikin bargonta, gabanta ya faWi tuna abin da ya faru jiya, sai dai ba ta motsa ba, sai addu'a da take yi a karkashin zuciyarta.
Ya matsa sosai ya rungume ta, yana yi mata numfashi a wuya.

"Idan ina fushi, ki daina kula ni" ya faWa kamar mai raWa.

Ba ta iya tanka masa ba, bai kuma sake ce mata komai ba, sai da ta ga babu alamar zai yi mata wani abu, sannan nannauyan bacci ya Wauke ta.

Tamkar wani zai ?wace ta, ya ?ara ?an?ame ta a jikinsa. Sai ?amshin turaren sa take yi.

A cikin baccin ta ji muryar ?aisar "Ba kin shige cikin bargo ba, idan ki ka kuma Waukar littafin nan ki ka karanta, sai na baki mamaki, sai na yi miki abin da ba ki taSa tsammani ba"

"To ina ruwanka da bargon da na shiga, ya naga kamar ka na kishi da mijin nan nawa ne?"

Tsaki ya ja ya ce "Da me zan yi kishin? Haryanzu ba ki san a hatsarin da ki ke ba, wauta da shirme ne kawai yake Wawainiya da ke. Kin ?i ki buWe ido ki kalli gaskiya. Gaba Waya kin ma manta da batun tantance waye shi, duk da irin abubuwan da ki ke gani da ya saSa da Wabi'ar bil adama"
Ayshacool
"A'a ba kyau zurfafa bincike, tun da Allah ya sa ina samun shinkafar da zan ci, ba ya saka ni kuka, babu tashin hankali ai gara na ha?ura na lallaSa haka. Duk wani abu da yake yi da ya saSawa Wabi'ar Adam wannan kuma na san kai ne, kai ka ke ?ulla komai. Na san so ka ke ka kashe mini aure, saboda kai duk yadda za ka yi hana ni jin daWin rayuwata, shi ka ke yi"

Galala yake bin Nana da kallo baki buWe cikin mamaki. Ya ce "Gaskiya ne, idan ya gama baki jin daWin za kuma ki WanWana kuWar ki, banda ina duba wani abu da da kaina zan bayar da jininki ga matsafan nan ki mutu uban kowa ma ya huta!"

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
Nana ta saci kallon ?aisar, jikinsa har fitar da haya?i yake yi saboda fusata.

Ko a jikinta ta ce "Amm dan Allah ka gaya mini ya aka yi da Lanti a gurin yin girka? Ya aka yi ka hau kanta, tun da na ga ba da kai a ka fara yi mata girka ba, kuma ya aka yi ka canza sunanka? Ya aka ?arke da sarkin aska kuma a garin? Ta yaya duk nake da ala?a da wannan abubuwan?"

Wani irin takaici ya turnu?e ?aisar, ya tashi a fusace da niyyar ya yi jifa da ita, ko ya samu ya huce, sai kuma ya fasa kawai ya fice ya bar ta a gurin.

Ta ce "Wallahi sai na kai ?arshen littafin nan, ko da kuwa za ka kashe ni ne, sai na ga ?wal uwar daka, sai na karanta har ?arshe ko me za ka yi sai dai ka yi"

Sannu a hankali yake shafa fuskarta, yana kallonta, kamar wata jaririya haka ta yi mi?a sannu a hankali, sai da ta ban?are gaba Waya. Ita gaba Waya ta manta da shi a kan katifar, a zatonta ita kaWai ce a kan katifar, sai da ta ji ta a jikin mutum. Ta buWe idonta ta kalle shi. Sai kuma ta Wan tsorata, ta yin?ura da sauri. Amma ya ri?e ta yana kallon ta.

"Amm lokacin salla ya yi ko?" Ya Waga mata kai alamar eh.

"To bari na je na yi alwala"

Ya cika ta tashi, ta je ta yi alwala, sai da ta fito sannan ya ce "Zan yi wanka"

Ta ce "Wanka kuma? Yanzu?"

Ya Waga mata gira daga kwance.
"Ka yi da safe mana, gari da sanyi yanzu"
Ya lumshe idanunsa ya buWe, ya ce "Tare mu ka kwana a shimfiWa, kuma ya dai kamata na yi wanka"
Ba ta ce komai ba, ta yi shiru, Allah ya taimake ta, tana da ruwan zafi a tea flask ta haWa masa. Ya yi wanka ya yi alwala ya fita Masallaci.

Nana kuwa bayan ta idar da sallar asuba, ta zauna a inda take ta fara karatun Alqur'ani.
Ya dawo ya tarar da ita, ya tsallake ta, ya nemi guri ya kwanta.

Wajen ?arfe takwas ya farka, tuni Nana ta gyara Wakin yana ta ?amshi, tana zaune a kusa da socket, tana caji tana danna waya.

Ya Wora hannunsa a kan cinyarta, ya rufe fuskar wayar, ta waiwayo ta kalle shi ya ce "Ina kwana?"

MurguWa masa baki ta yi ta ture hannunsa. Ya tashi zaune, ya matsa kusa da ita ya ce "Na yi laifi ne?"

"Ai ka san me ka yi mini"

Ya ce "A'a abun tun shekaranjiya ba ya wuce ba?"

"Ni ba wannan ba, jiya na yi ta baka ha?uri amma ka haWe rai ka ?i kula ni, ka ?i cin abinci ma" ta ?arasa maganar tana hararsa

Ya Wan yi murmushi ya sake matsawa, tamkar zai shige cikinta ya ce "Na ce idan ina fushi ki daina kula ni"

Ta no?e kafaWa ta ce "Ni ba zan iya ba"

Murmushin fuskarsa ne ya f???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?aWaWa cikin matsanancin farin ciki ya kama hannunta ya ce "Ki yi ha?uri, idan raina ya Saci, ko bani da lafiya, bana iya magana. Wasu lokutan ina kasa magana haka kawai, amma ya fi idan raina ya Saci."

"To ni da ba ni na yi laifin ba, sai ka daina yi mini magana? Na fi ka jin haushin abin da aka yi maka fa"

"Na sani, ban san ya aka yi nake iya magana sosai ba idan ina tare da ke, ina iya yin sati ban iya yin magana ba, kuma ina son na yi amma ba ta fitowa. Amma ke yanzu ina yin magana da ke sosai, ina jin daWi"

Nana ta kwashe da dariya ta ce "Bagware idan ka yi magana dole sai mutum ya gane kai ba bahaushe ba ne ba"

Yayi dariya ya ce "Na fiki iya Hausa sosai, buzuwata saka kaya muje sayo abun karyawa1"

Cikin murna Nana ta ce "Yauwwa, dama ina son na fita na ga waje, tun da aka kawo ni ban taSa fita ba".

Dama ta yi wanka, ta saka hijjabi a kan kayanta, shi ma ya saka kaya, suka rufe Wakin su ka fita.

Sosai unguwar ta yi wa Nana kyau, duk da ruwan da ake yi, babu alama a unguwar saboda akwai wadatattun magudanan ruwa, ba kamar unguwarsu ba, da ruwa Waya sai unguwar ta shafe kwana uku ma?il da ruwa da azababben sauro.

Ya saka hannunsa ya ri?o na Nana, ta Waga kai ta kalle shi, ya kashe mata ido. Sosai abin ya ?ayatar da ita.

"Sayyid"

Ya kalle ta, yana jiran jin abin da za ta ce.

"Dan Allah ina son ka bani dama, na je gida na duba Baba, yana ciwon ?afa tun bayan biki ?anwata ma da suka zo, ba ta da lafiya. Kuma ka ga a al'adarmu yakamata mu je mu yi wa mutane bangajiya"

"Mene hakan?"

Ta yi murmushi ta ce "Mu yi musu sannu, saboda hidimar biki da suka yi, ka ga Shukura ma babu lafiya tana asibiti, maman yaron da nake raino"

"Tom"
Ayshacool
Nana ta ce "To yaushe za mu je?"

"Zan gaya miki"

"To na gode sosai mai rawani"

Gurin da yake zuwa sayen ?osai suka je, Nana ta yi mamaki ganin har a manyan motoci ake zuwa gurin sayen ?osai, da kunu gurin matar.

Nana ce ta yi wa mai ?osan magana ta gaishe ta.

Matar ta ce "Laa kece matarsa ko 'yar uwassa?"

Nana ta yi murmushi ba ta ce komai ba.

"Allah sarki, yana zuwa sayen ?osai ai, na nawa za a baku? Ki ce masa na ce kwana biyu bai zo sayen ?osai ba, ban iya maganar su ba"

Nana ta ce "Ai yana jin ki"

Matar ta ce "Haba dai? Ba kurma ba ne?"

Nana ta kwashe da dariya ta ce "Yana magana"

"To ai kullum ya zo kuWi yake bayarwa kawai, ko ya rubuta"

Ya yi mirsisi kamar ba a kan shi ake magana ba, ya ciro kuWi a aljihunsa ya bawa Nana.

Kamar Nana ta san matar, suka din ga hira, ta sallame su, suka nufi gida.

"Sayyid dan Allah ka din ga yi wa mutane magana, ko dan saboda yanayin rayuwa. Ka ga da yawa ana Wauka ko kai kurma ne" shiru ya yi mata, haryanzu ba ta gama fahimtar sa ba.

Ba ta damu da rashin bata amsar waccan maganar ba ta sake cewa "Yauwwa, dan Allah akwai gidaje a bayan gidan nan ne? Ina son sanin gidan Anty Haula, ina son na kai mata ziyara nima"

"Babu gidaje a baya"

"Amma ta ce mini gidanta a bayan inda muke yake"

Ya ce "Mu duba tare" ya biyo da ita ta bayan layin, wasu irin manyan gidaje ake yi, sai dai duk kangwaye ne, babu ma alamar wani gida da yake da mutane a gurin.

"Ina ga ban gane kwatancen ba, idan ta sake zuwa na tambaye ta. Amma sai na din ga jin hayaniya a bayan Wakin, kamar akwai mutane a gidan" kawai ya kalli Nana ba tare da ya ce mata uffan ba.

Ko da suka gama karyawa, ro?onsa ta yi tana son shiga cikin gidan, ta gaida Hajiyar. Ya ce? "A dawo lafiya, idan kuma da maza ki dawo" ta jinjina masa kai tana murmushi.

Yau ma a falon saman benen, ta iske Hajiyar gidan, tana waya a matu?ar fusace.

"Ni wallahi na gaji, idan ka dawo ka san yadda za ka yi da ita. Ni me ake yi wa Yusra a gidan nan, balle a ce depression ya kama ta? Ga anti depressants Win nan, mun je mun ga Likita an bata, amma ta ?i sha. Sai kuka, ba damar na yi mata magana ko nasiha ce sai ta hau kuka ta ?ule ta wuni a Waki"

Nana ba ta iya jin abin da ake faWa a cikin wayar, ta gama bambaminta, ta kashe wayar.

Nana ta gaisheta ta amsa, ta Wora da cewa "Yi ha?uri kin same ni ina waya ne"

Nana ta ce "Babu wani abu, bari na gyara falon"

Matar ta ce "Yauwwa dan Allah da kitchen ma"

Nana ta ce "To" ta fara gyara Wakin, tana cikin mopping ta fara jiyo wani sauti, da ta rasa sautin mene? ne, kamar ana buga wani abu. Ta basar ta ci gaba da aikinta amma sautin ya ci gaba da fitowa daga wata siriryar hanya.

"?aisar" ta furta a hankali. Kwana biyu hankalinta ya Wan fara kwanciya, amma ta fuskanci matsalolinta na ?o?arin sake dawowa.

Ta gama mopping Win falon, ta tafi kitchen Win, nan ma ta fara tattarewa kamar ba kitchen Win mata ba. Kaca-kaca ga tarkacen kwanuka wasu abinci duk ya bushe.

Ta haWa kwanukan a sink, ta fara wankewa.
A hankali ta ji sautin nan ya biyo ta har kitchen Win, ya ci gaba da nufo inda take, ba ta waiwaya ba, ta fara karanto addu'oin da suka sauwwa?a a bakin ta.
Aka jefo mata kofi a cikin sink Win, mai jefowar ta nufi hanyar barin kitchen Win. Tamkar an dasa Nana ta kasa motsi, sai da ?yar ta kalli ?asan rigar matar har ta fice.

A hankali Nana ta fara jin sanyi, gabanta ya fara faWuwa, hakan ya tabattar mata da akwai matsala. Kawai ta Wauraye hannunta ta bi bayan matar.

Tamkar ana hankaWata ta ?arasa ta buWe ?ofar Wakin. Wata farar mace ta gani a Wakin, a zaune fuskarta ta yi ja alamar ta yi kuka. Ta zubo wa Nana ido.

Nana ta taka a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login